Showing 186001 words to 189000 words out of 397328 words

Chapter 63 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70093

sa, fara'ar sa ga waɗanda yake yi wa, cin abincin shi da ma kula da kan shi duk suka ja baya.

Haka ya shirya jiki a saɓule cikin kyakyawar shiga sannan ya bar gidan bayan ya bar makullin shi a hannun mai kula da shi kamar yadda ya saba, asibiti ya dace ya nufa a lokacin, amma saboda wannan lamura da suke ta dagula masa lissafi sai ya ji kamar ma wani zazzaɓi zai rufe shi, sai kawai ya ɗauki hanyar gida dan ya san yanzu maman Jolie ba ta gidan bare ta dame shi da wata kissar ta, yaran kuwa da ya shige ta ƙofar falon shi ba ma zasu sn ya dawo ba bare su ma su takura shi. A hanyar sa ta zuwa gida ya kira asibiti ya tambayi ko Dr. Sunusi yana nan? Da aka tabbatar masa yana nan ya ce a faɗa masa ya shirya shiga tiyatar da shi ne zai yi wani izuri ya taso masa, dan shi a ganin shi ɓata ma lokaci ne ya wani kira shi ya tsaya faɗa masa ya shiga ɗin, sai ya ga hakan kamar neman alfarma yake bayan kuma shine yake musu alfarma tunda shi suke ma aiki.

Ko da ya tabbatar ya gama da maganar asibiti ya kashe wayar sa gaba ɗaya, tunda jiya da yamma an tabbatar masa da saukar kayan asibitin da ya tura China lafiya, to bai da matsala da kowa yanzu, dan haka ma yana zuwa gida ya aje wayar gefen da ba zai ganta ba daga saman gadon shi bare ya ji sha'awar kunna ta sannan ya shiga tunanin ta ya? Ta ina? Ya zai yi ya samu yarinyar nan Yusrah? Wacce take neman zame masa *ƙadangaren bakin tulu*.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
30/05/2024, 18:32 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍??🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*48*



Kamar jiya da waya ta dinga duba lokaci har ta sallaci sallar asuba, bata koma bacci ba face karatu da ta shiga taɓawa a Alƙur'anin da aunty Intisar ta saka mata a jakar ta gefe ɗaya irin ƙaramin nan masu ɗan gida mai haɗe da sallaya da carbi ƙarama, saida ƙarfe shida ta yi sannan ta miƙe ta shiga ta yi wanka sosai ta fito ta shafa duk abinda take shafawa sannan ta saka kaya.

Doguwar riga ce kalar bleue dark da kallabin ta, ba ta shafa komai ba hatta da kwalli ba bayan turare da ba ya hawa kai ko saurin shaida ka iso wajen, tana kammala shiryawa ta dai ɗora ɗan kwalin a kan ta ne amma bata ɗaure shi ba yadda zai tsaya, zaune ta yi bakin gado ta ɗauki wayar ta da har lokacin kiraye kirayen Intisar ne jibge har da na Yaya Mubarak ma da Bilal sai dai basu kai yawan na Intisar ɗin ba.

Connection ta buɗe, nan fa saƙonnin aunty Intisar suka dinga shigowa birjik, duk ba ta tsaya kula su ba ta fice zuwa lambar Yaya Mubarak da ta ji Intisar ɗin ta ce sam ba ya sauka a online ƙa'ida, saboda yanayin kasuwancin mahaifin su da suke kula da shi, da kuma jiran saƙo ta email ɗin shi akan wani aiki da ya nema yake kuma saka ran ganin gayyata a kowane lokaci, wanda ita kanta aunty Intisar ɗin babban burin ta kenan, ba wai tana son auwa U.S bane ta zauna, sai dai yaran ta dake hannun matar da ita gaskiya yadda ake kula da tarbiyar su bata mata ba ya sa take so ta je, da ya gama abinda ya kai shi a shekara uku ko biyar ko shida, wallahi komai zai faru sai dai ya faru amma da yaran ta za ta dawo ƙasar nan.

Yadda ta yi tsammani kuwa ta same shi a kai, nan ta danna wajen voice sannan ta fara magana cikin salama da nutsuwa sosai da ƙanƙar da kai da girmamawa gare su har da ƴar rawar muryar ta kamar za ta yi kuka, saida ta gama voice ɗin da ya ci minti ɗaya da arba'in da uku sannan ta tura ya je, daga haka ta ɗan leƙa saƙonnin Yaya Bilal shi ma, amma duk tarin su sallamar sa kaɗai ta amsa da tambayar sauka lafiya da ya mata, sai ta ɗora da rubuta _"Na gode da kulawa Yayana."_

Tana fita a lambar shi ta shiga ta aunty Fureira, duk da ta san da tazarar lokacin ita da su amma dai za ta ajiye saƙon, nan ta mata voice ita ma ta yi sallama ta gaishe ta sannan ta mata albishiri da ganin Safwan, har ta shaida mata ashe Yayan aunty Intisar ne ya *taimaki* Safwan? Yanzu haka suna tare an masa aiki tun jiya, su taya su addu'a ya farfaɗo lafiya a kuma ga anfanin aikin, saida ta tura voice ɗin ya je sannan ta ɗan yi shiru tana nanata kalmar *taimakon* nan da ta ambata, shik tana da tabbacin taimakon Safwan ya yi? Me ya sa ta ji ta kasa faɗawa aunty Fureira gaskiyar lamarin mutumin? Sai ta zaɓi ta ɓoye har da wani cewa shi ya taimaki Safwan? Taɓe baki ta yi tana ayyana _"Abun bai da wahala ai, tana tabbata ba taimakon shi ka yi ba ai ga waya, kuma aunty Fureira ma kaɗai tijarar ta ta ishe ka wallahi."_

Daga haka ta sauka gaba ɗaya ta miƙe dan saka wayar ta a jaka da abubuwan da ta san za ta iya buƙata, dan har pad aunty Intisar ta sako mata ta ce saboda kp ba lokacin al'adar ta bane yana iya zuwa mata saboda canjin yanayi da abinci da za ta riska anan, dan haka ta ce ta zama a jakar hannun ta kar ta yarda ta bar ta a wani wurin... Wayam aka ce mata ɗauki jakar inda kika ajiye, dafe ƙirji ta yi a tsorace sosai ta furta "Inna lillahi wa'inna..."

Sai kuma ta tuna jiya ashe ta baro su a ɗakin gardin can da ta masa allura, sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta juya da azamar ta dan nufa ɗakin kafin ya mata binciken masifa a jaka ko ya saka mata wani abun da za'a shiga kallon ta ana zunɗe da baki. Ba ta isa ga ƙofar ɗakin ta ba aka ƙwanƙwasa, sai da ta fara kallon agogo ta ga ƙarfe bakwai ce ta yi sannan ta sake duban ƙofar, tana zuwa saida ta ɗan ɗaga ƙafafuwanta ta leƙa ta wata ƙaramar huda da aka yi ta ga ma'aikaciyar wurin ce sannan ta tsaya kan ƙafafuwan ta tare da jawo ƙofar ta buɗe tana ɗan ƙaƙaro murmushi.

Gaishe ta ma'aikaciyar ta yi tana turo ma'ajin farantan abinci, Yusrah da mamaki ke kallon abun irin dai kamar wata matar gwamnan nan fa, ko wa yake biya ko zai biya? Waccen mutumin ko? Har ta gama ajiye mata su inda ya kamata ta tambaye ta ko da abinda take so ta ce a'a sannan ta fita tana rufe ɗakin ta juyo da niyyar ta ci abincin, amma kuma sai ta tuna jakunkunan ta masu mahimmanci, dan haka kawai ta fito daga ɗakin ta tunkari na shi.

Ma'aikacin dake kula da nashi ɗakin ta samu yana ta faman ƙwanƙwasawa amma shiru, ƙarasowa ta yi tana tambayar shi lafiya? Shine yake sanar da ita yanzu zuwan sa na uku kenan yana bubbugawa amma shiru, kuma a reception an tabbatar masa da bai fita ba, shine ya je ya sanar da babban su wataƙila ba lafiya aka bashi makullin, amma kuma dokar su bai kamata ya fara kutsawa ba yana sake bubbugawa ne ko za'a buɗe.

Da kulawa ta dube shi tace "Ina makullin?"

Nuna mata ya yi yace "Gashi." Karɓa ta yi ta shiga buɗewa kamar kati dai haka, tana ware ƙofar ɗakin suka hange shi kan gado duƙunƙune, daga kuma kwanciyar ta sa sannan rufe ruf cikin zani ya tabbatar musu ba ya jin daɗi ne, da hanzari ita da ma'aikacin suka shiga ɗakin, ma'aikacin ne ya ɗan buɗa zanin yana taɓa jikin shi da kiran sunan shi da yallaɓai amma idanun Aswan gam gam a rufe sai rawar sanyi yake yi. Da sauri ya kalli Yusrah da ke juyawa tana duba jakunkunan ta inda ta barsu yace "Madame, bari na je na kira likita ya zo ya duba shi."

Ya juya da niyyar tafiya tace masa "A'a dakata, zan duba shi da kaina, nima likita ce, tun jiya na fara duba shi."

Gyara tsayuwa ya yi yana kallo ta buɗe jakar da ta saka kayan magungunan ta, abun awon jini ta ɗauko ta buɗe shi a kwalin shi ta ciro ƴar allurar kamar reza sannan ta nufo gurin shi, durƙusawa ta yi gaban shi tare da kamo hannun shi na hagu ta riƙe kan yatsar sa, tana soka abun wannan ɗan zafi zafin ya sa AA dake cikin raɗaɗi ya ɗan ɗaga idanuwan shi da sukayi masa jajir suka kuma yi nauyi sosai ya dubi wacce ke gaban shi, lokaci ɗaya kuma ya maida su ya rufe saboda wahalar da yake ciki shi kaɗai zai iya misalta ta.

Yusrah kuma dake matse yatsar tashi jini ya ɗan ɓullo ta ɗasa jinin a wurin abun awon nan tana dubawa da kuma ayyanawa a ran ta _"A ido dai jikin ƙarfafa, amma taushi lutuf uwa ruɓaɓɓiyar ayaba, ni ma dake mace na fika juriyar wahala? Hmmmmm!"_

A sakanni abun awon ya nuna mata zazzaɓi ne kawai wataƙila na damuwar da ya saka a rai, dan haka ta ɗaga kai ta kalli ma'aikacin nan tace" Kar ka damu za ka iya tafiya, zazaaɓi ne kawai."

Jinjina mata kai ya yi yana ficewa daga ɗakin da yi masa fatan samun lafiyar, miƙewa ta yi tana yana kallabin abayar ta da kyau sannan ta shiga haɗa allurar da ta dace da shi, saida ta gama ta dawo gaban shi ta sake ranƙwafawa ta ja zanin har zuwa damtsen shi, waina idanu ta yi ganin har yanzu ba wata rigar arziki bace jikin shi, to mai ƙananan hannaye ce dai ya saka ya kwanta, haka dai kamar mai tsoron taɓa shi ta soka masa tsirin allurar, nan ma saida ya sake buɗa idanu ya kalle ta amma ya rufe, tana gama masa allurar ta daidaita komai ta fita daga ɗakin zuwa nata ta ɗauko abincin ta, dan ita kam yanzu da tasan tana tare da Safwan ba za ta yarda yunwa ta kwantar da haka ba ya tsere mata da ƙane, dan haka take ci duk da ba sabo a ciki ba kuma dan yana mata yadda take so ba.

Nan ɗakin nashi ta zo ta zauna ta shiga cin abincin tana kallon shi lokaci lokaci, tun tana ganin jikin nashi na rawa yana wani nishi nishin wahala har ta ga ya ɗan ragu, zuwa can ta ji babu numfashin nan da yake yi sannan ta ji sauyawar numfashin alamar kamar bacci ya ɗauke shi.

Saida ta gama tsaf da kamar minti sha biyar ta miƙe ta zo kusa da shi, a hankali ta ja zanin da niyyar taɓa goshin shi ta ji ya zafin yanzu, amma daga irin gumin da ta ga ya haɗa kamar wanda ya yi gudu ya tabbatar mata da zazzaɓin ya sauka, taɓe baki ta yi ta ɗan ƙara jan zanin zuwa ƙasan jikin shi haka dan ya rage zufar nan...

Amma sai ya zamana kamar ta daddaɓa shi, irin buɗa idanun nan ne ya yi na tar tar da son tabbatar ma kansa da gaske mutum ne tsaye a kan shi? Ko kuma mafarki ne yake yi? Yana ganin ta ya wani yi luuuuu da idanu sannan ya sake buɗewa dai a kan ta, saida ya ji gaban shi ya faɗi da tunanin me take masa kuma anan? Me take kusa da gadon shi? Me take nema a jikin sa da take taɓa shi wai? Kai fa shi ba ya son fitina, ban da neman shi da bala'i me ye na yin abu kamar me son farmakar sa? Ita bata san yadda yake nesan ta kan shi bane da mata? Shine take masa wannan abubuwan kamar mai shirya yadda za ta auna masa ciki...

Da sata irin ingarman muryar da ta gama jigatuwa yace "Ke, ke baki san yadda za ki taimakawa mutum bane ta hanyar kira masa likita idan ba shi da lafiya dan a duba shi? Ko burin ki shine na mutu dan ki ɗauke min yarona?"

Da mamaki irin na kai jama'a ɗin nan ta fara duban shi, amma sharri irin na AA sai ya ja zanin rufar dake jikin shi yana rufewa da shi ya dalla mata harara da cewa" Ke me ye kike kallona haka babu riga a jikina? Wai ke dole sai kin taɓani ne za ki ji daɗi, me yake damun ki ne wai?"

Sai kuma ya ja tsaki ya na tashi zaune yana sake kallon ta ganin ta tsare shi da idanu, shi ma tsareta ya yi da idon yace" Me ye?"

Girgiza kai ta yi ta taɓe baki tace" Abun arziƙi sam bai gaji su kare ba, ina ce ba dan na agaza maka ɗin bane har ka samu damar kallona kana faɗa min magana?"

A zafafe ta juya inda jakunkunan ta suke ta duƙa ta ɗauka ta riƙe ɗaya a hannu ɗaya kuma ta rataya a kafaɗa sannan ta juyo ta dube shi lokacin yana kallon inda yake jin zafi a hannun sa yace" Ba dai allura kika min ba yanzu ma?"

Da irin faɗa faɗan nan har tana murguɗa baki tace" E ɗin, da matsala ne."

Shi ma da sigar faɗa sosai yace" Ni ɗan ki ne da zaki zauna kina min allura? Ke ba'a gaya miki kira wa mutum babban likita bane dan ya duba shi? Ba fa na son haka, ki kiyayeni fa."

Yusrah kamar za ta haɗiye zuciya dan takaici tace" Ni fa asibiti nake son zuwa, ba zama ina sauraron wannan masifun naka ba, ka sa a kaini asibiti na ga ƙanena?"

Saida ya ɗan dafe kai cike d takaicin jin tana masa magana kamar mai bashi umarni, yaye zanin rufar ya yi gaba ɗaya ya sauke ƙafafun sa daga kan gadon ya tangale guiwar hannayen shi kan cinyar shi sannan ya kalle ta, sosai yanayin shi ya bata tsoro har ta kawar da kan ta dan ba ƙaramin haɗe fuska ya yi ba sannan yace "Ni ba sa'an ki bane da zaki bani umarni, infact, kar ki sake min magana irin haka, sannan yau ba zaki je asibitin ba."

Tsakanin shi da Allah ya gama yarda ya tsorata ta ba kuma za ta sake yi masa rashin kunya ba saboda yadda ya ga tana tsilli tsilli da idanu, amma dake *wata tafiyar* jarabawa ce ga ɗan adam sai kawai Yusrah da ta ji zafin wai ba za ta je asibiti ba ta kalle shi da mamaki sannan ta masa shashashar tambaya wai _"Ba zan je ba? Saboda me? Ƙanena ne fa?"_

Dan haka ya sake kausasa mata sosai yace" Ba zaki je ba, haka na faɗa, idan kin isa kuma ki je ga hanyar nan kiga yadda zamu kwashe."

Saida ta sauke numfashi tana saita nutsuwar ta da haɗiye ɓacin ran ta sannan buɗa jakar maganin nan ta jawo wani kwalin magani guda huɗu ne a jikin shi kuma babban magani ne duk yana cikin siyayyar da Yaya Mubarak ya mata, takowa ta yi irin a hassalen nan ta aje maganin kan gadon gefen hagun shi ta kalli tsabar idanun shi da irin ita fa ya gama ɓata mata rai ɗin nan tace "Ka tabbatar ka ci abinci idan aka kawo maka, sannan ka sha wannan guda biyu yanzu, da yamma ka sha biyun, idan ka sake kwanciya ba lafiya ba zan duba ka ba, sai dai a kira babban likita ya duba ka, wannan umarni ne matsayina na *likitar ka*."

Tana gama faɗin haka ta juya a fusace ta fice daga ɗakin ta shiga nata tana aje jakunkunan zuciyar ta sai tafasa take yi da takaicin halin mutumin da baka da wani haɗi da shi ya nemi saka maka hawan jini ba gaira ba dalili.

AA kuma ya ɗan jima zaune inda ta bar shi yana ayyana _"Kenan dai ba za ta ji tsoron sa ba ko? Kenan dai aljanun ta basa ƙaunar shi ko? Kenan dai tana so sai ya nuna mata shi ruwan tulu ma kawai zai sha ya kirta mata ba daɗin da sai aljanun ta sun fita ta hanci bata ankara ba?"_

Ƙwafa ya yi ya tashi ya shiga wanka tunda da sassafe ne yana cillawa maganin da ta aje harara da furta" Ba za'a sha ɗin ba, mahaukaciya kawai, a haife ki tare da twins har ki nuna min kin yi karatun likitar da zan iya yarda da maganin ki? Hauka aka ce miki nake yi."

Yana wanka ya ji room service na buga ƙofa amma ya share sai da ya gama a tsanake ya fito ɗaure da towel ya buɗe, abinci ne aka shigo masa da shi ya aje yana tambayar sa ko da abinda yake so


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login