Showing 213001 words to 216000 words out of 397328 words

Chapter 72 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70080

d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*54*




Da mamaki tace" Ni ɗin ce ƴar ka?" Ta faɗa tana nuna kan ta.

Taɓe baki ya yi ya dube ta a shashaƙai yace "Ke ɗin, ɗiyar ƙannan ka ai ƴar ka ce, ke da Safwan dukan ku ƴaƴana ne."

Juyawa ya sake yi ya ci gaba da tura kujerar Safwan, ba ta matsa daga inda take ba ta bi shi da kallo tace "Waɗannan mutanen sun min halaccin da ba zan iya zuba idanu ina kallon su a damuwa ba, suna son juna su, kuma matsala ba daga dukkan su bane, ba zai yiwu na bari ka hukunta su akan laifin da ba nasu ba, zan raka aunty Intisar ta koma gidan ta, idan ya so ka kasheni ban da damuwa, amma dai zan yi farin cikin na taimaki mai halin girma..."

*Maganganu* da Anna ke ji sama sama ya sa ta ɗan nufo corridorn, tana leƙowa ta gan su tsaye daidai da Yusrah ta gama faɗin haka ta kama hanya za ta wuce har ta bi ta gaban shi ta sake kallon shi da ɓacin rai sosai" Kuma ni ba ƴar ka bace haka ma Safwan, fin ƙarfi kawai ka nuna min ka ƙwace shi, sannan aunty Intisar za ta koma gidan mijin ta, kuma wallahi ka rage masifar nan dan zai tsofar da kai da wuri, a yi mutum ba'a magana da shi ba'a samu matsala ba, haba."

A fusace ta kama hanya za ta wuce ɗakin su, Anna dake kallo da saurare mutuwar tsaye ta yi ta kasa motsawa, ba dan AA da ya bi Yusrah da kallo yana haɗe wahalallun yawu ba na rashin sanin madafar da zai kama da zai dinga maganin yarinyar, kan ta tsaye take faɗa masa magana kuma ya kasa ɗaukar mataki akan ta, bai san me ya sa ba? Saboda me? Ko a filin daga ya manta rabon da ya yi faɗan da aka taɓa lafiyar jikin sa, amma Yusrah ta haure shi da ƙafa a cikin shi tare da gantsara masa ciwo, tun ƙuruciya har yarinta ba wanda ya taɓa cin kwalar shi, amma Yusrah ta ci kwalar rigar shi ta faffaɗa masa maganganu, amma har yanzu tana raye, kuma tana takawa da duka gaɓɓan jikin ta, *me ya sa*???

Yadda ya raunana murya yace "Y. Turaki." Shi ya saka Anna farfaɗowa da shirin kai wa Yusrah ɗauki, dan tunanin ta ya bata zai lahanta ƴar mutane da tafi ɗaya tak, amma...amma...amma sai ta ga bijimin ɗan ta ya wani karkata kai suna kallon juna murya a tausashe yace "Ke ba zaki gane me ya sa nace ta zauna ba, maman ki tana da zurfin cikin da ba zaki iya gane me take so ko me ye bta so ba, ina tabbatar miki akwai abinda yarinyar nan take ɓoyewa, ina ji a jikina akwai abin da ake mata a gidan nan wanda ko zaki shekara da ita ba zaki gane ba kuma ba zata faɗa miki ba, ina so ne na gano matsalar sannan na magance ta kafin ta koma, amma ban da niyyar hanata komawa gidan mijin ta na dogon lokaci, please, ki yi ƙoƙarin fahimtata mana."

Wani luuuu ta yi da idanu tare da Anna da basu san tana kallon su, sai kawai ta turo mishi bakin nan tana kawar da kai saboda Safwan da ya juyo yana kallon su duk da bai cika fahimtar maganar tasu ba tace" Na gane, amma dan Allah kar ka sa suyi ta zubar da hawaye, ni ba zan ji daɗin haka ba."

Sai kuma ta shiga tura Safwan tana cewa" Bari na shirya shi da sauri kar mu makara."

Da sauri Anna ta ɓace daga gurin tana mamakin wannan abu har riƙe haɓa take, to ita lafiyar Yusrah ce ma ke bata mamaki, a ce ta iya tafiyar da Aswan haka? Wanda Aba ke ta ƙunbiya ƙunbiyar sanar da shi maganar Nabihat, da fa ya ce da ya zo sai sanar da shi, amma ɗazu ya ce a bar shi har da safiyar gobe ya ƙara hutawa wai.

A tsanake ta gama shiryawa da Safwan ta fito ta samu aunty Intisar ta mata sallama haka ma ta sanar da Anna sun tafi sannan suka fito tana turo Safwan, Anna da kallo ta bi bayan ta sannan ta yi murmushi tana girgiza kai, har lokacin motar uncle Hamat na gidan, sai AA da ta hanga cikin mota zaune amma ƙafar sa ɗaya waje, tun kafin ta isa ya fito ya kama Safwan ya ɗauke shi ya saka a bayan motar sannan ya naɗe kujerar tashi ya saka a boot sannan ya shiga shi ma.

Suna tafe Yusrah na duba saƙon Manal dake faɗan _"Ba dai kika tafi kika barmu ba, saboda kar ki ɓatawa Akhi rai? Ba damuwa mu ma gamu nan zuwa, kuma ku aje mana duk abinda kuka ci?"_

Dariya ta yi sosai da ta fito da haƙoran ta har sauti na fitowa, jin kamar idanun shi a kan ta ya sa ta haɗe dariyar sannan ta shiga maidawa Manal cewa _" Wato a hanya ma wani abu ake ci? Na taho ne saboda dole sai ina wajen kafin Dr. ya fara taɓa Safwan, ai kinga tarin filles ɗin sa da na taho da su."_

" Hmmmmm!" Ya faɗa yana taɓe baki da ɗauke kai, haushi haushi ke shirin kama shi, dan ya dakatar da hakan ba tare da ya kalle ta ba a harshen faransanci yace" Ki aje wayar nan har mu sauka, bana so ɗana ya zargi wani abu fa."

Kallon shi Yusrah ta yi, sai kawai ta gano wani abu ɗaya, wato in dai ita da shi ba zai taɓa bari ta zauna lafiya ba? Da mamakin hakan ta maida mishi da faransancin ita ma tace" Saboda me? Ba fa nice nake tuƙi ba."

A ɗan kausashe yace" Hakan ya raba min hankalina biyu ne, ki aje kawai nace."

Sai kuma ya ja ƙwafa mai ƙarfin gaske, rasa yadda za ta yi da shi ta yi, idan ta bari ɗin fa ta bi yadda yake so ne, to kuma shi a wa? Dan kawai tana raga masa saboda aunty Intisar da kuma ƙanen ta da ta kasa yarda ma ɗari bisa ɗari son shi yake? Sai ya nemi ya taka ta haka? Gaskiya ba zai yiwu ba, gyara zaman ta tayi tana ci gaba da danna wayar ta tace "Idan hakan na damunka ka tsaya sai na sauka na koma baya."

"Saboda yaron ki ne ni? Ko kuma dreban da aka waɗancen yaran suka ɗaukar miki?" Ya faɗa a zafafe sosai.

Da mamaki baki buɗe ta kalle shi tace "Wane yara kuma?"

Banza ya mata ya ci gaba da tuƙi, dan haka sai ta ci gaba da latsa wayar ta tana magana da Manal, vibration wayar shi ta yi ya ɗauka yana duba sunan ya ɗaga, shiru ya yi alamar yana saurare kafin ya ɗaga murya da tsawa tsawa yace "Aikin banza, ni nace maka a bashi komai da yake da buƙata amma ban da waya, kan ka ɗaya kuwa? Idan ka bashi waya uwar wa zai kira? Abinci sau uku a wuni, kai idan ma zai iya ci sau ashirin ko hamsin ka bashi tunda akwai, amma ko rana ban yarda yana gani kowane lokaci ba, idan kuma ka kuskura ka bashi waya, wallahi ba za ka yi shekarar nan a garin nan ba."

Yana gama faɗa ya kashe wayar ya aje yana jan wawan tsaki, har ya ɗaga kan shi da niyyar ci gaba da tuƙin shi kawai ya ga kamar tana kallon shi, gaba ɗaya ya kalle ta sai ya ga kuma shi take kallo irin ko mamaki ne yake bata ko me? Harara ya cilla mata ita kuma ta yi gaggawar cabketa tare da mayar masa da taɓe baki tana girgiza.

Madubin gaban shi ya gyara ya hangi Safwan, sai ya ga hankalin shi na kan tab ɗin shi yana ta game, dan haka ya kalle ta ƙasa ƙasa yace "Me ye kika ƙura min idanu? Ban dai yi kwantan da zaki haɗani da tarkacen ki ba, Y. Turaki ki rasa su wa za ki kula sai su kawu da su Baba da su mc masu saka rabin wando a ƙugu, hmmmm!"

Zuba masa idanu ta fara yi, sai kuma ta kalli gaban ta tace "Na rantse da Allah da Dr. zai nuna min allurar da ana wa mutum bakin shi zai liƙe ko? Tsaf zan danna maka ita sai dai aunty Intisar ta yafe min, haba mana dan Allah, tunda sanyin safiya kake sakani magana alhalin hakan ba halina bane."

Sai kuma ta jinjina kai irin haba ɗin nan tace" Kuma ni samarina ba tarkace bane, wallahi duk nutsatsu ne, amma ka daina haɗani da wannan tsohon, bana so na faɗi abinda ba zai maka daɗi ba."

Ita ta yi maganar surutu bai dame ta ba, shi ya afka a tunanin shin me yake damunsa ne? Ya salam, me yake damunsa ne? Idan yana tare da yarinyar nan surutun da yake yi shi da kansa sai ya jima abin ke faɗo masa har zabura yake yi da mamakin hakan, menene hakan yake nufi? Lallai yarinyar nan ita har ta san bata da surutu ko? Yarinya bata san nine ban san surutu ba sai a kanta? Duk ta bi ta fitine ni tana neman koya min masifa.

Ita ma shirun ta yi tana duba bakin hanya, maganar su da aunty Furera take ta tunawa, irin yadda aunty Furera ke saka masa albarka, ko dan ta ɓoye mata ainihin waye shi? Yanzu haka ta ce wai gatanan kwana kusa sai da ƙyar ta rarrasheta kan ta yi haƙuri idan ya warke sumul sai ta zo, tana tausayawa auntynta sosai, tana fatan ta samu albashinta na farko dan ta yiwa auntyn abinda ko da ta baro gidan ta zo na ɗan lokaci ba zai saka ƴaƴan a damuwa ba, yau ɗin nan a ko ina ne, kuma ita ta san aunty Furera bata da shi, tana da wadatar zuci ne kawai.

"Tell me, menene haɗin ki da uncle please?" Ya faɗa a hankali bayan ya murza sitiyarin motar ya sha kwanar da zata sada shi da asibitin direct.

Idanuwanta ta rintse tsohon mikin dake can cikin ranta na abinda bawan Allahn nan ya yi mata na taso mata, haka kawai ta ga bikin zuwa sai dai rashin zanin ɗaurawa zai hana mata zuwa, haka kawai ta saka a ranta ta san cewa idan zata faɗa masa damuwarta yana iya yin tsaye ya rama mata, sai dai tunanin cewa uncle fa uba yake a wajensa ya saka ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Babu komai tsakanina da shi."

"Y. Turaki?" Ya faɗa yana ɗan kallon ta, Yusrah ta lashe leɓenta a hankali ta ce" Believe me."

Kansa ya ɗauke ya yi shiru suna daf da shiga asibitin ya ce" To menene dalilin da yasa kika bar asibitin sa rana tsaka? Bayan ko da kina stagiaire a can albashin ki ya fi na wanda ake baki a nan?"

Idanuwanta ta ɗauke daga gefen sajen fuskarsa bayan ta yankewa kanta hukuncin ba fa zata iya faɗa masa ba ta ce" Ba komai fa, kawai shan ruwana ne ya ƙare a can ɗin."

Yanayin da ta yi maganar shi ya san da ƙaryar banza da wofi ne yarinyar nan ta masa, amma kuma ya ƙyaleta ya ƙi ce mata komai, abu ɗaya ya sani shine dole zai samu kusanci da ita, dan yana matuƙar son wannan information ɗin, ɗaya ne daga cikin abinda zai haɗa kafin ya watsa abinda ke cikin takardunsa.

Bai kuma ce mata komai ba har suka gangara suka shige asibitin, motar su na shigowa kai tsaye wajen parking suka wuce, da mamakin ganin Mukhtar wai har ya riga shi ya sauko yana sauke Safwan ma kafin barista Mukhtar ya ƙaraso suna gaisawa, dueƙusawa ya yi ya ba Safwan hannu suka gaisa yana tambayar shi jiki, Yusrah ma da ladabi ta gaishe shi ya amsa sannan ta karɓi tura Safwan ɗin a hannun shi ita tana gaba su suna baya suna ɗan taɓa hira akan jikin Safwan ɗin.

A ƙofar office ɗin Dr. Siddik AA ya ba wa Mukhtar haƙuri ya ce su zasu shiga dan miƙa Safwan, amsa mishi ya yi da ba komai sannan suka shiga ciki tare da Yusrah. Barista Mukhtar kuma yana nan tsaye tsawon mintuna har ya fara ɗan kai da kawowa yana danna wayar sa sai ga su Manal da su Anna da suka ce za su zo dan su ji ya za'a ƙare da jikin Safwan ɗin.

*Dammmm*! Gaban shi ya faɗi a sanyaye, take zuciyar shi ya ji tana wata irin sabuwar harbawa, ya ji wani lamari ya ziyarce shi da bai taɓa jin shi akan kowa ba sai yanzu daga ganin nutsatsiya kuma sanyayyar fuskar sanyin *Abrar* dake tafe tare da su Nawal kamar hawainiya tana sakin tattausan murmushin da ya dace da kamanin ta da farar fatar ta.

Barista Mukhtar ɗin ne ya fara gane su Aba da Anna, dan haka ko da ya musu magana yana gaishe su da girmamawa sai Aba ya ɗauki muryar shi tunda basu taɓa haɗuwa fuska da fuska ba suna dai waya, nan ya sanar da su suna ciki wajen Dr. ɗin, suna maganar kuma sai gasu sun fito Yusrah na tura kujerar Dr. Siddik na biye da ita AA a baya, nan Dr. ya dakatar da su dan zasu shiga da Safwan wani ɗaki ya ɗora aikin daga inda aka tsaya na aikin da aka fara.

Da ya tabbatar musu za su dawo da shi ɗakin da aka kwantar da shi babu kowa a ciki, nan su Manal da Abrar da ta fara tsarguwa da kallon barista Mukhtar suka nufi ɗakin suna ihun zasu jira har su fito, barista Mukhtar kuma shi wallahi da yana kallon fuskar ta wata luwai luwai da ita haka, sai wani gashi a mummurɗe dake gaban goshin ta da wajen kunne kamar saje mai silɓi sosai dake nuni da kanta ba dai gashi ba, sai ya ji kamar kar ya daina kallon ta. Ai bai tsaya ɓata lokaci ba ya rufa musu baya da yaji Aba ya ce wa Anna "To mu ma ko zamu tafi mu duba jikin Alhajin ne mu dawo sai na aje ki anan, Sk na jiran mu a waje."

Da gamsuwa Anna ta amsa da "Ba damuwa, muje ɗin kawai."

Sai anjima suka ma yaran da AA da ya juya dan raka su yana waiwayen barista da ya fara lura da kallon da yake wa Abrar yana ayyana _'Shi kuma ko me ye haka uwa maye? Ni fa bana son jaraba wallahi ka zo ka ja min raini a idanun yara.'_

Amma dai sai ya bi su Aba da niyyar bari ya dawo idan ya ga ya ci gaba da kallon ta ya wanwanka masa mari ko ya dawo hayyacin sa, yo ina dalili?

Zaune ya tarar da su barista Mukhtar inda ya zauna yana fuskantar Abrar ne, kallon ta yake yi sai idan tana shirin kallon wajen shi ne sai ya yi gaggawar ɗauke kai. Surutun da suke yi kafin shigowar sa ne suka ɗauke sai ƙus ƙus, haka suka ci gaba da jira har sanda Yusrah ta shigo ta sanar da su ga Safwan ɗin nan, wani ma'aikaci daban ne ya shigo da shi akan kujerar shi, nan su Manal suka tashi daga kan gadon aka kwantar da Safwan sannan ma'aikacin ya fita bayan ya tabbatar musu ga Dr nan zuwa yanzu.

Saida Dr. Siddik ya shigo suka gaisa da barista Mukhtar sannan ya shiga yi wa Safwan abinda ya dace da yi masa allurar bacci sannan ya shiga faɗawa mahaifin Safwan ɗin bayani kamar haka "Ma sha Allah, Elhaj aiki fa ya yi kyau sosai, yanzu abinda ya rage shine zaku bar mana Safwan a nan, saboda aikin shi ba ya son yawan cakwalkwala, gashi kuma sister Yusrah ba za ta iya kula da shi ita kaɗai ba a gida, to ma fi a'ala a bar shi anan ina ga zai fi, tunda za'a dinga duba ciwon a kai a kai sannan da yi masa alluran sa akan lokaci, ina fata ba wata matsala da hakan?"

Iska ya feso daga bakin shi cike da rashin jin daɗi ya kalle shi yace" Dr. yanzu dole sai my boy ya sake yin nesa da ni? Ba zai yiwu a bamu likita ni ko nawa ne sai na dinga biya yana duba shi a gida? Bana son zama ba tare da shi ba ne."

Yusrah ita tasan zaman shi a aasibiti zai fi, ko me za'a ba likita ya je dan duba shi a gida akwai kayan aikin da ba za'a iya ɗaukar su aki gida na, dan haka ta karɓe da cewa" Amma fa hakan shine daidai, ni ban ga wata matsala ba anan, zai fi samun kulawa a asibiti fiye da gida, a gida sai likita ya zo sannan zai duba shi, sannan akwai abinda zai bayar da wahala wajen ɗaukar sa zuwa gida."

Kallon ta ya yi da wata harara harara yace" Ɗana ne fa."

Ɗauke kai ta yi ta furta" Sannu." Tare da ficewa ma ta bar musu ɗakin, dan haka su Manal ma suka miƙe suna ma Safwan Allah ƙara sauƙi suka fita, ganin haka ma sai barista Mukhtar ya miƙe da sauri yana kiran Nawal da" Ƙanwata, ƙanwata."

Dakatawa ta yi ta amsa da" Na'am Yaya."

Da irin kunya kunya yace" Ƙanwata idan ba damuwa me zai hana ki bani lambar...waccen ƴar uwar taki?"

Juyawa ta yi ta kalli ƴan matan uku sannan ta kalle shi tace" Gasu nan dai su uku tubarkallah, wace a ciki Yayana?"

Saida ya ɗan sunkuyar da kai yace" Mai jar abayar."

Dariya ta yi tace" Au! Wai Abrar? Ba damuwa Yayana kawo na saka maka."

Miƙo mata wayar ya yi ta saka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login