Showing 1 words to 3000 words out of 403653 words

Chapter 1 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

8

Bismillarrahmanin Rahim.......✍️🔥🕊️


BLACK WORLD🔥😥




Dik da tsananin tsoron da take a cikin ranta hakan bai hanata ɗago kai ta fara kallonsa tun daga kan Lion chest ɗinsa har izuwa kan his beautiful full neck attention grabber ba.

Da kyar take iya motsa idanun nata amma ta dage sai ta kalli face ɗinsa kusa da kusa domin ta tabbatar da mutun ne ko ba mutun ba, because she had never seen a beauty like him.

Ta ɗauki a kallah 1 mins tana kallon zanen tattoo na Black Tiger dake saman lion chest ɗinsa, zanen ya fita sosai, ga bakar damusar ta wage baki, waɗan nan garma garman hakwaran nata masu tada hankalin ɗan adam sun zanu da kyau, sai da ta ji mummunar faɗuwar gaba na ganin hakwaran damusar.

A lokacin da ta sauke kallonta a kan heart-s romance pink lips ɗinsa sai da ta dakata cak tare da kura masu idanu tana yi masu kallon ƙurillah, ko makiyi ya gansu yasan sun kawatu sun kuma haɗu sun kai a mutu a kansu, sai wani irin shining suke yi kamar ya saka lips balm, kai kyansu ya wuci tunaninku. Ba shakka Allah ya yi halitta a nan sai dai muce Masha Allah, .

Tsabar karfin hali irin nata da kyar ta iya hakura da kallon laɓɓan nasa amma sai da ta yi gaba da idanunta izuwa saman romance nose ɗinsa da yake dogo bai zut ba, ɗan dai'dai haka gwanin birgewa, haƙiƙa skin ɗinsa ya kai a shagala da kallonsa, wannan ya babbata da gaske bai taɓa fita rana ba, ya tabbata dai tun yana karami ɓoyesa ɗin ake yi, ni sai yanzu ma na gane dalilin ɓoyesa da babansa yake yi, ashe kyansa ne ya yi yawa da zai iya ja surutun jama'a a kansa da kuma hankulan mutane, in ya fito zai hana dikkan matan da zasu ɗaura idanu a kansa yin wani aiki ya hana zuƙatansu nutsuwa, shiyasa babansa ya ɓoyesa na tsawon shekaru, amma fa a nawa tunanin ni princess Teema ato bamu san dalilin baban nasa ba, abin da muka sani dai komai da dalilin yinsa, da alama nasu dalilin ma mai karfin gaske ne.

Bin wasu kyawawan black curly sajen dake gefen kumatunsa da kallo ta yi. Ya ilahi sai ji ta yi kamar ta kai hannu ta shafa ko tsoro babu, suna kwance luf a saman skin ɗin nasa mai kama da madubi saboda kyalli. Ya ji hutu malam.

Dik kare mashi kallon ƙurillah da take yi yana tsaye yana cigaba da abin da yake yi tamkar bai san da wata halitta a wajen ba, kamar ba shi ne ya jawota gabansa with his magic ba.

Cak ya tsaya daga creating wannan haske da yake ƙoƙarin yi a lokacin da ya ga sauƙar idanunta a cikin kwayar nasa. Bai taɓa tunanin tana da zarrar iya sanya kwayar idanunta a cikin nasa ba, dan a cewarsa zaratan maza masu rai da lafiya ma ba zasu iya ganin face ɗinsa ba bare kwayar idanunsa, sai ga shi ita kuma ta mace ma da kallon idanun nasa, kyansu sun ruɗeta da har ta manta in da take ta kafesu da kallo babu ko kyaftawa.

Haƙiƙa hakan ya girgiza shi kaɗan, dole ya dakata da abin da yake yi domin ya dawo da kallonsa a kanta ya ga zata iya su kalli juna ido cikin ido ne? Idan har ta iya ganinsa ido cikin ido bata kawar da kallonta ba to ya zama dole ya kasheta, domin ta cika ƴar baiwa. Babansa ya bashi labarin tabbas dik wadda zata iya kallonsa ido cikin ido in ma mace ko namiji to ya sani tana da baiwar irin nasa, idan ma ya yi wasa zata iya bugesa, kuma kada ya yarda ya zauna inuwa guda da wanda zai ga cikin kwayar idanunsa babu tsoro, idan ya yi hakan tabbas ayyukansa ne zaku koma baya........ Tashin sense.

Ita kuwa ya subhanallah, sexy romance eyes ɗin nasa ta kafe da kallo ko tsoro hakan bata ji ba, ita dai taga abu mai kyau ya tafi da imaninta, idan ka kalli idanun nasa a fisge sai ka yi zaton design of fish ne saboda girmansu, amma ba haka bane, romance-s-eyes ne, ga shi shikuma ba ɗan soyayya bane, amma wlh yanayin idanunsa irin na riƙaƙƙun ƴan love ɗin nan, ga shi baya buɗesu dikka, suna ɗan lumshe. Kaifafa dasu tamkar eagle eyes.

Idan ya kalleka da su kaifinsu da gwarjinin dake cikinsu sai ya razanaka yasa ka ji faɗuwar gaba.

A hankali ya juyosu a kanta, suka ga juna ido cikin ido kuma kusa da kusa. Wlh yarinyar nan ko gezau bata motsa ba, kai ko kyafta idanun nata ma bata yi ba, sai ma ɗan kara warosu waje da ta yi na mamakin kallon cikin nata da ya yi.

Ya ɗan ji a jikinsa, ya kuma fara yarda da cewa tana da baiwa irin nasa, domin kuwa ita ma idanunta kaifafa ne sosai, idan baku manta ba Kamran baya iya ganin cikin kwayar idanunsu, shin kun tuna hakan? To ba Kamran kawai ba, dik wanda zai ga Sweetie ko Pretty idan ba mai dakakkiyar zuciya ba babu wanda zai iya jure ganin kwayar nasu gaskiya....... DA ALAMA SUNA DA WATA ƁOYAYYAR BAIWA DA GASKE NE, TO WACE IRIYAR BAIWA KENAN? MU JE ZUWA.

Tsabar ta shahara ma har da fara ƙoƙarin motsa hannunta domin ta taɓa face ɗinsa ta kara tabbatarwa mutum ne ko aljani. Sai dai kash bayan idanun nata babu wani abin da yake iya motsawa a jikinta, ya daskarar mata da komai, da zata taɓa shi ta ji karshen rashin tsoro kenan.

Kai gaskiya Sweetie akwai karfin hali, innalilahi ni narasa ma a wani point zan ajiyeta, tab kai abin da mamaki gaskiya.

Sakin wannan madubin hannun nasa ya yi ta yi kasa kamar zata faɗi, sai kuma ta tsaya a saman iska bata kai kasa ba, amfani ya yi da scepter ɗinsa ya yi magic kafin kyaftawa da Bismillah ta ɓace daga gabansa ta manne da wall na ɗakin ta ɓangaren hagu.

Dik da haka bata tsorata ba, hasalima bata kawar da kallonta daga kansa ba, shi kuwa tuni ya zare idanunsa zaga cikin nata.

Da kyar ta kai kallonta a kan swan sofa chair dake shirye ta wajen wall glass dressing room dake cikin ɗakin, waɗan nan swan design chiar ɗin sun haɗu matuƙa ga shi sun ji dollof mai laushi da tsantsar kyau da tsada.

Komai na cikin bedroom ɗin nan white, gold and milk color ne, sai kuma jikin furniture da aka tsantsarawa kwalliya da zallar madarar gold. My people's Allah ya yi arziki ta yi mubaya'a a wannan empire ɗin, headboard na gadan Black Tiger duniya ce guda, wall headboard ce, wato kayin gadon manne take da jikin bango, a haka aka yita wanda tsawonta ya kai har tana taɓa saman ɗakin, sannan aka bi gefe gefenta da wasu kwayayen fitillu masu bada sky blue ligh mai matuƙar ɗaukar hankali, yanayin yadda aka tsara wall headboard ɗin nan sai mutun ya kwana ya wuni yana kallo ba tare da ya sani ba, saboda haɗuwarsu.

Dik wata flowers da kwalliya dake jikin wannan wall headboard ɗin da ɗanyar gold aka yi ta wanda nasan kun san da hakan, design of butterfly ce head na bed ɗin, dai'dai tsakiyar butterfly ɗin gold ce haɗe da wani kwai mai bada haske white light, sai ya haskaka gold ɗin tana wani irin kyalli mai jan hankalin wanda ko baka yi niyar kallon gadon ba baza san lokacin da idanunka zasu kai wajen ba saboda wannan kyalli na gold ɗin.

Ita kanta Sweetie bata san lokacin da ta kai kallonta saman bed ɗin tana jinjinawa girman gadon da kuma haɗuwarsa, kamar ba'a duniya ba, kamar kuma ba za'a mutu ba, shifiɗun alfarma dake saman bed ɗin kawai ya isa sanya mutun ya ji ya ƙoshi da komai saboda haɗuwarsu.

Shi kuwa sarkin azzalumai wato King Black Tiger, baiwar Allah tana can yana kalle kalle shi kuma yana sihirinsa dan ya kasheta.

Tsakar ɗakin nasa ya nuna da scepter ɗinsa, hakan yasa nan take wajen ta zurma tamkar rami mai zurfin gaske, magic eyes ɗinsa ya juya nan take wasu irin kifiyoyi masu kaifi da tsinin gaske suka bayyana cike a cikin ramin har baki, kasan kifiyoyin wuta ce take ci mai tsananin azabtar da har in da suke suna jin hucinta

Wasu irin bakaken kunamu masu duhun jiki sosai manya manya da su ne suka sake bayyana a saman kan tsinin kifiyoyin nan, sai wasu snake da suka bayyana a jikin kifiyoyin sun fasa kai da baki, kiris suke jira su fara kai sara.

Har lokacin idanunta a kansa, da alama bata firgita ba.

Da scepter ɗinsa ya yi amfani ya janyota izuwa gaban wannan rami ta hanyar amfani da magic ɗin nasa. Sai a lokacin ta kawar da kallonta izuwa kan ramin dake gabanta.

Wani irin tsorata ta yi na ganin zabga zabagn kunamun dake yawo a cikin ramin, abin mamaki kuma wutar dake ci kasan ramin baya taɓa dabbobin, babban abin da ya ɗaga hankalinta ma shi ne waɗan nan macizai da suka fasa kai suke jiran kiris su kai sara, wannan wani irin zalinci ne? Da me bawa zai ji idan aka jefashi cikin wannan rami? Shin da wutar dake ci a kasa zai ji ko dai da waɗan nan shegun baƙaƙen kunamu da bakaken kumurcin macizan? Ko da kifiyoyin dake tsaitsaye masu kaifin bala'in, hakika kuma ta wannan hanya Black Tiger ya fi yawan kashe dik wanda ya taɓa ganin face ɗinsa, cikin wannan rami yake jefa mutun hakan yasa ko gawar mutun ba'a sake gani, shiyasa tin farko nace maku dik wanda ya shiga cikin wannan part ɗin nasa ba'a sake jin ɗuriyarsa, ya tafi kenan, to ga hanya ta farko da azzalumi Black Tiger yake bi domin ɓatar da su.

Mahaukacin razana ta yi, nan take zuciyarta ya fara duka tara tara! Idanu ta zaro tana kallon cikin ramin tamkar kwayar idanun zasu faɗo ƙasa, jikinta dik a daskare ba damar ta yi motsi ma bare har ta ce zata gudu, yadda zuciyar tata take bugawa tamkar ta fasa kirjinta ta fito waje.

Kwata kwata kallonsa baya a kanta, amma yana iya sarrafata, haka zalika bai motsa daga in da yake tsaye ba, ga mirrorn da yake creating haske da shi a sage a saman iska.

A hankali ya saitata da scepter ba tare da ya kalleta ba, baya baya gangar jikinta ta fara yi yana nufar cikin wannan rami. Ihu take son yi amma babu dama, dan babu wani abin da yake iya motsawa a tattare da ita face idanu, ya datse mata bakinta baiwar Allah ba halin yin kuka sai dai azaba ya kasheta.

Saura kaɗan ta ƙarisa afkawa cikin rami azaban zafin wutar har ya fara ɗuma fata izuwa tsokar jikinta, sai raɗaɗi take ji.

Dai'dai wannan lokacin Ronnie da ya fito daga cinema dake part na yayan nasa ya turo kofar ya shigo, abin mamaki kuma yayan nasa ya rufe kofar fa, amma yana zuwa ya buɗeta, dik yadda aka yi dama yasan yadda ake buɗe kofar ta koma wacce hanya yayan nasa ya rufe, anya shi ma bashi da tsafi kuwa?. Kofar Black Tiger fa ba irin kofofin da kuka sani bane.

Dama da ya yi fushinsa cikin cinema ya shiga ya yi zamansa saman luntsuma luntsuman sofas dake wajen, ya kunna Tv wai dan ɓacin ran da yake ciki ta kau kada zuciyarsa ta buga, sai dai kash ya gaza samun kwanciyar hankali, haka kawai ya rinƙa jin gabansa na faɗuwa shi ne ya ce bari ya dawo su sasanta da yayan nasa kila ya samu natsuwa. Shi ne dalilin dawowarsa kenan.

Innalilahi, ba karamar razana ya yi ba a lokacin da ya sauke idanunsa a kan face ɗin Black Tiger, shi hankalinsa ma bai kai kan Sweetie ba tukun nan, saboda ɗakin yana da balai'n girma sosai, so tsakanin in da take da in da black Tiger yake akwai rata sosai, hakan yasa bai lura da ita ba.

Kusan mutuwar tsaye ya yi, ya zaro idanu yana ganin abin da bai taɓa gani ba. Ko yanayin kirar jikin Black Tiger bai taɓa gani ba, abin da ya sani dai shi ne kullum na Allah yayan nasa yana cikin wasu irin kaya mai kama da na Spider-Man, sannan kayan tana da wata jela a bayanta kamar dai alkyabba haka, babu abin da mutum zai iya gani a jikinsa, harta idanunsa Ronnie bai taɓa gani ba, ya dai san kullun da sassafe yana zuwa wajen yayan nasa su yi gym a tare.................Ina fatan yanzu kun gane dalilin da yasa Ronnie ya iya dukan master Devil dik da cewa shi ya bashi horo?

Yana zuwa da safe kullum su yi gym a tare da Black Tiger ba tare da sanin kowa ba, kullum sai ya tsaya a tsakiyar bayan Black Tiger da kafafunsa Black Tiger yana press up Da shi.

Kunga kuwa mutumin da kamar Ronnien shararren ɗan Wrestling zai tsaya a tsakiyar bayansa kuma ya yi press up da shi ai ba zaku haɗa hotonsa da kowa ba, shiyasa Ronnie ya take master Devil a samun nagartaccen horo.

Kamar daga sama ya ji ance out!! Kuma tabbas Black Tiger bai motsa kyawawan laɓɓansa ba, ba shi ya yi magana ba amma kuma lion voice ɗinsa ce ta furta wannan out ɗin, shi kansa Ronnie ya shaida lion voice ɗinsa ce.

Sai dai ya ɗan tsorata dan Black Tiger bai buɗe baki ba.

Kasa motsawa daga wajen ya yi, ya shiga ruɗani sosai na ganin yayan nasa. Kamar walkiya haka idanunsa ta wutsiya suka hango Sweetie da saura kaɗan ta karisa shigewa cikin wannan bakin ramin azabar.

Ai a miliyan ya juyo da kallonsa mai gabaɗaya a kanta dan ya tabbatar. Ya subhanallah ai bai san lokacin da ya ƙarisa wajen ba sai dai kawai ya ga kansa a gaban ramin.

Ko tsoron yayan nasa bai ji ba ya kai hannu a miliyan ya riko hannunta dake sankare kamar wadda ta zama ice block.

Da karfi ya janyota domin ya fito da ita, sai dai ina ya kasa koda motsata, tana daskare kamar gunki.

Black Tiger dai yana tsaye kamar bai san da su a wajen ba. A hankali gangar jikin Sweetie ya nufi karisa shigewa cikin ramin.

Kin sakin hannun nata Ronnie ya yi yana kallon cikin kwayar idanunta ya ki motsawa daga wajen kuma, a cewarsa sai dai su tafi cikin ramin a tare su mutu tun da yayansa ya ki ya saketa ya samu ya janyota ta fito. Idan ran Ronnie ya kai miliyan to yau ya ɓaci, tin tini yake neman ya sanyata a idanunsa yayansa ya hanasa dama, ashe dama kasheta zai yi shiyasa ya ɓoyeta na tsawon lokaci? Ronnie ya tambayi kansa!.

"Ronnie get out!". Lion voice ɗinsa ta daki kunnuwan Ronnie dake tsaye a kan ƙafafunsa sam bashi da niyar motsawa daga in da yake ko ya saki hannun Sweetie, idanun nan nasa sun yi jajir kamar wuta, sai wani uban zufa yake haɗawa kamar wanda aka watsawa ruwa a fuska, saboda hucin wutar dake cikin ramin ta taɓa shi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali na wuce misali.

Ko motsawa bai yi ba tamkar ba ƴaƴan nasa bane ya yi mashi magana, ga dikkan alamu suman tsaye ya yi, dan bai taɓa tsammanin kamanin Black Tiger haka yake ba, bai taɓa tsammanin ƴaƴan nasa king of beauty, handsome, gorgeous! Sexy man bane, bugu da kari bai taɓa sanin ta haka Black Tiger yake kashe dik wanda ya keto ya shigo cikin wannan part ɗin ba.

Magic eyes ɗinsa ya juya, idan ya juyasu kuma alamar zallar madarar rashin imani zai aikata, Ronnie yasan da haka amma yana tsaye bai motsa ba. Wasu irin dogaye dogayen itatuwa marasa ganye ne suka bayyana a bakin ramin suka yi mashi zobe, suma bakinsu kamar kifiya a feke.

Still Ronnie bai tsorata ba bai kuma da niyar sakin Sweetie, daga shi har ita azabar zafin wutar karkashin ramin yana taɓasu sosai, hakan ya haifar mashi da wannan zufar da yake haɗawa.

Scepter Black Tiger yasa a in da ya turasu gabaɗayansu biyu cikin ramin. A tunaninsa Ronnie zai tsorata ya saki Sweetie idan ya ga zasu faɗa ciki dikkansu biyu, sai dai kash, Ronnie dai da alamar ɗan a mutu ne a kan kyawawan mata. Ya tsare sweetie da ido suna kallon juna ba halin yin magana, ta zaro mashi idanu sai ya kara jin ya samu kwarin gwiwar da zai iya mutuwa a kanta, karku manta kaifafan idanunta suna ɗaya daga cikin abin da yasa yake kaunarta, bare kuma da ta zaro mashi su, ai abin ba'a magana.

Ganin haka yasa Black Tiger bai bari sun ƙarisa shigewa ciki ba, ya yi saurin fitar da su dan kada Ronniensa ya cutu.

A bakin ramin ya dakatar da su, sai huci mai zafi ne yake fita daga bakin Ronnie, da alama ran maza ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.

Shammatarsu Black Tiger ya yi ya raba hannun Ronnien da nata, kafin Ronnien ya yi wani motsi tuni ya turata cikin ramin ya kuma yi amfani da magic ɗinsa ya daskarar da Ronnien a wajen dan ma kada ya ce zai bi bayanta. Ya ɓatar da waɗan nan itatuwa da suke bakin ramin sannan ya yi yunkurin rufe ramin a shafe babin Sweetie kenan.

Sai dai abin mamaki abin ɗaure kai shi ne, wani irin haske ne ta bayyana a cikin ramin mai hasken gaske, kofar ramin taki komawa ta rufe. Ya yi mamakin ganin hakan daga ta ciki, daga ta waje kuma mamakin bata bayyana ba.

Tafiyar magic ya yi kamar wani walkiya sai ga shi a gaban ramin domin ya duba menene? Shi kuma Ronnie yana daskare ba motsi kaman gunki.

Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa lokacin da waɗan nan magic eyes ɗin nasa suka sauka a cikin wannan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login