Showing 1 words to 3000 words out of 397328 words

Chapter 1 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69986

17/02/2024, 15:51 - Les messages et les appels sont chiffrés de bout en bout. Aucun tiers, pas même WhatsApp, ne peut les lire ou les écouter. Appuyez pour en savoir plus.
17/02/2024, 15:49 - Vous avez créé le groupe "GIDAN TYP"
17/02/2024, 16:13 - Vous avez supprimé Sœur Meerah
18/02/2024, 13:08 - Vous avez changé l'icône de ce groupe
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_,


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*1*





Wani irin tattausan murmushi matashiyar da za ta iya kai shekara 21 zuwa 22 ta saki tana kallon tsinin allurar, ɗan dannawa tayi daga ƙas ruwa suka fita ta bakin allurar, hakan ya bata damar soka tsinin allurar a cikin bunburutun robar ruwan dake saƙale aa jikin ƙarfe sannan tatsiyaye ruwan ciki, take ruwan suka canza kala daga fari zuwa yellow shar.

Hannun matar dake kwance ta ɗan kama tana sake daidaita shigar ruwan a jikin ta, duk hirar nan da dttijuwar ke mata tana bata labarin yadda zazzabi ya galabaitar da ita da amai daga daren jiya zuwa wayewar gari, ba ta ce mata ƙala ba sai murmushi kawai da take yi, saida ta gama za ta isa ga gado na gaba ta kalli fuskar matar cikin wata nutstsiyar muryar d tayi daidai da zubin ta tace "In sha Allah Mama, za ki ji sauƙi."

Daga haka tayi gaba zuwa gado na gaba, ruwan da aka saka mishi wanda suka kusa ƙarewa ta dub, sannan ta kalli matar dake kusa da shi da alama mahaifiyar shi ce tace "Mama, idan ruwan ya ƙare ki yi mgana a cire mishi."

Da murmushi matar ta amsa ita kuma ta fito daga ɗakin, fitowar ta tayi daidai da fitowar wata nurse daga ɗakin haihuwa hannunta ɗauke da abun da ba ka iya gani bare ka san menene sabod an sa baƙin zane irin wanda suke shinfiɗawa a gadon haihuwa an rufe shi, hakan ya sa *Yusrah* dake kallon nurse ɗin tana saka hannayen ta cikin aljihun farar rigar da ta sauko mata har guiwa take kallon ta da matsanancin mamaki.

Irin duburburcewar da taga nurse ɗin tayi lokaci guda sai abun ya sake sakata ƙare mata kallo, take kuma nurse ɗin ta sake tabbatar mata da bata da gaskiya saboda murmushin da ta ƙaƙaro mata tana faɗin "Uhmmm! Ummmm! Doctor Yusrah, har kin...fito kenan? Barka, dama...zan je na kai saƙon nan ne."

Shirun na Yusrah bai damu nurse *Sakina* ba, dan magana komai daɗin ta ko rahar ta Yusrah dama sai tayi niyya take amsawa, kallon da take mata ne kawai ya ɗan saka tajin tsarguwa, da sauri sauri ta wuce ta corridorn ta buɗa office ɗin babban Docteur ɗin ta shiga. Har ta shiga office ɗin kuma Yusrah na bin ta da kallo, saboda ita dai a fara aikin bautar ƙasar (stage) ta a asibitin nan wasu abubuwa ne kwanakin nan tun da babban Docteur ya dawo take gani da suke neman ɗaga mata hankalin ta, amma ba ta san komai ba, kula ba ta da hujjar da za ta yi magana, dan haka yanzu ma jan bakin ta tayi ta yi shiru tare da nufa ɗakin hutun da ake kwantar da matan da suka haihu.

Ba ta jima ba ta fito daga ɗakin ta nufi wajen zaman su, tana zuwa ta samu biyu daga cikin abokanan aikinta mata da maza uku suna ta hira da cin abinci, sai dai su anan asibitin suke aiki dama saɓanin ita da tayi babbar sa'a aka kawota nan yin gwajin ta, wanda kamar yadda malamin ta ya gaya mata ba'a yin haka, amma buƙatar mai aiki mai nutsuwa da aminin nashi ke yi kuma birge shi da take yi ya sa ya turo ta nan, kuma ya bata tabbacin idan tayi ladabi da biyayya to ko bata da ƙwarewa aikin ta a hannun ta yake. Duk da hakan ya bata mamaki, duba da asibitin kuɗi ce kamata ya yi ace zatayi aikin gwajin ta a asibitin gwamnati, sannan an mata alƙawarin aiki ko babu ƙwarewa? Sai abun ya ɗan so damun ta har take tunanin wace irin asibiti ce haka to? Amma da ta tuna tana buƙatar aikin ko dan iyayen ta, sai ta kawar da tunanin ta gefe take aikin ta da kulawa kamar yadda aka koyar da ita.

Ɗaya daga cikin samarin ne yace mata "Ustaza bismillah?"

Kallon shi tayi a tausashe, mamakin mutane take da yau idan ka zama kai baka da hayaniya irin ta wasu, wai sai a dinga yi maka izgilanci da ire iren sunayen nan, saboda ana ganin ustazai ko malamai ne kaɗai a haka. Taɓe baki tayi ta girgia kan ta ba tare da tayi zaune ba a sanyaye sosai tace "Alhamdulillah."

Sai kawai ta sake gyara safar hannun ta ta leda ta ɗauki abun sauraren numfashi ta rataya a wuyan ta, sannan ta ɗauki kwalin dake sanƙame da ƙananan allura na ɗiban jini da kuma abun awon zafi, hanya ta kama za ta fito wata ta juyo ta kalle ta tace" Ina kuma za ki je Yusrah?"

Ba tare da ta juya ba tace" Duba majinyata."

Da sauri matar ta sake cewa" Tun safe kike aiki fa, ki ɗan tsagaitawa kan ki mana ki huta, idan na gama kari zan duba su ai."

Ba ta juyo ba, haka kuma ba ta ce mata komai ba kawai ta wuce abun ta, tana fitowa ta ja kujera dake kusa da sikelin ɗaukar nauyi ta zauna sannan ta dubi matar dake rumgume da ɗan ta tace" Bismillah?"

Haka ta fara duba mutanen, duk wanda ta auna ta ga ciwon ƙwarai ne take ta ke miƙewa ta je ta ɗauko allurai ta kwantar da shi a gado ta ƙara masa ruwa, idan kuma ka fi son allura ne sai ta maka ta rubuta maka magani, ta duba mutum uku a na huɗu wata ta fito ta karɓe ta, amma duk da haka ba ta zauna ba waɗanda duk ta san an saka ma ruwa ta dinga bi tana tambaya ya jikin? Sannan ta sake duba tafiyar ruwan.

Haka rayuwar Yusrah ta kasance tunda ta fara aikin wucen gadin ta a asibitin nan, ba ta hutu b ta zama dan hutu idan ba sallah ko cin abincin rana da ba wani sosai ba ma take ci.

Yanzu haka yamma ce lis lokacin tafiyar ta gida ya yi, dan haka ta miƙe tana haɗa kayan ta dan tafiya gida, ita kaɗai ce a ofishin duk sauran suna wasu sashen na daban, tana yane kanta da babban kallabinta na doguwar rigar ta aka ƙwanƙwasa ƙofar...

Kafin ta bayar da izinin shigowa aka turo k'ofar, hakan ya tabbatar mata d'aya daga cikin likitocin ne, dan haka à saib'ance ta d'aga ta kalli Sakina da ta shigo da sassarfa tana fad'in "Yusrah, ba dai tafiya zakiyi gida ba?"

Fararen idanunta t zuba mata sannan ta amsa da "E, da matsala ne?"

Jinjina mata kai tayi tana k'ok'arin saka safa a hannu tace "E, mai haihuwa aka kawo yanzu, da zaki taimaka min da na so haka, tunda kinga iya su Abdul da Faruk ne kawai yanzu, sai kuma Dr."

Tun ma Sakina bata gama magana ba Yusrah ta hanzarta d'auko farar rigar da ta cire ta mayar sannan ta d'auki safa ita ma tana sakawa suka fice daga ofishin zuwa d'akin haihuwa.


*PALACE ANZA*


A tsawace yace duk da ba wani ɗaga murya yayi sosai ba saboda tsabar hutun da ya gama ratsa su ya musu shamaki da duk wani abu mai kama da tashin hankali yace " *AA*! Idan ina magana ina so ka zauna ka sadda kanka ka kuma bi umarnin da nake umartarka da shi, abin kunya ne a yau ace ɗan da na haifa ne ke riƙe da bindiga yana kuma zuwa aikin hawa da sauka har na dare, duk irin matsayin da zaka taka a soja ba zasu iya biyanka ba, kai ɗin jarumina ne wanda ya dace ace gwamnati na girgiza wajen biyanka, ko dan karatun da ka yi ya dace ka daina shan zafin rana kana AC, ka sani ba zan iya kallon ka a haka ba, ba kuma zan kuma yarda ana kawo min ƙarar ka daki waccen ko wannan ba, mutuncinka ya fi ƙarfin haka, jinin *ANZA* ke yawo a jikinka *ASWAN*."

Elhaji ALIYU ANZA ke faɗi muryarsa sama sama tsaye ƙiƙam a tsakiyar falonsa sanye da doguwar farar jallabiya jikinsa na fitar da raɓa irin ta sanyin acn da ya kwana ciki ya kuma tashi cikinta.

A hankali matashin bijimin ingarma namijin da ke zaune ya ɗan karkata dubansa wajen Hajia kuma Annar sa ko zata katsewa mahaifinsa hanzari, sai ya ga hajiarsa mace mai cike da classs ta ɗan ja farin glass ɗin idannuwanta ta mayar da dubanta gefe ta ɗaure fuska, domin ita ɗin ta fi mijinta son yaronsu ya ajiye wannan aikin, sam ba aikin yinsa bane, eh lalle a sojan babba ne shi, amma akwai na sama da shi sannan sam basa son irin yadda duk girmansa a sojan yake zuwa yana haɗuwa da yarensa suna gabatar da aiki irin na wanda bashi da babbar grade haka, uwa uba *ASWAN ALIYU ANZA* mutum ne mai zafin gaske, baya ce masa komai a daku da shi, duk da matsayinsu na riƙaƙƙun ƴan siyasa hakan ba daidai bane a yanayin siyasar su.

A hankali ya sake duban mahaifinsa dake jiran jin cewarsa a kan lalle sai ya bar aikin da yake so har zuciyarsa, a hankali ya ɗaga laɓɓan sa da yanayin da sam ba ya so iyayen nashi su gane shi ya ce" Dad, ina son aikina."

"Umarni na baka ka ajiye shi, ba aikin yinka bane!" Mahaifinsa ya katse shi ya juya ya haura sama ransa ɓace, da wani irin kallon mamaki ya bi bayak shi, yana nufin ya gama magana kenan?

Wani irin ɓacin rai ne ya zo masa wuya ya tokare shi, a birkice ya miƙe bai ce da mamansa komai ba ya nufi hanyar fita, a makare ya ƙarasa wajen aiki, yana zuwa ya faka motarsa a baibai ba tare da bin ƙa'ida ba, wanda hakan ba baƙon abu bane ga waɗanda suke nan kuma suka san shi sannan ya fice ya nufi office dɗinsa idannuwansa har rufewa suke, hakan ya sa ko masu masa barka da shigowa bai iya kula kowa ba ya shige office ɗinsa ya rufo ƙofar.

Kai kawo ya kama yi ransa a jagule, shin ya ya zai yi da umarnin wanda ya isa da shi? Idan ya bijire a wannan gaɓar da bijirewar ta fi komai daɗaɗa tunaninsa ya ya makomarsa a wajen Ubangijinsa? Shin laifi ne? Ya ya zai yi ne! Ya duba sama da ƙasa bai ga aikin da ya dace da rayuwarsa ba sai wannan, shin ba za'a barshi ya mori nasa neman ladan ba sai an cusa mi shi abinda a bayyane ya san ba halali bane haramun ya fi yawa a ciki?

Ƙwanƙwasawar da aka ma ƙofa yasa shi saurin kallon ƙofar, kawai a jikin shi ya ji ba wanda ya san shi bane ya zo masa yanzu, a jikin shi ya ji ko ma wanene bai ga halin da ya shigo office ɗin ba, dan haka ya gyara tsayuwrsa ya sake tsare ƙofar da idanu cikin wata murɗaɗɗiyar murya yace "Yeah."

Turo ƙofar aka yi aka shigo, tun bai gama kallon fuskar ba ya ɗauke kan shi saboda ya kula da kakin dake jikin wanda ya shigo, na sama da shi ne, shi ke gaba da shi a wurin aiki har ma da shekaru, to amma shigo masa yanzun bai masa ba gaskiya.

Shi kan shi colonel ya fahimci sabon rashin mutumin da A.A Anza ke niyyar shuka masa, amma saboda ko a soja ai akwai babba sannan girma girma ne, sannan ba matakin da bai taka ba wanda Anza ɗin ke kai daga ciki har da na *zafin kai*, sai kawai ya tunkare shi har da juyawa ta ɓaren da yake har da fuskantar shi sosai cike da gadara da son nuna shi ne gaba da shi yace "Kai ne ka umarci su *Mika'il* su motsa daga madakatar su daren jiya? Ka san me hakan ya haifar? Me ye dalilin ka na umartar su bayan umarni da ni na basu? Me ya sa Anza?"

Ɗan ja baya yayi kaɗan daga matsewar da col. ɗin ya masa, sannan ya dafe kan shi da hannu ya rintse idanu yana lumshe su sanann ya buɗe fess saman manyan takalmin shi na soja masu halakar da bawan da aka daka da su, ba tare da ya ɗago ba muryar shi kanta a hargitse take fita saboda ɓacin ran dake hauhawar masa yace "Yallaɓai..., zan zo office ɗin ka muyi magana, bana cikin yanayin yanzu."

A wani harziƙe col. yace "And so what? Sai me dan baka cikin yanayin Anza? Ina magana da kai..."

Kallo ɗaya tak ya mishi da idanun shi irin manyan nan, ba su rikiɗi ba ko kaɗan, sai dai kallon ne ba na rahama ba ko alama, dan haka ma col saida ya dakata daga maganar, A.A kuma ba tare da ya rusuna kallon da yake mishi ba yace" Yalla...ɓai, nace maka..zan same ka office ɗin ka, zamu tattauna akan matsalar, dan Allah?"

Haushi da takaicin kallon wulaƙancin da AA ɗin ya masa mai nuni da shi ma ya raina sa kenan kamar yadda ya raina sauran mutane ya sa col. ɗin daka masa tsawa da cewa "Ba zan je ko ina ba AA Anza sai ka sanar da ni abinda nake son sani, wa ye kai? Wa ye kai da zaka ce naje za ka same ni? Ka san girman laifin da ka aikata kuwa? Kasan da an samu waɗanda suka karya doka suka shigo mana ƙasa da haramtattun kaya, ko dai da sanin ka ka aikata haka? Tunda ai mun samu labarin motar asibitin da ta wuce ta bakin bodar (boder) ɗauke da bilyoyin kuɗaɗe motar asibitin mahai..."

Wata mahaukaciyar wawura ce ya ma col. Ɗin tare da cira shi gaba ɗaya ya raba shi da ƙasa,, a hargitse ya kaiwa kofar office din nasa duka da ƙafarsa yana ruruko ido , kafin col ya ankara ya gwara shi ga bango har saida drower dake shaƙe da litattafan da nashi ne kasancewar sa ma'abocin son karance karance ta tangaɗa har wasu litattafan suka zubo, cikin wani irin hargagin bala'i da tsananin ɓacewar rai idanun shi har rufewa suke yi muryar shi a sama kamar zai sanar da duk wani dake cikin compagnie ɗin yace "Na ce a'a, na ce ka je zan zo, me ya sa ba zaka gane yarena ta sauƙi bane? Mahaifina tsaran wasan ka ne? Shin ban gaya maka bana yanayin daɗi bane? Ba zaka fahimce ni bane har sai na aikata ba daidai ba?"

Dukan da ya yiwa kofarsa da karar muryarsa ya saka sojawan dake kofa masu tsaronsa da masu tsaron colonel afkowa office din a rikice dan a cikinsu babu wanda bai san waye AA ba

Kusan kowane sai da ya zabura gannin ya makure Col Garba a jikin garu shi kuwa sai kakari yake yi shi bai summa ba shi bai yi rai ba

A birkice suka shiga kokarin kwatarsa, da karfinsu da kalamansu da kuma neman agaji, cikin ikon Allah suka kwace shi a lokacin da idannuwansa ke neman daukewa dif numfashi na neman gagararsa

Wani irin jan numfashi ya yi a fitar hayaci, kamar wanda ya ratsewa alburushi sai kuma ya zazaro ido yana warce hannunsa daga hannun yaronsa yana juyowa ya kalli AA dake tsaye kikam sun sake shi du sunna jiran motsinsa dan ba zasu bari ya yi kisa ba ai kau?

Rai bace yana haki muryarsa sama sama ya ce"Ni ka shaka ka daka? Ni ka yiwa haka? Yau sai an bi min hakina a gidan nan dan ba zan yarda b..."

Dan motsawa AA ya yi, hakan ya sa Col yin waje da gudu yaransa na mara masa baya, su kuwa Yaren AA din suka yi aniyar rike shi har sai da ya ce" Kai ku sake Ni" sannan suka sake shi suka fita waje sai haki suke kowa da abinda ke ransa dangane da ASWAN ALIYU ANZA

Kirjinsa dake zafi ya dafe a hankali ya zauna saman kujera yana dan rike kansa ya saki

Ƙara dafe gaban goshin shi yayi inda ɗaya hannun yake ƙara damƙe table ɗin nan kamar zai raba shi gida biyu yana kallon shawagin sojoji a harabar ma'aikataar kowa da sabgar da yake yi wacce ta dame shi, amma shi sai huci yake yi kamar wani kububuwa yana jin har yanzu bai saki ba, bai huce ba har yanzu, yau shi da kan shi ma zai je bakin madakatar ya yi aikin kwana, ya ga uban da ya isa ya hana shi duk da matsayin shi ya wuce nan, aikin banza kawai tunda mutane ba sa gane yaren ka a sauƙaƙa har sai sun saka ka kauce ƙa'ida.


*_SAJEERAH_*🖊️

*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login