Showing 57001 words to 60000 words out of 382072 words

Chapter 20 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28385

kai da koma suna raba abinsha dana ci da aka tana dan hakan.
A yau din duk wanda ka kalli fuskan shi a cikin su a sake fuskan shi yake wurin duk dako zaman jiran mutum dayan da suke wanda ya jawo masu wanan nasaran da suka samu din a yanzu don kayan da suka shigo lafiya.
Sannu a hankali suka koma jan tsuki a tsakanin su don bata lokacin da sukeyi a nan din har yakai dai sun soma maganan kan zaman banzan da sukeyi din a wurin duk akwai komai na more rayuwa a wurin har mata.
Sai can suka fara hango mutanen shi na hannun daman shi dakan shigo suyi dan kuskus kafin ya shigo surin ke nan lokacin hankalin su ya fara kwanci da zaman nasu.
Kamar yadda kowa ya shigo ta kofan gaba shi sabanin hakan don ta kofan dake baya na dakin taron ya shigo masu duk suka maida kallo su gareshi.
Don Allah yaba yaron zati da kira na halitta duk inda irin su suka shiga ansan da suna wurin ga kuma kwazo da Allah ya bashi na neman kudi duk da gwaunati na ganin sana,an nasu haramtaciya ce ga kasa shigo da kaya a bayan idon jami,an tsoro ba kasa.
Ga wani dan saje daya aje a fuskan shi wanda ya kara fitar mai da zatin shi a fili yayi masa kyau ainun a hankali yake takowa tako irin na kasaita da isa da izza da gani shi kasan abinda ya taka a hakan.
Taken shi suka fara mai na young billoniear yana dan daga hannu a hankali yana jinjina masu a hankali zuwa wurin da yasan shine wurin zaman shi din.
Bai zauna ba din sai da yaje gaban wasu tsofi biyu da suka girme masa yakai runsune kasa yadda ake gaida manya a cikin al,adan hausawa ya gaida tsofin kana yabi sauran da hannu yana mika masu suka gaisa.
Kafin ya dawo wurin zaman nasa ya zauna bakin shi na cike da adduan don yasan komai sai bawa ya danganta da Allah yake samun galaba dama kuma ko can abinda ya dakatar dashi ke nan bai fito da wuri ba.
Haka kuma yasan cewa lamarin nasu saida hakan don duk wanda ke daki toron nan yasan abinda ya taka kafin ya shigo wurin.
Tun mikawa wani dan maiduguri hannu wani lokaci yaji kanshi yayi mai nauyi wasa wasa har abin yaso ya kayar da kasa sai gyaran Allah aka samu baikai kasa din ba shi wancan din ya kwanta a lokacin.
Bayan shugaba mai suna shugaba yayi adduan bude tarone suka shiga tatauna abinda ya kawosu wirin a lokacin.
Daya bayan daya suke tashi kowa kuma a cikin su yana da inkiyan sunan da ake kiran shi dashi a cikin su wanda kowa yasan da take nasa.
Alh baba shine uban gungiya shiya fara magana sai Alh Rabi maliya mai bi masa sai shi Aliyu yayyayafi don yawan alherin sa ga mutane su suka laka mai sunan ko su kirashi da dollers boy.
Shine na uku a cikin kungiyan tasu a yanzu dama duk wani kwaran shike karban su ya fiddasu a hanya har a cin ma nasara.
Yaro ne da kudi abokin manya don shekarun sa baifi sha takwas zuwa sha tara ba a lokacin amma ya kerewa sa,anninsa dama wayanda suka girme masa ga shiga kasuwanci a yanzu wurin harkan kasuwancin su.
Aliyu ga kyau ga kudi ga ilimi duk Allah ya hada mai uwa uba ga kyau ga kwarjini sai dai kallo daya zaka dauka shi din miskiline na gaske don yana da wuyan sabo da mutane.
Sai dai idan ka ganeshi baida girman kai mutane ke masa wanan fasaran do rashin ganewa saidai sam Allah bai sako mai tsoro ba ko fargaba don irun mutanen nan ne da idan sun tasa abu a gaba sai sun sameshi.
Yadda yake da kafiya da naci yasa yayi fice a cikin abokan harkan nasu dan shi Allah ya bashi tausayi da jin kan nakasa dashi sosai ga taimako idan yaga mabukaci har sukai ido biyu da maishi.
Kudi kan zamuce gadon su yayi a wurin mahaifin shi da yanzu tsufa da ciwo ya riskeshi saidai sun raba hanya da mahaifin nasa don shi smogal ya zaba a yanzu don yaga yafi ci a wanan zamani
Don haka ya fada harkan motoci da kaya masu muhinmanci da gwaunati ta hana a shigo dasu a cikin kasa saidai saukin abin shi baya yarda yayi abinda zai zubar da kimar mahaifin shi ko kadan.
A wani vangaren kuma yana harkan zinare duk ta barauniyar hanya abinda ya kara bunkasa karfi shi da kudin shi ke nan a yanzu.
Wanan yasa shi saurin fice a cikin abokan harkan nasa a yanzu sunan shi ya daga ko wanan haduwan akan wani sabon ma,aikacin da aka turo yabi didigin su a nan gida Nigeria.
Alh baba yaci gaba da bayani shi kamar haka bayan yayi sallama yace kowa nan yasan abinda ya taramu a wanan wurin a yanzu.
Wanan matsalan babban abune da zai iya kawo muna cikas a yanzu cikin harkan nan namu don a wanan karon idan badon dollers boy ba da yanzu kayan mu na wanan shekaran sun zama tarihi a rayuwan mu wanda hakan zai iya kawo koma bayan da yawan mu a wurin nan.
Kai suka shiga gyadawa tare da yan kuskus a tsakanin su kowa na fadin albarkacin bakin sa kan irin fargaban da suke ciki a da kan kayan su din.
Alh baba yaci gaba da jawabin shi yana fadin mun san cewa akwai aiki ja a gaban mu yanzu kan irin matakan tsoron da aka daukan muna ga wanan harkan.
Na turo wakile daga cikin mu su gana da shugabanin wanan jami,an tsaron abin ya kiya don shugaban su wani karamin yarone ke jagorantan su.
Don kwata kwata yaki yarda da tayin da mukai masa na goro asalima sai kokarin bincken da yakeyi a kanmu yanzu haka.
Don yayi ikirarin duk wanda ya fada a hannun sako kayan sa ba zaiji dadi a wurin sa ba kun san yaro a yanzu shike da kafi da naci akan aikin shi don haka wanan yaron ya zama dole mu san abinyi dashi don musan yadda zamu zauna dashi don harkokin mu su tafi daidai yadda suka saba.
Kowa yayi shiru a wurin yana nazari a cikin zuciyar shi na hanyar da zasu bullo ma wanan matsalan da yanzu ya kunno masu kai.



ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , , , , , , , ,

1️⃣8️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AS SALAM, , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL DON DARAJAN ALLAH KI BIYA KI KAUCEWA SHIGA HAKKON WANI YAR UWA, , , , ,


Abu sun mai yawa lokaci guda na rashin nasaran kama wanda suke nema da rashin sanin koshi waye har yanzu don sunayen da maishi ke amfani dashi na bugi.
Sai kuma case din yarinyar nan daya dauka yasa a ransa zaiyi bincike da kyau yasan meye tsakanin su da mahaifin shi don shi hat ya fara zargin ko dai yaran diyan daddy sune a yadda yaga damuwa a tare da daddy din.
Hakan bai mai ba yayi saurin kawar da wanan tunanen a zuciyar shi da sauri ya koma wani tunane semi boda ya kira a fili inda hjy halima tace muna zaune yanzu.
Kafi kuma yaja tsoki yace wanan wani rayuwane ku kaka gudu kuna canza wuri kamar marasa gaskiya dasu aiko fulani yanzu basu yawan canza wuri haka barkatai kamar ku.
Dole yasan hanyar daya bullo wa yarinyar nan ya gano komai nasu kafin daddy ya sake juyowa zancen nasu koma meye idan ba mai yuyuwa bane ya yi maganin abin kafin a farga.
Chuku ya fado mai a rai don shine kadai zai iya bibiyan lamarin ya gano gaskiya kamar yadda a yanzu ya gano masu dollers boy dake ta faman yi masu yawo da hankali saidai har yanzu din basu gane taka maimain ko waye shi ba sosai.
Amma har kasan zuciyar shi ya fara zargin wani a tare da boy din yanzu wanda kuma yake fatan kada abin ya kasance hakan gaskiyane nan gaba.
Waya ya daga ya kira chuku tare da mai bayanin komai yace ya gane yarinyar sosai kuwa kuma zaiyi aikin nan da gobe in jesus name yafada.
Ya tura mai kudin zirga zirgan da zaiyi wanan aikin yayi ta faman yi masa godiya yana jin dadi har cikin zuciyar shi da wanan kudin daya turo masa haka masu yawa don wanan dan karamin aikin daya sashi kan mace.
Ya mike daga wurin da yake zaune din zuwa gado don tunda yayi sallah yake zaune yana azzakar har ya fada tunanen duniya kuma.
Bai dade da kwanciya ba wayan shi ya fara ringing ya ya mika hannun shi ya dauki wayan dan tsuki yaja don ganin mai kiran nasa a lokacin don ba wani bace sai Nazira amaryan shi daya bari gida kullun tana masa korafin ya tafi ya barta a gida ita kadai.
Dauka yayi da sallama saidai muryan da yajine sabanin nata din ya bashi mamaki har ya dan daga hannu yana kallon lokaci tare da mamakin me ya kawo uncle Nuhu gidan a wanan lokacin takwas saura na safe.
Wani gaisuwa ya shiga yi kafin Uncle din ya katse shi da fadin kai ba gaisuwan ka nake so bani dalilin tafiya kabar min ya zaune a gidan ka ita kadai nake son ji ?
Idan ma aiki kake takama da ka tafi yi meya hana ka dauki matarka ku tafi tare don ka rainawa mutane wayau ne kome da bakatafi da ita ba can ku zauna tare.
Shiru yayi yana sauraren mahaifin matar nasa kawu a gare shi har lokacin da yaji ya tsaya da magana yace kawu ayi hakkuri tun farko abinda na guda ke nan don kowa yasan yadda aikina yake.
Dakatar dashi Alh Nuhu yayi a fusace yana fadin kai idan ka rainawa iyayyen ka wayo niba zaka raina min don na gane komai da kakeyi a yanzu da sanin su kake iskancin nan.
Dan murmushi yayi kafin ya ja nunfashi yana fadin ayi hakkuri na kusa kamala abinda ya kawo ni nan zan dawo a cikin satin nan insha Allah.
Ka saurareni Alh Nuhu yace na baka yau zuwa gobe duk abinda kayi ka dawo gida idan ba haka ba zamu saka wando kafa daya dakai a garin nan don naga nema kake ka mayar dani mutumin bamza a garin nan yanzu.
Idan na gama zan dawo ya fada Abubakar din yana kashe wayan bai jira cewan kawun nasa ba ko yaji abinda zai kara fada gaba ya kashe wayan kai tsaye gaba daya ta dauke a cikin kunan rai yayi cilla ta gefen shi yana huci.
Nagane mutumin nan sai nayi da gaske idan ba haka ba raina min wayau zaiyi a garin nan ya fada a cikin hasala ran shi yana baci sosai da halin son kai da Alh Nuhu ya nuna mai yanzu din.
Daga nan ya wuce kai tsaye ya shiga bath room wanka yake yana faman jan tsuki shi kadai a ban dakin har ya fito ya fara shiryawa.
Yau tun tashina nake jin raina na baci gaba na kuma yana dan faduwa lokaci lokaci wanda ban saba da irin wanan yanayin ba a baya sai ranan nake jin hakan.
Ko umma ta fahinci halin da nake ciki na rashin walwala a tare dani don ta tambayeni lafiya nake kuwa nace lafiya ta kalau kawai dai yau bana jin dadin rayuwanane kawai haka na tashi.
Koma meye Allah zai kare min ke don nima a yan kwanakin nan ina yawan yin mafalkin da baida kyau a gareni addu,a nakeyi da neman tsari a kan hakan .
Dan murmushin yake nayi ina fadin balle ba wanda ya sani don ba wuri daya nake zama ba a garin nan ko ina ina shiga ina yawatawa gobe kuma na canza unguwa.
Amma sai naki fada mata komai wani tunane nayi akan kudin nan ranan dai na bata kuma nasha fada sosai kan yadda na bari har muka kara haduwa dashi duk da alherin da yaiwa umma amma tayi min fadan hakan ni dai ban damu ba tunda na rabu da kudin a jikina.
Kwana biyu ke nan bayan bata kudin nake jin yawan faduwan gaba a tare dani yau da zan fita amma don karfin hali haka na daure na shirya na bar gidan.
Nayi duk wani shirin da zanyi don fita na zo gaban umma na rusunna ina fadin zan tafi a cikin harshen yarbawa tayi min adduan tsari na kalli amar dake kallona na nace me zan sawo ma yau idan zan dawo yace min nama dariya nayi nasa kai na fita ina tunane don mun kwana biyu gaskiya rabon mu da nama a gidan.
Saidai muga mutane nacin nama muna kallo don umma ta saba muna da hakan zamu iya zama da dadi da wuya duk wanda ya samu a rayuwa zamu iya kasancewa a hakan.
Kuma hakan yana da kyau sosai don uwa ta nunawa yaro jin dadi da halin wadata a kullun abune mai muni da iyayyen yanzu basu gane ba ka koyawa dan ka ba kullun ne ake zama a vikin daula ba koda kuwa akwai wadatan ga mutum ya daure ya koyawa dan shi zaman duniya a yanzu.
Haka nabar gida ina tafiya kamar wace wani abu e damuna a lokacin har nazo bus stop na shiga motan Obalande duk da nasan yan wanan yakin yarbawane zallah a cikin sa sai yan yaruruka kalin dake zama a cikin su duk da hakan kuma ba jittuwa a tsakanin su amma haka na hau mota a ranan sai obalade din.
Tunda na sauka nake bin ko ina da kallo tunda ba unguwar na sani sosai ba aharawa daya na fara yankewa shine in bi layin mabarata don yanayin da nake ciki ranan ba zan iya tallaba.
Har na zauna na hango wani tsoho mai sayar da maganin gargajiya zaune na nufi wirin shi na dan dade tsaye ina nazarin shi kafin in ce ya ban ko kadan sari.
Kallona yayi yana mamaki yace zaki iya nace eh zan koma wani side in zauna ba a wurin da yake zan tsaya ba a cikin gurbatacen hausa na nake magana haka dashi.
Na dubu biyu na sara don ban yarda na sara da yawa ba tunda gwadawa zanyi ina murna har na daga yake fadin in tsaya ya bani wani siri da zanci kasuwa dashi na tsaya.
Yace in miko hannu na mika mai yake fadin don su yarda da ke kinga wanan layin na tafin hannun ki guda uku nace eh .
Yace don a gaskanta maganin ki sai kice wa mace ta baki hannun ta ki duba idan namiji ke bi mata a wurin haihuwa zakiga layin nan biyu sun hade dayan ya ware nakasan ke nan.
Idan kuma mace ce wace ke bi maki a wurin haihuwa zaki ga daga sama basu hade ba sun dan rabu wanan kawai idan kinyi zasu gaskanta magabnin ki su dinga saya zaki dawo idan kin kokarta na fada maki.
Har kasa nakai ina masa godiya na karba na fara tafiya ina dan waigen tsohon a cikin tsoro don taba min hannun da yayi tunda umma tace mu daina yarda ana taba mu .
Idan an tabamu mubi mutum mu rama ko waye a haka ake daukewa mutum kurwan shi a cinyeshi ko a bashi wallaha gashi yau rigima yasa na amfakawa tsoho waini tallan mahani.
Sai da nakai titin babba inda ake hada go,slow na tsaya na fara bin motoci ina fadin by local medecine for ur body medecine de here.
Wata mace ce naga ta tsaya a tana kallona na je dan kusa da ita ina fadin buy medecine madam.
Meka give u d one when ur ogo no go look anoda woman again tace dani (waire,) wai ni mahaukaciya tana fadawa na gefen ta wani magana suna dariya.
Nace madam no be lie i talk woo na true true i de talk make show u something ban tsaye ba na figi hannun ta daga cikin yaga motan ina bude tafin hannun ta nace.
Na woman de follow u for d birth abi na dago ina kallon ta ta dan fisge hannun ta tana cewa woman for where ?
Nace emm after ur mama born u d one who de follow you its a girl abi ?
Kallon yar uwar nata tayi tana fadin see dis small girl how d u know all this nace eh na my work naw even you can ask me sometin now apart from dis.
Kallon juna sukayi kafin dayan dake gefen ta tace oya look here who de follow me na rike hannun nata da sauri kafin ince na boy naw.
He naw tall dan u na kwatanta shekarun tane na fadin hakan da wasa ashe gaske ne haka dinnne kuwa.
A


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login