Showing 255001 words to 258000 words out of 382072 words
rubuce.
Muka fito zuwa wurin biya ya basu card dinshi aka cire kudin nan sukai packed xin su aka kai muna a motan da mukazo da ita bamu muka isa masaukin mu ba sai tara na dare a gajiye naga an iso masaukin namu.
Tunda moton ya tsaye yake fadin karfe bakawai na safe zan bar garin nan ba lalai bane mu sake haduwa daku nan din don haka ku kula da kanku har lokacin tafiyan ku yazo.
Zaku zauna tare da Alaja a nan din don sai kun tafi kun barsu idan na dawo zamu wuce gida tare dasu lokacin sun gama hutun su da zasuyi.
Sai kuma ya dan juyo ya kalleni sosai yana fadin nagode da kokarin komai da kikai min Sahiba wani iri naji a raina na dago kai na dan kalleshi ina fadin.
Ba sai ka gode min ba ni ya kamata na godema ga irin kokarin da kake muna a rayuwa da badon kai daka tsaya min ba har rayuwana dana mahaifiyana ya inganta a yanzu da bamu san inda rayuwan mu zai kasance a yanzu ba.
Wani irin lumshe idanun shi yayi lokaci guda sai kawai naga ya yunkura zai fita daga motan tare da fadin is OK nasan pain din ku a yanzu take care daga haka ya rigani fitowa a motan.
Nima na fito tsayawa yayi yana saita kanshi kafin ya daga kai ya kalli saman benen dake gaban mu na dakunan kwanan bakin hotel din.
Naga ya juya yana magana da driver daya dauko mu din a cikin larabci lokacin ne kuma muka jera zuwa ciki inda zamu kai dakunan kwanan mu.
Alaja da yar ta dake tsaye saman suna kallon dawowam mu suka kalli juna suka tabe baki suna jiran hawowan shi saman na karasa inda masaukina yake na shige ciki.
Ban san ya akayi aka shigo da wanan kayan da muka sayo ba dakina nidai na fito wanka danaje don yin alwala na samu an shigo min dasu a dakin.
Da mamakin hakan na tayar da sallah ina gamawa a lokacin abincina yana ajiye naci sai barci ranan ban ko tsaya duba sakon wayana ba don gajiya.
Har naso makara gayin sallah washe gari don a gurguje na fada ban daki nayo alwala na fito sai da na idar ne na fara tuna ko yanzu ya wuce a lokacin na dubi wayana karfe takwas saura yan mintina.
Idona na lumshe ina tunanen abubuwa da dama a raina kafin na girgiza kai a hankali na dan jingina jikina da bangon dake kusa dani na dakin.
Zubur na mike ina bude idona daga rufen da suke na daga na nufi wurin kayan da na gani a dakin ko an kwashe na samu kayan suna nan a inda suke ajiye har lokacin.
Binsu nayi da kallon mamaki tare da tuna irin makudan kudin da ya kashe wurin sayen kayan don irin kudin da naga an rubuta a jikin kayan.
A lokacin idona yakai saman takardan dake makale a gefen kayan na dauko da sauri ina karantawa a hankali na koma baya kadan daga wurin na kai zaune.
Ban dago ba ina wurin cikin zurfin tunane yanzu duk ni ya sayawa wanan kayan ashe dama kayane fa da aka kashe kudi masu yawa wurun sayan su don ni na dauka ma a shagon mu nacan zamu saka.
Tunane nayi to ni yanzu wani irin godiya ma zanwa wanatn mutumin ne wai na dade a zaune ina tunane gashi bama zan iya cewa ga irin kayan dake cikin packed din ba lokacin.
Tun ina dan tunane har na fara gyangyadi a wurin haka yasa na mike na koma na kwanta barci nayi sosai a ranan ga abokan tafiyana suna son ganina gashi ba layin kasan a wurina.
Saida nayi barcina na gaji sannan na tashi nayi wanka sai lokacin na nemi abinci na danna masu kan a kawo min abinci a dakina.
Bayan naci na koshine na kara watsa ruwa a jikina na zauna a gaban mirrow ina kallon kaina a ciki yadda naga sauyi sosai a jikina.
Fatana yayi wani lub lub dashi a yanzu tankar dai dama can a cikin daula na taso ban taba wahala ba a baya.
Ashe ko wani jikin dan adam hutu yake son samu dan lokaci kankani zakaga fata ya murje saboda samun hutu da haka harna shirya a cikin wani dogon riga baki mai laushi mara hannu saidai rigan dinkishi har kasa ya sauka min xinkin wani mai shara shara dashi haka ta kasa na dan dira bakin gyale a kaina dake daure ba kitso.
Wanda duk da rashin kitso bai hanashi cikowa ba a lokacin don mai masu kyau da nake amfani dashi a kaina din.
Dakin yemisi na nufa don mu gaisa don tun shekaran jiya rabon da muga juna nan na samu bata nan don nayi nocking ba bude ba yasa na juya don komawa nawa dakin.
Amma kuma sai naji na gaji da zaman dakin ina bukatan in dan zaga cikin wurin in mike kafana na mike don fita haraban wajen.
Karaf muka hade da Ganiyat data fito itama daga nasu part din a cikin wani irin shigan da bai dace ba ace tayi shi don kawai tana a wurin da ba garin su ko kasanta ba don na tabbatar da ba zata taba shiga lagos a cikin wanan shigan ba ko dan yayanta ya tafine baya kusa dasu.
Saidai kuma naga ita ko ta damu da haka duk da kallon da yawan mutane suke mata a wurin baisa ta ji wani darr ba a lokacin muka hade ta dan rugumoni tana fadin a, a Sahiba ashe kina nan baku tafi tare da brother dina ba na dauka tare zakuyi tafiyan dashi ai.
No team din mu suna nan ba tare damu ya tafi ba sai naga tayi murmushi kafin ta kalloni da kyau tana fadin aiba dole saida team zaki tafi ba don ke yanzu ogan su ce.
Don me ba zakibi shi ba wai, ina cutship kukeyi a yanzu ke dashi kuna son ku fahinci juna a tsakanin kafin auren ku dashi don haka ba wani abu bane idan ya wuce dake ai a yau din don kowa yasan soyayya kukeyi a tsakanin ke dashi yanzu.
Jin kalamin ta yasa na dago da sauri na dan mata kallon mamaki ta gyada min kai alaman eh tare da fadin kada kibi zancen Alaja ko wasu can masu gulma.
Duk da nasan mommy mu bata son alakan ku kedashi tace ke din baki dace da brother ba sam, saidai ni banga rashin dacewan da mommy ke fadi ba a kanku nan.
Don gaskiya brother na ya iya zabe sosai wallahi saidai kawai abinda mommy din take fadin a kanki shine kawai yanzu matsala a wurin ku.
Kina da kyauki da kyau diri da tsari duk da ake nema a jikin mace, ta nunani da hannu tace komai naki alhamdullahi gaki da ilimin ki sosai don naji yayana na fadin kina da ilimi sosai a both side a kanki.
So ni banga laifin a nan ba dan ya zabeki a matsayin pience din shi da har zaisa ita Alaja tace wai bata yarda ya gabatar dake a matsayin wace zai aura ba a yanzu.
Tunda harke yake son ya aura don kina bashi tausayi da kuma kaunan ki da yakeyi right ta dan daga gira tare da kara kura min idon ta sai kuma ta nisa tana fadin.
At this age da kike ya kamata ki huta hakana sahiba, ke din baki cancanci wanan rayuwan wahalan ba kamar wani namiji ko yaushe kina kan aiki nasan abinda yayana ke kallo a gareki ke nan yanzu don nasan halin shi.
Amma mommy bata gane me yake nufi ba har tana fadin bata yarda ya kawo mata ke a matsayin sarakuwa ba ke mai juju ce a kanki.
So ni ban damu da duk abinda kike dashi ba a kai tunda yayana yana son ki a hakan da kike, meye matsalanta tunda bada ita zaki zauna ba.
Don nasan yayana nasan halin shi yana da ilimi da hankali da hangen nesa gashi da tausayin na kasa dashi duk da mahaifiyar mu bata son hakan tace halin daddy din mu da haka akai poisining din shi da goro a kauyen su.
Ni nasan idan ba yaga dacewan ki dashi ba daba zai taba yarda ya nuna mata haka ba don ita wanan dai yar yuhanus taso ya aura a yanzu amma ni sam batai min ba.
Shi kuma ya nuna mata kece ya yanke zai aura don haka yana da right da zai zabowa kanshi abinda zuciyar shi ke so a yanzu.
Amma taki ta gane hakan ita duk da shita samu da nice nan kingan ni da kawai zan fitar zancen tane in yi abinda nake so a rayuwana tunda ita tayi nata zamanin.
Na kallo ta cikin mamaki don na sandare a lokacin ina jin abinda ban taba zaton jin shi ba daga bakin ta itako ta dauka zancen nata yai min dadin saurarene a lokacin.
Taci gaba da fadin wai kin san me yasa mommy keson ko yaushe ta dinga zabawa brotherna mata ya aura ?
Kai na girgiza mata kamar zombi tace ba komai bane fa don ta dinga juya matar yadda take sone kawai ne daga ita har brother dina.
Kin san Mum nada wani hali da baida kyau ita burin ta a ko ita taga ta mallaki kowa da komai yadda takeso shine kawai dalilin ta nayi mai zaben matar da zai aura ko yaushe kada ta auro mai wace zatafi karfin ta.
Ke din nan tace akwai juju a kanki ba zata taba yarda yayana ya auri mace irin ki ba a cewanta don zaki dinga fada mai halin da kowa yake ciki da abinda zai faru ga rayuwan kowa don tun lokacin a lagos ta tsorace da lamarin ki.
Nan kan dan munafukin murmushi na sake a fuskana tace ai kin san matar shi ta farko itace ta nema mashi ita yar abokin daddy muce ita.
Haka ta dinga juya ta har mutuwar ta bata isa ta sake da mijin ta ba mommy bata bari sam yanzu ko da wuya ta kara samun irin ta kuma.
Haka bayan mutuwanta ta aura mashi wata a America saidai ita kan wanan mommy bata san ta fita wayau ba sosai don haka auren bai kai ko ina ba suka rabu a cikin wata shidda dayin auren nasu.
Don haka ba kowane yasan da zancen wanan auren nasa ba don ko Nigeria bamu tafi da ita an ganta ba don hakama wasu basu sanda auren ba .
You know what ta tambaye na girgiza kai tace ke mai sa,ace gaskiya kinsan abinda yasa nace hakan na dan kalleta sai tayi murmushi.
Tare da fadin idan na fada maki brother dina bai taba soyayya ba zaki yarda da hakan wallahi shiyasa nake son shi dake don abinda zuciyar shi ke sone ke.
Murmushi na sake kafin nace nima ina son ki saidai ina son ki sani tsakanina da yayan ki babu wani soyayya ko wani zance makamancin hakan gaskiya.
Aikine kawai ya hadamu tare bayan haka ba wanan abin da kile zato a tsakanin mu na zancem aure ko wani abu can.
Idan Alaja taso ta kwantar da hankalin ta ni aikine ya hadani da danta ba wani zancen soyayya ba can kawai dai ni taimakon juna mukeyi dani dashi.
Sai zancen juju da take fada saukin abin ba zuwa nayi na saya ba wanan kyautane daga Allah daya nufeni da hakan don haka ko ita bata wuce wanan matsalan ba a wurin Allah.
No kada ki damu ko ki dauki hakan da zafi sonda nake makine yasa har na fada maki sirin mu gaskiya .
Kada ki damu Ganiyat wanan ba wai na dauki abinda zafi bane kawai dai ina son Alaja ta gane cewa ni danta baya gabana don haka ta hada shi da d uk wace take so .
Ina fadin hakan na juya zuwa dakin da aka saukemu a cikin
sa da ace a Nigeria nake ko kusa da gida ranN babu abinda zai sa kara kwana .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
7️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAYYU , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Mun fita da tawagan mu don yo sayayyan tsaraba a lokacin na dan sawo abinda nake bukata a zuciyana daidai wani har umma da Ammar da yaran Abdul makwabcin mu don sune yan uwa na kusa a gareni yanzu da nake ji dasu.
Har lokacin sosai nake jin zafin zancen Ganiyat a zuciyana wanda ba ita nake jin zafi ba sai ogan mu da mahaifinyar su da suka dinkeni ta baibai ba gyara ba dalili zasu dora min wahala a kaina.
Ni sam ba zancen soyayya a zuciyana don banma taba jin son wani ba balle harkan soyayya ya wahalal dani haka yadda ta dauko min din.
Sai ranan da zamu tashi da rana ne an fitar da kayan mu gaba daya zuwa airport kowa yana mamakin irin kayan dana saya bance da kowa kala ba muka fito a nan muka hade da Alaja data fito don yin sallama damu gaba daya sun hadu a reception din wurin a lokacin ne muka fito ni da yemisi a karshe.
Tun kan mu karaso wurin mukai arba nida ita haka kawai naji gabana ya fadi abinda ban saba jiba ga kowaye na kalla kuwa bana jin komai ga mutum ni.
Amma haka na daure na karasa wurin har kusan inda take zaune muka gaida ita a cikin ladabi ta amsa ba yabo ba fallasa tana juyawa wurin jimoh taci gaba da fadin abinda suke fadi lokacin.
Mu zamu tafi na fada kai tsaye ina mikewa a lokacin Aisha Ganiyat ta iso wurin itama a cikin fara a aka shiga mata barka da fitowa tare da sallama .
Mun tsaya mun gaisa da ita kafin naji muryan Alaja na fadin munji dadi sosai da wanan ziyaran taku bisa ga aiyukan da kukaimuna shima kuma din ya biya kowan ku hakkin shi dake kanshi.
Me yuyuwa wasun ku daga wanan zuwan shine na karshe a garesu wasu kuma zasu iya dawowa da fatan ba zaku manta da halarcin dana ba a gare ku.
Don ba karamin kokarin bane daukan dawainiya haka ga mutum ga tallakawan shi harku shida kai tsaye don haka sai ku gudewa Allah ku kuma tsaya a matsayin ku na cin arziki a wurin mu kada mutum yace zai wuce gona da iri don yaga wuri.
Saboda hakane tun farko bana son mu rabi tallaka don su ko yaushe gani sukeyi kamar a banza mutum ya samu dukiyan shi .
Sai kaga sun rabi mutum sun shige mai jiki kwana biyu sai su bullo mashi da wani hali na daban sabanin yadda sukazo a cikin talauci ka mayar dasu mutane.
A lokacin zasu nuna ai dakai dasu din duk daya kuke a yanzu don haka duk maison aikin shi ya kiyaye ya tsaya a matsayin shi na dan aiki ko ba haka ba ?
Tana kallon Jimoh take karasa maganan kai haba mama i don't think a cikin mu akwai irin wa yan nan mutane don haka abar zancen nan zaifi.
Idan kasan kanka kasan wanine Felix ka bari kawai in fadi maganata don in akwai mai niyar yin hakan ya bari yemisi tace gaskiyane sai dai bana tsanmanin cewa akwai masu irin wanan halin a nan gaskiya.
Mu nan ai yarda da sanin ya kamata ne ya kawo mu wanan matsayin bawai on contrac muke ko wani abu ba so banga inda wanan zancem ya taso a cikin mu ba.
Aka sari irin tallakan nan anfi samun su a cikin students ko wasu masu zuwa yin safara na kasa da kasa sai kiga sun samu wani mai kudi ko wani kusan gwaunati sun makale suna ha,intar shi ai amma mu nan mun san meya kawo mu na fada.
Kai gaskiya kika fada Sahiba Ganiyat dake bayana ta amsa aka sari students haka suke sosai kuwa nace kwarai ma kuwa da sunga mai kudi zasu like su nace tundai mata koda ba kabilan su daya ba saboda kwadan abin duniya zasuma iya auren su don kawai su mallaki kudin shi suci su zama wani abu nan gaba su dawo suna raina mutane kamar da farko suma din abin tausayi bane.
Shiru kowa dake wurin yayi lokacin da nake wanan maganan ido rufe Abduhamid ne yazo ya kama hannuna yana fadin ai bakiji ba Sahiba