Showing 63001 words to 66000 words out of 382072 words

Chapter 22 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28346

da wanda ke kusa dani ba a lokacin.
Duk ina sake sake a cikin zuciyana na yadda zan samu in kubuta a garesu shine kawai abinda nake yi lokacin.
Don nasan idan Umma na bata ganin ba ranan zasu shiga wani hali na tashin hankali su dauka an sace nine.
Duk a yanzun din ma ba zan iya cewa ga wa yanda suka dauke ni ba ma don ban san abinda nayi masu ba suka sakani motar su haka.
Saidai idona yana kyankyashe ko dar din hawaye ban sake ba sai bin titin nake da kallo naji an jefo min tambaya da what is your mother's name ?
Na dan juyo a dan firgice na kalli mai maganan saida na dan kadu da ganin shi lokaci guda haka a gabana .
Shiru nayi don ko bindiga suka saka min ba zance ga sunan umman mu ba a rayuwana saida na bayan yace min u no hear he de asking u.
Nace a cikin e,e niya i don't no her realy name we de call her with umma by name.
Dan shiru ya biyo kafin yace which tribe are you nace, my mama told us we are hausa fulani by tribe.
Okay yace ya dan gyara zaman shi kafin ya sake fadin, from which state nace she no tell me that i only know we come from north side dat what she told me.
Yace so ke baki san sunan gari ku bama a rayuwan ki yana gyada kai na dan bishi da harara muka shiga go slow daya fara marance.
Allah maijin kan bayin sa a haka yana min tambayoyin ina bashi amsa daidai gwargodon sanina wani yazo ya daki motan nasu sai wanda ke gefena ya fita fada da maishi.
Ban tsaya jiran wani abuba na balle motar nima na fita na yanka a guje sai gani na bullo wani unguwa da ma ban taba shigan shi ba.
Haka na tare me keke na hau zuwa wani titin ina zuwa na fada motar da zai kaini unguwar dake kusa da namu do ba,a samun mota daga nan .
Har lokacin gabana sai faduwa yakeyi Allah yasa kudina yana jikina can na barsu da buhun maganina na gudo har nakai gida ina tunanen hadina dasu da suke min wanan tambayoyin haka.
Sukuku na shiga gida har umma taso gane hakam nasan in na fada mata ba zan kara shiga gariba ke nan kuma ni ba zan iya zama a gida ba saboda sabo da fitan da nayi a rayuwana.
Don haka na shatata mata karya na samu na kwanta tare da karyan kaina ke min ciwo a ranan ina faman tunanen inda zan canza ba tare dana kara haduwa da wanan mugun mutum da a yanzu yake son shiga rayuwata ba.
Washe gari din na dai fitane ba zance ga inda zani ba kawai na sakai na bar gida na dade a bakin titi kafin na nufi surulere da niyan yin wani sana,a acan.
Ance ido wa ka raina don Alh Nuhu ga hjy Addah ya sauke haushin danta don ya taso Nazifa gaba da uwarta har gida suka samu hjy.
Sai abinda ya raga mata nacin mutunci hjy sai hakkuri da take bashi kawai a lokacin bayan haka bata iya furta komai ba.
Har yana ikirarin ta kira danta yazo ya sake mashi ya don ba gadin gida ya kawo ta nan tayi masu ba a cewan shi.
Hjy dai ta rasa na fada sai ayi hakkuri take fada jin abin yayi yawa yasa hjy karima fitowa daga part din ta kamar da gaske.
Tana dan basu hakkuri tare da fadin haka yake tun farko ya kamata, ace sun sanda hakan don haka aikin shi ya gada.
Nan dai ya kare masifan shi tare da jawa hjy kunne akan suyiwa dan su fada shifa bai daukan haka ga diyan shi ko kadan.
Tun fitan shi hjy ta zauna tayi shiru abin duniya ya isheta akan wanan aure da ba koyi wasu watanni da shiba an fara samun baraka haka a tsakanin iyayyen auren kan yaran nasu.
Abinda kowa ke gudu ke nan a yanzu yasa ba wanda ke sha,awan hada wani alaka dashi kan aure da diyan shi itama din dai kaddaran haka ya jata har ta furta a gaban yar uwanta cewa tana son zabawa dan mata .
Budan bakin ta sai cewa tayi da hjy me zai hana ki zaba mashi a cikin yaran yaya Nuhu gasu nan kyawawa dasu mazan yanzu ai irin su suke so .
Yan boka kuma ga wayewa wanan zancen ne yar uwan hjy din ta dauka kafin hjy takai ga yanke shawara takai gidan dan uwansu din.
Matar shi uwargidan shi naji hakan ta dauki zancen da zafi takai gaban mijin su tare da kara gyara zancen tayi mai kwaskwarima har Alh din yaji shima yana sha,awan wanan hadin a tsakanin yaron da dayan yarshi .
A take hjy ke fadin ai zasu fi dacewa da Nazifa nake gani don gashi dama shima din wayayye ne kuma dan gata kamarta.
Don shi kadai ne da namiji a wurin mahaifin su a yanzu sai nake ganin kamar hadin nasu zai dace gaskiya.
Shima Alh Nuhun a lokaci wani irin shu,umin murmushi ya sake don akwai abinda yake bukata a wurin wanan yaton nan gaba sai yake ganin ai wanan dama ne a gareshi ya samu.
Wanan ne dalilin hadin auren su daya taso haka kai tsaye kuma Alh Nuhun ya matse aka daura shi a kam lokaci.
Tun bayan daya gano cewa yaron yana son ya subuce masu a karshe yasa daurin auren cikin dan kankanin lokaci kuma akayi haka.
Yawan son diyan shi dayasa a zuciyar shi yasa yanzu da Nazifa ta kawo karan mijin nata ya rufe ido yayi masu cin mutunci ya tafi.
Tafiyan shi keda suya hjy Asiya ta shigo gidan a nan ta samu hjy a cikin tashin hankali da farko hjy ta boyewa kanwar mijin nasu amma saiga hjy karima ta fito itake labarta mata duk abinda ya faru da shigowan dan uwan nasu kan zancen diyan su din.
Budan bakin hjy Asiya sai cewa tayi ai dama yaya Nuhu mutumin banza ne baida tunane sam a rayuwan shi idan idon sa ya rufe yana iya yiwa mutum komai kan yayan sa.
Da alama kan yadda yazo gidan nan ido rufe shi da matar sa da yar tasu a gabanta ya fadawa maman Nabila komai da yake son fada.
Hjy dai tana jin su bata iya tankasu ba sai maganan banza suke fada game da dan uwan nata tana sauraren su kawai don tasan dama irin daman nan suke jira su fada mata cikin zuciyar su game da auren na Abubakar.
Don tana sane da son hadin yarta da hjy Asiya din ke so tun da dadewa kuma har ta gabatar da zancen gaban dan ta yaki yarda.
Wanan wace irin yarinyace haka kamar yar daba yarinya tana abu kamar wata mai tabin hankali ?
Anya ma kuwa wanan ba wahalan banza yakeyi ba akanta ita din kuwa yar uwasu ce kodai watace can na daban yake wahalal da kanshi akanta yanzu.
Zama ya gyara yana fadin to amma kuma ai kamarsu ya baci da yan gidan don ma har ita wanan din idan ga gata harta zarta yaran gidan yake gani wurin yin kama da iyayyen su.
Don da ganin ta kaga yar fulanin asali da ita saidai da ta bude baki tayi magana zakafi danganta ta yar wani kabila da ba hausawa ba.
Koma dai wacece ita ya sha alwashin cewa zai taimaka masu tasan ko ita wacece tunda ta shigo rayuwan shi a yanzu.
Haka kawai dan interview din da yayi mata da wanda ya hada tun farkon haduwan su sai ya gane yarinyar tana son tasan mahaifan ta da jaharta.
Kai mutanen mu na arewa akwai kaskantar da kansu a irin wanan wuraren da ba, a san daranjan su ba.
Ta yaya macen bahaushi zata zube yara kamar haka tana yawo a cikin gari wai tana tallan magani da sunan neman kudi.
Dan murmushi ya sake don tuno da kayanta data sake a cikin motar su ta gudu ta barshi garesu in ba shirme ba nawa zata samu ga wa yan nan kayan da ya gani a cikin jakarta.
Shawara da Nazari yaci gaba dayi shi kadai a dakin yaga dacewan bibiyan case din ya zauna mai a zuciyar shi yace koma meye tsakanin yau da gobene zai shawo kan matsalam su don zai binciko har uwan yarinyar nan yaji idan yaran ma suna da mahaifi.
Gaban shine ya fadi ya dauko waya ya fara neman layin chuku yake sanar mai cewa zuwa gobe yake son su kama yarinyar nan suzo da ita don akwai tambayan da yake son masu ita da mahaifiyar ta.
ALIYU MAKAMA THE BOY zaune yake a hadeden gidan shi dake Apapa Alabi street dake tall get .
Yana zaune kasa don nan yake zaton zaiji dadin zama a wanan yanayin daya daure mai kai a yau don yau dai taron nasu ba,a watse shi da dadi ba.
Don shawara yasha bambam a tsakanin da abokan kasuwancin nasu dake da shawara daban daban kan yadda suke son su canza arkalar su a yanzu.
Shikan gaskiya a wanan katon yasan zasu raba hannun riga dasu don baida ra,ayin shiga wanan harkallan tasu tun farko.
Don bai fara wani kasuwanci ba irin na mahaifin shi saida ya dan koyi wasu abu daga halaiyar mahaifin nasa na gaskiya.
Shi tun farko dama bai yarda da wa yan nan kurayen kudin da yake tare dasu ba kuma bai taba zaton suna wanan haramtacen sana,an haka a cikin tafiyan su.
Hannu ya mika ya dauki cup din dake gaban shi cike da lemo tattaciya ya dan kurba ya mayar ya aje a inda ya dauka.
Don yadda yake jin kanshi a yau sai yaji kamar ya kurba ruwan guba ne a cikin sa lokacin don bacin rai.
Taya yayyafi zai masa haka ya boye mai abinda ya saka a cikin kayan shi har yayi kasadan fitar mai dashi tun daga turai har nan kasan ba tare daya san hakan ba sai yanzu da yaron shi ya tsegunta masa hakan da sukai mai.
Akarshe dai yasha alwashin zai masu yankan baya ta yadda zai iya fitar da kansa daga zargin da aka fara jefan shi dashi zai nuna masu shi din jan koma ne idan su kifaye ne masu kwakwalwa daskare.
Da wanan tunanen ya mike tsaye daga inda yake zaune din zuwa dakin kwanan shi don yau baijin fita ko ina don yadda yake jin kansa din.
Haba dole ashe yan sanda su nemesa haka ruwa a jallo don wanan abin yace a fili rai a bace dan guntun murmushi ya sake don shawaran da zuciyar shi ta zauna a kai lokacn.
A haka barci ya dauke shi mai nauyi har da mafalkin sun hade da yan sanda ana gumu dashi kan wanan case din daya zauna mai a rai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




ANA DARA GA , , , , , , , , , ,

1️⃣9️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,MIN, , , , , ,

PAID ONLINE NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA KADA KI RAINA GIRMAN ZUNUBI, , , , , , , ,


Adduan ku nake nema ga bakunan ku masu albarka yan uwa Allah ya yaye muna matsalolin mu ga baki daya dani daku duka amin.
Duk da ba wani sabo mai tsawo a tsakanin su har yanzu a matsayin su na ma,aurata a yanzu hakan bai hana ita ta kawar da komai ba a fili don irin tsananin son da take mashi har cikin zuciyarta ta nuna bata damu da yadda yake daure mata ba.
Yanzun ma dakin ta shigo a cikin kwaliyan ta tun bayan fitan ta daga dakin misalin karfe taran safe ta shiga nata dakin waya tayi da yar uwarta kuma aminiyar ta na gidan su tana bata labarin irin gwarzon min mijin da Allah ya hore mata daga sama irin wanda suke mafalkin samu ita da aminiyar nata a kullun.
Yau ma dai Nazifa bata barshi ba don itace mai neman shi bashi ke nemanta ba duk wanan a cikin wayen wata yake kuma take nuna hakan cikin rashin damuwa don tasan wata rana daina hakan zaiyi idan sun saba.
Aure irin na fulani asali sukeyi a family su wanda kwatsam zakaji an daura auren wance da wani ba tare da sun san juna ko sabiba a tsakanin su kuma a zauna lafiya baka taba jin bakin su ga hakan.
Ta shigo dakin a cikin takon izza da isa da gadara irin na yan gidan su da suke jin Naira na motsi a jikin su sun kuma tashi da wanan akidan kaf din su maza da matan su haka suke da nuna isar su acikin jinin su hakan yake masu.
Da dan fara,anta a fuskan ta taja tayi tsaye tana bin shi da kallo tare da tsuke fuskanta lokaci guda tana kallon shi a gadarance tace dashi.
Wanan jakar da kake hadawa fa na menene shi ta fada daga inda take tsaye fuska daure hakan yasa ya dago jin yadda tayi mai magana a cikin gadara yana kallon ta kai tsaye shima ya bata amsa da fadin tafiya zanyi yanzu.
Babu wani shakunta ko firgici a fuskan shi ya bata amsa kai tsaye kana ya juya yaci gaba da abinda yakeyi din.
Tashin hankali tace ina kuma zai tafi bayan Abban ta yace zai zauna da ita har na tsawon sati uku a gida yanzu ko sati daya bai rufe ba da dawowa har ya fara shirin wani tafiya can.
Zip din dan jakar tasa yaja ya mike gabanta yana kallon firgitatun idanun ta da suka juye tankar tana cikin maye a lokacin.
Cikin daurewa yace lafiya dai naga duk kin canza lokaci daya ko wani abune ya faru kuma ?
So nake na gaskanta wai da gaske tafiya zakayi kuma a yau din nan bayan Abba ya fada ma sai kayi sati uku tare damu a nan ko zakayi wani tafiya a yanzu.
Yayi murmushi tare da girgiza kanshi kadan da daga kafadan shi yace shi Abban naki ya fada maki hakan game dani ?
Wata karfafan ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin nasan kunyi hakan da Abba don Abba ba zai mun karya ba ka sani idan kuma kace zaka tafi yanzu zan daga waya na kirashi.
Ya saki murmushi yana duban ta kafin yace a wanan karon kan ya fada maki ba daidai ba don ni bamuyi hakan dashi ba.
Na shiga uku kana nufin ke nan Abba karya yayi min ko me ya Ababakar don haka maganan ka ke nufi a yanzu.
Anyway duk yadda kikace haka din ne nidai nasan ba mace nake ba balle har a kafa min doka inbishi dole ina fatan kin gane.
Ya sure jakar shi tare da wayoyin shi ya rataya yana fadin sai na dawo da sauri tayi kanshi a rude tana fadin.
Wait wallahi ba zaka tafi ka barni ba ni ban gane wanan irin rayuwan ba kullun ace mutum na hanyar tafiya ni kwata kwata sam ban ganewa hakan ba.
Hannu yasa ya jayeta a hanyar yayi ficewan shi rai bace bai ko kara waigo ta ba ya fice daga gidan yana jin wani iri a zuciyan shi a lokacin har zuwa lokacin da faruq yakai shi airport ya shiga jirgi suka daga.
Duk da yasan ranan babu jirgin lagos haka ya daure zuwa Abuja daga can ya fada na lagos din din kiran da chuku yayi mai na gagawa akan mu.
Yanzu kan sai ince faduwan gaba ya zama min jiki har na dan saba da hakan a rayuwa ganin ba abinda ya sameni tun ranan.
Haka na fita daga gida sai ras ras nake ji lokaci lokaci ina dauke da dan buhun sassake na ganyanyaki sai garin magani a kule.
Apapa na nufa kai tsaye inda nake zaton cabawa ga matan wurin don a gaskiya ina ciniki sosai a wanan erea din idan nakai kayana can.
Wata hamshakiyar mace ce ta fito daga motan ta tana kullewa zata shiga wani botiq nake mata talla ina fadin, madam come buy local medecine for pink,
Ta dan kalloni a yatsune taci gaba da tafiya nace madam try,am nd see ego work for u well,well sai taja ta tsaya wuri daya na sake fadin may try my medecine and see ma god go give u fine fine pikin i swear.
Da mamaki take kallona na sai ta karaso har inda nake din tace dani how d u no, dat i no born ? nd i de looking for dis medecinen ?
Emm, i just look at u and saw u problems in ur face na fada yadda masu magani ke fadi idan zasu sharota ga mutum.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login