Showing 324001 words to 327000 words out of 382072 words
dashi.
Washe gari kan da dawowab mu sallah aka daura tafiya zuwa makka na dauka tafiyan wasa ne ashe tafiyace mai nisa a tsakani dukda motocin lafiyayyune amma sai wani tsawon lokaci muka isa birnin makka din kusan tafiyan yini guda a hanya.
Duk na Annabi ya roka Allah ya karawa Annabi daraja dashi da sahabban sa da mu duka musulmi na duniya amin don tafiya mai nisa mu gamu a mota munga nisan tafiyan ballesu da a kafa sukai wanan tafiyan saman dabbobin su.
Ranan muka isa masalacin makka mukai dawafi dukko da tarin gajiyan da muka dauko din kamar yadda sunna ta koyar ayi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
9️⃣8️⃣Y, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR RA"UF, , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Sai asuba muka dawo masaukin mu kowa a cikin gajiya yake lokacin barci mukayi sosai a ranan don haka bamu samu zuwa masalaci ba sai asuba.
Karfe ukun dare muna cikin masalci nafila muka fara gabatarwa sai muka dora da dawafi mun gama daidai lokacin da aka fara kiran sallah asuba muka sake dauro alwala don jiran sallah asubahi.
Koda muka dawo masaukin mu dake wani hotel a kusa da masalacin ba nisa sosai da wurin wanka mukayi a daidai lokacin da room service ta shigo tana gaidamu wata bakar fatace matar.
Bayan mun gaisa take fadin itace mai kula da mu da duk wani bukatanmu har ranan da zamu bar garin muna tare da ita don haka idan wani abu ya shige muna kai mu nemeta zatayi muna bayani komai.
Nidai kallon ta kawai nakeyi har ta kare bayaninta tafita bayan t tambayi abinda za a kawo muna muci lokacin suka fada mata.
Ba a jima ba sai gata da irin abincin da suka bukata din ta kawo muna suke tambayana ko zanci abincin na dan bata fuska kafin nace da zan samu amala shi kawai nake son ci a lokacin.
Ga mamaki sai naji tace baida matsala suna da duk wani abincin da muke dashi a can gida nageria a nan ai in bata yan mintuna zata dawo.
Abu kamar wasa sai gata da abincin har miyar danyen ewedo da nama manyan yanka da ake mashi ta kawo min har dakin su umma saida sukaci wanan abincin.
Saidana koshi nak kafin na ture abincin a wani masalacin unguwan mukai sallah azahar har da la,asar sai dare zamu koma haram kamar yadda aka tsara muna komai.
Illa ranan jumma,a ne zamu jecan mu wuni sai dare zamu dawo namu masaukin mu huta hakan yake a tsare kowan mu ya sani kuma.
Yau bayan nayi barci na falka na shiga na dauro alwala nazo na tayar da sallah a dakin da muke din don ban sauka zuwa masalaci ba.
Bayan na idar na dauki wayana ina dubawa daga inda nake zaune saman sallaya duban startturs nakeyi indona ya sauka ga abinda ya Abubakar ya rubuta.
Masha Allah finaly my sister got marrige in madina Alhamdullilah wish you happy marrige life.
Sai Felix daya rubuta Suprase friend dina tayi aure bada saniba ba abin mamaki yana nuna alaman ba ruwan shi.
A a mamakine ya kamani a lokacin to kowa sai habaici akan aure akan suwa suke wanan maganan hakane ?
Idona ya sauka kan na Muniyat data rubuta komai ke da farko yana da karshe yar uwa muna maki fatan alheri da dacewa a gidan auren ki zamuyi missing dinki .
Muniyat kuma again akan zancen aure itama na fada ina dagowa a daidai lokacin da Faiza ta turo kofan ta shigo da kaya niki niki a hannun ta sunje sayayya sun dawo ke nan lokacin.
Tsayawa tayi tana kallon yanayina don a rude nake a lokacin na dan fita hayacina sai kuma na juyo na tsaya ina kallon ta kafin nace look Faiza tell me something you know ?
Akwai wanda zaiyi aure ne dama a cikin yan uwan ku kamar ya ta tambayeni nace wani abu naga ya Abubakar ya rubuta a wayan shi na bude ina nuna mata.
Saida ta dafani tace haba kila watace can yake tayawa murnan hakan kin san maza ai yadda suke.
Ban tsaya jiran wani abuba na kara nuna mata na felix din na nuna mata na muniya sai cewa tayi ai yanzu lokacin aure ne dama a Nigeria zai yuyu yazo masu lokaci gudane kuma.
Shigowan fatima dakin dauke da kaya itama yasa muka juyo muna kallon ta take fadin wai wai yau naga iyakar yawo ta fada saman gado lokacin faiza ta samu ta sulale ta shige ban daki itama.
Na rasa abinda zanyi lokacin sai kuma hankalina ya dauku kan Fatima dake nuna min irin tsaraban data sawowa yan dakin su da daddy sai mommy .
Tambayan ta nayi ina nasu anty Nabila da anty hauwa sai na yaran ya Abubakar ta dan dago kai ta kalleni kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru.
Look kiyi kokari ko yayane ki saya masu dan wani abu na fada na juya zuwa bangaren da nake zama nakai zaune tare da maida bayana a jikin gadon.
Ina tunanen rayuwan hausawa wanan halin wai dashi ake haihuwan sune ko dai daga sama suke tashi dashine kusan abinda ya jawowa family din daddy din mu matsala ke nan har yakai ga sunyi kisan shi da hannun su .
Anya kuwa zan iya aure a North side na fada irin wanan abubuwan yayi yawa sosai don dai namiji da wuya ya zauna da mata daya irin kudu koda sunyi biyun ba a zama wuri daya nake ganin sunayi don haka ba lalai bane dan uwa yasan halinda dan uwa yake ciki duk da akwai masu karamin karfi dake hadawa wuri daya saidai ban taba zama dasu nasan irin rayuwan da sukeyi ba suma a can.
Kofan dakin aka turo sisterce ta shigo dakin da alaman a gajiye take lokacin itama don tare suka fita dasu Faiza din.
Nayi matuwa a wancan shagon da muka fito karshe cabdijam Faiza dake yarfe hannun ta ta fada yanzu komawa zakiyi kuma gaskiya kuma ya mukhutar yana tayi muna fada wai mun daukeku munje yawo daku tun safe.
Au ashe yana nan ni tun a wurin dawafin farko ban sake ganin shi ba ai faiza ta fada sister din tace ina zai tafi keko ba a kare abinda ya kawomu ba duk da shi ai yaci riban umurah tunda gashi da galleliyar amarya a kusa dashi tana dan kama bakin ta.
Ba zata dagoki ba ai wanan Faiza ta fada saina kallota sai kuma sukayi shiru wai meye amfanin a dinga boyewa anty Sahiba wanan zancen tunda an daura aure ni gaskiya fada mata zanyi tunda dole tazo ta sani kuma taga mun munafunceta muma Fatima ta fada.
Jin ta ambaci sunana yasa na mayar da hankali a kansu don su a zaton su bana jin hausan da sukeyi sosai lokacin don haka bazan gane ko me suke fadi ba na kuma ji saidai in tsaya in mayar ne ba zan iya ba lokacin.
Fatima ki maimaita zancen ki na fada a cikin hausa duk suka kalloni sai takai zaune tana fadin dama dama wai ba wani abu bane fa anty Sahiba dama aure ki aka daura da wanan mutumin tun a madina.
Shine wai kada a bari ki sani ni kuma naga idan munyi hakan bamu kyauta maki ba gaskiya gara mu fada maki ki sani cewa su baffah sun daura maki aure zaifi.
Tunda aurene ba wani mugun abu ba da za ace kada a fada maki irin kallon da nake jafa mata harda dagowa a yadda nake yasa yarinyar tayi shiru ta kama bakinta lokacin.
Na nuna kaina nace ni aure No bakiji dai da kyau ba aure fa na fada ina mikewa tsaye a fusace kamar walkiya nakai kofa na tura dakin su umma.
Suna zaune abinci sukeci a lokacin yadda na fado dakin da yanayin sallamana yasa umma din dago kai da sauri ta kalleni .
Nima ita na kafe da ido tambaya suke lafiya kuwa ai kamar jira nakeyi nace abinda naji yarancan na fada yanzu gaskiyane ?
Ni Sahiba aka daurawa aure da wanda ban sani ba ko me kamar ya baki sanshi ba umma ta fada kafin na aje magana ta tana fadin.
Shi mukhatar din ne wanda baki sani ba kome ko kuma zamuyi maki abinda zai cutar dake kike gani haba mairo kada ki mata fada a yanzu haka mama kudidi ta fada tare da fadin ba a bugun mutum kuma a hanasa kuka don kusan da kwanan zancen haka dama gun yarinyar nan.
Tunda anyi abin nan ba,a shawarace ta aji ra,ayinta ba aka nuna mata isa da fin karfin iko aka aiwatar da hakan don haka yanzu lalashi ya dace da ita ba daga murya ba.
Sai kuma ta kallo ida nake tabar kallon umma din tana fadin zo yata ki zauna in fada maki yadda komai ya zo muna har muka aikata maki hakan bada sanin ki ba.
Kallon hannun nata nayi da take miko min kamar mugun abu ta rike kafin na juya da sauri zuwa dakin mu na fada saman gado lokaci guda batare da nasan abin yi ba a lokacin.
Don kuka ko wani abu yaki zuwa min a lokacin sai runtse idanuna da nayi kawai ina ganin duhu a zuciyana.
Shi mukhatar dinne baki sani ba ko me wanan kalamin na umma ne yake min yawo a kwakwalwana a lokacin .
Me haka ke nufi dayi don ban fahinta ba ban kuma yi da wani cewa na tashi aure ko ina neman miji ba balle har suce su zarga min aure bada sani ba .
Aure aure fa ina impossible na fada ina mikewa zaune da zuman fita daga dakin mama kudidi da mama Amina suka ahigo dakin namu.
Hankalin su a tashe mama Amina kamar yadda su faiza ke kiranta dashi don ni a wajena gwaggonace ita don mahaifinsu daya da mahaifina saidai ita wanda take aure mai karamin karfine shi don haka ba a jinta a cikin yan uwa hakama gwaggo kudidi duk dakin su daya tana auren wani malamin makarantane itama tana kuma koyarwa ita din saidai karfi bai kaiba haka.
Sahiba yata ta fada tun daga kofa ki natsu ki kwantar da hankalinki ki ki saurare mu munyi waya da ya Hamza yace yana shigowa yanzu don Allah ki natsu kin ji sahiba ta fada a tausashe.
Dan guntun murmushi mai kama da yake na sake a fuskana ina fadin haba mama why da zakuyi min haka why now why please sai lokacin naji hawaye ya zubo min.
Dukkan su biyu kasa daurewa sukayi suma hawayen suke sakewa a lokacin don yadda na nuna din ina mamaki ya nuna yanayin don mahaifina baya raye yasa sukai min hakan.
Sallaman su baffa hamza tare da umma yasa kowa ya juya garesu suke kallon su suka shigo dakin shima fuskan shi a kaina tun daga kofa ya fara fadin .
Haba haba Sahiba why now na dauka mun isa dake kina daukan mu kamar mahaifin ki kin san darajan mu a wuyan ki shiyasa har muka yanke wanan shawaran haka ai.
Tunda kin san dai ba zamu taba cutar dake ba kan hakan, yayi mamaki kwarai lokacin dana daga mai hannu a cikin wani irin yanayi ina .
Tare da fadin stop that nonsense talk uncle hamza da ace kai ubanane na gaskiya baza ka taba daura min aure da wanda kowa bai sani ba sai cikin dan lokaci.
Haka ba zaka taba aurawa diyar cikin kaba aure da bata sani ba yadda kai min din nan a yanzu Sahiba umma ta fada da karfi daga ida take tana matsowa gareni.
Ko gezau banyi ba na dago kai na kalli umma din da a yanzu itama komai ina ji zan iyayi kan wanan abinda sukai min din.
No kyaleta mairo na fahinci irin zafin da takeji a zuciyar ta a yanzu idan an matsa mata komai zata iyayi baffah Abdullahi ya fada a tausashe daga inda yake tsaye yana kallon abinda ke faruwa.
Nima abinda na fahinta ke nan ko kadan banji zafin zancen taba gareni baffah hamza ya fada daga inda yake ya fara takowa zuwa bakin gadon da nake zaune.
Ya kai zaune a kusa dani ya dafa kafadana yana fadin yaushe kika taba ganin uba zai iya cutawa yarshi sahiba ?
Idan kinyi tunane irin wanan baki kyauta ma son da kaunan da muke maki ba a yanzu mun barku kuda mahaifiyan ku a baya lokacin da bai dace ace mun barku ba.
Yanzu kuma kun dawo garemu muna fatan mu baku soyayyan da mahaifi ya dace yabawa yarshi ko irin kauna na uba da yarshi .
Da ace mukhatar mutumin banza ne ki sani mune mutane na farko da zamuki yarda dashi koda kuwa kece kika kawo muna shi a matsayin zabinki gareki idan bai muna ba ba zamu taba yarda ki aure shi ba.
Saidai ki sani cewa bamu maki wanan zabin a banza ba sahiba munyi hakane don mu nunawa duniya cewa ke din yar albarkace mai bin umurnin iyayye .
Duk da wayewan da mutane suke ganin kinyi a yanzu munyine mu nuna masu cewa wayen wanki da rashin tashin ki a cikin da bakiyi ba.
Bai hana kiwa na gaban ki biyayya yadda ya dace ba duk ko da irin abinda wasu yan uwan mu suka aikata ga mahaifin ki bai hana kiga girman mu a idon ki.
Kwarai kuwa sahiba mutane da yawa suna dauka yanzu baki kallon mu a iyayyen ki sun dauka kin watsar damu kamar yadda muka watsar dake a baya.
Saidai har gobe ba duka aka taru aka zama daya ba dole a cikin zuria akwai na gari akwai baragurbin don haka yanzu damu dake zamu taru mu kara dawo martaban gidan mu dana iyayyen mu da wasun mu suka zubar a baya a idon duniya.
Shiyasa da tsohuwan nan tazo muna da bukatan son hada iri a tsakanin ku dasu mu kuma mukaji nauyin ta nacewa mu nuna mata bamu yarda da hakan ba tunda duk abinda sukeyi suna yinshine don darajan mahaifin ki a idon su.
Sai mukaga idan bamuyi hakan ba wa zamu basu kamar yadda suka bukata tunda shi ammar dana mijine ba zancen aure a gareshi yanzu.
Kiyi hakkuri idan muyi maki ba daidai ba sahiba a madadina dana yan uwana harda mahaifiyan ki muna neman gafara akan hakan da mukai maki.
Jin maganan shi ta karshe yasa na sake wani irin kuka mai gumji wanda duk ke wurin saida yafitar da hawayen tausayi yadda nake fadin how can stay with this man ?
Ba tare da nasan komai daya shafi rayuwan shi ba ba wani nawa wanda yasanshi don ko ya Abubakar ina ganin bai sanshi ba haka kuma sai a yanzune kuka sanshi.
Wanan karon baffah Abdullahine yai magana yana fadin indan wanan ne daughter ki kwatar da hankakinki .
Bamu daura maki aure da mukhutar ba saida mukai bincike muma mai tsanani a gareshi muka gano shi mutumin arzikine mai mutunci da kima a idon jama, a.
Tun bamu san zamu hadu dashi ba ta sanadin ku muka san waye mukhatar a bakin jama, a don haka ba wani abu na muni da aka sanshi dashi gaskiya na zahiri.
Ya kare da fadin kodan yadda mahaifiyar shi ta nuna maki kauna da taki mahaifiyar da tayi na,am da wanan hadin kiyi hakkuri ki daure ki zauna dashi.
Kodan ki fitar damu kunyan yan uwan mu da suke shirin muna dariya a kanki sahiba ki daure ki zauna da wanan mutumin insha Allahu zakiyi alfahari dake da kowa naki kan wanan auren nan gaba.
Umma ta dawo ta saitin kaina tana fadi a cikin yarbacin in rufa mata asiri kada wanan zancen kukan da nakeyi ya fita har zancen ya koma kunnen su taji kunyar hakan tunda yan uwan ubana sunyi bugun gaba dani a yadda al,adansu yake.
Kuma basu bayar dani a wurin banza ba insha Allahu zanyi alfahari da wanan auren don Allah kada in yarda in nuna masu ban yarda da irin tsarinsu ba na fulani.
Haka dai tayi ta maganganu a cikin harshen yarbanci da baji sukeyi ba har dai na dan rage sautin kukan da nakeyi a lokacin .
Dukkan su sunyi shiru a lokacin da alaman rayukan su baida dadi kamar yadda nawa yake a ciki faiza da fatima kuma sun rakube a