Showing 231001 words to 234000 words out of 382072 words

Chapter 78 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28410

Sahiba ta kawo ke nan a raba gaban daddy ya bada ras ras haka na modibbo din yace ko bata nuna maka abinda muka gani a jug din rubuce bane ?
Yanzu dai take fada min an kawo mata gudunmawa sai ga wanan ya shigo shiya hana ta karasa fada min to bari a kawo kaga abinda muka gani a ciki na firgici.
Kai bamu wuri Daddy ya fada da cewa ya Abubakar ya fice ya basu falon sai baffa yace inafa zashi tunda wanan abin a yanzu ai ya shafi kowa a nan nake gani sai ga hjy karima ta shigo dauke da samfur din jug din dauke a hannun ta tana bude ledan tare da fadin.
Koba wanan ba ai Sahiba ta kashi kudi a nan wallahi shiko ya Abubakar sai fadi yake a zuciyar shi me sahiba ta aikatane yanzu ?
Mikawa mijin ki Baffa yace da hjy karima daidai mommy na shigowa falon ke nan suke wanan magana tana gaida su hannu kawai baffa ya daga mata yana nuna mata wurin zama .
Kafin ya juya yanacewa daddy ka duba daidai kasan inda akai rubutu zakaga me aka rubuta a jikin kofin nan na hannun ka
COURTESY, SAHIBA SAMBO NAMADI & AMMAR (YUSUF) SAMBO NAMADI, , , , , , , , , ,



ANA DARA GA , , , , , , , ,

6️⃣8️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MATIN, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋


Tafe yake cikin tako irin na mazan zamanin da suka san kansu a cikin isa da izza ba sai ya fadi koshi wani bane a wajen wayewan don kallo zaka mashi kawai hakan zai nuna kansa.
Ba komai yasashi cicika da shakan iska ba a yau sai zancensu da maminsa data tare shi dashi da safe na wai ga Nabila nan ita take son a hadasu don zumuncin ta da dan uwanta ya kara karfi a tsakanin su bayan na diyar gwaggo Asiya da muka sha biki a baya.
A cikin mamaki yake fadin wata Nabila dai mami yana tambaya a cikin mamaki don shi indai Nabilan daddy ce sam bata taba burgeshi ba yarinyar yaji mami din tace Nabila dai yar wurin yayana Aliyu mana daka sani ita nake nufi kasan dai mutane suna fadin dani take kama ko sosai kaima kasani ?
And so what mami don kuna kama ai bake din bace don ni bata taba burgeni ba a rayuwan duk da kaman da ake fadi ta dan kwaso ki.
Asalima dai ni ban taba jin kowan su yan dangin nan acikin zuciyata ba gaskiya mami na fada maki idan na tashi aure ni da kaina zan kawo maki yarinyar har gidan nan insha Allah amma ni ban faye son wanan aure na hadin da kuke son ayi ba garama idan kai ka gani kace kana son abinka.
Jin hakan mami tayo kanshi tayi mai kaca kaca a lokaci har hakan yasa ya guda ya dauki key din motarshi ya fita zuwa hotel yaje can ya kama daki ya wuni a ciki yana barcin shi hankali kwance don sanin gidan nasu yau da taron jamma, a.
Sai yanzu daya dawone kuma ya samu iyayyen nasu dukansu biyu kamar hankalin su a tashe yake don yaji mami dake rike da wani flasks a hannun ta tana juyawa take fadin gaskiya Alh abinnan yana da mamaki sosai amma haka kawai yaya sunan zaizo daya da nasu haka.
Idan ba diyan marigayi brother bane ta yaya zasu rubuta sunan shi da Sahiba Sambo namadi da Ammar sambo shima dayan ?
Jin sunan da mahaifiyar tasu ta kirane yasa ya dago kai yana kaiwa zaune saman kujera ya dago a cikin girgiza don jin abinda mami din ke fadi lokacin yana mata kallon mamaki.
Kasa hakkuri yayi yana fadin wace Sahiba dai kuke magana a kansune yanzun mami badai Sahiba dake lagos zaune da kaninta da mahaifiyan ta ba wace tayi zama nan garin gidan daddy shekarun baya ?
Wani kallo iyayyen nasa suka jefo mashi mai dauke da tambaya uwar tace kasan sune dama ?
Ya dan kada kai kafin yace kwarai kuwa sanima na sosai tun tana karama tana talla a lokacin nasanta a lagos.
Sai kuma yai shiru kan abu biyu daya tuna na farko kallon da iyayyen nasa suke mashi sai nabiyu yana son sanin akan me ake maganan su yanzune wai ?
Wai dama mami kin sansune wai ?
Ya tambaya a cikin mamaki kamar ya nasan sune kake min wanan tambayan hauka a yanzu kuma ?
Indai wace kasani ne abaya din itace yanzu ta bullo muna da wani zancen daya dade da shudewa a garemu cewa wai ita din diyar marigayine yayan mu dan gidan Baffa namadi marigayi ne ita.
Da wani irin mamaki a fuskan shi ya dan dago daga saman kujeran da yake kai zuwa bakin kujeran yana fadin .
mene mami kika fada Sahiba dai da kaninta diyan uncle dai dana sani wanda aka kashe aunguwar mu na farko sai kuma ya koma ya mayar da jikin shi saman kujera da kyau yana lumshe ido kafin can ya budesu yana fadin ?
No wander nake ganin yaron nan Abubakar ko yaushe tare dasu wani lokaci ashe yasan irin halakan dake tsakanin sune amma aini basu taba fada min komai ba kan hakan.
Kuma is hard inshaga lagos banje wurin su ba don haka kawai Allah ya hada jina dasu don suna da kirki sosai kuma suna ban tausayi abinda ya hadani dasu ke nan tun farko ba wai nasan kosu suwaye a gareku ba.
Zuwa lokacin da yake zancen wani irin kallo iyayyen nasa ke mashi a lokacin na mamakin jin abinda yake fada mai kama da almara a bakin shi.
Hakan bai dameshi ba yaci gaba da fadin ashe gaskiya duk haduwa uwar da yaran zasu tambayeni ke suce a gaidake sai na dauka kulawane hakan kawai suke nuna min ba tare daya damu da canjin yanayin mahaifiyar tasa ba a lokacin.
Wani irin kuka mami din ta fashe dashi tana fadin yanzu dama mairo tana raye ashe su yaya sun sani basu fada muna ba ?
Gara da bai fada ba din don karshe sanin ba zaiyi dadi ba a lokacin yanzu ko sunyi sake da alama dan zaki ya girma don ANA DARA GA DARE YAYI NE A YANZU KAN A WANAN GARIN.
Gidan Alh Nuhu da shima iyalan shi sun samu kyautan a wurin hjy karima don yan uwa masu ido da kwali ta rabawa kyautan a ranan ba, aba yaku bayi ba wai sai gaba.
A babban falon gidan matan shine da yaran su suna rike da gifts din a cikin jimame sai nanata sunan da maida magana kan yadda sunan yazo daya haka.
Don su abinda yasa basu yarda wasu nasu bane sunan Ammar din a sanin su ai ya dayace a lokacin kuma sunanta Fatima sunan mahaifiyar shi Sambo din ke nan aka sakawa yar ana kiranta da maamah.
Wanan kuma ance sahiba take da Amar shine ya dan rudasu a lokacin don haka basu yarda ba sunane kawai yazo daya dai amma ina aka samo Namadi din kuma shi suke muhawara a kai yazu.
Yo idan ita dince ma sai me tunda su basu kula da mutane ba mune zamu bisu haka kawai ai akace sun bar gida muguwa mata kawai duk a ance basu ma raye a yanzu ai.
Hjy salma bakanuwace mahaifiyar Nazifa matar ya Abubakar itace ke wanan zancen don a watse a bar maganan don sunyi har ya ishesu a lokacin ta gaji.
Guduwa fa tayi don sheri mutuwan mijin ki da yan kwanaki ki kwasa ki gudu ai ta gamu data Allah a can ta mutu a wullakance cikin duniya.
Inma yarce bata mutu ba ta dawo wa zai yarda da ita a yanzu tunda bata da shedan hakan kumama ai bata san komai ba yarinyar dake karama sosai a lokacin me zata karas a lokacin.
Gyaran muryan maigidan da yakeyi naku natsu gani tafe yasa wasu suka kwasa da gudu wasu kuma suka zauna a tsorace sun kasa gudu lokacin.
Sannu suka fara mai suna mikewa bai tsaya ba basujin kuma ya amsa masu ya shige zuwa part din shi kai tsaye.
Matan nasa ne suka kalli juna lokaci guda suna fadin kada dai ki fada masa wanan labarin yau son ba zamu sha da dadi ba gidan nan kin sani laifin daba namu ba ya shafemu mai suna Ladi din dake da girki tace waya aikeni aiken fadin mutuwan sarki ba a bakin Ladi ba kan.
Daddy ya gama karantawa ya dago kai yana kallon yan uwan haihuwan nasa da matan shi kafin yace tabbas nagani diyan Sambone ba karya sukayi ba .
Kafin ya dukar da kai na dan wani lokaci ya dago yana fadin ku koma dakunan ku wanan zancen mazane ai bai shafeku ba.
Baffa Abdullahi yace wai naga saboda su akace yar tazo wirin taton a yadda mata suke fada min kafin inzo don ma ban tsaya sauraren suba nayo nan.
Su tafi daga baya saji duk yadda akayi daddy ya fada cikin daure fuskan shi lokaci guda haka yasa suka mike hjy karima zuciyar ta na cike da tambayoyi akan hakan banda mommy da tasan komai wanan ranan takejiwa gashi ya fara tunkaran su a yau din nan .
Allah ya gani wanan hanin da taiwa yarinyar a ranan dama ya daga mata hankali sosai tunda gabanta ya fadi har lokacin take jin kanta a wani irin yanayi na daban.
Modibbo ma ya mike zai bi bayan mahaifan nasa yaji muryan uban na fadin ina kuma zaka ai sai ka tsaya kai masu bayani don shi ya san komai akan ganin su din can Ikko.
Ikko suke suka tambaya yace kwarai amma yanzu bansan a inda suke ba tun bayan da nasan ganin nasu ba alheri bane ga ahalin mu ga baki daya nasa ya mayar dasu a lokacin baki a laikum basan yadda akayi ta dawo ba yanz.
Baffa Abdullahi ya gyara zama yana fadin af tunda tasan gida me zai hana ta dawowa kuwa a yanzu ni a ganina tunda sune ai sai a nemesu kawai yanzu zaifi.
No ku bari ku gama da jama, a zaifi sauki modibbo ya fada a kausashe ga iyayyen ido tar ba tsoron komai a lokacin mahaifin ya kura mai idanu .
Ya mike yana fadin nasan ba zata sake dawowa ba ko wanan don Faiza da Amira da fatima tazo amma rayuwan ta yanzu ba a nan yake ba kuma.
Yai masu saida safe ya fita don shima hankalin shi a tashe yake lokacin da abinda ke shirin faruwa a ahalin su don yasan mutum dadaya ne kawai rigiman bai shafa ba a yanzu.
Ni kaina nasan na kashe kudi ba kadan ba don kudin dana taba din ina kokarin muna tanadine a lokacin amma ciki nayi karfin halin tabawa na labta wanan uban sayayya da nayi din na bukin.
Bin tarin kayan falon na sake yi da kallo ina fadin ba zanje wurin yinin bukin nan ba umma amma da dare zamu halarci dinner da za ayi don lokacin ne nasan yan family din maza da mata suna zaune wurin .
Ki dai bi a hankali don kowa ya rigaka kwana yana rigaka tashi sun fiki sanin ta kan duniya zasu iya yin abinda zai shafi lafiyan ki ko mutuncin ki kin sani.
Ban fito ba umma saida na nemi sa,ata a wurin Allah don haka Allah yana tare damu ko yaushe tunda bamu da hakkin su akan mu tace wanan haka yake Allah ya kara tsaya muna na amsa da amin.
Nasan Faiza ta zuba ido kuma zata kira waya bata sameni ba da yake ranan Friday ne ban jima a wurin aikin muba dana kammala komai a ranan a bangaren mu yanzu sai sammaci da za a turawa ko wanin su da dakatar da wa yanda zamu dakatar ne a wurin aikin ranan monday kawai ya rage muna kuma mun shirya yadda abi zai kasance a ranan.
Tun bayan magariba muka fara shiri don ban son zuwa da wuri sai wajajen goma na dare tare da duk abokan aikina na da muke tare na gaiyace su don haka su zasu mara min baya a wurin an kuma tsara ga yadda abin zai kasance damu tunda rana.
Yadda nake shiri haka aka wuni da kuskus a wanan wunin a gidaje da dama saidai abinda ke daure masu kai bai wuce tambayab kansu da sukeyi har in mune toshi dayanyaron fa dan waye ?
Gabin ban zoba yinin bukin sai aka fara share zancen wasu sun manta da maganan amma manya kan yana a cikin zukatan su fam.
Annoucement din da aka farane a wurin ya jawo hankalin mutane inda Bello ya samu sayen mc din da kudi mai yawa ya fara shelan sanar da mutane dake wurin zuwan mu hakan yaja hankalin duk hall din a lokaci guda.
Ga sanarwa ta musanman ga amarya da ango cewa kanwar ango kuma yaya ga Amarya miss Sahibat Sambo Namadi yar uwa ga ango da amarya ta iso wanan wurin da tawaganta daga lagos zasu shigo don taya amarya da ango murnan wanan ranan.
Ya Abubakar dake zaune shi da nazifa da sai ranan daddy yasa yaje ya dauko ta ba wani musu yaje gidan yayi sa, a Alh Nuhu baya gida ta biyoshi suka dawo har lokacin da suke zaune wurin dinne din ba wani sakewa a tsakanin su.
Yayi wani irin juyowa shi tsorin shi a lokacin kada inzo da yaran shia san suna wurina yaji amma bana shigowan mu ba don yasan a yanzu zan iya yin fiyema da hakan ai yasani a yanzu.
Cool music aka saka na hakan ya kara jawo hankalin mutanen wurin kowa na baza ido yaga wanan da aka fada an bude muna hanya sosai don aikin kudine bamu shigo ba saida aka shirya komai na shigan namu.
Mazan saye suke a cikin suit mata mu hudu matar Adnan muniya da yemisi saini sai mazan majiya karfi wurin su goma a bayan mu dauke da manyan sacks dake dankare da kayan rabo.
Kallo ya koma kanmu ina tsakiya sai walkiya nakeyi don bakin kayan dake jikina dare ne suna da shining dake sasu walkiya dinkin rigace daya matseni sharp din cock cola dina ya fito a fili kaina yasha ado shima ga sarka mai dan karen kyau a wuyana yana walkiya.
Murmushi na fara duk table din da yan uwan mu suke kamar an fada min sai na dagawa mutanen zaune hannu hakan kuma baisa na tsaya sai nufar inda amarya da ango suke nakeyi sauran na bina a baya.
Ganin na hau steps din inda suke zaune yasa suka mike Baby ta haroni da sauri ta fada saman jikina na dan bude idanun ta ina share mata fuska kafin inji muryan angon na fadin sannu da zuwa yar uwa na juyo gareshi har lokacin ina rugume da yarinyar a jikina tana dan kukan da bansan ko na meye ba a cikin harshen turanci nayi mai magana dashi kadai yaji menace ya danyi murmushi na nuna mai abokan aikina suka fara gaisawa dasu itama nasa ta gaisa da matan abin da muka shigo dashi yan matan dake tare damu da samar suka fara bi table table suna ajewa nan take wurin ya rude da hayani har muka samu gaba dayan mu muka sulale daga cikin wurin ta kofan baya ba bata lokaci muka bace wa kowa dake tare da mamaki.
Kuwa bayan yaki don an turo wai abi bayan mu saidai ko kuran motocin mu ba a gani ba har na masu rabon kayan da aka raba din wanda shi ya dauke hankalin mutane suka hargitsa wurin jakkane wani dauke da kayan wanka wani kuma kayan shayi wani riga mai hoton amarya da ango haka kayan sukazo launi launi duk abinda ka samu shine rabon ka.
Gara kafito kaji meke faruwa don abune daya shafi Sambo namu marigayi dai daka sani jin hakan ya tsaya sauran wayan har ya fito a gigice cikin dakin suke zayyana masa abinda ke faeuwa wai ashe tun jiya yarinyar ke barazana a ahalin mu amma an rasa wanda zai fada muna wanan zancen.
Kai Sani kaga yarinyar ne da idon ka wanda aka kira da sanin ya gyara zama yana fadin umm,humm bari yayace wallahi naganta buhari ma ya ganta kama da uban su sak saidai don ita mace ce kawai ta dan bambamta da uban amma namjin kan ai kakine kawai na Sambo din.
Kayan dake gabanshi ya kalla kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login