Showing 123001 words to 126000 words out of 382072 words
na kawowa umma sharawa akan mu dan fara sana,an drinks a dayan shagon mu huta zaman gida da mukeyi din.
Da farko umma bata yarda da shawarana ba wai sai modibbo yazo ta tambaye shi idan yin hakan ba zai zama laifi ba garemu.
Gashi shi kuma baizo din ba bai kira kuma wayan mu ba duk shidin ya aje muna waya a gidan don amfanin mu amma kuma sai gashi bai taba kiran mu ba har lokacin nan.
Ranan na taso daga barci na dawo falo ina zaune na umma ta fito tana fadin ni sana,an zamu fara ne mu dan rika fita waje ko banza mu fahinci yan unguwan nan da muke cikin sa idan muna fita.
Nadago ina fadin umma kardai tunena ya zama gaskiya mutanen nan hanyan rabuwa damu suka nema kada mu caza masu fitina a kansu suma.
Eh to nima ina tunanem hakan wani lokacin jin har modibbon shiru yanzu bai kara waiwayo mu a nan ba.
Koma sun guje mu sun muna gata a yanzu ai umma tunda sun muna sanadin sanin gida da yan uwan mu.
Ga wanan gidan da yanzu muke zaune a cikin sa duk da bamu san matsayin mu ba cikin gidan nan shin hanya aka daukan muna ko zaman su yakeyi muke zaune a ciki ?
Ban tsanmani a matsayin haya muke ciki duba ga abundaya fada ranan daya kawo mu gidan nan kawai mu zubawa sarautan Allah ido yanzu muga makomar mu nan gaba.
Sai kuma naga umma din tayi shiru ta shiga tunane nake fadin umma don in kawar da tunanen data fada yi din nace umma akwai kudin da zamu fara wanan sana,an ne a yanzu.
Akwai kudi mana a hannuna ko kin manta da kudaden dake ajiye a wurina tunda dadewa ne suna nan banyi komai da suba har yanzu.
Jin hakan hankalina ya kara kwantawa tashi umma tayi ta dauko kudin muka zauna muka kidaya ko wani umma ta dauresu daban ta ajiye su a wuri daya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
3️⃣7️⃣ BY, , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,EZZ
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA KADA MU RIKE JUNA DAKE, , , ,
Watan mu daya yanzu a logos ke nan ba wanda ya kara waiwayan mu daga fanin yan uwan mu don haka bamu san halin da suke ciki ba damu.
Muma bamu san halin da suke ciki ba a can ga karatun mu ya tsaya a lokacin shine babban abinda yafi damuna a lokacin .
Kudin hannun umma na karba naje company nayi odar drinks din dai danayi niyar mu sayar da nake ganin shine zai kawo muna samu a yanzu.
Zuwa yamma ko sun iso muna dashi an loda a cikin shagon dake kallon wajen gidan nike zama a shagon ina sayar da kayan don mun samu har fridge mun saya mun saka a ciki.
Haka kuma na budewa Amar dan qures karami na saida katin waya shima a nan yake zama a shagon shi din don yau da gobe bai bar komai ba tunda yaron ya fara girma a lokacin.
Haka nake wahalace wurin ganin rayuwa ta inganta muna ni da kaina na sama muna addimition muka koma makaranta.
Idan mun tafi umma muke bari a gida da yanzu mun saba da makwabta duk da ba ruwan wani da wani a can lagos din kowa tashi ta fidda shine a garin kowa ka gani yawanci kazo nazo ne ake zaune.
Nasha wuya wurin samun nawa addimition din don har saida na danganta da sarkin hausawan agege ya kama min na samu gurbin karatun a inda nake so.
Kamar yadda suma basu waiwaye mu ba hakane muma din muka gaji muka fitar dasu a cikin ran mu a yanzu.
Lokaci baida wuya ga Allah , har karatun mu yayi nisa a yanzu ga Allah ya tarfawa garin mu nono sana,an mu tana ja sosai.
Don haka bamu cikin damuwa ko fargaban abinda zamuci dama shine damuwa na a lokacin.
Sahiba kan ta canza a yanzu natsuwa da wayewa yazo min don girma ya fara kamawa nakai sha tara ga shekaru a yanzu.
Weekend ne don haka yau nake da burin shiga kasuwa in sayo abinci don bana wasa har in bar abinci ya fada a gidan.
Na shirya tsab dani na fito a shago na samu su umma nake fadin umma na fito zan shiga kasuwa zan duba abinda bamu dashi a gidan.
Umma tace dani kada in dade akwai alaman hadari yau nayi masu sallama na fita ba mota don haka na fara takawa zuwa inda nake tsamanin samun mota da sauki.
Lagos market nacewa dan Nape din yance inter nashiga muka dauki hanya akwai mutum daya dana samu a cikin motar dana shiga din ban damu da maishi ba nima na shiga motan na zauna a ciki.
Muyin nisa ga tafiya ina dan kallin gefen dama naji maishi yana kokarin yaba min wani bakin kyale a kaina.
Iya abinda na tuna ke nan a lokacin sai bude ido nayi na gan ni a tsakiyan mutane a kaina sun rike ni wurin kamar a gefen titi muke dasu.
A hankali nake dan tsuntar abinda mutanen wajan ke fadi suna cewa A, weee see d people when try to kill d girl with d ritular .
Ita kuma ashe akwai tsari a jikinta ta mayar dasu haka suna zaune tufafun jikin su duk ya yage fuskan su da gani sun sha duka na fitan arziki sosai.
Abin ne ya daure min kai bayan na daga kai na kalli gefen da mutanen suke zaune sai ga wani a cikin yarbanci ya miko min ruwa a gora yana fadin.
Karbi ruwa kisha Allah ya kareki yau da sun halakaki sai Allah ya baki sa,a sune suka halaka daga mai Nape din har shi wanda kuke baya zaune kunzo nan kun tsaya dasu kuna ta dabe duk kin yaga masu riguna kince sai sun rufa da wanan bakin kyalen da suke son yafa maki a jikin ki suka ki yarda su yafa shine aka samesu wurin nan akai masu dukan tsiya.
Hannu nakai saman dan kwagirin dana daura daga ciki na naji yana jikina na karbi ruwan na dauraye fuskana kawai dashi na mike tsaye.
Kasuwan da ban yarda na karasa ba ke nan koda suka tambayeni unguwar mu nace a agege nake suka kwashe zuwa can .
Naki yarda in fada masu inda nake don nasan lagos nasan mutanen cikin ta sosai da sherin su don haka nayi masu karyan unguwa suka kaini wani waje kusa da gidan sarkin zabarmawa nace nan ne unguwan mu din.
Wani lungu na samu na labe a ciki saida suka wuce na fito na bulla wani titi na samu mai adaidaita ya kaini gida.
Ban fadawa umma komai ba saidai a yanayin data ganni kawai tasan babu lafiya lokacin don haka ta biyo ni zuwa ciki tana tambayana ko lafiya ?
Lafiya kawai nace na shige na samu gadon dakinta na kwanta naja bargo na rufe jikina daku sai lokacin tsoro ya kamani kuma.
Ga lissafin ya Abubakar yau shekaran daya da watan shi shidda rabon shi damu gashi hankalin shi yana wurin mu amma kuma ya kasa yarda ya turo wani inda muke yana ganin yin hakan zaisa wani yaji a unguwar da muke zaune.
Ashe tun bayan sati biyu da kawo mu wanan gidan da yayi tafiya ya kamashi zuwa can ma,aikatan su don haka baya kasan ga baki daya shi .
Lokacin kan mu gaba dayan su muna dauka sun fita zancen mune yasa bamuji duriyan ko mutum dayan su ba kuma.
Gashi yasan a wanan lokacin abincin daya aje muna ya kare ga karatu yasan mun bar zancen shi ke nan yake tunane.
Yayi mamakin da mahaifin shi tun bayan tafiyan mu bai sake jin ya tuntubeshi da wani zancen mu ba kuma idan sunyi waya dashi.
Hakama mommy mahaifiyar su ba wanda ke tambayan shi ko yana da labarin mu tun da muka tafi sai hakan yake bashi mamaki sosai.
Allah ya gani yana jin tausayin wanan a halin sosai a zuciyan shi don yana ganin an danne muna hakkin mu sosai saboda son zuciya da tsoron wani yasa an kasa aiwatar da komai a kan hakan.
Ciwo nayi sosai da faruwan hakan sai daga baya nake fadawa umma abinda ya faru dani hankalin umma din ya tashi sosai don haka ta kwashe sai wurin wani malamin yarbawa da ta dade da sani a tsohon uguwar mu din .
Saidai mun samu tsohon yanzu ya dan tsufa sosai don haka ba lalai bane ya iya sheda ta sosai amma duk da hakan mun samu ya taimaka.
A cikin bayanin shi naji yana kiran mamiwota wai ni din aljannun ruwa nake tare dasu don haka yana da wuya aci galaba a kaina ai.
Sai gashi yana fadawa umma cewa mutanen da dukiyan mu yake wajen su har sukai sanadiyan zuwan mu nan yanzu wasun su susan muna raye hankalin su ya dan daga da hakan.
Jin ya fara irin wanan zancen na tashi na fice daga wurin zuwa dan waje kadan na zauna nan na dinga ganin irin manyan motocin da ake parkerwa a wajen masu kudi suna zuwa neman isimi na kuma gane ba shi kadai ke aiki a wajen ba.
Duk na gaji da zama ina jiran umma can kamar ance in dago idona wurin wata mota dake tsaye a wajen tun zuwan mu sai idona ya hango min wanda ban zata ba a lokacin.
Yana waya ya bada baya bai kallon gefen da nake zaune din haka yasa na mike da sauri a daidai lokacin da umma da Amir suka fito daga dan wurin da nake zaton mutumin babalawo ne shi ba Alfa bane kamar yadda umma tace dashi da zamu zo.
Dan karamin hijjab din dake kaina naja na gyara rufe fuskana da kyau dashi ta yadda ba za a gane ko wacece ba a lokacin gashi dole sai munbi inda yake zamu wuce.
Allah Allah nakeyi inga mun bar wajen don yanzu gaba daya ban son in kara ganin wani wanda na sani a wanan bangaren na mahaifan mu ga baki daya naji kawai na tsanesu ma a lokacin.
Bin mu yayi da kallon mamaki har wanda suke tare ya fito suka shiga mota hanyar da mukabi suka biyo ya hangomu mun tare mota zamu shiga.
Cema driver yayi ya bi bayan mu a hankali yaga inda zamu har suka biyo mu har gidan sai da sukaga umma tasa ke ta bude kofan ta kuma rike min hannu mun shiga suka bar unguwan namu.
Amma abinda mamaki yace a fili ga wanda suke tare din a kaduna ya barmu yanzun kuma ya ganmu a nan lagos har da gida me hakan ke nufi ke nan.
Zancen su da mahaifiyar shine ya dawo mashi a rai da tace mudin yayan abokin kawun shi ne dake lagos yayi tafiya mai dadewa yasa ya kwaso mu zuwa gidan daddy din kamar yadda daddy ya fada mata a lokacin.
Ke nan mahaifin namu ya dawo ne a yanzu ko kuwa kodai wani plan ne hakan dama aka shirya ne sai yaji hankalin shi sam bai kwanta ba ga zancen mu din haka kawai yaji yana son yasan wani abu game damu lokacin.
Bayan kwana biyu shi kadai yazo ya hango umma zaune a shagon ta tana sayar da kayan sanyi da rechage card ya dan dade tsaye kafin yaja motar shi ya tafi.
A wata yamma kuma weekend ne haka kawai yaji ai ya biyo titin namu ni ya fara hangowa tsaye da yaro a hannu na na fito daga shagon mu din yaji gaban shi ya fadi.
Yaron wata nerboug din muce na dauka don ina da son yara zata fita zuwa kasuwa ta bar yaron a wurin mu shine yake kuka na daukeshi a lokacin ya ganmu tare da yaron.
Tambayan kanshi yayi akan me ya damu da mutanen nan ne hakane kamar wasu yan uwan shi na jini ko yan uwan nasa ma yaushe rabon shi dasu yanzu.
Nikan zaman gida yayi yawa jiki bai saba hakan ba don dole kuma in dinga fita mu samu abinda zai kara tallafa muna ga karatun da mukeyi mai tsada don su can ba free education sai ka biya kudin komai.
Haka yasa na samu aikin dare yamma in taso goma na dare a wani babban shago dake unguwar mu din baida nisa da gidan mu sosai.
Idan na dawo daga school zan saka uniform din aikin wajen in tafi aiki sai dare nake dawowa sai dai aikin ya fara fita min rai saboda wani lokaci koda zan dawo hanya ba mutane da yawa sosai.
Shiyasa tun wanan abinda ya faru dani yanzu sai nake jin tsoron hawan Nape idan dare yayi yasa nake sin barin aiki a shagon.
Manyan mutane yan kwalisa masu ji da kansu maza da mata ke zuwa sayayya wanan shagon da nake aiki din wasu suyi muna alheri wasu kuma musha disgawa a wajen su duk da muma dai neman kudine ya kawomu shagon ba wani abu ba.
Gashi duk wanda ke shagon sai sun maka interview sun ga idan ka cancanci aiki dasu zasu daukeka aiki a wurin don tasare tsareb su saidai akwai kudi sosai yasa mutane ke neman aiki a wurin suyi.
Nima wata kawata yar school din muce ta kaini wurin da wasa sai ko suka daukeni gashi suna jin dadin aiki dani don ina jin yaruka kala kala a bakina don yawon gidan haya da mukayi a baya tun ina karama.
Yau ma duk da nagaji don mun dan wahala a makaranta hakan baisa na zauna na hutawa rayuwana ba a gida .
A gurguje na shirya zuwa aurin aikin duk da nasan na makara a lokacin zasu iya korana inyi hasaran kudin ranan ke nan.
Don sai sun cire a karshen wata a cikin abinda suke bamu din yasa ban son missing din ranan zuwa aikin don kada dan abinda suke bamu ya ragu.
Tun a kofa ganin ogan gaba daya a waje yasa na sha jinin jikina duk da yana magana da wani hakan bai hana in tsaya in gaida shi ba a wurin.
Ina fadin good day sir har ya amsa cikin daga hannu na dan wuce sai kuma naji yace dani wait wani lokaci kika zo aiki ke nan ?
Sorry sir na samu dealy ne daga school ban dawo da wuri ba sai yanzu na dawo na kara fadan sorry sir ina dukar da kai.
Sai ki koma yau baki da aiki ke nan ya fada yana kawar da kanshi gefe daya ka barta ta shiga tunda ta bada uzurin ta .
Kai na dago na kalli wanda ke maganan farine sosai mai zubin iyamurai ga dan saje a fuskan shi yana saye a cikin suit baka data karbi jikin shi.
Saidai kana kallon shi kasan boko ya ratsa jikin shi da yawa haka wayewa sai yake min zubi da yanayin wani wanda na sani.
Ga shekaru kuma baikai ya Abubakar ba ko ya mustapha saidai do jin dadi da samun wuri zai iya kaisu ga gani idan mutum yayi mashi kallon tsoro.
Thank u sir na fada ba tare dana tsaya jiran komai ba nashige daga ciki na barsu a wurin a gurguje na fara aikina don na samu har an kawo wata ta a madadina ta tsare bangaren da nake aikin ko.
Tare suka shigo da ogan mu suna zagayawa na kara gaidasu ban kula ba ko sun karba min don dai naci gaba da zagaya wurin da nake din ina duban masu shige da fice a gefen wurin.
Sun danyi tako baikai biyu ba wayan shine yayi kara yaja ya tsaya yana daukan wayan tare da fadin hello Didi,
Tun suna magana da turanci har suka koma kamar larabci daga inda nake zaune na saka earpieces a kunne na ina bitan karatuna don ban yarda na yarda karatun dana samu a zaman mu na kaduna ba.
Na hango wasu sun zo part dina suna duba kayan zasu tafi basu mayar da kyau ba nake fadin zaku jawa mutane hasara ga banza kuma ba saye zakuyi ba ku kuja min matsala ga mutanen nan da basu san kaddara ba.
Ya juyo ya tsaya yana kallona a cikin mamaki na gyara kayan ina dan kara kakabesu na koma inda muke zama na zauna kafin custurmers su shigo wurin ga hasken a ko ina ya haske wurin ga baki daya ba zakace darene ba a lokacin do haka kalan wurin ya bada ma,ana sosai.
Mun saba ganin irin su yan kwalisa suna shigowa shagon don haka ban damu da isan