Showing 288001 words to 291000 words out of 382072 words

Chapter 97 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28340

ta fada jikin umma dake zaune duk da ba,a bamu wajen zama ba munyiwa kan mu matsugunni mu.
Su waye wa yan nan kuma ta fada tana kallon faiza don son jin bayanin mu bakine sun zo gaida yayane da jikin shi.
A, a umma so you're on the way ? I don't know that you people a coming yanzun nan na fita zan tafi office din mu wani aiki dama.
Kafin ya juya akan mu yana fadin Sahiba you are welcome Yusuf how far now ta sake juyowa da kyau ta zuba min ido don jin sunan daya ambata a lokacin.
Wai wanan din ce
Sahiba dama ta fada tana watso min wani kallon tsana da nima na bita dashi jin ta ambaci sunana ya jiki mukai mashi kafin ya juya yana fadin ina matar nan mai aiki sa a kawo masu abin sha mana yana kallon matar nasa.
Wace tayi kamar bata jishi ba lokacin umma tace a, a abarshi dai wallahi a koshe muke mu kan ba kishi ba yunwa an gode ta fada tana murmushi a fuskanta tare da dan shafan yarsu data kwanta mata a jiki.
Uban yace kinga mama ko Aimana sai umma tace ashe bata manta damu gaba dayan su sun shedamu hakan ya bani mamaki sosai wallahi.
Wani kallon mamaki takewa kowa na falon na yadda muka san yaran nata haka bata da labarin komai ita shine ya daure mata kai hakan.
Muna cikin magana ya bamu labarin rashin lafiyan nasa yaran anty Amarya suka shigo gidan da sallaman su ai nan na manta da ita muka buge da hira sosai dasu kamar a baya.
Mikewa mukayi zuwa waje don sunce suna son muyi hotuna a tare dasu kafin in tafi har umma suka fito suka sakemu a wajen hakan ya hana muyi sallama da ita har muka tafi bayan nayiwa su Fatiman har Faiza alheri daga jakkana muka kuma sauke tsaraban da mukazowa yaran ya modibbo din dashi.
Mun isa Yola kamar yadda aka shirya cewa zasu zo su taremu daga gidan babban wan su umma dake cikin garin yola yanzu zaune.
A wanan ranan na sheda ashe muna da yan uwa raye a duniya irin so da kaunan da suka nunawa ganin mu don mun samu gidan nasa a cike da yan uwa da sukaji zuwan mu sukazo don ganin umma din damu.
Nan kuma aka zauna ana jajanta mata abinda ya faru tare da adduan samun nasara a kansu sun dai sha tsina da mugun fata a wurin dangin umma din.
Kwanan mu uku a yola cikin jin dadi da nuna muna karamci muka nufi kauyen su umma din kai tsaye a ruggan su mukaya da zango .
Nan ma munga kauna da so a wurin su sosai anan na sheda idan asalin kyaumu ya fito duk zaka gansu zubin daya dogaye farare masu kyau da zubin filanin farko dasu har saika rantse su din wasu yare ne na waje.
Saukin abin dai nama ne don haka ina cin abinda aka sarafa muna naman dashi ba wani kyama amma duk abinda ya danganci abin ruwane shi ko menene kuwa ko kamshin naji zan bar wurin idan ba Allah ya gyara ba har amai nakan yi wani lokaci.
Idanuwana sukan juye su canza kalla zuwa ja jajir kaina ya dinga ciwo tsawon wani lokaci wanan yasa a yanzu dana fara wayau nake kiyayyewa bana yarda da abinda zai jawo min matsala kuma.
Saidai ashe wai haka yan uwan mu na gefen umma dana gefen mahaifiyat mahaifina suke dayawa din su suma basa cin abin ruwa saidai ba duka ba suma don akwai irin su umma da kan danci itama din ba damun ta yayi ba sosai.
Tsaraba sosai mukaje dashi kwanan mu biyu a wurin su kuma muka kara gaba zuwa wajen dangin mahaifin mu ta fanin mahaifiyar shi.
Naji dadin wanan tafiyan na kuma san muna da gata ashe a duniya mmuma kuma muna da yan uwa na jini dake matukar son mu a duniya.
Nakan ji manyan su na fadin kamata sak da wace ta haifi mahaifiyar Abban mu da tsayina da komai wai har yatsun kafa nata ne na kwaso suke fadi.
Ana gobe zamu shiga kotu muka koma laduna badon mun so rabuwa dasu ba suma din hakan tare da muna alkawarin wasun su zasuzo har idan muke su gane mu suma.
Tunda muka shiga kaduna barci nakeyi ban falka ba sai yamma lis don gajiya da kewan yan uwa ina faman rayawa a raina cewa yanzu kan naga inda yan uwa suke masu son mu.
Bayan sallan magariba ne muna zaune falon gidan wayan umma yai kara ya Abubakarne ya kirata yana tambaya ko mjn dawo ko muna yola din.
Muna cikin kaduna dazun nan da yamma muka dawo umma ta bashi amsa yayi muna sannu da zuwa yake fadin.
Gobe insha Allahu za a shiga kotu daddy ma yana nan ya dawo sati daya ke nan watau tun tafiyan mu yola ya dawo shima kasan.
Washe gari mun dan so mu makara a lokacin don zuwan kotu har mutane sun dan fara kus kus akan rashin halarta mu din sai gamu.
Hakkuri lauyan mu ya bada aka fara shari,a yadda ya dace ayi din inda alkali ya nemi daddy daya ba umurni dawowa kasan don tuhuman da ake masa yazo ya kare kan shi a kotun.
Dadi ya fito cikin kamala da shiga na jallabiya mai ruwan madara sai yar hular dara ja akanshi daya saka don kare mutuncin shi duk wanda ke zaune ya bishi da kallo.
Kamar yadda akewa kowa tambaya a kotun haka akaiwa daddy din shima tambayan bayan an karanto mashi laifin da ake tuhumar su dashi din.
Ya dan girgiza kai na dan lokaci saida ya danyi dan shiru irin na manya kafin ya dago kanshi yana fadin zan bayar da sheda akan abindana sani iya gwargwado in Allah ya yarda.
Kamar yadda kowa ya sani marigayin abokinane sosai kuma kanina aminina haka muka taso dashi a gidan mu yai rabin rayuwan shi kaf kafin ni na fara aiki shi kuma saboda kwazon shi gwautin jaha a lokacin ta turashi karatu waje.
Bayan ya kammala karatun kuma yazo ya samu aiki a can sai rayuwan shi kancan kaf ya koma can waje saidai kaf din mu yan family din mu dani yafi yarda .
Don haka yana turo kudi nan ina masa tanadi kamar yadda kowa ya samu akeyi har wani tafiya da yayi ya samo wasu mahaukatan kudi ya turo na sai mai filaye manya kudu uku masu girma.
Wanan ne abinda ya fara jawo muna matsala a tsakanin mu nidashi don yace zai yi manyan gidajen mai irin na waje na nuna mashi ba haka ba komai a sannu ake binsa.
Duba ga yadda yake matashi a lokacin ko aure baiyi ba tun daga wanan lokacin ya fita zancen filin kuma bai kara min maganan shi ba har sai bayan yayi aure har matar ta haihune yayi wani fita sai gashi wanan fitan ya dawo da mahaukacin kudi irin na wancan shekarun.
Sai a lokacin ne ya samu waiwayan filayen shi ni kuma duba ga yadda muke dashi lokacin har na taba filin nayi amfani dashi wurin nawa bukatan.
Na nuna mashi lokacin kwara daya ya rage a cikin filayen kuma shine mafi girman aka a ciki take ya nuna min nacin ranshi ya dai wuce a hasale abinda bai taba min ba.
Nima nasan ban kyauta ba gaskiya sai hakan ya dan fara jawo matsala a tsakanin mu dashi ya daina kulani ya daina dai yi dani kamar farko.
Wata rana ina maiduguri nazo weekend da yamma yan uwan haihuwan shi su Nuhu suka sameni bayan mun gaisane suke fada min ai sunzone su kara ji a bakina wai ashe Sambo shike da wanan katon filin na hanyan fita gari nace eh ai wanan bashi kadai bane ma akwai wasu filayen bayan wanan kuma manya ne suma .
Nan muka buge da fira dasu abinka da dan uwa nan nake ta labarta masu irin dukiyan daya samu da abubuwan da yake dashi.
Allah ya gani ban fada don wani abu ba lokacin amma bayan kwana biyu sai ga Sambo din yazo min rai bace yana fadin bai taba zaton zan masa hakan ba.
Don me zai bani amana kuma inci inje ina fadan duk wani siri nasa ga jama, a a lokacin dai dukkan mu kurciya yaci mu don nan muka rabu baram baram dashi kowa na fadawa dan uwa bakar magana duk irin hakkurin shi ranan bai raga min ba.
Bayan munyi hakan dashine da kwana biyu muka wayi gari an kashe shi saidai amatsayina na dan sanda binciken farko na gano cewa yan uwane suka halakashi lokacin.
Nayi yunkurin yin wani abu sai ga batar matan shi abinda ya kara daga hankalin kowa na ahalin mu ke nan kuma .
Shiru har wata uku babu labarin ta sai ranan sukazo suka sameni da zancen tunda Sambo ya rasu iyalin shi kuma sun bata abinda zaifi a raba dukiyan shi kawai tunda dukiya bai azuwa tunda ba, a san ranan dawowan iyalin shi kaduna.
Haka yasa na kara zargin su na kirasu a sirce nayi masu magana sai suka so su mussanta hakan karshe dai da sukaga na gane gaskiya duk da basu fito filin sun amsa laifin su ba lokacin.
Sai cewa sukayi in ma son dukiyan shi dake hannunane banson in bayar in tafi da dukiyan in rike amma sai na basu wanan filin ko kuma dukkan mu a tuhumeni nima.
Inda ni kuma naga hakan ba karamin banan suna bane a wurina yasa naja bakina nayi shiru a lokacin tare da fatan duk lokacin da wanan case din zai taso ya kasance ina raye a yishi .
Don a yadda na kula Nuhu dai gashi nan tsaye idan bai ci arzikin nan na Sambo ba zai iya samun matsala lokacin don yadda yabi ya zare kan abinda dan uwan nasu ya bari kuma a yanzu bashi da wanda zaici sai su din don diya mace ce ya bari a duniya a zaton mu.
Sai dai duk da rufe wanan case lokaci zuwa lokaci nakan tuno da wanan nauyin dake saman kan mu don haka na samu lokaci na ware daga cikin dukiyana iya abinda nake ganin nasune a wurina na debe masu shi.
Amma kuma daga baya sai kuma na fara wasu harkala da kudin sai dai ban yarda na hadasu da nawa ba har lokacin .
Kwatsam wata rana saiga iyalan marigayin sun sauka a gidana dana daya gano su a lagos yazo dasu.
Nayi iya kokarina wajen yin shawara da zuciyana in baiyana din na boyesu ga kowa a lokacin suma kuma din na hanesu da baiyana kansu ga kowa.
Nayi kokari a lokacin naga na hada kan dukiyan su in basu saidai na kasa hakan a wurina gashi lokacin na fahinci su Alh nuhu kamar zasu gane su kashe su ni kuma bazan so in zama sanadin hakan a garesu ba lokacin.
Yasa na umurci dana da na shirya wa plan cewa ya kwashesu ya mayar can lagos din har zuwa lokacin dani zan shirya fitar masu da dukiyan su in danka masu a hannun su .
Sai kuma rai da dukiya wanan yasa na sha,afa da zancen su gaba daya don kudin da yanzu nake juyawa sai ga wanan zancen ya taso don haka naaan za a kawo kaina yasa na tsaya saida na cire masu komai nasu na dawo da shirin danka masu abin su a yanzu.
Humm, umma dake gefena ta fada tana dan jijiga kafanta a cikin takaicin jin wanan cin amanan da tasan duk shirin magana ce kawai don ya kare kan shi a yanzu daga tuhuma.
Saukin shi dai dayane shine baya cikin kisan amma makushe dukiyan harda shine don ai bai taba fadawa kowa wanan zancen ba haka sai yau.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

8️⃣6️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,AKHIR , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Taben da lauyan mu yayine ya dawo da hankalin kowa a kotun aka dan rage surutun da akeyi a lokacin kowa na fadin ra,ayin shi.
Kallon su akeyi yana kallon daddy yana murmushi har ya isa wurin shi ya tsaya yana dan jijiga kai.
Ya kalli daddy din yace well Alh kotu taji bayanin ka a yanzu saidai idan ba damuwa akwai dan tambayoyin da nake son in maka.
Yana fadi fuskan shi a wurin alkalin dake zaune yana dan rubutu a lokacin a farar takarda daya dauke mai hankali ya gyada kai alaman an baka.
Ya dubi Alh yace Alh a cikin bayanin ka naji kace kun sami sabani da marigayin akan wani abu nasa lokacin ko zaka iya fadawa kotu abinda ya jawo maku wanan matsalan.
Sai a lokacin ne aka san ya shigo dame kareshi a kotun ya daga yana gabatar da kanshi tare da fadin wanan tambayan ai an wuce wurin tunda yayi bayani ko .
Alkali ya daga mai hannu alaman ya bari a tambayi daddy din ya koma ya zauna shi kuma yaci gaba da kallon daddy din yana sauraren shi.
Daddy ya gyara tsayi yana fadin eh to a lokacin dai daya ban ajiyan ya kawo min shawara naji rejecting to ba wani abu bane illa nayi amfani da kudin wurin gina wani wuri a garin lagos a lokacin.
Inda ya nuna min don me zan masa hakan bayan ga kudirin shi nason ya gina gidajen mai shine burin shi.
To mu a nan marigayin yayi bayani a takardan sirin shi cewa ka bashi mamaki don ka dauki kudin shi da yake da buri ka gina babban hotel a garin ikko na kanka dashi.
Haka abin yake ko kuma kana da abin fadi a nan dan murmushi daddy ya sake a fuskan shi yace shine dalilin fadan namu dashi.
Dama nasan idan na fada mai hotel zan gina don yafi wanan burin nasa da make ganin shirmene a lokacin ba zai taba yarda da hakan ba.
Don shine ma ya nuna min baida ra,ayin gina hotel a rayuwan shi don irin abubuwan da za a aikata a ciki.
Amma sai naga rashin wayaushi nabi baya nina gina a kashin kaina sai wanan yayi matukar batawa shi sambo din rai sosai har yakai ga furta min kalami da fadin.
Brother kana ganin kamar ka cuceni ne ni kadai to kasani kanka ka cuta da wanan abin dakai min don bani kadai ka cuta da hakan ba.
Fadin hakan sai naji raina ya baci dashi nace yau ni kake fadawa haka sambo akan dukiyan ka sai ya kalleni yayi murmushi bayan ya mike yana fadin.
Ka bani mamaki sosai brother ban taba zaton kai zaka iya yin wanan abin na sonkai ba gareni .
Anan lauyan ya tare shi da fadin sai kace dashi me kai kuma kallon lauyan daddy yayi kafin yace naji haushi sosai a lokacin yasa nace dashi akan kudin da bamu tabbatar da ida ka samoshi ba har kake kokatin min rashin kunya.
Idan bakai hankali ba sai na saka an bincike ka inda kake samun dukiyan ka haka sai me kuma ya baka amsa lauyan ya tambaya ?
Daddy yayi shiru idan ba laifi zan fadi abinda marigayin yace maka lokacin ya kalli alkali ya daga mai kai alama go ahead gareshi.
Kaika sani duk inda haram yake bana wajen kada kudi ko dukiya ya rufe ma ido ka dawo kana dana sanin hakan a baya.
Hakane ko Alh lauyan ya tambayi daddy din shiru daddy yayi yana fadin yaron nan abinda yai min ke nan lalai hurda damai ilimi yana da wahalan fahinta yafada a ranshi.
Na fada daidai ko lauyan ya tambaye shi sai kai kuma kaji haushin mayar maka da hakan da yayi yasa ka dauki alkawarin baiyanawa yan uwan shi duk sirin shi daka sani ko.
Wanan ke nan ya wuce wurin ya koma fadin sai zance na biyu shine ko Alh zai fadawa koto inda wanan dukiyan na baya suke yanzu bayan mutuwan mai ita ?
Eh to gaskiya zance ni kadai nasan inda kudin sambo yake a lokacin amma sanin kowa yasan ya dawo da wani abu mai muhinmanci wanan tafiyan.
Shine na fadama sun sameni a gida kan wanan kudin muka bincika kudin suna nan yadda ya ajesu a bankin shi .
To a wanan lokacin muka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login