Showing 30001 words to 33000 words out of 382072 words
wuce sun bar gidan amma kowa na waje cirko cirko ana faman mayar da magana kan zancen.
Dukawa nayi naci gaba da wankin kayan da nakeyi daga can bayana naji muryan wale na fadi.
U sahiba wen wan trobe for ur self thank god that day d man no kill u sai kowa ya kallo ni na daga ina fadi.
Wale, i beg , me i no wan wahala wooo, mey u no comfire me wit that men sha bi i no dem before ?
De fall me down, nd my food dont fawl, nayi i say mey de pay, nd de pay me , de give me anoda food ogwa ? witin consen me with dem again ?
Maman shi tace dashi, wale may u no cary ur wahala come rich me shabi u no say dat mater no be smol case wooo .
Uwar ta kwaba shi tana koran shi daga gidan ya fita yana wani irin tako na yan iska tabi shi tana zagi.
Na dauki kayan dana wanke na nufi wurin da muke shayi a nan idona yakai kan wayan dake kasan yashe bayan wani kwandon roba na kayan iya bisi dake kusa da dakin mu.
Na faki idon mutane na duka na dauka na tura a aljihun dan rigan dake jikina da sauri na karasa shanyin na koma dakin mu har lokacin umma na waje na bi wayan da kallon mamaki ni kadai a dakin.
Ko da ban san waya ba nasan cewa wanan wayan babbace kasancewa umma na waje har lokcin bata shigo dakin ba.
Yasa na fita don zuwa in debo ruwa a inda muke diban ruwa fitana yayi daidai da sake dawowan yan sandan gidan.
Suka zo neman wayan duk an tara mazan gidan da yan matasan mata kan wayan sai binciken su akeyi kan wayan.
Don ya nuna a cikin gidan wayan yake kuma yanzu sunzo signal bai nuna wayan na gidan ba duk an bincika ba a samu wayan ba .
Inda Allah ya taimakeni shine ba wanda ya kawo ranahi a kaina cewa wayan yana hannu na a gidan har yan sandan suka tafi don ya nuna an bar gidan da wayan lokacin.
Hankalin shi ya tashi matuka na rashin ganin wayan nasa daya fado gurin mayarwa a aljihu bayan sun gama waya an fada mashi wanda suka zo nema baya gidan ya bar kasan ga baki daya.
Yabi ta ghana ya fita har yabar kasan ghana din a lokacin shine dalilin da suka bar yan gidan mu din suka koma bincike ga landlord din gidan ta yaya ya bashi gida haya a ina kuma suka hadu dashi har ya bashi hayan ?.
Ko dana dawo kowa na dakin sa wasu kuma sun gudu sun bar gidan a lokacin fita na sake yi na je nemo muna abinda zamuci duk da mun dawo da abincin da hjy ta bamu kafin mu bar asibitin.
Sai dai shi Amar yace tea zai sha shi yasa nafita wurin nema kayan hada shayin a hanya ne wayan ya fara vibration a cikin aljihuna sai dan kara har hakan yasani firgita.
Don sam na manta da zancen wani waya dana tsunta ga baki daya sai lokacin har kiran ya katse ban san yadda zan dauka ba ashe tun wurin diban ruwa ake ta kiran layin ban sani ba ina can ina daga bohol.
Ashe hjyn su modibbo ne take kiran layin dan nata tunda ya bar gida basu samu wayan shi ba sai wanan lokacin shine hankalin su a tashe ta samu aka dauka kuma ya katse
Aka sake kiran layin nayi sa,a na danna daidai na dauka naji muryan mace tana fadin haba modibbo ka daga muna hankali haka ?
Nayi shiru ina sauraren hausan matar da muryab ta ta sake fadin wai bada kai nake magana bane ga daddy kuma yana ta kokarin neman ka tun dazun.
Ba mai wayan bane na fada tare da fadi me ego hausa kosi hausa fa hausa kadan kadan mama don jin danayi tace daddyn ku.
Who are you aka fada wanan karon muryan namiji ne nace iam d one who found d phone i don't know d owner self.
Kinji me take fada aka fada a cikin wayan ina ganin wayan ta fadi maine watace ta tsunta nace eh na samune a cikin gidan mu dazun.
Ke wacece ni ni sunana sahiba na fada kai tsaye a cikin hausawa gwari gwari mai kama dana yare wani unguwa na fadi sunan unguwa .
Na karashe da fadin a fada mai yazo ya karbi wayan shi idan kun same shi nakarashe da nagode.
Allah yayi maki albarka nace amin woo nagode kada ki kashe aka fada a kausashe nace oyah oda
Yan tambayoyi ya dinga min ina bashi amsa a cikin irin hikiman su na tsufin ma,aikata har ya gane komai da yake son ji a wurina ban sani ba .
Muna gama wayan dasu na kali wayan ina jin dadin jayi waya mai tsayi a cikin yaren hausa duk da bansan da wanda nayi wayan ba a lokacin.
Shi kuma daddy su neman layin wani abokin aikin dan nasa yayi ya fada mai ya nemi moddibon ya fada mai yadda mukayi.
Kodana shigo gida nake fadin ni bazan sha tea ba wanan abincin zanci wanda ya saura muna na rana.
Har na fara ci na tuno nake ba umma labarin wayan dana tsunta din har iyayyen maishi suka kirani.
Da farko kirji ta buga amma tana jin har nayi kwantancen inda za a sameni a karbi wayan sai ta dan sake take min fada dana tsunta me yasa ban bata ba a lokacin ?
Nayi shiru kafin ince umma naga kowa a wurin ne lokacin kin san kuma gidan nan da tsunce.
Modibbo yana kwance daki abin duniya ya dameshi na rashin ganin wayan shi gashi kuma bukatan abinda suke ganin zasu kawo karshen shi ba samu ba a garesu.
Yaji anyi nocking din kofan dakin shi da alaman akwai wani a kofan lokacin dake son shigowa wurin shi .
Ya mike daga shi sai dogon wando da fari singlet a jikin shi haroon ya gani tsaye a kofan mamaki ya kamashi.
Sun gaisa ya bashi wuri ya shiga dakin suka kara gaisawa da shi yace oga yace na zo na fadama anga wayan ka a hannun wata yarinya Sahiba.
Sunan ya maimaita a cikin mamaki Sahiba a ina ta samu wayan ya kwashe yadda mukayi da mahaifin shi ya fada mai.
Nan ya nufi wurin dan jakkar kayan shi da sauri ya dauko riga ya zuru ya dauki bindigan shi ya soka a bayan shi suka fita a waje yake fadawa security din da su biyo shi anga wayan shi a wanan gidan hannun wata yarinya.
Suka biyo shi da sauri baya suka shi shiga motocin su zuwa gidan mu basu samu isowa ba sai sha daya da wani abu duk yan gidan sun dawo a lokacin sai yan kalilan ne basu dawo ba.
Mukan har mun kwanta sai jin jiniyan mukayi a kofan gidan naji umma na fadin kai innalillahi wanan masifa yau da me yai kama hakane ?
Kamar mahaukata suka shigo duk abinda suka gani a gaban su suyi ball dashi ina yarinyar da ake kira Sahiba suka fada.
Ga kowa ya fito hankali a tashe matan daga su sai daura gaba wasu kuma sai dan guntun wando a jikin su .
Umma na kokarin budan kofan aka bamko kofan da karfi tace subbanallahi wetin we do again ?
Sahiba are you ?
Sukace wa umma ta girgiza kai kafin tace na my daughter be Sahiba sukace ina nake ?
Sai gani na fito daga dakin ina mutsukan idanu aka tambaya a bayan su kun ganta eh ya bada amsa tare da fadin karamace fa ogo.
Ku kawo ta nan ya fara tunkudani na juyo ina fadin na wetin i do ? i no be criminal woo stop pushing me like dat.
Ai kafin yace me gulma ya fara tashi a gidan kowa da abinda yake fadi har gaban ogan nasu aka kaini naja na tsaya gaban shi kim kam.
Where is my phone ya tambayeni nace saka hannu a cikin aljihun riga na dauko na mika mai ai sai gida ya dauka olusi omo buruku.
Na dis smal rat stil d officer phone ?
smol girl like u shame on u omo kowa dai yan gidan namu da abinda ke fitowa bakin shi lokacin .
Wani tsawa ya daka duk aka natsu yace yarinyar nan ta tsunci wayana ba sata tayi ba don ta kira parents din na ta fada masu da inda zamu same ta.
Kuma mahaifina yace nayi mata alheri don wanan halin nata na kirki data nuna ba wanda zai tsunci wayan nan ya maida min shi kamar yadda ta mayar min a yanzu ba tare dana sha wahala ba.
Don haka ga wanan ki rika ya fada yana miko min kudin da sai lokacin ya kalleni ya gane yarinyar nan ne ranan ashe ?
Yasan ban shedashi ba don irin yadda yayo shiga ranan ba zan taba sheda shine ba a yanzu gabana tsaye .
Ya juyo ya kara kallona yana miko min kudi na gurgiza kai tare da fadin i no de colete ur money i just do wam becouse of Allah.
Tsuki yan gidan suka fara suna fadin olopopo see d person wen no get any tin de reject d money now .
Eh i no go coletem my religion no teach me like dis wani officer ne daga bayan shi ya amshi kudin a hannun shi yana fadin where ur mama.
Na nuna mashi kofan dakin mu yace ur mama go colect d money naw yana dan washe baki.
Shiko yana tsaye ya soka hannu daya cikin aljihu ya kura min ido a cikin mamaki hali irin nawa.
Suko yan gidan namu sai fadin suke ehh givan to her mother she will colectam, suna wani bubuda mashi hanya don ya wuce.
Su kuma na fadin haba dis enosent girl can do dat may she found it some where mafi yawan su haka suke fadi suna kallon yadda za a kwashe tsakanin mu dasu.
Har guntun dan sandan yayi nisa a cikin muryan shi na kasaita yace dashi look Samuel called d mother for me first.
Duk mama na tsaye a kofan mu a cikin tashin hankali tana jin abinda kowa ke fada lokacin kafin ma ya karaso itace ta fito suka juyo tare.
Sunzo wurin ta dan tsaya a inda nake tsaye itama tana kallon yawan su duk wai a kaina suka zo can yace da ita.
Yarki ta tsunci wayana ta kuma kira azo a karba shine nake son bata alheri don halin data nuna na kwarai taki karba.
Ai domin Allah yata tayi hakan ka tambaya nan kaji idan mun taba rigima da wani tsakanin mu da kowa a gidan nan sai mutunci.
Daga gefe suka shiga fadin gaskiya ne kwarai kuwa hakane don baka sanin ma suna gidan nan idan ba sun fito ba agansu.
Oya ki karbi kudin nan don hakan umurnine na tabbatar da na baku alheri don yaba abinda kukai min don kinga wayan nan duk wani baiyanin sirina yana cikin sa kuma tunda ta dauka bata taba shi ba.
Woman colet d money u be luck woman to born pikin like u knowadays with good heart wani tsohon iyamiri dake sayar da kayan part na mashin din hawa ya fada daga gefe inda suke tsatsaye.
Woman colect de money now iyamirin ya kara fada sai umma takai hannu ta karbi kudin don iya shegen bariki sai suka ihu da tafe wai har sun manta wa yanda ke zagaye dasu a lokacin .
Nan dai gulma ya kare bayan sunga sunyi godiyan hakan da akai musu suka shiga motocin su suka tafi.
Tafiya sukeyi amma hankalin shi baya tare dashi duk da yana bin wayan shi da bincike a lokacib don ya tabbatar ba a taba mai ita ba bayan batar ta.
Saidai hakan bai hanashi shiga zurfin tunanen da yakeyi ba tare da tantama ko a ina yasan wanan fuskan a baya.
Haka nan a bangaren mu sai bayan wucewan shi ne umma takai kudin a hancin ta tayi saurin cirewa da sauri don irin kamshin da taji kudin nayi.
Nima a daidai lokacin kwakwalwata ta hasko min kamar shi da wancan guy din daya taba ban kudi a cikin mota lokacin dana fita da ruwa.
Umma na fada da sauri a cikin hausa nake fasin kamar wanda ya han kudi da nake tallan ruwa fa shine wanan mutumin.
Tambayan da zan maki yanzu ke nan kika rigani ashe shi din dan sandane ke nan nifa Sahiba wanan abin yanzu ya fara bani tsoro gaskiya.
Fada muka ji an rikice dashi a wajen gidan mu tsakanin yarabawan gidan da iyamurai da muke haya tare.
Da sauri muka fito don hayaniyar yayi yawa duk dako darene wai wani iyamuri yace da ace yaran yarbawan gidan suka tsunci wayan nan ba zasu bayar don duk barayi ne son kudi yayi masu yawa sasai.
Tofa ashe a gaban iya wale ya fada aiko nan ta saka kururuwa duk sauran yarbawan suka fito a cikin dakunan su ana fada.
Saida kyat suka watse a lokacin nikan nayi barci ni da Amar sai umma dake zaune tana sallah take jin abinda suke fada a cikin fadan nasu.
Washe gari kuma tunda asuba suka dasa fadan a inda aka tsaya a cikin zafi iya wale ke fadin wai e go say dat naw for yaruba becos sahiba mother na his ashawo.
Inna lillahi naji umma ta fada da karfi na dago daga saka takalman da nakeyi na dan kalleta a inda take zaune din.
Naji tana girgiza kai tare da fadin ni iya wale zataiwa kazafi a gidan nan kan wanan maganan yanzu kuma.
We all know dat u are sleeping with her when your wife is not in d town shabi na lia i de talk ta tambayi sauran.
Ai kafin umma tace me nakai waje ina fadin iya wale so ur tin don come to my mama again ?
Na kalleta kallo a cikin fushi cikin turanxin su na lagos nace yau zan fadi abinda kikeyi da mazajen su a cikin dare idan suna barci basu sani.
As from today u wil not tell lie for any body again in dis house no be u i see dat night with baba tunde on d floor ?
An dat day again d same tin i saw u nicked baba Alaba de for ur back abi na lia i talk ?
Swear if i tell lia for u naw, haba kai kace wani irin ruwan zafi na wasa matar shi yadda ta yanka ihu hankalin kowa saida ya tashi wurin.
Ita ko iya wale dafe kirji tayi tare da fadin yeh Sayiba ehmi ?
Yes u iya wale, na u a i saw dat day in d night with dem abi na lie i talk a wani irin maraice tace ah haba sayiba why why please ?
Why u de telling dem lie sayiba ?
Shabi lie no good wen u tell dem lie naw for my mama ai kafin tace zata bada amsa iya Alaba ta zo gaban ta tana girgiza tare da gyara danmaran da tayi tana fadin .
Ai sai ihu ya tashi suna fadin sham sham on u iya wale , u no de feel sham sleeping wit somebody husband wuuuu.
Danta wale yazo daga baya ban sani ba ya kai min duka sauran mazab gidan suka taso mai suna why , why go beat her ?
Sai fadan ya koma a tsakanin su suka shiga zagin shi iya wale da yau taga masifa daga inda take ido yayi ja ta shiga surfawa wale din kuma ashar .
Wanda da alama bata ma san abinda takeyi ba a lokacin don tashin hankalin data shiga a lokacin kan abinda na fada tayi.
Nikan bayan na gama hada fadan na tatara na bar wirin cikin sulalewa na shige dakin mu na zata umma zatayi min fadan hakan danayi mata don tana babba sai naji shiru bata tanka min ba.
Wayan shi ne yai kara daga gefen shi ya dago yana kalon mai kira daddy ya gani don haka ya daga da sauri yana fadin daddy yanzu nake batun kiranka na bari gari ya kara wayewane dama.
Gari kan ai ya waye na yau sai kuma gobe idan Allah ya kaimu kuma sai yayi murmushi wa daddy nasa .
Shi kuma yaci gaba da fadin masha Allahu dada waya dai ya shiga