Showing 336001 words to 339000 words out of 382072 words

Chapter 113 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28398



BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, JAMI,E, , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋

Zaune nake falon mu na mike kafafuwana saman dan table dinnda muke cin abinci koyin wani abu wanda yake aje a falom da tun zuwan mu gidan a nan muka sameshi.
Tv ke aiki a lokacin amma hankalina bai wurin abinda akeyi a tv din don na lula cikin tunane a lokacin don yanzu sam rashin fitina aiki ya fara damuna zuwa yanzu.
Wayata dake gefene ya dauki karan kira na shigo min kallon wayan nayi sunan ya Abubakar ne saman screen din wayan nayi mamaki hakan tare da mika hannu na dauka ina mashi sallama.
Ya amsa a cikin wani murya me nuna yanayin damuwa a gareshi lokacin a hakan muka gaisa dashi kafin yace dani sahiba sai baffa ke min bayanin yadda sukayi da maigidan ki kuma.
Na danja numshi kafin nace akan meke nan kuma yaya na tambaye shi cikin sonjin akan me sukai magana kuma yanzu ?
Yanzu kina ganin abar zancen nan ba tare da daukan wani mataki ba a kansu kamar yadda mijin ki ya fadawa baffah shiyafi sahiba ba tare an tsaya yanke masu sharian irin abinda suka aikata ba ?
Dan guntun murmushi na sake a bangarena ina fadin hakan zaifi yaya don haka shine kaanciyan hankalin kaf family din mu.
Abban mu dai sun kashe shi ba zai dawowa ba don haka mun barsu da Allah ya sakamuna kan abinda suk aikata muna din.
Bari ga Allah shine saukin mu a yanzu da muke son shiga yan uwan mu muma kamar yadda kowa yake cikin su zaune lafiya.
Idan ka lura mu biyune mahaifin mu ya bari a cikin ku sai kuma mahaifiyar mu dake tare damu a yanzu kayi duba ka auna yaya idan munja da yawa yaya makomar mu zai kasance a cikin ku nan gaba.
Ku din duk kun fimu yawa ku yan,uwa na kusa dana nisa suka sani muma fa jinin kune amma ana wasan boyo damu a cikin ku .
Barin wanan zancen a yanzu shine kawai saukin mu ba kaina nake dubawa gaba ba don Ammar nake duban abinda zaije ya dawo a garseshi cikin ku shina miji.
Wani iska naji ya furza tare da tareni ga fadin abinda zan fada yace na fahince ki sahiba na kuma gane dalilin ki yanzu nayin hakan.
Idan suna da kunya da tsoron Allah ko tunane da kansu ya kamata su dawo da komai dake hannun su yanzu ba sai kun tambaye suba kuma.
Sai a saka masu ido a ga irin nasu tunanen tunda kin tula masu kasa su zauna a cikinsa har in akwai tunane zamu gani duk da nasan yana da wuya yanzu suce zasu iya dawo maku dashi tunda daddy ma ya kasa hakan.
Ka bar zancen daddy don ko yaci ya kula damu bana mance alheri komai kankantashi gareno gidan kune silan dawo damu cikin mutane har muka kai haka a yau ga idon mutane ko wanan wani abune mai girma daya kamata abawa maraya ai.
Kun bamu wurin zama kun bamu ilimin da muke amfana dashi a yanzu aiko kaga daddy yayi muna komai a rayuwa ina fadi hawaye yana sauko min a idanuwana.
Burina daya shine in samu dai kawai a zauna lafiya damu dasu don yin hakan shine saukin mu a cikin su.
Ba babban bakin ciki garemu kamar ace yan uwa duk sun gujemu sun juya muna baya duk akan wanan maganan daya mu kasance bamu da kowa da zamu kalla a matsayin dangi a garemu ai kaga hakan ba zai muna dadi ba nan gaba.
Shiru yayi yana saurarona har nakai aya kafin ya nisa yana fadin akan hakan zaku hakkure da abinda yake mallakinkune sahiba kowa yasanda dukiyan kune a hannun su.
A cikin wata murya kasalaliya na kira sunan shi da brother Abubakar please abar wanan zancen kamar yadda nace zaifi sauki ga kowan mu.
Yace OK amma ki kara tunane sai nayi murmushi kawai ba tare danace komai dashi mukai sallama na kashe wayan ina tunane.
Sahiba wanan wani irin sunane haka ita din yar wani yarene wai data iya wanan karfin halin manewa mijina haka ta fada a fusace tana kallon babban yaron shi data tsare a falon ta tana mashi tambaya a lokacin.
Kasa yayi da kai kafin yace a gaskiya ba zance ga yareta ba saidai nasan ita din a lagos take zaune da kowa nata shine iya abinda na sani a yanzu.
Kyaleshi tayi ta zurfafa a cikin tunanen dayasa har ta manta dashi tsaye wajen a lokacin shine ya kawar da shiru da fadin may i ?
Ta gane me yake nufi tun bai kaiga karasawa ta nuna mashi hanya da hannu a hasale ya samu ya fita da sauri ya barta a zaune ita da kannen ta.
Wai kinji bayeraniyace fa a ina ya hado yar yaruba kuma kai maza sai a barsu inda aka gansu yar uwan nata datazo don maganan ta fada.
Zaiganta mana tunda munafukine duk inda zai shiga ya gano ta tunda yayi niya ai zai iya ganin tunda jaraba ke cinsa har da yan yare ya jajibo dashi da ita duk zasu gane kuran su a gidan nan.
Amma naji ance ba a kasa daya zaku zauna bai da ita wai a can Hong Kong ita zata zauna ko Dubai ke kuma kina nan paris.
Zancen banza yake wallahi ai inda duk ya ajeta a tare zamu zauna da yakw munafukin namijine ai kinga bai fada min komai ba har yau a kan zancen.
Inba ni dana fito mai da zancen ranan muka kwasa dashi ba har ni yau mukhatar zaiyiwa barazan saki akan wata arniya can.
Wanan ne ya daga min hankali wai yau mukhatar ne akan wata yake ffadin haka har zance ya bazu a cikin munafukan yan uwansa sai yawo suke da maganan.
Ban taba sanin basa son ki ba haka a tare dashi saida wanan zancen ya taso maku kaf dinsu sun zube min a yanzu wai murja har yawon rabon anko take da kanta tana fadin auren yayan su da amaryan sa zata tare ne.
Injin bata kai gidan ki ba ta juyo tana tambaya yar uwan nata da sauri ita kuma tace da ita haba dai ai ko tasha giyan wake ba zata nufoni da wanan shirmen ba iyasu suke haukan su ai.
Zan gwada masu nice kuwa ai yanzu gani na dira a kasan duk mai iya shege sai yayi mu gani don koshi basai zanzo ba wanan zuwan.
Ai hakan yafi gara da kikazo ayi komai a gaban ki zaifi duk wani mai shirin iya shege yanzu zai shiga hankalinshi yan iskan banza kawai .
Kafanta dake mike saman tintin din dake a gabanta ta dan ja tana gyarawa kafin wasu yan uwan shi mukhatar din su shigo gidan da sallama.
Sun sheda muryan su don haka kowan su yai shiru ba tare da amsa sallaman nasu ba sai ita suwaiban ke fadin munafukai su hansai ne fa suka shigo don gulma.
Sunzo su samu na karasawa dayan dake mike daga dan nesa dasu tana jin duk abinda suke fada haushi ya hanata tankawa take fadi.
Wai koba kowane a gidan suka kara fada da dan karfi akwai mana kun shigone bakuga kowa ba zaku damemu da sallama haka don Allah dayan budurwan ta fada a hasale.
Ikon Allah tau, aka fada daga wajen ai muna sallamane munji ba a amsa muna ba suka karaso ciki da wani sabon sallama din.
Wani kallon banza ake watsa masu ba yadda suka iya don hjy ce surukarta ta turosu tunda sunji labarin isowan ta kasan duk da ba haka suka saba ba dama da tazo zata aiko a sanar da sarakuwar nata ta bayat da dan abinda sukazo mata dashi a lokacin.
Saidai wanan karon abin yasha bambam don ji kawai tayi ana fadin anga gidan bude ko dan nata ya shigone ko ?
Tsohuwar tayi mamakin hakan saida tasa a bincika ake fadin ai matar gidan ne ta sauka a daren jiya saida tayi mamakin jin zuwan ta kasan don basu saka ran zuwanta ba a wanan lokacin.
Nan dai tayi masu irin wullakancin da takeso ita da yan uwanta saidai sun kyaleta don irin gargadin da mahaifiyarsu hjy tayi masu kafin zuwan su gidan yasa suka kyaleta.
Zaman shirun yai min yawa yasa na mike don yin wani abu a gidan don na saba da jagaliya yanzu da ban fita sai a gida nake kai da komona ina wasa jini ga aiyukan gida.
Wayana dake gefe ne ya dauki tsuwa hannuna na dauraye na dauki wayan Fatimace muka gaisa tana tambayan su umma nace duk lafiya suke sai Amira ta karbi wayan muka gaisa tace ga anty baby nace tazone don sam na manta da zancen sakin da akace anyi mata.
A sanyayye yarinyar ke fadin ai ina gida anty Sahiba mun rabu da D salati na saka tare da tambayan yaushe haka ya faru ?
Anty Sahiba manir baida hali ko kadan nan dai take fada min matsalolinsu na cewa ba abinci ba kula gashi yaki bari taci gaba da karatu.
Karshe kuma yan gidan su kaf suzo sun tare a gidan su sai wahala take faman yi dasu amma basa ganin hakan harshi manir din har hakan yayi sanadiyar barewan cikin ta, don wahakan da mami tai magana sai suka nemi zagin ta maganan dai gashi nan .
Don da ji matsene yaron ya shiga ciki ashe dama da inuwan mahaifin shi yake yanzu kuma ba mahaifin nasa komai ya jagule masu yanzu ga baki daya.
Har hakan yazo ya faru aikin da ban iya karasawa ba kenan ina tunanen zancen ya Abubakar lokacin da za ai auren da yake korafin cewa rayuwan yarinyar zasu lalata kawai basu sani ba.
Amma ita uwarta dadi takeji yarta ta samu maidan abin hannunshi har tanawa su Nabila da hauwa shagube a kan hakan.
Yanzun kuma ga yadda abin ya kasance masu a karshe dai ba dadi yadda babby din ke fada min rabuwan nasu sai yarinyar ta ban tausayi.
Koba komai iyalan gidan daddy sun nuna muna kauna don haka ba yadda zan iyawa mahaifin su wani cin fuska haka don su har gobe a yar uwansu na jini suka daukeni fiye da kowa a cikin dangi.
Shima haka modibbo tun bayan wayan mu dashi kalamaina suke damun shi a rai don shi baiga abinda zaisa muce mun yafe dukiyan mu alhalin hakkin mune a hannun iyayyen su.
Da suka kwace da karfi da yaji daga manalakinshi kowa ya sani don me yanzun zamuce mun barsu dashi me hakan ke nufi kenan a yanzu.
Da wanan damuwan da yake ciki ne har yashigo gaida mommy data kula dan nata yana cikin damuwa a lokacin ba zato yaji ta jefo mashi tambaya .
Hira take mai na sabon saurayin da Faiza tayi Bello dan zaria duk yan uwan nasa na zaune a falon don hakan dabian sune zama a cikin falo tare dashi idan yazo saidai har in wani abu na muhinmin zasu tattauna da uwar yan uwan nasa zasu daga su basu wuri ko idan sun san da zancen ba zasu fito ba ma .
Yayi kuri ya rike haban shi da hannayen shi yana kallon kasan dakin da idanuwan shi a lokacin yaji muryan mommy na fadin wai kai lafiya kake kuwa ana ma bayani ka yi shiru haka meke damun zuciyar ka kuma ?
Har lokacin bai dago a yadda yake ba saida hauwa tace yayan mu dakaifa mommy take magana sai lokacin ya nisa da dan karfi ya juyo yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda.
Lafiya kake kuwa ta sake maimaita tambayan ta tana kallon fuskanshi tare da kara nazarin shi lokaci guda.
Fuskan shi ya shafo a cikin yanayin damuwa kafin yace wallahi mommy zancen su daddy ne dai yake daure min kai wai mutanen nan suce abar zancen har su daddy su yarda da hakan ?
Ma,ana fa sun barsu da Allah kuma sun yarda da hakan ya fada a cikin wani irin yanayi na damuwa sosai a lokacin a fuskan shi har zuciyar shi.
Wai su Sahiba kake zance dama yace wallahi mommy to nima nayi ta tunanen hakan ai saidai ba yadda zakayine tunda mahaufin ku yanzu na kula ko zancen baison ajemai dashi.
Nima abindana gani ke nan mommy toba sai mu saka mai ido ba nidai yanzu nasan mutanen nan basu rikemu da komai ba wallahi.
Ko mutumin nan daya fito neman Faiza ta dalilin tane faiza tace min ya santa har suka kulla dashi to akan me zata faman rike bayun Allah a raina su suna bin nawa da alheri.
Jiyan nan hjy karima ke fada min ko tana ganin nasani ne tunda nafi kusa da su oho ? Wai sunyi waya da sahiba din akan zancen baby dake gida ko haka bai ishi mutum ba don Allah ?
Ta juyo tana kallon dan nata amma mommy ai daddy yayi masu shima akace inji Nabila da tunda aka fara zance ta hade fuskanta wuri daya.
Babu abinda ke cin zuciyar ta sai zalla bakin ciki da takaicin jin an ambaci wanan yar rainin wayau sahiba don hassadan Sahiba ya fara yawa a zuciyar ta har yakai yanzu tana kokarin cusawa yan uwanta wanan akidar.
Saidai a kullun ta dauko zancen batacin riba a wurin yan uwan nata don sai su nuna su basuga wani illa ga Sahiba ba gaskiya wanan yasa yanzu take yi iya ita don kawai Sahiban da sunan nata a yanzu yake yawo a cikin dangi dama wa yanda ba dangi ba duk sun fara sanin ta.
Shiyasa yanzun ma da taji an dauko wanan zancen yasa ta saka bakinta saidai bata sha da dadi ba a gurin mahaifiyan nasu da yayan su don sun zageta tas.
Abinda yasata tashi a cikin fushi ta shige zuwa cikin daki tana magana ciki ciki don katsetan da akayi kan hakan a yanzu ta rasa meyasa mommy din ke ra,ayin duk wani zancen daya shafi sahiba a yanzu.
Meya kawo haka ta tambayi kanta tana jan tsuki tare da kara jin tsanar yarinyar a zuciyar ta aai meya dama haka wani lokaci abu ks kasancewane ?
Wai yau sahiba ce take taka duniya yarinyar da abaya can saima sun bata wani abubuwan take amfani dashi wai itace yanzu ta koma haka lokaci guda.
Ba abinda ya kara ja mata takaicin yarinyar sai irin yadda har iyayyen su a yanzu suke nuna ita din fa ai watace don kawai suna takama da cewa dukiyan hannun iyayyen su nasune kome ?
Tsuki taja tana lumshe idanu tare da fadin shiyasa tun farko sam yarinyar bata kwanta mata a raiba ita balle yanzu data koma wata yar kabila sosai ga ba nauyi ko kunyar kowa a idon ta sam.
Saidai shi Abubakar modibbo na fitowa daga cikin gidan ya samu motan baffah hamza danasu baffah Abdullahi sun shigo ashe suna wurin daddyn su lokaci.
Bai tsaya ta kansu ba yaja motanshi ya fita gida bai dade da fita ba sai gashi suna neman shi an kira wayan shi yace yanzu yabar gidan gashi ya kama hanyar zuwa kano.
Sun nemi ya dawo don haka dole ya juyo ya dawo don amsa kiran su saidai yana shiga falon ya samu basu biyu bane tare da daddu din kamar yadda ya zata ya samu harsu baffah buhari dasu baffah gyade sunan gidan wurin daddy din a falonshi.
Yan mintuna bayan shigowan nasane baffah hamza ya fara magana kan haduwan nasu yana fadin duk da wanan tarom a yanzu kai modibbo bai shafeka ba namene mu iyayye zallah.
Amma a wanan zaman dole mu nemoka don kai kasan abinda ya dace ga abinda muke tattauna a yanzu din wanda ba komai bane sai zancen auren yar uwanka tace lagos watau sahiba.
Duba ga yadda abin ya taso haka lokaci guda ba tare da masaniya ba ko wani shiri don haka mukeson a bangarem mu mu iyayye musan irin gudun mawan da zamu taimaka dashi a wurin wanan sha,anin duk dashi mijin ya nanata muna cewa shifa matar shi kadai yake so baison wani abu daga garemu.
Dan murmushi kusan kowa ya sake kafin tsohon nan yace don ya raina da kuran mu ko me ya fada a dan bacin rai.
To nima dai na fadi hakan a gaban shi amma saiya nuna min koda bashi bane yana da hakki da nauyi akan yarinyar shima.
Baya ga haka zai zama kamar barnan dukiyane tunda shi sam baya zama a kasan na kuma duk da haka gidan ko yaushe a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login