Showing 39001 words to 42000 words out of 382072 words

Chapter 14 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28443

ba zaku daina kiran shi da boy din nan ya nuna diyan hjy Altine yana fadin jifa inda kanen sa suka kai yanzu da girma za,a wani saura kiran shi da boy.
Murmushi wanda aka kira d boy din yayi ya mike daga inda yake zaune yana fadin uncle ashe ka tashi ke nan na zata barci kakeyi ai.
Ya mike daga zaune da yake yana saye a cikin kananan kayan da sukai matukar mashi kyau a jikin shi zuwa bakin gadon da daddy yake kwance din a sama.
Kamar yadda yakanyi da danshi modibbo hakan yakanyi da dan kanwar tashi ba ita kadai ba har hjy Atine dake da yan mata guda biyu suma suna samun kulawan kawun nasu sosai a cikin so da kaunan junan su.
Yaushe ka dawo ke nan daddy ya tambaya yace yau da safen nan daddy nazo gobe kuma zan koma don yau naso in juya sai na samu bakaji dadi ba kuma.
Dan murmushi ya sake yana fadin suka kwantar dani a nan ba badan naso ba don kawai dai banda yadda zanyi ne na yarda na kwanta din.
Amma dai yaya ai kwanciya yana da amfani a gareka tunda kaji doctor yace sai ka dan kwanta din kwanciyan a yanzu shi yafi ga lafiyan ka.
Kofan aka turo hjy karimace da wanan kawar nata suka shigo duk suka kalketa suka kawar da kansu gare ta don yanayin wayewan ta ya nuna yar bariki ce ita bata da isashen kamun kai sosai.
Alh ashe jiki ya ki karima ta kira tana fada min tana magana tana wani kwarkwasa a gaban shi abinda ya kara basu takaici ke nan a dakin.
Allah ya gani abinda tun farko suka guda a auren shi da karima ke nan abinka da namiji ga abinda ya gani yana so yace yaji ya gani sai yayi.
Gashi har yanzu rabo ya ratsa a tsakanin su yan maya uku resas suka haifa bai kuma sa ta natsu ta daina wasu halaiyan da basu so a gareta ba.
Da shima kanshi Alh da alama yaji nauyin hakan sai ya basar yana fadin ya gode ya juya yaci gaba da zancen shi da boy din yana tambayan shi yanzu kana wani kasane boy ?
Ya dan yi murmushi yana fadin daddy ba inda bana zuwa saidai yanzu din nafi bada karfi a kasan Ukraine don shigo da alkama a nan kasashen muna Africa da muke karancin su sosai.
Masha Allah ashe kana wanan harkallan hakan yana da kyau sosai ina dai fadama duk lokavcin da kake bukatan wani taimako a cikin sana,an ka ka nemeni zan taimaka maka insha Allahu.
A daidai lokacin hjy karima ta wani tabe baki tana fadin muje ko kubura sai kawar ta juya tana fadin Alh ya ya kara sauki ta juya ba tarewa kowa magana ba a dakin ta fita.
Boy da moddibo kawunan su yana kasa kowa da iri takaicin da yaji a hakan saidai kawai a shanye ba dan anso ba.
Babu wuta a cikin hasken farin wata muke zaune sai dai ina can dan nisa dasu kadan ina jin hiran su da nake tsunta guda guda.
Ko barci yarki keyi a zaune koko gajiyan aikin da tayine yasa ta shiru matar da umma ke kira da Ladi ta fada.
Kawai dai nasan bakuntane ba wani abu ba tana tunanen wancan unguwar da muka barone don bata so tasowan mu ba can.
Ikon Allah yarinya nan din ai zaifi maku saukin komai dama ai don hjy nana ne kuka koma can Allah kuma baiyi zaman naku mai tsayi bane a can din da ita aka rabu.
Wacece hjy nana na tambayi kaina don ban taba jin umma na zancen ta ba a gabana har yau wama umma ta taba zance ni a gabana na ba kaina amsa da hakan.
Mikewa nayu tsam na hankade labulen zuwa cikin dakin namu din na kwanta ga duhu ga kukan wasu kwari a bayanbdakin masu shegen kara a kunnen mutum da zasu hana mutun yin barci da dadi.
Allah ya gani ganin farko da nayi wa wanan unguwar na tsaneshi ga baki daya a rayuwana a haka nayi barci sai dai banfi awa biyu ba dole na falka don yunwa ga kuma karan kukan wanan halittan dake ban tsoro.
Duk da duhun dakin amma hakan bai hanajin muryan umma ba tana fadin nasan dole ki falka dama don babu komai a cikin ki tun karywan safe da kikayi kafin kije school.
Gaskiya ba zan iya cin wanan abincin ba dana gani kamar ma bayin yau bane guntayen tuwon masara da miyar kubewa fari tas dashi an zuba miyan a ciki.
Bana jin yunwa umma kukan wanan abine ya dameni na bata amsa a cikin duhun nima ina gyara kwanci saman tabarman da nake kwance.
Shiru naji umma tayi bata kara tanka min ba har wani barcin ya kara daukana bayan na gaji da tunane ni kadai a cikin dare.
Washe garima haka na tashi sukuku dani bayan na gama sharan fadin kewayen mu da aka mayar kamar juji a gidan wanda a yanzu duk na gyara shi tas da wanab safiyan.
Na debi ruwa na watsa a jikina na dawo na zauna na shafa mai naji umma na fadin ki karbi ga dari biyu ki fita ku samo abinda zaku karya dashi kafin mu san abinda zamuyi nan gaba.
Karban kudin nayi na fita na fara dan zagayawa ina kara kallon yanayin wurin da hausawane zube ashe kamar mutum yana a cikin arewa ne zaune.
Saidai kowa kuma a wurin da irin sana,an da yafi kwaraiwa akai ga masu tallan abubuwan da ban san suba nan ina ta kallo na nufi wata mace dake soyar masa na mika kudin ta bani masan tana ta zuba duk sai naji kazantan hakan nayi dana sani banje gurin ta ba saye don akwai har maza dake wanan sana,an a wurin.
Haka na dawo gidan da jan kafa na zauna tare da dangware kwanon abincin a gaban Amar na koma na rakube gefen kofan dakin nayi shiru ina tunane.
Ba zakici abincin bane ke umma ke fadi tana bude kwanin dake rufe ta girgiza kai ta jawo kwanon zuwa gaban Amar yana gani yake tambaya na waitin bi dis ?
I no sebi eat dis kind of food wooo u ko ta kalleni tana tambaya nace i no go eat now i don bele ful na fada ina kawar da kaina gefe daya.
Tace no be u buy yam for breakfast ta dauki daya tana kaiwa bakin ta kagin tace eatam naw go enjo am is test good now.
I no sabi eat dis kind of food before i will drink gari da gradnut later na fada ina mikewa tsaye don barin dakin na fito na tsaya ina kalle kalle a wajen gidan.
Sai ga wasu tafe da ganin su mata da mijine zasu fita na bisu da kallo matar tana saye da hijab a jikin ta shigan ta ya banbanta sosai dana wanda na saba gani.
Har suka fice a gidan na sauke ajiyan zuciya ina mamakin su a raina kafin naji muryan ladi a kusa dani tana fadin yanzu nake zancen ku ai a zuciyana ko kunyi dabaran neman abin karyawa nace ?
Dan juyowa nayi ina kallon ta kafin na dan kago murmushi a fuskana ina fadin A karo ma tace adukwbe yar nan haka uwar ku tayi sakacin da yaren wasu ya shige maku harshe haka ?
Tana inane ita uwar taku na nuna mata dakin mu da iska ke dan kada labule a hankali ta juya ta nufi can din da abu a hannun ta zuwa aurin umma din.
Ta dan dade a cikin dakin tare da umma wanda bansan ko akan me suke tataunawa ba har tayi wanan dadewan haka a ciki.
Ni kuma ban shiga ba tunda bansam zancen da sukeyi kada in shiga injiwa kaina haka din ne kuwa don ta shiga tawa umma zancen sana, a ne sai aka kira wayan ta ta tashi.
Ganin ta fita din daga dakin yasa na koma dakin na samu wuri na dan kwanta sai barci a can cikin barcin nake jin muryan ladi na fadin.
Ke yanzu ai ko baki fita kin nemo kudiba yanzu kina da jari don wanan yar zata iya nema maki duk wani abinda zaku bukata idan tana da kwazo da basira.
Ga wanan unguwar namu cike yake da samari majiya karfi suna harbin iska ga banza balle sun kyala ido sunga wanan yar taki ai kakanki ta yanke saka ke nan ke.
Haba ladi ni kaina bayi shanshamci ba tun barin gida danayi kin sani balle na saka yar mutane ga hanyar halaka.
Kin dai fadi gaskiya kan da kikace gani da ita a gaba tunda ba issashen lafiyane dani a yanzu .
Eh ko can din inda muka baro itace tsaye damu ga komai tana samo muna dan abincin da zamuci a cikin wuni da dan kwabon da zamu sarafa rayuwan mu a kullun.
Amma sam ban yarda ta aikata abinda kimarta da mutucin ta zai zube a idon duniya ni banyi ba ita kuma bazab sakata ba son bamu da gadon yin hakan.
Cikin dadin baki irin na Ladi din tace yo ai ba gado bane abun indai ka riga ka shigo bariki ai shike nan ka zama dan gida ga wanan harkan.
Ladi ina da abinda yarinyar nan zata dan rika juyawa yana zama kudi a yanzu a hannu na muna samun rufin asirin mu a cikin sa insha Allahu ba sai mun zubar da kiman mu ba.
Kin sani kuma kinmafi kowa sani yaran nan ba shegu na haufesu ba suna da ubansu da yan uwan ubansu nadai gudu da sune don sun rasa mahaufin su ana son a juya a kansu yanzu kuma.
Yo ai shike nan dama ni abinda nake jiye maki ke nan a yanzu kuzo ku zauna kuna zuba ido sai anci an raga a baku shine banso daku .
Ko a can ma idan muka fito basu san mu bamu san suba ban yarda mun zubar da kimar mu a can ba balle nan da yake kamar kasan hausawa a wanan wurin.
Har ladi tabar dakin ban gama fahintar inda zancen su ya dosa ba sai daga baya na fara gane kan zancen su ina hada kalmomin ina fahintar zancen su dana ji din sunayi.
A raina nace ke nan dai ya tabbata umma ta gudu daga gida damune don kada a cuta muna ke cikin wanan halin na wahala data kwanmace ma ganun mu hakan.
Su waye suke neman rayuwan mu bayan sun ga na mahaifin mu har mu suke son su karasa ake nufi.
Idan har hakane kuwa zan kara taimakawa umma wurin ganin mun kula da rayuwan mu kamar yadda umma ke tunanen yi akan mu ko yaushe.

Likita ya shigo ya duba jikin Alh yaga yayi yadda yake so sai kawai ya rubuta mashi sallama don shima bai son su kwana a nan gara ya koma gida zaifi mai sakewa da wakwala don sanin halun Alh da yayi bai son kwanciya asibiti ko kadan sai in ya kama dole.
Aka tataro aka dawo gidan dashi Modibbo ne ya jawo shi a hankali tare da matan shi su biyu suna bayan motan a zaune.
Har suka iso gida motan shiru ba wanda yayi wani magana sai maigidan ne da dan sa ke dan hira jefi jefi a motan.
Shiya kama mahaufin nasa har zuwa dakin shi ya zaunar dashi saman gado kafin ya kunna mai Ac da bai sake sosai yana kokarin fita.
Ji mana modibbo sai ya juyo da sauri inda mahaifin nasa yake zaune yace tambaya nake son yi ma tsakanina da kai a yanzu.
Daddy akan me ya tambayi mahaifin nasa yace akan wanan yarinyar dai ta lagas da kace kaman su yana zubi na diyań gidan baba namadi.
Shikan modibbo da nai san kai ba yace wallahi daddy kamarta dasu har ya baci harda dan lutsawan nan na kuma tun su duk tana dashi a fuskanta.
Sai dai ita wanan din ko hausa bata iya sosai ba shine maraban su da yan gidan kuma ita wanan din ta dara su haske sosai gaskiya.
Kasan gidan ita wanan yarinyar a lagos din na sani don dani aka tafi karbo wayan gidan gidan hanya din nan ne mai girma sosai don mutanen gida suna da yawa sosai gaskiya daddy.
Zaka kaini in gansu ya fada abinda yasa modibo yayi saurin juyowa ke nan yana kallon mahaifin nasa a cikin mamaki.
Lafiya dai kake son ganin ta daddy don ba yar nan bace fa na fada ma ita din yar nan bace kama ne kawai da sukayi a fuska.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , , , , ,

1️⃣3️⃣

BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA YAURI, , , , ,

PAID ONLINE NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA KADA MU RIKI JUNA DANI DAKE, , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALLAHU, , , ,

Dan kwana biyun nan duk a shiririce nayi shi ba walwala ga kuma yunwa na batun kasarani don tsanda na kasa cin wani abin kwarai a cikina yanzu tun zuwan mu semi din komai ya tsaya mun cak.
Ina ganin yan iska da yan duniya saidai wanda nake gani yanzu a semi boda ya cunawa wanda muka baro a baya can.
Zaka ga yarinya da shigan kafirai amma idan ta juye harshe tana hausa sai kin rike kanki don mamaki.
Hakama diyan su maza duk wani iya shege ya kare a wanan wurin ko yan Agege da Alaba rago da can ne dalilin hausawa kamar kana arewa da zama sun dagawa yan seme boda kafa wurin iya shige.
Haka yasa fitama bai ban sha,awa yanzu haka zalika banyi gigin fara wani sana,a ba can da zan dan dogara muna dashi inda kudi zai shigo muna.
Ga wanan hiran da naji umma da ladi sunyi ya kara min wani irin natsuwa a yanzu ga baki daya na koma wata shiru shiru dani a nan din.
Yau kan na kudiri fita in zaga ko ina na garin inga gari gari ya ganni in sama muna abinyi don sai dan kudin dake hannun mu ne umma ke zara muna dan sayen abinci dashi dasu sabulun wanki dana wanka.
Wani dogon rigana mai kama da kaki na saka sai takalmana da na ciro a cikin kaya ina goge kuran shi don in saka.
Umma ta kalleni yau yarbancin take ji tace dani enbelolo ma,ana ina zanki tafi sai dana dan bata fuska nace i wan worker round to see d town b4 i start bussines .
Don mind ur self here uno go enjoy dis place well, na bad people de stay round d place .
Umma why we come here now why choose d place dan stay there at Ajagule me i no pit stay here woo na fada ina mike wa tsaye.
U don no anytin dat worry us at dat place since i no peole don familier wit u naw at Ajagiule.
Na mike tsaye ina fadin na yim u carry us come dis yeye place when person go die for notin haba pity us naw umma.
Wani tsawa ta daka min har saida na gigice tana fada a haka har na sulale bata sani ba na fita daga gidan na fara tafiya.
Kamar yadda kowa ke tafiya a wurin haka nima nake tafiya ba tare da kula kowa ba balle ma ban san suba balle na tsaya kula su har nakai titin su na zaga ko ina ina bin garin da nazari.
Ba laifi don garin akwai shegen girma kamar sauran unguwanin lagos din da cinkoson abin hawa sosai ga yare kala kala a wurin har nazo iyakan layin na zaga wani layun shima na kewayo da zan dawo na tsaya wani shago na auni filawa da sauran kayan hadi har roban da zan saka kayan a ciki duk na saya na juyo zuwa gidan mu ban wani sha wahala ba wurin gane gidan don na saka shedan da zan gane hakan.
Na samu umma a cikin damuwan rashin sanin inda na nufa sai gani kwatsam da yan kayan dana sayo na shigo gidan .
Suna tsatsaye dasu Ladi cirko cirko sukaga shigowana ladi din tace ai na fada yar nan tana da wayayyen kai ba zata bata a garin nan ba.
Kinbi kin tayar da hankalin ki ga hakan, nikan gaidasu nayi ina kokarin shiga dakin mu da kayan naji ladi na fadin meta sayo ne take kokarin shiga daki dashi ?
Kamar ban jita ba na shige abina dakin ina fadi may ur evil eyes back to u, uno de see dis tin today.
Daddy ka bari zan ga yarinyar na bincke ta wasu abu kafin ka ganta wai duk yanayiwa mahaifin nasa hakane don ya kwantar da hankalin shi.
Saidai mahaifin yaki don cewa yayi idan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login