Showing 120001 words to 123000 words out of 382072 words

Chapter 41 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28447

dago kai da sauri na kallesa saidai babu alaman wasa a gareshi lokacin.
Da kyat na iya budan bakina nace dashi back to lagos again broda?
True true talk me i no wan go back to that side again na bata raina yace kije zamuyi magana leter dani da ummaki daku



ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , , , , , ,

3️⃣6️⃣ BY, , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHAIM AR RAFI,E

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON ALLAH NA KUDINE KADA MU RIKE JUNA DAKE, , , , ,

Na kasa boye mamakina ga hakan sai kallon shi da nakeyi a lokacin ko banyi magana ba kasan abinda zuciya ke raya min a lokacin.
Sam ba zanyi fatan komawan mu lagos da zama ba gara rayuwan mu nan cikin yan uwa sau dubu da zaman lagos da mukayi babu kowa namu a wurin.
Sai kuma na dago kai na kalleshi kamar a firgice ba komai na tuna ba sai mai zai maishemu lagos da zama a lokacin ?
Sahiba kyale yayan ku da wanan zancen nasa don ba a kai karshen maganan ba inji mommy ta juya wurin shi tana masa fada don me zai fito da zancen a gabana haka ?
Juyawa nayi na bar part din nasu zuwa part din mu a cikin rashin kuzari a tare dani don nikan arewa tayi min yafi zaman lagos a gareni duk da da farko kamar na shiga matsi saboda zama wuri daya da ban saba dashi ba a lokacin na bude idona cikin motsa jiki da fita neman nakai a rayuwa.
Haka yasa ko a nan in dai ina gida ba zan fita school ba nice a ranan zan gyara gidan ko inansa baki daya.
Tun mommy na fadan hakan har ta kyaleni don ta fahinci zama a kazantane bana so yasa nake aikin da kaina don a yanzu yaiwa Asabe yawa duk aikin gida ita daya keyin sa ga gyaran gida ga aikin kitchen.
Ban samu umma a falo ba sai Amar dake zaune yana kallon ball a tv na samu wuri na kai kwance ina faman tunane.
Har umma din ta fito tana fadin Amar ya canza chanal ya damemu da zancen wanan kwallon tun safe.
Ban iya fada mata komai ba har yakai an wuni sai da zamu kwanta barci ne damuwan hakan yai min yawa na fadawa umma zancen.
Shiru tayi na dan lokaci kafin tace dani Alh ya fada min hakan ga kwanaki amma yace sai idan sun kai ga yanke shawara don yin hakan yana cikin shirin su da suke muna.
Amma zasu nema muna inda zamu zauna da kuma karatun mu don karya tsaya a can din duk dai yanzu da zuwan mu nan din muna neman rufe shwkara biyu ke nan kuma duk lokacin umma tana boye ba fita takeyi ba ko a cikin gidan.
Sai mu yara da ba,a iya boyewa ne muke dan fita muna zirga zirgan mu ba tare da takurawan kowa ba a zaman mu din kaduna gidan daddy.
Naji umma tace aiko ba komai yanzu mun san yan uwan mu mun kuma san garin mu da gidan mu ko ba komai muna da madafa a rayuwan mu nan gaba.
Shiri sosai ashe daddy yayiwa komawan mu lagos din kan abu biyu zuwa uku ya yanke shawaran yin hakan na farko zaman mu a nan ya fara kawo zargi a kanshi.
Kan yawan tambayan shi da akeyi mu din su waye a gareshi don duk wanda ya ganmu sai ya tambaya saboda zatin da Allah yai muna daga ni har amar kanina din daban muke a cikin yan uwa.
Haka ya fara daga hankalin daddy har ya nemi shawaran ya Abubakar a kan yadda za ayi .
Sai na biyu yasan ko bai samu matsala da kowa ba dolene ya samu matsala da anty Amarya don abu ba abu ba zata kai kara a aurin shi kan mu ya fara fuskantar baraza daga wurin ta kuma.
Sai kuma idan muna nan ba zai samu fitar da duk wani abinda yake son aiwatarwa din yadda ya dace dashi din ba shine dai dalilai masu karfi da yakai daddy yanke shawara a yanzu mu dan nisanta dasu.
Don haka sai aka fake da fadin cewa mahaifin mu da yayi tafiya ya dawo don haka zamu koma lagos din da zama kuma.
Hankalin kowa ya tashi da jin hakan har anty Amaryan don sabo abune mai wuya ranan rabuwa da yan koke koken mu ranan muka bar kaduna zamu koma rayuwan lagos da a lokacin nake jin kuncin hakan a zuciyana.
Wanan karon ma jirgin muka bi zuwa lagos din muka sauka da yamma a local airport dayake duhu ne mun samu mota na jiran mu shiyazo ya kwashe mu zuwa gidan da zamu zauna a Apapa.
Wanan ne mafarin canza komai a rayuwana da nake son baki labari a yanzu yar uwa.
THIS IS LAGOS
Tun lokacin da nayi arba dashi na runtse idanuwana nake jin wani iri a raina har muka kawo inda zamu ban bude idanuna ba.
Jin an tsaya yasa na bude idona na ganmu a wani kofan gida me bene hawa daya da get da komai a gidan duk da garin ya dan canza min anyi wasu sauye sauye hakan bai hanani gane unguwar da muke ba a lokacin.
Yana gaban mota zaune ya nazari a cikin wayan shi ya dan juyo yana fadawa Amar da cewa Amar dis is ur new house in lagos.
Sai yaron ya dan kakaro murmushi a fuskan shi muka fito aka bara fitar muna da kaya har lokacin ina dan dunkule a cikin half cover din hijjab baki dana saka wanda naji ana kira da half sunna a arewa.
Masha Allah umma ta fada tana fadin sai ku fita mu shiga daga ciki ko ta fada muna hakan yasa na dan motsa a yadda nake zaune da ido sunyi min ja a lokacin.
Duk da ganin gida ya dan sa na rage jin abinda nake ji a zuciyana saidai hakan bai sakani jin farin ciki ba a lokacin don rabani da yan uwana da barci ne kawai ke rabani da fa,iza aminiyata kuma uwar dakina a gidan daddy ke nan.
Ga ya Abubakar ya hanamu dauko kaya da yawa a cewan shi in munzo hutu ai zamu samu na amfani a nan fadin hakan yasa nasan zamu dinga ziyaran su ke nan lokaci lokaci.
Ni dai Allah gani nayi har na gwamace abarwa Alh Nuhu da sauran mutanen da suka cuci Abban mu a lokacin dukiyan da daddy ke kokarin kwato muna a hannun su da dawowan mu nan lagos din.
Saman ne namu donshi muka hau gidane irin ginan zamani komai akwai a cikin sa kamar daulan da muka bari a kaduna nan ma haka akai muna gata a gidan.
Bayan yasa key ya bude gidan ya mikowa umma makule ya nuna dakin farko yana fadin umma wanan na farkon zaki zauna.
Sai wancan Sahiba ta zauna a cikin da jin haka na dago kai na kalleshi ya juya ya nuna wasu biyun dake gefe yace Amar zai zauna a cikin wanan na farkon don shi namijine sai dayan da ba kowa shima akwai komai a cikinsa sai a jewa baki shi da fatan gidan yayi maku haka don shine nagani kamar zaku sake sosai a cikin sa a nan.
Kasa din duk nakune da zaku iya komai da kuke so sai kasan idan kuna da bukayan dan haya nan gaba sai a samu wanda aka yarda dashi ya zauna a ciki.
Sai lokacin umma dake zaune saman dayan kujeran dake falon tace dashi ai ba kowa a cikin sa yanzu ke nan ?
Eh umma don ban san ra,ayin ku ba ga shaguna nan kuma koda zaki samu masu hanyan su nan gaba shima naku din ne zaku iya bada hanyan shi.
Allahu akabar yanzun dai a takaice muke da alhakin duk wanan gidan ke nan a yadda na kula ga bayanin ka modibbo ?
Ya dan gyada kai yana murmushi yace hakane umma ba,a samu babba wanda yafi wanan din kuma wanan a karshe sai yaban sha,awa muka saye sa.
Ban san irin godiyan da zan maku ba a yanzu ubangiji ya dada rufa asiri yasa a gama da duniya lafiya muka amsa da amin.
A sanyaye nace dashi yaya mun gode Allah ya kara rufa asiri yace amin amma daddy ya kamata ku kira ku kara gode mai da wanan din.
Ya Amar komai yayi ma ko akwai abinda kake bukata kuma Amar din ya kada mai kai da a, a mun gode yaya.
Yace to umma ni zan tafi zan tafi masaukina baida nisa daku nan sosai gaba da kune kadan sai idan na samu lokaci zan kara leko ku insha Allah.
Kamar ince don Allah kada ya tafi don ina ganin ya tafi ke nan ya barmu a nan har abada ba zai sake dawowa garemu ba kuma idan ya tafi.
Yadda nake ji din ne yasa tun kan yayo kaina na mike zuwa dakin dayace shine nawa na bude na shige ciki ina sake kuka.
Tsayawa nayi kuma turus ina karewa dakin kallo don irin yadda aka kawata dakin da komai na dakin pink ne har gadon da wardrobe sai kuma na tsaya ina kallo.
Juyowa na sake yi da sauri na fito na samu har ya tafi ko sai umma dana sama zaune itama tana kukan fadawa nayi a jikin ta ina fadin shike nan umma suma sun tabu damu ke nan ?
Basa iya zama damu kuma umma kowa yana gudun mu ke nan a yanzu kada Alh Nuhu ya kasheshi ko ?
Sahiba nima tunanen da nakeyi ke nan tunda naga ashe ba tare da modibbo din zamu zauna nan din ba ashe.
Shike nan umma shikw nan sai kuma na sake fashewa da kuka don ba zan iya yin magana ba a lokacin don yadda wani abu ya tokare min zuciya.
Jikin umma na fada ina kuka itama kukan takeyi Amar kan yayi zaune yai tagumi ya kura muna idanuwan shi bai iya yin komai ba.
Saida nayi kukan ya isheni naji umma tana fadin mu je muyi sallah kada lokaci ya shige muna bamuyi sallah ba akan lokaci.
Dakin daya kira dana umma din muka shiga tana gaba ina bayan ta gadone da wardrobe milk colour da surkin baki sai mirrow da ban dakin har tawul an rataye sabo a kofan bandakin.
Sallah mukayi muka idar mun dade muna addu,a wanda wanan ranan addu,a na zuwa ga mahaifinane nayi shi sai daddy da sauran yan uwa da nahiwa.
Bayan mun idar ne sai lokacin zancen abinda zamuci yazo muna jin Amar ya fara zancen abinci yasa namike nafita falon.
Kitchen din dana gani na bude subbahanallahi nan ma dai basu kasa damu ba gaskiya don akwai komai a cikin kitchen din da zamu nema ga store din shi nan shake da abincin da zamuci.
Fridge da freeze na a ciki don haka na bude ai kira na kwalawa umma tazo tagani itama bata tsaya ba jin kirana sai gata ta fito da sauri daga dakin.
Ta sameni a kitchen din na nuna mata hawaye ke zuba daga idon umma din wanda ba zance ga dalilin shi ba a lokacin.
Takawa nayi zuwa wurin gas din dana gani ina son in dafa muna koda indomei ne muci mu kwanta a lokacin.
Sai kuma na bude warmer din abincin dana gani abuncine ciki maizafi har yana tururi a lokacin na juyo na dan kalli umma din itama ni take kallo.
Abincine fa umma tace nima shina gani ai aikin modibbo ne nasani yasa a kawo kafin mu iso nan kila.
Shina fito dashi falon muka zauna mukaci kukan waya nake ji da sauri muka dago kai muna kallon juna da umma.
Wayace ke kuka a gidan haka yasa na mike da sauri ina bin kukan wayan inda yake fitowa a dakin umma har Allah ya taimakeni naga wayan a karkashin filo tare da kwalin shi a gefe daya.
Na dauka don na iya a wayan su Fa,iza daya zama kamar wayana a lokacin don nike faman jagulan shi sai idan an kirata zan kai mata.
Na dauko wayan nazowa umma dashi ina fadin wallahi umma wayace sabuwa har da kwalin ta a cikin dakin ki wurin pillow.
Wani kiran ne ya sake shigowa na daga da bissimillah gami da sallama abakina aka karba min.
Muryan mommy ne don bazai bace min ba tana fadin Sahiba kun sauka lafiya ?
Ban iya karba mata ba sai kukan dana sake kawai a lokacin ina mikawa umma wayan ta karba tana fadin menene waye kuma ?
Muryan mommy taji tana fadin nice mairo ya kuka sauka ya jama, a da yaran ta amsa da lafiya mun barku lafiya dai ?
Ta amsa da Alhamdullahi kafin tace kun tafi kun barmu da kewan ku har yanzu sai umma ta danyi dariya tana fadin .
Gasu zaune sun kasa sake jiki tun zuwan mu na kasa gane masu balle yartaki ai gaba daya a hankali tashe take a gidan nan.
Dada hjy sai kuma mukazo muka samu dawainiyan dayafi wancan da muka baro a nan kuma.
Layin ne ya katse mukai kira baya shiga a lokacin dole muka kyale haka muka bar zancen neman layin na mommy din.
Mikewa nayi na duba kofan a rufeyake tunda zamu shiga sallah dama na rufe kofan don ina jin lokacin da yake fadin mu saba da rufe kofan kada a barshi a bude.
Lokacin da muka shiga dakin ne na bude troler kayana dana shigo dashi in dauki kayan barcina bayan na ciro na saka wando da riga na saka hula a kaina.
Sai naji in bude wardrobe din in ga girman shi ko jakkar kayana zai iya shiga ciki umma na fadin daki kai kayanki wanan can dakin dayace shine naki don zaifi kunga nan sai ku barmin ni kadai.
Maganan ce ta makalewa umma don kayan dake cikin wardrobe din da aka jera a cikin shi.
Nan kuma hankalin mu ya dauku ga kallon kayan fita nayi zuwa dakin na duba haka din ne kayan ane a ciki shima na fito kamar mahaukaciya naje dakin Amar shima hakane dai na sama a cikin nasa.
Dole muka dawo fslon muna jin wanan karamcin nasu a garemu dare har Amar ya fara barci muka shiga zuwa cikin dakin muka kwanta.
Washegari kan kusan makara ne don banyi barci da wuri ba saboda tunane yan uwa da kawaye da abokan arxiki da muka baro a kaduna.
Bayan nayi sallah ban kwanta ba duk da gidan baida datti amma saida na gyara ko ina na cikin gidan tsab na koma dakin nan da yake a matsayin nawa nayi wanka na fito.
Wardrobe na bude na tsura mai ido na dan lokaci kayan an bambamtasu a mazaunin su shiryawa nayi cikin wani simple material dogon riga na fito abincin danayi muna na breakfast na fito dashi falon.
Na tayar da umma data dan samu barci a lokacin don saboda bata barci sai wajajen tara na safe zuwa goma sha dayan rana.
Mun ci munsha Amar daya damu sai a kunna tv na kunnawa tv din yake kallo nikuma na koma saman kujera na kwanta don umma tace kada ayi abinci sai na dare tunda na safen ya rage da muka dafa bamu cinyewa duk da ba yawa wanda nayi din amma mun kasa cinyewa duka.
Barci ne ya daukeni a wurin kuma na samu nayi barcin sosai harda mafalkina na yan uwa dana bari a can da sauran mafarku dai na dinga yi.
Sallah azahar ne ya tayar dani lokacin bayan nayi sallah dinne muka zauna da Amar can umma ta fito ban san ya akayi nayiwa umma tambaya ba da fadin.
Wai umma kafin Abban mu ya rasu shi mai kudine sosai irin daddy ko dai shima wanan filin da suke magana yake dashi kawai dama ?
Sahiba ta fada a cikin mamaki yaushe kika koma haka ko zama arewa ya koya maki wasu akida na shiga cikin maganan manya ne ?
I am sorry umma ban tambaya da wani nufi ba haka kawai tambayan yazo min a raina na bata amsa ta kawar da kai ga kallona.
Nima din jinin jikinane nasha a lokacin don ban dauka maganan zai taba zuciyat umma haka ba mun dade a wurin zaune ba wanda ya sake wani magana a cikin mu kuma.
Zama wasa wasa ya kama mu a unguwar har yakai na fita na zagaya unguwar nagani har iyaka duk yanzu nasan na wuce level din talla da nayi ada can baya a lagos din.
Saidai kasuwancin bai fita raina ba son haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login