Showing 165001 words to 168000 words out of 382072 words
don zuwan dayayi wurin mu din.
Niko a yanzu kaf din su a matsayin makiyan mu nake daukan su dan yadda suka barmu cikin diniya a watse babu kulawa lokacin da muke da bukatan hakan garemu.
Bayan sun fita umma ta dawone aiko ta hauni da fada wai ban kyauta ba da ban rakashi ko nuna kulawana da zuwan shi ba .
Shiru nayi ban dago kaina ba balle in bata amsa don nasan abinda zan fada ba zai mata dadi ba shine kawai nayi shiru a lokacin.
Suna zaune a gaban tsofin suna mayar da magana bayan sun gama saurare dayan tsohon yace su barshi dasu kada masu nuna cewa sunzo wurin su don tasan halin mijin nasu karyazo ya zama matsala a tsakanin su kuma.
Ta dawo gida Allah ya taimaketa ba wanda yasan fitanta har ta dawo don kowa na part din shi a lokacin don haka babu mai tseguntawa mijin nasu fitan ta.
Duk da Allah ya dorata a kanshi yana dan daga mata kafa ita don yana son ta ita ba auren su na filani yayi da ita ba.
Wurin barikancin su can ya hadu da ita ya auro ta don yaso kawai suyi zaman banza a watsene sai gashi har abin ya kaisu ga aure tsakanin su.
Akayi kuma sa,a yana ji da ita sosai cikin iyalan nasa don tayi iya harka dashi yadda yake so saidai duk da hakan idan halin shi ya motsa yakan mata rashin mutunci sosai.
Basu zo ba sai bayan kwana biyu da zuwan salma din gidan su saiga tsofin sunzo su sameshi a kan zancen yar shi din da dan wajen dan uwan nasa Alj Ali dcp.
Da farko fada ya soma yi yana fadin shi za a kawo iskanci yaro yayi ba daidai ba zaice yana son ganin shi zaice aiba fada sukayi da matar shi ba balle yazo ya ganmu.
Kai jam jam jam Nuhu wala hankali o da ace yau Namadine ke raye zai shiga zancen zurian ku har zaka iya musa mashi.
Dayan kuma yace amma Nuhu ka ban kunya da mamaki ni da nayi bugun gaba ina fadin acikin kaf babu mai jin maganan mu da girmamu sai kai don haka ba zamu samu matsala wurin ka ba na bada wanan shedan a gaban yan uwanka.
Son girma da yabo gareshi don haka tsohon na fadin haka kanshi yayi girma ya fara fadin ba hakana bane baffah yaron ne yake da girman kai da izza irin na uban shi yasa nake son nuna masa shi ba kowa bane wallahi.
Shi kowane kuwa, dayan tsohon ya fadi yayi saurin kallo shi yace kwarai kana matsayin mahaifin shi kuma surukin shi zakace baida kowa shiko keda kowa a garin nan tunda har gaku iyayayyen shi da rayuwanku.
Sai yayi shiru kamar yana nazari kafin can yace dasu naji baffah na kuma gode da zuwan ku gareni in Allah yaso zata koma idan na kimtsa.
Haba Nuhu haba dai ai kamata yayi tunda har kaji maganan kuma ka yaba da zuwan mu a matsayin mu na yan uwan mahaifin ku ya kamata ne ka bamu dama yanzu mu mayar da yarinya dakinta tunda ba fada sukayi ba sukace.
Ya kara yin shiru na dan lokaci kafi yace kada fa hakan ya jawo mata gori a wurin shi nan gaba yan tsofi har suna hada baki wurin fadin haba haba sam bazaiyi haka ga yar uwan shi ba ai.
Nan dai sukai mai dadin baki da bashi girma har dai yaji ya zugu yace a shiga ciki ai mashi magana da hjy salma karshe ma dai shiya mike sai ganin shi kwatsam sukayi yana fadin Nazifa ta fito ta koma gidan ta gasu baffah a waje suna jiran ta yanzu.
Komai dama ita Nazifa din ta gama shiryawa tana batun sulalaewa ta mayar da kanta gidan tane koda iyayyen nata basu yarda ba sai gashi Allah ya kawo saukin abin manya sun gyara zancen.
Sun isa gida saida suka buga maigadi ya fito a bakin shi suke jin cewa maigaidan yayi tafiya a safiyan ranan ya tafi.
Allah ya taimaka makulin daya bata da zatazo yana hannun ta shi tayi amfani dashi wurin bude kofan suka shiga tare da dan mata nasiha kan zaman aure ta daina daukan zance tana kaiwa mahaifan ta.
Badon Allah ya gyara uwarta tayi dubaran tun karansu ba auren nan babu abinda zaisa ba, a rabashi a wanan lokacin tunda kowan su yahau haka.
Ba gida suka nufa ba gidan hjy Addah suka nufa don sun san ba lalai bane su samu daddy a gida lokacin tundashi ba mazauni garin bane shi sosai.
Sun sameta sun mata bayanin duk abinda ya faru sun kuma ce idan moddibo din ya dawo a yasamesu sukai mata sallama ta kawo masu abin arziki tayi masu sallama suka tafi a cikin dadin rai.
Washe gari koda na tashi nayi sallah kamar kullun na dauko waya na samu sako daga Oga Sha,aban cewa na sameshi goma na safe.
Nayi mamakin ganin wanan sakon duk da nasan hakan nada nasaba da sakon dana zauna na tsara mashi ranan .
Saidai ina tamtama a zuciya ko hakan ya zama laifi a gareni ke nan a yanzu don haka korana ko warning dina zaiyi don da dukan mu yake nema dole Felix ne zai nemeni.
Don haka sai tsoro da fargaba ya kamani lokaci guda a cikin raina daidai ba yadda na iya haka na tashi na shirya bayan na fadawa umma zan fita ana neman mu nayi mata bayanin kan bukin mutuwan da za ayi din asabar mai zuwa.
Itama dai bata goyi bayan wanan dabi,an ba nasu saidai tace nayi taka tsantsan da aikina a gama lafiya kowa da nasa irin al,adan tunda na saba ganin yadda sukeyi lokacin da nake talla har pure water na leda dana gora muna kaiwa a wurin mu saida masu a ranan muna ciniki sosai idan ana taron.
Nagama shiri cikin atamfa dana dinka buje da riga na dora hijab a saman dan kwalina kamar yadda na saba idan zan fita.
Na isa katafaren gidan nasu ban samu wani matsala ba son a yanzu masu aikin gidan sun saba dani ko don ganin mu tare da sukeyi lokaci lokaci.
Wanda ke tsaron kofab shiga falon shi na tambaya idan oga ya fito ya sanar dani cewa yana ciki yau tun safe yake karban bakin shi.
Kafin in shiga saiga Felix ya iso wurin tun dags nesa yake washe min baki yana fadin wa nake gani kamar beauty don haka yake kirana idan ya tashi min sheri.
Har ya iso inda nake yana fadin kai kai kai kinga yadda kika hadu kuwa kamar wace zata gasan kyau haka gaskiya kayan nan sun matukar karbi jikin ki sosai.
Na watsa mai harara ina fadin kaifa baka rabuwa da zolaya ni bashi ba don Allah kiran me oga ke min a yau kuma ?
Kafada ya daga tare da ware hannayen shi yana fadin ni ina zan sani yarinyar Oga na sani ko wani sirin zaku tatauna a yanzu wanda baku son kowa ya sani.
Sake hararan shi nayi ina nufan kofan sai kuma naja na tsaya don ban yarda ya sakani gaba ba haka shi yana bayana ba.
Muje mana ya fada yana nuna min kofan nace ka fara shiga kayi min iso sai na biyo ka a baya ya kwashe da dariya yana tura kofan.
Bayan shi nabi muka shiga banyi zaton yasan ina bayan nasa ba saida nayi sallama cikin zazzakan muryana duk da bana ji koda ya amsa min saboda girman falon da nisan da muke dashi a tsakanin mu.
Waya yakeyi ga wasu tsofin yarbawa guda biyu zaune a gefen shi da irin rigan sakin nan nasu nada a jikin su cikin natsuwa nake tafiya har na dan karaso inda suke suna bina da kallo a cikin harshen yarbanci na gaidasu suka amsa .
Felix ya nuna min wurin zama nakai zaune shima ya zauna daga barin gefena na hagu har lokacin tunda yai muna kallo daya ya dauke kanshi bai sake kallo inda kowan mu yake ba.
Kaina a duke yake ina kallon zanen kafet din da aka malala saman ties din falon mai ban sha,awa zakace hakine ba sakashi akayi ba idan ka ganshi don kyau.
Jin yayi shiru ya gama wayan yasana dago kai don ganin me yakeyi muka hada ido dashi a daidai lokacin da yake mikawa tsufin nan kudi.
Da sauri na dukar da kaina a cikin kunya kamani da yayi ina satan kallon shi shima idon nasa ya kawar yana magana da tsofin a hankali duk da muna falon ba zamu iya jin me suke fada ba a lokacin.
Tsofin suka mike suna mashi sallama kafin su juyo garemu suna muna sallama nabisu da idanu har suka bacewa ganina na nisa ina juyowa gare su.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , , , ,
4️⃣9️⃣ BY , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL ALIYY, , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KUKAN KURCIYA JAWABINE MAI HANKALI KE GANEWA ALLAH YA BADA IKON BIYA, , , , , ,
Da inyi shiru gara ina tunatar daku gaskiyan abin ki biya shine ka,ida ki karanta don namu ba irin nasu bane namu ba takarda bane rubutune ta yanan gizo ki biya ki karanta shine ka,idan abin yar uwa kin biya ki karanta a cikin salama ba tare da shiga hakkin wani ba bawai ina magana akan nawa ba kawai a, a yar uwa idan ance paid novel ne son Allah kikai zuciyat ki nisa ki daurekibashi bayan don kariyan ma,aunin ki sai mai hankali da imani zata fahinci kalamina Allah yasa mufi karfin zukatan mu a matsayin mu na musulmai ku yafe min idan na fadi ba daidai ba gareku.
Falon ne yai shiru na dan lokaci kaina na kasa duke ina danna wayana da ba komai nake duba a ciki ba lokacin don kawai na kawar da shirun da falon yayi ne a raina.
Jin shirun yayi yawa yasa na dago kaina naga me yakeyi a lokacin kawai sai na samu niya kurawa ido ashe yana kallon abinda nakeyi da wayan.
Nauyi da kunya naji lokaci guda cikin sarkewan murya na daure na kokarta na dan zamo saman kujera ina gaidashi cikin girmamawa.
Saida yai dan jim ya amsa min da yaya gida da aiki nace Alhamdullah ina komawa saman kujeran na zauna.
Shirune ya kara biyo falon na kamar minti biyu kafin yayi gyaran murya duk muka dago kai muna kallon shi lokaci guda.
Yace a cikin muryan nan nasa mai taushi irin na ustazai ina fatan kin san dalilin kiran ki da nayi a wanan lokacin a cikin hausa.
Na girgiza kai alaman ban sani ba ya dan murmusa a karo na biyu danaga murmushin shi na farko a jos da yake tare da kakan shi sai kuma yau dayai min a falon nasa.
Naji yace OK menene ra,ayin ki akan bukin da za ayi sturday na mahaifina ko bake kika turo min da sako bane ya fada yana tsureni da idanun shi.
Ban dago kai ba don nauyin shi da nake ji sosai saima wasa da nakeyi da yan yatsun hannuna da suke zara zara sun sha penti don fashin sallah da nakeyi na digasu da safen nan don kwaliya.
Muryan shi naji yana fadin kinyi shiru ko bakya magana ne kece fa kika kawo wanan sharan yanzun kuma sai ki min bayani yadda ya dace inji a gaba idan zan iya.
Na dago kaina fararen idanuwana suka sauka akan shi dana dan kalleshi kafin in bude bakina ina sake dan murmushi daya kara baiyyanar da asirin kyau na a fili ina fadin Sir .
Subbahanallahi yace a zuciyar shi yana lumshe ido gaskiya badai kyau ba amma bata waye bane har yanzu don akwaita da sauran wayewa saidai akwai kamun kai da ake son macen musulma dashi kam gaskiya.
Nasake fadan Sir saboda naga haka baya cikin tsarin musuluncine kaima ka sani don haka da wanan abin gara kawai ayi abinda Annabin Allah ya koyar damu game da mamatan mu da zaiyi saurin kai lada a garesu.
Shine addua ta hanyan kai sadaka tare da abin sallah a masallataiya da sadaka a inda ya dace mai zai hana a aika da sadaka ga gidajen marayuwan na gaskiya da suke neman taimako irin haka a ciyar dasu da niyar ladan yakai ga marigayin.
Masha Allah yace ba tare da sanin kalman zai fito a bakin shi ba lokacin don tunda na fara magana suke kallona dashi da Felix din suna kallon yadda hakorana farare suke jere kamar anjera min sune haka ga wani dan wushirya a tsakanin su daya dan kara min kyau idan ina magana.
Mai akin shice ta shigo dauke da tire da dan kofi a cikin sai data gaishe mu ta aje mai tana bude kofin a gaban shi hayaki ya dan tashi daga cikin kofin mai nuna zafin ruwan shayin a lokacin.
Bayan fitan ta dan shiru ne ya kara maye gurbin falon saida ya dauka ya dan kurba sau biyu ya rike kofin yana fadin .
Ummm,humm ya ustaz ya fada a baiyane ke muke saurare ko kin gama bayanin ki ke nan kallon shi nayi na dan sake murmushi don jin sunan daya kirani dashi da ustaziya dan kawai na fadi ga yadda za ayi a addinan ce.
Shiru nayi naci gaba da wasa da yan yatsuna ban dago kai ba bayan murmushin dana danyi da farko can naji muryan shi yana fadin.
Kinyi shiru ko baki tsara komai bane game da hakan nawa kike ganin wanan tsarin naki zaici ko baki lissafa ba kika gabatar da shawaran ?
Da sauri na dago kaina don jin abinda ya fada don na zaci a cikin fushi yayi maganan saboda shishigin da nayi masu nabada wanan shawaran.
Kofin shayin shi ya kara kaiwa bakin shi ya kurba ya aje saman table din don ya fahinci ba zan fadi wani abu ba akan hakan .
Ya aje yana fadin cikin mamaki ok kina nufin wani zan saka yayi wanan tsarin da kika kawo a yanzu ko me dole keda kika tsara abin kece zaki aiwatar da komai daya shafi hakan a yanzu shiyasa na kiraki a nan yanzu.
Ya mayar da kansa ya jingina a kujera yana fadin ina fatan kin shirya yin hakan daga yanzu don yau wednesday babu wani sauran kwanaki garemu.
Milayan nawa za a baku ki gudanar da wanan aikin da tsare tsaren ki ki fada yanzu a tura maki kudin sai a fara komai yadda ya dace ayi.
Shi aikin Allah idan za a yi ba dole saida kudi mai yawa ba ko kudi kalilan sai su wadatar da wanan plan din ai.
Sai naga ya bini da kallon mamakin jin abinda na fada sai kuma ya koma lumshe idanun shi kamar ba zaiyi magana ba a lokacin.
Wani irin mamakine yake yi na yarinyar nan don ya gwadata da dama a fannin kudi tana cinye jerabawan shi da yake mata din.
Felix ya ambata yayi wani amsawa da sauri yace ka miko min chack dina da biro a daki na rubuta mata yanzu felix din da bai san zancen da akeyi ba don shi baijin hausa kuma a cikin hausa muke maganan dashi a lokacin.
Felix na shiga bai kara kallon inda nake ba sai zaman daya gyara yana lumshe ida da tokare haban shi da hannun shi daya ya dora fararen kafan shi saman dan table din gaban shi yana cigaba da tunane akan abubuwa.
Na dago kai na dan kalleshi idon shi a lumshe sai kuma nakai kallona a inda tsufin nan suka tashi dazun da muka shigo naji gabana ya fadi lokaci guda.
Sake kallon shi nayi yana zaune a yadda yake din nace Sir dai ko ba kudi mutumin kwaraine shi ga kyau ga kirki ga kuma kwarjini na fada a raina.
Ido na tsura mai ina kare mai kallo dan gashine irin da matasa zamani ke bari yanzu a fuskan su zagaye a fuskan nasa bakikirin ya karawa fuskan nasa annuri sai dan baki karami hanci har baka farine kuma sol dashi kamar wani jinsi ne na wani nahiyar.
Abinda nake ganine yasa nayi magana da ya maye gurbin shirun da falon yayi a lokacin ina fadin ya kamata ka dinga nisanta kanka ga duk wani wanda ya fito daga fannin mahaifin ka mace ko namiji don suna binka da mugun nufi a koda yaushe.
Idon shi ya bude ya tsaya yana kallona har na gama fadin abinda zan fada din ya wani murmusa tare da fadin nasan da wanan tun ina karami basa kaunana sam gaba dayan su
Yanzun ma da abinda suka shafama a kujeran nan idan da son samune lada ka yarda