Showing 348001 words to 351000 words out of 382072 words
Komai an saka a gidan babune kawai babu cikin sa hatta abinci kusan na wajene da komai na bukatan mace .
Ranan ma a gidan yan uwa suka kwana amma da shirin su kan tafiya komawa kaduna Allah kadai yasan yadda nake ji a zuciyana a lokacin.
Suko sai hidimar gaban su sukeyi kowana kokarin hada kayan shi wuri daya don an fada masu karfe takwas na safe jirgi zai tashi su zauna da shiri .
Wani zazzabi zazzabine nakeji don haka na kwanta bayan na idar da sallah na ranan saidai ba barci nakeyi ba ina dai kwancene kawai ina kallon yadda yan uwa ke shiri amma badani da fatima ba lokacin.
Anty Amaryane ta shigo dakin lokacin gani kwancen da tayine yasa ta fadin lafiya dai ko Amarya ?.
Sanyi takeji Fatima ta fada kafin na samu bata amsa kallon Faiza tayi tana fadin kun samu abinda kuka bata tasha ko ?
Anty kinsan halin yar nan taki fa ni wallahi tsoroma nakeji kada yazo yai mata yawa haka a jiki ta kasa komai sai kuma ta kama baki kota tuna da anty take maganane oho ?
Au kema kinbi zancen gwaggonin ku ke nan ashe Faiza da suke fadin wai yau ango ya shigo ya kwana a nan duk da sun san muna nan don gulma.
Wanan wai wani haline haka su gwaggo keyi ne don Allah wai haka dazun fa suka kama diban kayan kitchen wai zasu samu simple a sayo masu idan mun koma gida har saida dayan matan yarbawan nan tayi masu magana kan haka bai dace ba ai.
Anty hauwa ce ke maganan a lokacin ta kara fadin ko a gida naji mommy na fada wai sin dibi kayan cikin akwatunan nan masu tsada.
Don Allah ki bari hauwa anty tace wallahi ai shiyasa kikaga mommy ta dauki kayan ta mayar dasu dakin daddy.
Watau dai mutanen nan sun tabbata yan son banza ke nan dai wanan wani irin haukane haka wai don sunga abin kamar banza suke yin hakane wai ?
Wayana dake gefena yayi kara na kai hannu na dauka sokone daga Felix yasa na bude da sauri ina karantawa.
Da farko murna yayi min tare da addua, sai na biyu da yake sheda min wai sunyi gobara a shagon su na Idi,iroko dake lagos sunyi hasara sosai a wajen.
Ban bata lokaci ba na tura mai da sakon jajen kan hakan ina tayasu bakin ciki da abinda ya faru din shima ya turo min daya gode.
Wanan labarin daya ban ya tsaya min a zuciya dan nasan wajen sosai wurine babba da ake aje kaya idan an shigo dasu kafin a raba zuwa garuruwan da za a kaisu.
Tun jin wanan labarin na dunkele a wuri daya ba abinda nake tunawa sai irin dukiyan dake makare a wajen a gaskiya na tausaya kwarai da wanan abinda ya faru din.
Ina kiran ummana da Amar dako wani lokaci yana kirana kai da kai mu dan yi hira ko ya fada min wani abu don ban bar gidaba saidana canza masu waya ga baki dayansu.
Hakan yasa yanzu yana kirana sosai don suna kaduna suna jiran mutanen lagos da zasu tafi tare zuwa gida duk da Faiza ta kwarmata min cewa wai ance ai a nan kaduna su zasu zauna yanzu.
Nasan umma ba zata yarda ba dan garama da ace ina gidane har yanzu mukazo idan nace zamu zauna a nan zamu zauna din tare.
Waya take ta faman kira amma ta kasa samun shi don haka ta kara hasala dashi sosai a zuciyarta don saita dauki hakan ai rainin wayau ne yake mata at list ya kamata ya kira yaji lafiyan ta ai kamar yadda ya saba yi a baya.
Bata samu jin labarin shiba sai baya karfe tara daya dawo gidan zuwa lokacin ta gama kuluwa dashi sosai a lokacin.
Watau sai daya gama rawan kanshi ga amayarshi da yan uwanta ya dawo gida kilama ko yanzu din wani abu yazo dauka ya shigo tunda tasan dole ranam a gun amarya zai kwana tunda ta tare.
Yawan mutanen dake gidan a lokacin bai hanashi shigowa part din nata ba haka ya fara gaisawa da mutanen da suka rage basu tafi ba har yakai kofan dakin nata yaja ya tsaya don muryan mutane da yakeji daga cikin dakin hakan ya tabbatar mashi da ba ita kadai bace a dakin lokacin.
Kamar sun san yana tsaye wata ta bude kofan zata fito a lokacin hakan yasa ta san da yana wurin tsaya da sauri ta fara gaidashi cikin dan daga murya don naciki su sanda zuwan shi a kofan.
Nan matan dama su hudune a dakin kuma suma da safe zasu tafi bakine abokanta da sukazo daga nisa sai yan uwanta mutum biyu suma.
Ya dan dauki lokaci kamar yana duba wayanshi kafin yasa kai ya shiga dakin da sallama yana duban inda suke zaune.
Tare da wata matar abokin shi da tazo daga Niger republic aminiyar ita hjy falmata dince sosai kuwa tun shigowan shi ta fara mai ba,a da ango ke nan
Ashe amaryan zata bari mu ganka kafin tafiyan mu dan murmushi ya sake yace ai a marya bata rikeni ba kafin yai magana ne yaji hjy falmata din ta lailayo wani ashar tana fadin wane uban ta da zata hana a ganshi har ita din me ita din banza.
Murmushi yayi gajere daya tsaya iya baki da gefen fuska kafin kuma lokaci daya ya daure fuskan tasa yace.
Meya kawo zagi a nan kuma yanzu falmata ina hanaki wanan zagin dake son ya zauna maki a baki yanzu fa bazan lamunci wanan ba a gidana.
Jin ya yarfata a gaban mutane a zaton ta duk a kan amaryan tasa yayi mata haka ta sake fadin don an zagi bayerabiyar taka kake wanan halakon haka wai ?
Zagi kan ai yanzu na fara tunda kun fara min da munafunci ta tare kunce sai yau yau din ma da zata tare din saika dauketa kakaita wani gida kuka barni nan zaune.
Da wanan gidan da wancan din duk ba nawa bane ya tambaya da mamaki don me zaka dauketa ka kaita wani gida na daban ?
Mukhatar yaji an ambata daga bayan shi sai kuma lokacin ya farga da tana dakin ashe can daga baya tana lazumi don haka kuma ya sheda muryan anty hafsat din da tazo daga Cameron yartace ubansu daya uwane suka raba da Falmata din .
Macece kamila mai addini mijinta ya rasu da dadewa tana zaunene a can ne don dangishi sun hata wucewa .
Saboda zaman mutunci da sukayi da ita tana da hakkuri da sanin ya kamata bata da yawan hayaniya sosai ita kamar sauran gata kuma malamace ta addini sosai don shine aikin mijinta dama malunta yazo maiduguri a nan ya auri hjy hafsat din yatafi da ita kasan su.
Ka dawo ashe ta fada ta kawar da zancen yace eh naje duban wani aikine garin Calaba sai yanzun muka dawo ya fada a dan ladabce.
Jeka ka huta daga baya mayi wanan zancen amma ba a nan ba yanzu duk a cikin yare suke fadawa juna magana a lokacin.
A sanyayye ya juya ya fita bayan yayi mata godiya don a wanan lokacin yakai iya makura da matar nasa dake abu kamar bata da hankali.
Har ya kai dakinshi a gajiya da kana kallon shi zakaga zalla bacin rai a tare dashi da damuwa kuma yana kallon kannen ta dake zaune gidan shi amma basu iya gayar dashi ba lokacin suma suna taya yar uwarsu bacin rai ke nan a hakan.
Tun shiga shi dakin ya fara kokarin cire kayan dake jikin shi lokacin yana maijin zuciyan shi ba dadi haka ko dan bai saba da irin wanan hayaniyar bane ya zo mai a hakan.
Ita falmata tasani ba yayi aure bane don damuwa da mace shi sam ba irin mazan nan bane dake lakewa a jikin mace ita ta sani yana aurene don ida sunna ma,aiki S, A, W ne.
Don me zata biyewa zancen wasu a yanzu ta bata tsakanin su bayan tasan yayi mata iya kokari a rayuwan zamanta dashi don kawai ya dauko wanan yarinyar yanzu a cikin su zata fito mai da wani hali na daban da bai santa dashi ba yanzu ?
Tsuki yaja ya karasa cire yar cikin dake jikin shi tare da fadin zan koya maki hankali ki gane kuren ki idan kin matsa wanan haukan haka .
Wanka yayi ya fito yayi sallah har lokacin ba wanda yai mai tayi abinci duk da uban yunwan dake cikin shi kuwa tun safe haka ya wuni hana rantsuwa ya dan sha juice a can da zaisha maganin shi.
Shiryawa yayi tsaba ya fito daga dakin da bai san ina zai nufa a lokacin bai yarda wani ya bishi ba shiya ja mota da kanshi zuwa gidan mahaifiyar shi.
Tsuki yaja don ganin ko nan akwai sauran mutane har lokacin amma haka ya daure ya kutsa kai ciki falon ya fara gaisawa da mutane sama sama.
Hjyn tasa tana daga cikin don haka ya kutsa zuwa cikin don zaifi mai sauki a lokacin nan ya samu ta idar da sallah suna zaune ita da kanwarta a lokacin.
Bayan sun gaisa din ne ta fara tambayan shi yaya jama,a yake fadin Alhamdullahi shima baya nan ya danyi tafiyane ya dawo yau din kuma.
To amaryan ka dai ta tare a gidan ta sai muce Allah ya bada ikon rike amana da hakki a tsakanin ku yanzu sai kuma kayi hakkuri da matar ka kasani don zataga an mata ba daidai ba duk ko da tasan gaskiya.
Ai wanan ba komai bane zan zauna da kowa da halinshi insha Allah ya fadawa yar uwan majaifiyar nasa a ladabce tace nasan zaka iya amma kuma sai ka kara hakkuri duk da hakan.
Don ita falmata ta manta da halarcin kowa da akai mata a baya yanzu ta koma kallon mu a makiyan ta tunda mun goya maka baya kayi mata kishiya a yanzu.
Kaga a nan idan bata kwantar da hankalinta ba zata koyawa na bayan rashin zama lafiya ke nan gidan ya rikice ma ga baki daya lokaci guda.
Nima abinda nake gani ke nan gareta yanzu don ko yanzu dana koma gida saida yatta ta rabamu wai nakai amarya wani gida na daban mun munafunceta ita .
Nan ma ta kira sai abinda ta manta a bakinta shine bata fada ba a lokacin ita duk ta manta da irin halarcin da akai mata a baya kan auren ku da ita.
Murmushi yayi don baida abin fada a nan tunawama barnan raine a gareshi yanzu maida kanshi yayi saman kujera yana dan lumshe idon shi a hankali.
Ita dai mahaifiyarshi bata iya fadan komai ba a lokacin don itama ba abinda zata iya fada a yanzu kan wanan hauka na falmata da yan uwanta da sukeyi a yanzu.
Waya ta dauka ta kira layin yar aikinta tana dauka take bata umurni data kawowa mukhatar abinci a dakinta lokacin, ba a jima ba sai gata ta shigo dakin har lokacin suna zance shida ummin shi akan abinda yake faruwa a gidan nasa.
Inda take kara lurar dashi nauyi da karfin ikon da yanzu ya kara rataya akanshi har lokacin daya kare cin abinci kafin ya bukaci su sister dasu fito gashi gaban shi ta zube kayan a falo ta fara mashi bayanin komai kamar haka .
Duba ga irin abinda suka kawo yasa zamu basu kowa turmi daya da dubu ashirin ya dago kai a cikin razana yace what ?
Samira haka mukayi dake don Allah cewa nayi me alokacin da zan baki kudin kayan nan na fada maki cewa ina son su san abu mai daraja a rayuwana suka kawo min bawai abin wasa ba.
Koba komai suka kawo min mace ai tukwaicin da zan basu yafi wanan balle kinsan muhinmancin yarinyar nan a wuri haka kuma da yanzu take a matsayin iyalina .
Zaki hada masu turmi biyu da dubu dari a matsayin tukwaici sai tsaraban kayan buki kiba ko wace haka ma mazan zakiyi masu final ya mike yana fadin Allah ya bamu alheri yafice gidan kai tsaye.
Gaskiya ban so brother yayi hakan ba amma yanzu ya zama dole a basu mutanen da basu san darajan taba sune za,ayiwa haka ?
Akul, na sake jin wanan furcin a bakin ki ke bake bama ko a bakin wani na sake jin wanan furucin mara dadin ji wallahi saina sabawa maishi fiye da tsamani.
Dukiyan kiki ko nasa shi bai manta da mafarin arzikin shi ba kuma yafiki sanin abinda yakeyi ai babu ruwan kowa da abinda sukai masu.
Ko kuwa duka suka taru sukai masu laifin da kike nufin sunyi din ko kuma ta nuna tana da wasu yan uwane bayansu din ko kinga wani bare ya kawota wurin mu yanzu ?
Yadda taga uwar nasu na fada da gaske yasa ta dukar da kanta kasa tasan abinda tayi ya batawa mahaifiyar tasu rai sosai hjy ce mahaifiyar su ta fito take wanan magana.
Bayan tafiyan hjyn daki ta mike ta dauko turamen zannuwan kamar yadda yace a lissafa a basu ko wani ta dora mai kudinshi a cikin envelope dauka sukayi suka fita zuwa gidan da aka kaini din dashi.
Ina nan a yadda nake kwance din mukaji sallaman shi a falon gidan suna gaisawa dasu gwaggo da sauran mutane, kafi kuma muji sallaman shi a kofan dakin .
Anty hauwace ta fara mikewa dan ta fita zuwa lokacin yasa kai zuwa cikin dakin ko mu hudune ciki a lokacin su suna hiran su ina kwance ina sauraren su lokaci.
Ya shigo suka fara gaisawa suna ce masa ango don yasan su tun a saudiya sukayi ba,a da Faiza tace itace yata yace basu yarda ba nice dai babba gareta.
Yanzun ma daya shigo hakan suka fara dashi yace a, a kanwa kune a ciki amma a nan zasu barki kada ku bar min matana ita kadai dole dai kema ki tsaya don Fatima kawai ai bata isheta ba yana magana yana kallon inda nake kwance.
Ga dai amaryan ka nan tun dazun take muna raki wai ita bata da lafiya kila dama ciwon son ganin fuskan ka takeyi ta damemu sanyi takeji tun dazun.
Gaskiya mukhatar mutum ne mai yawan ambato Allah a bakin shi don ko yanzun ma cewa a ouzubllahi meke damun ta faiza shine baku kirani a waya ba.
Duk da ban gari dazun nan na dawo daga calaba cikin mamaki Faiza tace dashi calaba fa yace wallahi tun safe na tafi calaba kinsan sha,anin aiki irin namu ai.
Zuwa lokacin ya kawo inda nake kwance din yakai hannun shi yana dan taba wuyana a lokacin duk suka fice daga dakin suka barmu dagani sai shi a dakin.
What is wrong with you ya kara tambayana tare da dan zama a daidai tsakiyan inda cikina yake zuwa marana.
Wani iri naji lokaci guda don hakan yazo min a bakon yanayi da ko ganin hakan ban taba yi ba balle hakan ya faru gareni.
Dan kokarin ja da baya nayi saidai jikin shi na saman dan abindana rufe jikina din dashi lokacin ya gane hakan da nake da niyar yi amma sai ya basar ya nuna kamar bai fahinta ba.
Muje kiga likita ya fada jin hakan yasa da sauri nace no nasha magani jikin yai min sauki yanzu ai nagode na fada ina lumshe idona lokaci guda.
Yana yuyuwa streas ke damun ki tunda baki huta ba tun last week kuke event kinga hakan zai iya jawo maki ciwon jiki a yanzu daki daure muje din likita ya duba min ke ?
No don't worry your self iam OK now na fada a kasalance sai ya bini da kallo kawai kafin naji yace wanan ne dalilin da zaisa na barki ki huta nan na dan lokaci sai daga baya zan dawo in tafi dake.
Nima zanso a barni nan na zauna zaifi min zuwa wancan kasan don na zaifi min zama kusa da mahaifiyata da dan uwana a saukake.
Sau nawa zan fada maki cewa ba zan barsu su zauna a nan ba suma ko kina daukan hakan wasane zamu tafi da farko daga baya zan turo a dauke su lokacin kin saba da can.
Kara lumshe idona nayi a hankali kafin nace dashi kana ganin hakan ba zai jawo wani matsala gun mutanen ka ba ina nufin yan uwanshi ya kuma gane me nake nufi din yasa yace.
Ina ruwan wani da family dina yanzu ko mahaifiyata itace ta zabi zama nan kasan nasan kuma saboda sister dinane dake nan zaune.
Don haka kuma ba zan tauyewa wani daga cikin kuba