Showing 381001 words to 382072 words out of 382072 words

Chapter 128 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28366

daga ke har mahaifiyar ki da dan uwanki duk zaman amana kuke a wajena yanzu.
Hawaye na fara sakewa masu dumi daga idona ya fara lalashina don jin sheshekan kukana dana fara a lokacin.
Sallah da kwana biyu rana da zan fita girki muka shirya umma da yara muka tafi gaida hjy mahaifiyar mukhutar a cikin rashin sa,a mun samu falmata ma taje da nata iyalan a lokacin gidan.
Nan aka fara kallon kallon a tsakanin mu dasu don shigar mu da yanayin mu ya fara firgitata don an dade ba,a hadu ba ga yadda yan uwan miji ke wani haba haba da ni da yarana suna ba umma wani girma na musanman a wurin.
Ganin hakan ya tayarwa hjy falmata din da hankali sosai bata dauki lokaci ba ta mike tana fadin su tafi mukarrabanta suka mike sukabi bayanta a fusace.
Tun a mota ta soma fada tana fadin you see kunga yadda ya daukaka rayuwan mutanen nan suka canza ga baki daya haka.
Yaran ga baki daya ai ya mukhutar suka dauko ga kama sai farine kawai na uwarsu dayansu ta fada shiyasa na rufawa kaina asiri da wanan shawaran da geshuwa ta bani da farko wai nace ba yaranshi bane.
Akan hakan wancan lokacin yayi min saki daya kan wanan zancen shiyasa yanzu bana daukan ire iren shawaran nan na banza don ko makaho ya laluba yasan jninshi yaranan.
Kai jisu farare tas kamar ka dauke karamar ta fada wa yan nan bakaken da kika rainane naku ta fada a fusace don sai taga kamar yar uwan ta raina nata diyan ke nan .
Shiru tayi kafin ta fada afusace waya sani ko mai ake shafa masu don su burge mutane wanan farin aiyayi yawa haka ga yara tunda ba diyan turawa bane su ?
Haka suka kai gida yan uwan na bayan mota suna tsunkular junansu suna mata dariyan kyata don sunsan gaskiya saidai suna tsoron su fada a fili ta hausu da sababi.
Sai dare muka dawo gida daga gidan hjy din don washegari zamu tafi kaduna don bandauki hutu maiyawa ba sati biyu kawai zanyi na koma Hong .
Don haka saida muka shirya tun kan mu fita zuwa gidan hjy mukhutar din komai na tafiya mun tanadeshi lokacin.
Washegari samako mukayi don a mota mukai tafiyan saboda zamu tsaya yola wurin yan uwan mu shine ya bamu manyan motocinshi uku kayi tafiyan dasu.
Mun isa yola da dan sauran lokaci mun bisu daga daga muka kwana biyu daga nan muka dauki hanyar kaduna .
Mun samu tarbo na mutunci wanda ban taba zato haka ba daga wurin yan uwan namu ko wanan karon a gidan daddy muka sauka inda mommy sai wani haba haba takeyi dani da diyana da umma.
Hakama anty amarya ta rasa inda zata sakamu a lokacin don jin dadin ganin yadda rayuwan yarta ya koma a hannuna gashi kuma da Amirah zamu tafi itama zata karatu awurina .
Muka fita zaga dangi don na samu anyi auren Faiza da Bello a lokacin ita da Anty hauwa sai anty nabilace batayi aure ba gamu har gidan baffah nuhu suka taremu a cikin mutunci har wasu yaransu munyi gaisuwan mutunci dasu lokacin da sukaji nazo .
Anan suke min korafin baffah nuhu din baida lafiya a can prison din don kwanaki ma saida aka kirasu ana sheda nasu wai ya rasu ashe dogon suma yayi sunje an kwantar dashi asibiti.
Yanzu dai ya dan samu kafiya amma jikin sai a hankali har yanzun dai gashi ba,a barin aganeshi koda anje wurinsu saboda irin tsaron da ake masu a wurin.
Naji badadi dan jin hakan saidai banyi wani abu ba a lokacin daga nan gidan ya Abubakar muka nufa mun sameshi a gida.
Matarshi taso ta share mu da muka shigo tana wani kwasan iska damu saidai kome ta gani sai gata ta dan sake har tana tsoma baki a cikin hiran mu dashi.
Don sosai shikan ya nuna kulawanshi garemu ya nuna kamar kanwarce ta ciki daya nake gareshi ya dauki yara ya dora a saman jikin shi sai zolayana yake a kansu.
A nan wurinshi nake jin ashe suna hurda sosai da uncle yanzun, ban sani ba don a bakin shi nake jin wai uncle ya gina wasu company da sunan su babami ana gab da karasasu yanzu haka.
Kallona Nazifa tayi da mamaki nayi kamar ban ganta ba lokacin zamu wuce sai gata tana fadin na bata number na mu dinga waya.
A wurin mota ma mun dade da ya Abubakar din muna magana dashi akan su baffah nuhu dake tsare su kuma su gefe dasu umma suna dan taba hira .
Kwanan mu biyar a kaduna muka barsu cikin dadin rai ana haba haba damu kamar wasu kwai a lokacin don kowa naji damu.
Nan muka barsu cike da alhinin mu don dan hakin da suka raina gashi a yanzu mun dawo mun tsone idanunsu yanzu kuma.
Abinda dai basu so yana biye damu don Alkawarine na Allah garemu arziki daga Allah muka gajeshi don nayi abubuwa da dama a kadunan kafin na koma maiduguri.
Ban bar kasan ba saida uncle ya shiga ya fita aka sako su baffah nuhu da yan uwanshi da alokacin suyi nadama yafi dubu na kashe mahaifina.
Gashi mun barsu da nauyin don munki karban ko kwandala daga garesu haka kuma ko maganan bamu karayiwa wani ba.
Uncle mukhutar kuma ya
rike mu tsakani da Allah ba cutarwa nima ban matsa masu ga shiga harkan iyalanshi yanzu akarshe dai fatima ta auri ya mustapha duk da mahaifiyar shi bata son haka amma Allah ya zana hakan garesu mukazo Nigeria aka sha buki.
Yarana hudu a lokacin gidan uncle maza uku mace daya ina kara godiya ga Allah da ya nuna muna rayuwa ingantace dani da mahaifiyata da dan uwana
Mai karatu nagode da lokacin ki da kika bani muka kai ga karshen labarin sahiba da yan uwanta Allah yasa mu anfana da duk ilimin da muka samu a cikkn labarin sabanin hakan Allah ya gafarta muna Allahuma amin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login