Showing 189001 words to 192000 words out of 382072 words

Chapter 64 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28400

mata yaranta.
Lokacin da sukaje harsu Nabila sun so su hana masu su amma sai mommy tace idan kun rikesu nan kuna da abincin basune ?
Shi kuma lokacin daya gama yazo gidan daukan sune ya samu har ta turo an dauki yaran sai ranshi ya baci da hakan sosai ganin hakan da mommy tayine take dan gyara zancen don bata kaunan tashin hankali a tsakanin su ko kadan.
Koda ya isa gidan haushi da kuma maganan mahaifiyar shi bai bari ya tada zancen ba sai wucewa da yayi dakin shi baiko tsaya kan yan uwan tana dasuke falon shi zube ba suna ta hayaniyan su.
Tun a wanan lokacin ya dauki zafi da ita sosai a gidan don yasa a zuciyar shi cewa ko baiyi magana da fatan baki ba zai nuna mata ita bata isa ba a cikin hikima.
Daga wanan ranan ya daina zama gida tun safe zai fita gidan sai yamma ya dan shi zuwa takwas kuma ya kitsa ya fita.
Baya ko kallon yaran idan sun nuna sun gashi sai ya nuna ya barta da abinta ta kula dasu don yana son ta gane kurenta.
Tun bata gane me yake nufi ba harta fara dagowa ta fara neman jin ba,asin hakan da yake yazun ta hanyan tashi da safe ta shiga dakin nasa ta sameshi yana shiryawa yana tsaye gaban mirrow yana daura tie a wuyan shi ta shigo.
Gaidashi tayi da kwana ya amsa bai fasa abinda yakeyi ya juyo ya dubeta ba tace wai naga kamar kana fushi danine fa ?
Yace ko da kikai min me tace toni na sani gani nayi ka daina wuni a gida ka daina cin abinci ka daina kulani dai har yaran ga baki daya ?
Ya juyo yana fadin na daina kulaki kamar ya yanzun da kika gaisheni ban amsa bane zaman gida kuma da kike magana idan na zauna a gida ke zaki ciyar dani koda kika zo gidan nan ina kin sameni ina aikina.
Ta dago kai tayi wani irin kallo bai kulata ba ya wuce wurin aje suit din ya dako yana sakawa kafin yace yara kuma ai yarankine dake da yan uwan ki don haka meye na damuwa don wani bai kulasu ba yanzu.
Yarana fa kace yace eh ba yaran ki bane na waye yana fasin hakan yasa kai ya fita zai bar gidan tace na sani aidama nasani.
Nasan don na aika an dauko mi su gidan ku kake wanan fushin haka don me zaka bar min yarana a can gidan haka kawai ina ji ina gani a sabauta min yara.
Kamar zai fita sai ya juyo yana kallon ta yace idan har gidan ku ba, a sabauta maki suba babu gidan da za ayi masu hakan ko kin dauka kowa kamar sune da suke kirarin cewa basu kaunan su a fili don tsaban iya sheri har da yaran da basu san komai ba.
Yana fadin haka ya fita ya bargidan ya barta zaune tana binshi da kallo tana mamakin zagin gidan su da yau yayi kiri kiri aitake tafara jin wani iri.
Mikewa tayi zuwa dakinta fuuu har ta dauko waya sai kuma tayi wani irin tunane ta tsaya idan ta kira fa rigima ya taso tasan halin mijin ta zaice ne aiga abinda yasa ta fada.
Hawayenane ya sako mata daga idanunta na bakin ciki da takaicin irin maganganun daya fada mata kafin ya fita a rana.
Gidan su ya nufa ya samu gida tsit don haka ya nufi part din mommy kai tsaye a falo ya samesu wasu kuma suna kitchen suna girka abin karyawa.
Nan suka shiga gaidashi yana amsawa ya zauna a falon yayi shiru hauwace ta shiga tana fadawa mommy zuwan shi amma kuma ta ganshi kamar yana cikin damuwane.
Da sauri mommy din ta fito ta sameshi a falon zaune yadda hauwa ta barshi din mommy ta fito tana fadin a, a yaya dai modibbo na ganka haka da safe haka ?
A jiyan zuciya ya sauke yake fadin nazo ganin daddy ne ina ganin kuma kamar bai bude part din shiba har yanzu don nags wurin a kulle yake.
Mommy takai zaune saman kujera tana fasun basu fito ba ke nan har yanzu nina rasa wanan iskancin wai mutum da tsufan shi amma idan ya shige daki da mace sai yakai wani lokaci bai fito don iskanci.
Mikewa yayi yana fadin ni zanje in dawo an jima idan ya tashi muryan hauce ke fasin yaya ga abin kari mana mun gama .
Da sauri mommu tace dashi ya fada maki bai karya bane da zai fito ko jan magana dai kawai irin naku zaki kawo muna.
Kawo min hauwa yace yana komawa zaune tare da fadin basu tashi ba koda na fito barin dan karya a nan din kafin in tafi.
Mun shiga office din yana zaune yana dubam.takardan dake gaban shi jin shigowan mu baisa ya dago kanshi daga abinda yakeyi ba.
Sai can ya dago kanshi yana aje takardan dake gaban nasa ya nuna muna kujera da hannu mu zauna mana nice na fara girgiza kai don sanin laifin da aka kamamu dashi na makara.
Ganin haka shima felix din ya nuna bazai zauna ba ya girgiza kanshi yana fadin aina dauka koda bani nan kune zaku saka ma abina idanu sai gashi kuma nazo na samu ba daidai duk da na bincika an fada min ba haka kuka sabayi ba amma ku kara tsarewa don Allah.
Da nazone da wani bukata a gareku da nike son ai aiki akansa sai kuma hankan da nagani yanzu yasa jikina sanyi ga abinda nazo dashi din.
Kallon juna mukayi a tsakanin mu nida Felix kowa na tunanen wani zancene yazo muna dashi kuma da zamuyi.
Kujera ya kara nuna muna mu zauna muka kai zaune kanshi a duke yana aiki kafin ya dago yana turo muna wasu takardu a lokacin aka turo kofa sauran mutum ukun mune suka shigo lokacin.
Fara duban takardan nayi na dan lokaci bayani ne akan company shi na kaduna da kano dake batun durkushewa a yanzu .
Nan yai muna bayani kan yana rokon zamuje can din muyi aiki dasu na dan lokaci mu gano mashi inda matsalan yake .
Shiru office din yayi na dan lokaci don ni sam ban ma kawo kaina ga zancen masu zuwa amma kuma abin mamaki zancen farko nice ta farko daya fara kiran sunana a wurin.
Na dago kai da sauri ina kallon shi a cikin mamaki yace na sani kina tare da mahaifiyar ki da kanin ki zaune haka kuma akwai masu iyali a cikin ku.
Don haka na tadarwa kowa yadda ya dace akwai wurin zama akwai mota da duk wani abin jin dadi dazaku bukata a can na tanadar maku shi.
Yanzu ina sauraren ku ku tsara yadda tafiyan zai kasance nayarda dakune na daukeku tankar yan uwana na jini don haka nake wanan shawaran daku yanzu saidai idan akwai wani wanda yaga hakan bai mai ba zai iya kawo nasa shawaran muji.
Shiru office din ya kara yi kafin oga Jimo ya fara magana yana fadin shi a nasa ganin zaifi kyau a fara tura Adnan tare da Sahiba suje wurin a matsayin sabbin ma,aikata daka dauka daga nan sai su dauki rohoton abinda ke gudana a wurin daga nab sai musan abinda zamuyi nan gaba kano da kaduna din kusan abu dayane ke tafiya dasu don haka zasu iya fara da kano din sai kadunan.
Hakan yayi Felix ya fada nasan Sahiba zata iya zata fimu sanin abinda ke gudana saboda kwazon ta bayan hakan ita mace ce kuma yarinya da zatayi saurin shiga ran mutane.
Felix na fada da karfi take annurina ya canza lokaci guda naci gaba da fadin aiki zanje ko bayar da kaina ga maza so mind your language please.
Hannu Sha,aban ya daga min da hausa yake fadin zancen felix ya dauka hakan shine daidai amma ni nasan zaki iya koba ta wanan hanyar ba Sahiba saboda kwazon ki na aiki da kike dashi ki taimaka min na gane abindake faruwa a can please.
Ido na kura mai na dan lokaci kafin na kawar ina fadin banice da ikon kaina ba kun sani a katkashin mahaifiyana nake yace ya sani shiyasa zan baku duk wani abinda zaku nema a can idan Allah ya yarda.
Hausan da yakeyi yasa basu gane me yake fadi ba a lokacin suka zuba muna ido suna kallon mu zanje gidan naku daga nan dani da jimo da Abdulhamid .
Idan na bar nan don tafiyan naku zai kasance a cikin satin nan mai zuwa ne idan Allah ya yarda don haka na yanke shawaran zaku tafi dake da Adnan yemisi da Abdulhamid zai shigo yanzu.
Jin su kawai nakeyi don ni zuciyana ya lula a duniyan tunane lokacin don sam bamma tare dasu don banji yadda zaman ya karasa ba a karshe.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

5️⃣6️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AR RAQIB, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Bayan fitan su dole nina tsaya don dama hakane muke dan shirune ya biyo office din kafin can na dago kai da sauri ina fadin breakfast Oga ya gyada min kai alaman a kawo mashi.
Ruwan tea ne sai cake na kawo mashi don nasan ko cake din sai kila yaci hakan da nayi mai yasa ya dan ji sauki a zuciyat shi sosai don rabon shi da abinci tun karyawan da yayi gida kafin ya tasone a cikin shi lokacin.
Ganin ya kurbe dan ruwan shayin sai dan kadan ya gutsuri cake din ya barshi nan nake fadin na kara mai ruwan zafin ne yace no barshi da sauri yaci gaba da aikin da yakeyi a cikin computer shi.
Jimo ya kara dawowa da wasu takardun dayayi aiki a cikin su sun dan dade tare suna magana kafin ya fita Felix ma ya shigo da nasa.
Bayn fitan felix din ne na shigo na samu ya hada kanshi da tafin hannayen shi biyu ya dukar da kai da gani yana cikin damuwa sosai.
Sai kuma hakan nima ya dameni don ban taba ganin shi a cikin irin halin nan ba haka mutum ne mai nuna jajircewan shi ga komai lalai wanan abin ba karamin abu bane a wurin sa.
Dan satan kallon shi na sakeyi har lokacin bai dago kan shi yana a yadda na sameshi zaune din sai nayi tunanen ko barcine ya samu a hakan na juya zan fita naji yace kina son wani abune ?
Ya dago manyan idanuwan shi ya sauke a kaina dama nace ko ayima odan abincine ka danci na fada cikin sanyin murya.
Murmushi naga ya dan sauke irin na gefen fuska din nan mai nuna ina cikin wani hali yace tea din da nasha is ok don ban iya cin komai a yanzu suna son suga bayana Sahiba .
Yau laifine don nakai abu a kasan haihuwan mahaifiyana suma su karu damu su samu ashe hakan yin laifine a garesu.
Sun mayar da dukiyana abin wawaso an rasa gane inda kudin ya dosa ko ya shige har suna kawo min shawaran na sayar da wurin ga wasu ki duba min mutanen sahiba.
Nayi mamaki kwarai da karfin hali irin na dan arewa a nan shiya nemesu da abin arziki don kasa ta karu dashi sukuma suna neman ganin bayan shi a yanzu din.
Tausayi ya ban sosai ganin yau yadda ya tsaya yana ban labarin abindake damun shi kamar wata yar uwanshi naji a lokacin.
Yasa har na kai ga bude baki ina fadin halin dan Adam ne oga ko naka sai a hada kai dashi a cutama indai dan arewa ne don haka sukaiwa mahaifin mu yan uwan shi na uba daya suka kashe muna shi kan dukiyan sa shine mafarin da mahaifiyar mu ta gudo damu zuwa nan lagos tun muna kanana basu san muna raye ba son kawai kada mu taso muce muna son dukiyan mu.
Da yardan Allah zamuje muyi aiki sosai insha Allahu sai mun gano inda suka shiga maka da dukiyan ka su fito dashi idan mutum nason kansa da lafiya.
Kodana gama magana na dago kallon da yake min na mamaki ne ya dan ban tsoro yace yes Sahiba na manta shaf da zaki iya sam raina bai kawo kan hakan ba da farko.
Amma yanzu hankalina ya fara kwantawa sosai wallahi saidai kuma naji kin jefo min zancen sun kashe mahaifin ki akan dukiyarsa wanan maganan da gaske kuma haka yake ?
Ban taba karya ba bazan fara ba yau abinda na fada ma hakan ne ya faru a gabanahaifiyata sukayi ta daba mai wuka har ya mutu su kuma suka handame dukiyan da baya.
Yaya akayi kuka tsira nan ma na bashi labarin komai daya faru a lokacin kamar yadda naji umma tabawa daddy dasu ya modibbo labari a ranan.
Shiru yayi ya zuba min ido yana kallo haka Yemisi ta shigo ta samemu kallona tayi kafin ta dauke ido ta mayar a kanshi tana mamaki.
Zan iya shigowa tace tana kallon shi zaki iya mana ya bata amsa ko kinga wani abune ta dai nemi wuri ta kai zaune saida ta seta kanta ta fara maganan daya kawota office din.
Nikan fita nayi na barta a ciki tana masa bayani aikina naci gaba dayi har ta fito tana dan watsa min harara a raina nace kinyiwa banza din ban san kinayi ba ma.
Da dare bayan mun ci abinci na fara ba umma labari saicewa tayi ai sun rigaki zuwa nan sun rokeni da rana kuma na tausaya masa.
Na nuna masa tausayi sosao kan hakan ubangiji Allah yasa hakan ya zamo silar fitan arzikin shi a gano inda suke a sanyayyena amsa da amin umma.
Amma umma zuwan mu kaduna din ba zai kawo wani matsala ba tsakanin mu da yan uwa a can na tambayi umma din ina kallon fuskan ta.
Sahiba aikine fa ya kaiki can ba wani shashanci ba sanan kuma kari da dadawa tare duk zamu tafi yadda sukai min bayani har Abdulhamid da iyalinsa meye na matsala a wanan kuma ?
Wanan fa wani hikimane na ubangiji idan kin kula da hakan saidai kawai a barwa Allah nasa sanin yanzu don shi yasan abinda ya shirya ga hakan.
Ba gidan kowa ko a karkashin wani zamu zauna ba kila har mamu kare wani baisan mun shiga garin kaduna din ba tunda ba sanin ki akayi ba a can dama.
Dole muka fara shitin tafiya saidai umma ta dan koka da sana,anta saiga Abdulhamid ya kawo shawaran cewa kanin shine zaizo ya zauna tare da matarshi su kula muna da gida idan umma ta yarda sai a barwa matar shago su zauna muna.
Yadda umma ta yarda da Abdulhamid ko dan uwantane ya tsaya a nan don haka a take ta amince da hakan.
A shiga a fita kan tafiyan sirin namu ba tare da kowa yasab da hakan ba ranan mun kusa tashi aikine sai ga kiran oga ya samemu lokacin muda zamuyi tafiyan duk muka hallara .
Office din yayi tsit kafin ya dago kai yace damu Alhamdullahi duk wani shiri ya kammala akan tafiyan mu din saidai matsalan daya fara hangowa a tsakanin mu yanzu kuma.
Ba wani matsala bane sosai sao rashin hadin kan da babu shi a tsakanin yemisi da sahiba don haka zai iya kawo muna rashin nasara a can idan muje can muna hakan.
Don hakane zai raba tun nan yemisi zata zauna kano tare da felix sai su zauna a can da sauri Filix ya dago kai yace ahh, why now oga ?
Yace hakane zaman lafiya aida sauki don dole kamar a wuri daya ake tunda ba nisa sosai kuma a karkashin abu daya kuke dukan ku a can.
Har ya kare zancen shi yemisi koni bamuyi magana ba an dai wayi gari kawai anga dukkan mu bamuzo aiki ba a ranan sai suka dauka mun fita wani aikine.
Munyiwa kaduna shigan dare ne dukkan mu sai wanda yazo taron mu dinne ya dauke mu ya kaimu kwatas din a unguwar GRA.
Tuncan kowa yasan nomban gidan shi don haka nuna muna kawai akayi nikan da umma mun tsaya addu,a hakama naga saura musulman sun tsaya addua.
Amar tun shigan mu yake bin gidan da kallo yana fadin wai dama ace nan din shine gidan muna lagos daya dinga jawo abokan shi nan ai.
Gidane madaidaici da dakuna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login