Showing 135001 words to 138000 words out of 382072 words
ajewa da dare tunda wanan titin namu babban hanyane na kowa.
Ko bakiyi wanan ba yanzu wanan kayan drinks din da mukeyi akwai kasuwa sosai a gareshi ana samu sosai a cikin sa matsala dai shine rashin jarin mai tsoka da bamu dashi a hannu da sai mu kara ya zamanto muna egent na company yadda za a iya sari a wurin mu.
Shiru nayi ina tunane don umma ta kawo babban shawara a nan saidai inda zamu samu kudin yin hakan ne a yanzu shine matsalan.
Dan shirune ya biyo baya kafin nace yanzu umma yaya zamuyi da wanan kayan tace dani wanan dai zamu jira yazo tunda yace zai shigo ya kaimu wurin wani da zai baki maganin matsalan ki.
Umma ni banda wani matsala banda ciwon kan nan dake yawan damuna wani lokaci shine dai din matsalana a yanzu.
Shidin dai ai ake magana do mutanen kanki suke haddasa maki wanan matsalan ciwon kan ai idan su taso maki gara tun wuri a nema maki magani a kanshi zaifi.
Amma umma kin san matsalan masu maganin nan a yanzu shine irin kudin da suke tsulawa mutum tunda ba ko yaushe ne hakan ke taso min da a barshi kawai zaifi.
Sahiba kin san matsalan nan naki ba karamar matsala bace fa yau da ace mutanen basu da fahinta kinsan abinda hakan da suka sakaki zai jawo muna kuwa ?
Ban dauki key din ba bankumayi magana a kan komai ba karshe ma na mike na shige daki ina tunane na bar komai a wurin.
Don ni almara naji zancen motan kamar a mafalki na dauki zancen waini sahiba ce da kyautan mota gun mutumin da ban san shiba ban kuma da wata alaka dashi.
Da yamma Abdulhamid dinne ya dawo gidan mu sun tsaya a falo suna magana na fito maka gaisa dashi yake tambayana yaya jiki nace da sauki .
Suka cigaba da magana da umma akan alkawarin gobe da yamma zai zo ya kaimu wurin mai maganin dayace din.
Umma tace ab gode saidai da fatan ba wanda za a kaucewa Allah bane wurin ya danyi murmushi yana fadin.
Shima baya shirin da irin wa yan nan mutanen sam inda za ai muna rukiya ne asan abinda suke so su rabu dani har abada idan hakan mai yuyuwane.
Sai kuma ya dauko zancen inda za,a aje min motana don sabuwace dallailiya ashe don ma komai nata a leda yake tukun ba a bude shi ba.
Umma tace akwai gareji a gidan nan sai dai ba a gyara shi ba yace ba matsala zai mayar da motar company ya kwana a can don akwai tsaro a wurin gobe zaizo dame gyara a gyara wurin da zan dinga aje motan a gidan.
Ya dan dago yana tambayana ko na iya mota da sauri na dan girgiza kai ina bata fuskana da kawar da kai yace ba matsala matarshi ta iya mota sosai za a samu lokaci ta koya min.
Hakan daya fada yasa na danji sanyi a raina ya mike tare da yi muna sallama umma na masa godiya yace tabar gode mai yana kwadayin ladan kula da marayu ne a garemu.
Odaro na fada daga inda make zaune ban tashi ba don ni jin komai nake har lokacin kamar a mafalki don har lokacin zuciyana bata gaskanta min gaskiya bace motar tawa ce wai.
Umma ta dan dade a waje saida ya nuna mata ko ina na motan kafin ya shiga yaja zuwa inda yace zaikai ta din ya tafi.
Sai bayan ya tafine umma ta shigo sai kuma hankalin ta bai kwanta da hakan ba sai zargi yakuma shiga zuciyar ta duba ga yadda lokaci ya koma yanzu .
Tun dai data tambayeni nace ni a wurin aiki kawai nake ganin shi bamu taba wani hurda dashi ba kona gaisuwa hakan yasa hankalin ta ya tashi kuma sosai da tafiya da motan da yayi din ni har ina mamakin hakan ga umma don ban zata itama ta sa motan a rai ba sai wanan lokacin ga nawa tunanen.
Ganin ta damu har tana tambayana shi inda nasan shi nace umma idan ma har gudu yayi da motan ai kanshi yaiwa do dai duk inda yakaita sai ya dawo da ita nan da kanshi.
Ina fadin haka na mayar da hankalina wurin kallon tv da nakeyi na fita zancen su itama umma din jin abindana fada yasa tayi shiru na dan lokaci karshe na mike zuwa dakina na kwanta na barsu a falon.
Washe gari dana tashi naji saukin jikina sosai bayan na idar da sallah haka na fito na danyi aiyukan da nakeyi a gidan kafin muka shirya zuwa makaran ta.
Bayan fitan muma umma bata zauna ba a gida don da zaran mun fita itama bata son ta zauna a cikin gida saita dawo shagon sayar da kayan sanyin mu ta zauna a nan.
Saidai ranan haka ta zauna a cikkn damuwa dan ta saka ido har ta gaji ko zata ga Abdulhamid saidai har yamma da muka dawo babushi babu alaman shi.
Hankalin umma ya kara tashi umma ta matsa sai naje ma,aikata na duba ko yazo inji dalilin rashin zuwan shi ban iya musa mata haka na shirya nabi hanya saidai banje can din ba.
Na dawo na fada mata cewa bai shigo ba yau amma ta bari idan Allah ya kaimu gobe na sake dubashi.
Umma tace ina ai mu tashi kawai muje can idan ba,a gane ba sai muyi karan shi kawai a station a nemeshi zafi.
Ina jin haka nace tayi hakkuri har washe gari zan dawo school da wuri sai asan abinyi a kanshi haka dai ta hakkura ba dan taso ba.
Washe gari ban dawo gida ba sai karfe hudu shima Amar sai uku da rabi ya iso gida mun samu umma a waje nan na zauna shagon wurinta muka gaisa.
Na cire dan hijab din dake wuyana sai na zauna sai yar dogowan riga yellow daya tsaya min iya wuyan kafa muna hira ina bata labarin accident din daya faru a hanya.
Umma ta matsu in gama bata labari ayi zancen daya dameta mota ya tsaya a kofan shagon ta da farko mun dauka masu tsayawa su sai kayan sanyi ne a wurin mu.
Saida mai motan ya bude ya fitone mukaga ashe Abdulhamid din ne ina jin umma na sauke ajiyan zuciya har abin ya ban dan dariya.
Yazon sun gaisa yake fadin umma tayi hakkurin rashin ganin shi a jiya wallahi matsala aka samu da Land lord nasu ya basu notis su tashi mai gida zai yi gyara na kuma bai basu notis din da wuri ba sai last week.
Nan dai aka tausaya mashi tare dan magana kan hakan yace yazone a tafi gun mai maganin kada dare yayi in kuma sai zuwa gobe ne hakan baida matsala zasu iya bari aje gobe din.
Umma tace ai ya dakata har hankalin shi ya kwanta zaifi tace ai ya bari harhankalin shi ya kwanta ya samu inda ya aje iyalin shi zaifi.
Da hausa nake fadin umma mezai hana ya duba bangaren nan idan zai masa sai yazo ya gyara su shiga har ya samu inda suke so.
Umma tace itama dai hakan ta gani idan wurin zai masa don zaman wurin haka ba kowa yana bata tsoro wani lokaci dakuna ukune da falo kitchen kamar yadda namu yake a sama.
Dakin bakine sai aka debi garejin mota daga gefen shi shi baikai namu dake da daki hudu ba a sama.
Umma tace dashi nace ba da wanan wurin zai maka ka duba ka gani sai ku dawo nan da iyalin naka har ka samu wanda kake so din idan kuma yayi ma shike nan ku zauna a ciki.
Da sauri yake tambaya ina wurin umma ta nuna mashi ya juya tace bari ta dauko key a bude ya gani ya ma rasa me zai fada a lokacin.
Ni ta tura na shiga na dauko mata key din ya bude ya shiga ya bude ko ina ya gani sai gashi ya fito yana wasan baki tare da fadin wuri yayi kyau sosai wallahi a nawa zasu dauka haya ke nan.
Da sauri umma ta tare shi da fadin ba wanan ya kiyasata ya gani ai yasan yadda ya kamata sai ya fadi yayi shiru na dan lokaci kafin ya dago yana murmushi yace dadai za a fada mai zaifi don kada ya shiga hakkin mu da yawa ba zai so hakan ba.
Shiru nayi ina sauraren su umma tace ai itace ya kiyasata yace to a raga mai ya bada dari biyu da hamshin a shekara idan bai tauye mu ba.
Umma tace dashi kabada dari da hamsi a shekaran Allah ya kara rufa muna asiri ya shiga mata godiya ba adadi.
A zuciyana nace ashe da tun tuni mun bada hayan wurin da mun dan samu mun rage ta wanan hanyar amma wurin yana kulle ba wanda aka bawa shi haya.
Yayiwa umma godiya sosai tare da addu,a kamar wanda zaiyi kuka a lokacin don bai taba zato ko tsamani zai samu ko kwatankwacin hakan ba a wanan halin sai gashi Allah ya kawo mai daga sama a cikin sauki.
Shiyasa kyautatawa yake da dadi koga wanda baka taba sani ba saboda baiga dai abinda yai muna ba har aka amince masa hakan.
Washe gari tun kan in fita zuwa school sai gasu da iyalin shi sun shigo gyaran wajen nan na fita na barsu suna gyara.
Ba abinda ya kara min dadi sai ganin su da yara maza nasan cewa Amar zai samu abokan wasa ke nan a yanzu yan uwan shi maza.
Ai kafin mu dawo daga school har sun kwaso komai nasu sun tare a ciki sai gidan ya dan canza min kamar ba gidan mu ba ga haske ansaka a ko ina ya kara haske wajen.
A gaskiya mutum dadi gareshi ko yayane don gashi mun fara ganin hakan tun yanzu nashiga gida umma ke fadin yau baki sun hanani bude shago sun tare aciki yau din nan.
Nace umma naga an gyara wuri yayi kyau sosai wallahi Allah ya bamu hakkurin zama dasu tunda musulmai ne yan uwan mu su tace amin nima adduan dana gama ke nan a zuciyana.
Wanan shine mafarin shigowan Abdulhamid a cikin rayuwan da ya shiga cikin labarin da zan baki nan gaba.
Satin mu daya tare dasu gaskiya ba wani matsala a tsakanin mu duk da ba zama nakeyi ba sai da yamma idan na dawo yamman ma ina shago amma na kula da yadda takewa umma biyayya sosai sun dauketa kamar wata yarsu ko yar uwa duk da matan takan dan so zama muyi hira saidai ban saba da sakewa mutane haka ba.
Ranan na takwas a gidan mu yazo da dare ya samu umma yana fada mata cewa mu fito muje don yayi magana da Alfa din yace yazo damu yau karfe takwasa.
Ba yadda na iya haka umma tasani a gaba muka shiga motan shi zuwa wurin a hanya ne yake ba umma labarin cewa.
Tun zuwan shi lagos yasan malamin sun zauna a unguwa daya dashi lokacin don shi dan lokoja ne ya shigo lagos wurun dan uwan shine daga baya kuma dan uwan nasa ya barshi ya koma cottono da zama.
Har dai muka kai yana bamu labaein shi a takaice har matar nasa da suke yan gari guda da ita daya aura yaren su daya dashi sai dai ita iyayyen ta na nan cikin lagos zaune .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , , ,
4️⃣1️⃣ BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HAKAM, , , , ,
ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA RIKE HAKKIN HAKA AKANKI BA, , , , ,
Wani tsohone zaune a cikin fararen kaya da farin gemen shi mai tsawo sai wano katon casbaha daya rike a hannun shi yana zaune saman wani farin dadduma mao laushi dakin sai kamshin turare yake tashi a cikin sa kokai waye sai kanka ya sara a wanan dakin don kamshi irin turaren da ya game dakin.
Muka shigo da sallama yana amsa muna da wa,alaiku mussalam da harshen yarbanci kafin ya juya wurin Abdulhamid yana fadin sune kazo dasu.
Yace eh wanan ce diyar tawa dana fadama tana fama da matsalan sai kuma wanan yar uwan nawa itace ta haifeta su biyune kanin ta yana gida mun barshi.
Dadtijun yace Allahu Akbar ya dago kai ya tsura min ido kuri kaman yana nazarina lokacin kallon shi nayi sau daya na dukar da kaina kasa don ba dabi,ana bane saka ido cikin na wani na dan lokaci mai tsawo haka.
Allahu akabar ya kara fada yana gyara zama tare da jijiga kanshi yace lalai yarinya tana da abubuwa a kanta masu girma saidai ba masu cuta mata bane don su din kamar na gadon gidane suke a jikin ta.
Zasu iya kareta a duk inda za,a iya cuta mata ko za a cuci wani sai kuma yai shiru kamar yana nazari a zuciyar shi sai can ya dago kai yana tambayana.
Omoge na dago kai don nice dai yan mata kadai a wurin yace ko zaki iya tuna haduwan ki da wani tsoho da kikai mai tallan magani kuma idan kin bayar ana dacewa sosai da maganin naki.
Umma na fadin wa Sahiba sam ai bata taba sana,a irin wanan ba yace ta dakata ni yake tambaya.
Da sauri na dago kai ina fadin eh na taba a baya na hadu da wani tsoho na fito talla ban samu abin dauka ba muka hadu dashi.
Shine ya bani sari kuma ya gwada min yadda zab dinga bayarwa in rudi mutane sai aka dinga saye sosai dana gwada din.
Ya dan girgiza kai yana murmushi kafin yace daga baya fa na fada masu kaf abinda ya faru na daina yace ki godewa wanda ya dakatar dake wanan sana,an .
Din sun so daukan ki zuwa ruwana kiyi kwanaki a wurun su da zaran kin fito zaki zama babban mamalawo don shi din ba mutum bane.
Mutanen ki yan ruwa suna da yawa a jikin ki sune kuma suke aiki da kakan ki a baya shine suka so komawa wurin ki lokacin.
Orishirishi Sahiba yaushe duk kikai wanan abin ni ban sani ba umma ta fada cikin damuwa tana kallona ta kuma juya ta kalli dattijun dake bayani.
Ba zaki sani ba ai don ba zasu bari haka ya faru ba yar ki nada wani irin tauraro mai haske duk inda take za a sanda ita haka wasu zasu sota wasu kuma da basu da zuciya mai kyau zasuji basa son ta sam.
Irin wanan ajannun na gode suna da wuyan sha,ani sosai koda ance za, a fitar dasu a jikin ta sau dai kawai su lafa amma basa tafiya suna tare da ita ko yaushe.
Sai ya kalloni yana fadin dai a cikin yarbacin da ake magana yarinya dan fita zan gana da iyayyen ki akan haka zanyi magana da ya shifi jinin ta kin san duk yadda yan uwa suke suna da dadin sha,anin sosai koda kuwa tasan su din masu matsalane a gareta.
Jin haka na bike gaba daya na bar dan dakin kafin su dade a ciki suna magana da umma ina waje na zauna ina faman bin mutanen dake zirga zirga a wurin da kallo.
Sunzauna sunbi layi suna jiran a akirasu lokacin don wasu ma a nan muka samesu wurin suna jiran iso daga gareshi ga kuma su umma suna ciki basu fito ba don ina jin maganan su daga inda na tsaya din .
Sai can suka fito din ran umma kamar a bace kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe daya haka muka shiga mota kowa baiyi magana a motan muka dawo gida.
Lokacin har yamma tayi sosai mun samu Amar a shago yana ciniki muka tsaya wurin shi sai da magariba ya kusa na mike na shiga cikin gidan mu.
Wanka nayi kafin lokacin sallah na kunna tv ina kallo kamar daga sama naji muryan ya Almustapha a gidan dan wajen gwaggo harin kaduna.
Kafun in tashi zuwa dakina har sun shigo shida Amar da umma Allah ya taimakeni a lokacin sallah kawai nake jira a tayar in tada nawa sallah.
Har ya zauna ban samu gaida shi ba saida ya zauna ya jawo Amar zuwa jikin shi suna hira da umma nayi mamaki yadda har umma ta sake dashi haka da sauri.
Yana tambayan ta yaya jikin tayi amfani da maganin ko ni mamakine ya cikani saida na mike nake gaida shi da zuwa daga haka na juya zuwa dakina.
Umma ta kirani tana fadin ban gane shi bane na girgiza kai na wuce ban tsaya ba na tayar da sallah har na idar ina jin muryan shi da umma din.
Mamaki nake daga