Showing 150001 words to 153000 words out of 382072 words

Chapter 51 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28344

Hankalin Nazifa da uwar yai mugun tashi tana fadin mama ya dawo kasan nan ban sani ba ke nan ko me mama ?
Bar dan iska daga shi har uwar tashi Addah idan ma wani makarkashiya suke kullawa ga hakan zasuyi kunya indai nice.
Don wanan auren mutu karaba dake dashi a duniyan nan har udan mashi din zubairu ya gani din.
Kira layin sa mu gani idan zai shiga mu tabbatar da zancen zubairu din idan da gaskene don shi ya faye shirme wani lokaci.
Nazifa ta dauki wani layi tana kiran shi sai kiran ya katse don yayi blocking din layin ta ga baki daya ba zata sameshi ba lokacin idan bashi ta cire hakan ba.
Kira barkatai yana mata haka ta kalli uwar tana fadin kiran yaki shiga umma kanwarta dake gefe tace da ita.
Mama a gwada kiranshi a layina idan zai shiga mu gani ana saka layin aka kira sai kiran ya shiga saidai bai daga kiran ba har ya katse.
Duk sun zuba mata ido ta dago tana fadin kiran ya shiga saidai bai daga kiran ba a lokacin don dama yana suspecting din kiran nasu ne ya shigo mai don ba mai kirashi da baida layin shi a wayan shi.
Gashi kuma ba kowane yasan da yana kasan ba da zai kirashi washe gari kuma ya nada ya tafi abin shi bai dawo ba ko mommy bata san yayi tafiya zuwa Abuja ba wani aiki a lokacin.
Washegari bayan sun gaji da zancen ne suka kira layin hjy Addah kira uku bata daga ba don in takirasu haka suke mata sai anga dama a daga mata kiranta.
Gashi ta rama kuma sunajin haushin hakan da tayi suna fama zunduma mata zagi sai gashi ta daga kiran.
Suka gaisa sama sama kafin suce da ita ashe moddibbo ya dawo garin bamu da labarin hakan hjy tace dasu oh baku da labarin dawowan shi ashe yanzu ko ai sati uku yake nema a garin nan ke nan.
What sati uku Addah amma daga ke har dan naki baku da mutunci ashe haka in ba aure kaddara bane mai zaikai Nazifa auren modibbo har kuso ku rainawa mutane wayau haka.
Kashe wayan mommy tayi don zuciyan ta ba zai juri jin wanan zagin da hjy din take mata ba alokacin .
Don zata iya ramawa hakan kuma zai haifar da matsala sun yi ta kiranta taki daga wayan sai da suka hakkura suka kyaleta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , , , ,

4️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL HALIM, , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA HAKKINSA BA DON NA KUDINE, , , , , , , ,

Allah ya nufa na zana exam dina na karshe a makaranta saura jiran jerabawa a garemu da fatan alheri yanzu kan sai kuma godiya a wurin ubangiji mai komai mai kowa daya nufeni da gamawa lafiya ba tare da samun wani tangarda ba a cikin karatun.
Yanzu fadi barnan lokaci shiyasa ake son iyayye su dage sosai a wurin yiwa yayan su addu,a musanman ke uwa don addu,an ki karbabane a wurin ubangiji ga yayan ki.
Tabbas ko rantsuwa nayi bana kaffara akai don adduan umma akan mune ko yaushe shine kuma ke bibiyan mu ba zama rokon abin duniya takewa rayuwan ta ba hakana.
Sahibat kan ba sahiban da yan kaduna suka sani bace a baya yanzu wanan sahiban idon ta ya bude sosai ta zama first clasa ko a cikin lagos din a yanzu.
Ba sahiba kawai ba har mahaifiyarta da dan uwan ta cigaban Sahiba suma ya jawo masi cigaba a yanzu.
Shagon sana,an mu shi kanshi ya girma ya zama babban shago wurin sarin yan guwa don kudin da nake samu idan ogan mu yazo kasan na aikin yawo da mukeyi dashi ga shago da karatun mu sai abinci kuma idan mun saye da yawa abincin zai daukemu har wani lokaci mai tsawo din baci mukeyi ba.
Yau ma ogan mu zai shigo kasan kamar yadda ya saba lekomu idan zai shigo din akan yo min aike a sabon wayana da yanzu ya canza min shi na ajewa umma nata ko ince na sai mata wanda yafi wanan sosai har Ammar.
Don canza wayan ya samo asaline ranan da mukai wani fita zai gana da wasu abokan sana, an shi dole mota biyu akai amfani dashi zuwa wurin meetung din.
Muna mota zamu tafi wurin ne aka kira layina naki daukan waya wani ya gani da kiran ya matsa na dauka yakai idon shi ga wayan .
Ammarne ke nacin kirana wai nabar gida ban aje mashi kudin exam din shi da nace zan bashi ba a cikin hausa nayi magana kada wani yajime muke fadi a lokacin.
Don in nayi turanci suna ji idan yarbanci nayi hakane zasu jini yasa na canza yarena da hausa ina fadin haba Ammar ka suba dakina karkashin filo suna nan na je maka kuma ka maida hankalinka wurin jerabawa kasan dai bamu da kowa Allah ne gatan mu a duniyan nan nima kaga karatu na dage nayi sosai Allah ya taimakeni ka daina wanan shegen game da kakeyi, karshe nace ka gaida umma kace mata mun fita ko,
A gaban mota nakan shiga tare da wanda ke jan mota idan zamuyi irin wanan fita daya kama na gaba dayan mu idan zamu fita sai in koma gaba suna baya su biyu.
Sam bai taba kullani ba ko ya nuna damuwan shi a kaina don da wuya inyi magana ma ya bani amsa direct yadda ya dace har na soma tsarguwan kaina da hakan.
Abin mamaki sai naji ana fadi idan zakiwa yaro fada ba haka ya kamata ki nuna masa ba ai ki daina ce masa baku da kowa mahaifiyar ku da dan uwan ki suba kowa bane a gareki ?
Saida na dan juyo nace dashi sorry sir a dan gimame daga hakan bai kara cewa komai ba tunane na lulayi na ashe duk lokacin dana canza harshe ina yaren hausa yana jina ke nan ban sani ba don bai taba nuna shi din ma yana da jinin hausawa a jikin shi don yafi shiga na kananan kaya ko ya saka irin jallabiyan nan mai tsada har wandon su na larabawa.
Lagos ce fa duk yadda ka dauko karyan ka sai kaga abinda ya rinjaye ka ga gani a wurin wani yasa idanuwan su ko dan wanki da gugane su a bude idon su yake a can.
Tunane na ya katse ne da yakecewa Felix ya tsaya wani shago sayar da waya ya fada mai ya fita ya zabo wayan mata iphone mai kyau ya sayo.
Felix din ya fita ya shiga shagon ya dan dade muna zaune saukin abin bai kashe mota ba AC na bugun mu a lokacin don haka ba wani damu .
Can sai gashi a lokacin har oga yaja tsukin dadewan shi yakai sau biyu sai gashi ya fito daga shagon rike da leda a hannun shi.
Yana shiga motan zai mika mai sai cewa yayi No give it to her ina zata bini da wanan matacen gwagwanin nata wai waya abin kyama kawai.
Mutuwan zaune nayi na kasa motsi kafin na mika hannu ina karba felix din yana min dariya don duk cikin su shine karami da Adnan sune kuma nawa yazo daya dasu.
Da kyat bakina ya budo nayi mai godiya da addua irin na musulmin da akaiwa alherin da bai zata ba ga wanda yai mashi kyautan.
Jin cewa zasu shigo aiki ranan tallata yasa na fito falo na samu umma a zaune nima zaman nayi ina saye da rigan barci mai sulbi sai zani dana daura daga sama sai hula baka iri mama cap din nan da akeyi a lagos yanzu a kaina.
Baki barci ba ashe umma tace dani na danyi murmushi ina fadin banyi ba umma yanzun suka turo min da sako wai ranan tallata oga yana gari zamu fita.
Tau aikin ya tashi ke nan wata uku yayi ke nan har zai shigo nace zai shigo umma ni aikin nan nasu ya fara fita min a rai yanzu umma.
Da Allah zaisa na samu aikin gwaunati zan daina wanan din tunda ba na dindindin bane shi na kama na gwaunati din zaifi.
Wanan din ma ai yana kokari sahiba ina laifin hakan da muke samu mutanen nan sun taimakawa rayuwan mu sosai a baya har ina zargin aikin da wani manufa kukeyin shi sai daga baya na gane aikine kawai dai na taimako Allah ya kawo muna a rayuwa.
Hakane umma mun samu sosai a wanan fammanin shiyasa nake son kada in shagala dasu zan fara neman aiki na dindindin a yanzu gaskiya.
Yanzu dai dole gobe in fita na samo dan rigunan da zan saka wanda zai fiddani nayi amfani dasu a wanan aikin ke nan don ban son tsarguwa ga hakan.
Akwai kudi a hannun ki ke nan ko na dauko maki wanda ke hannuna ajiye umma ta tambayeni nace da ita a, a umma wanda ke wurina zai isheni ai don ba wasu masu tsada kwarai zan saya ba.
Wani mai kudin idan kana tare dashi yana maka yafi son ka nuna yana maka din don haka ko kwara biyune dai ki sayo masu tsadan zaifi ummata fada.
Washe gari na shirya da dan rana misalin shadaya da rabi na fita naso zuwa shagon mu nayi sayayya a can sai kuma na fasa na nufi wani sabon shago dake Agege na gown din mata wata bazabarma ce bude shagon daga ghana tana shigo da irin gown din nan na dubai dinkakku.
Na shiga wurin suna haba haba dani aka ban wurin zama da drinks da ruwan gora yan matan dake tsaron kayan suka fara zuwa suna gaidani.
Saiga wata mace gajera kamar ta taba ganina ta nufoni a cikin fara a tana fadin sannu da zuwa kanwata barka da shigowa gidan nan.
Me za ai maki gyaran kai da kafa da yatsun hannu ko dress ga kikazo duba kawai na dan murmusa sai naji sha,awan gyaran kan ban san lokacin dana bude baki nace kai zan gyara da jikina sai dress din.
Wasa wasa sai gani a shagon nasu har uku na rana suna min gyara an gama ta fara nuna min kaya tana fadin kinga ke mysulmace wanan zai fitar dake da addinin ki zaki haska sosai month dinga ne suka fito ba kowa yasan su ba a kasan nan.
Kala hudu kawai na zaba a shagon na biyasu kudin su na fito har mota suka rakoni da kayana na shiga naja zuwa gida.
Wasa wasa saida ya share wata kusan biyu bai dawo kaduna ba yana can aiki ya hanashi dawowa a kuma tsakanin an kwasa tsakanin iyayyen Nazifa da nasa don kowa ya hau a lokacin wanan ya kara bude sabon babin kiyayya a tsakanin su sosai a lokaci.
A cikin wanan haklin ranan ya dawo gida duk daya gaji gidan su ya nufa kai tsaye an tareshi taro mai kyau duk da bai samu mahaifiyar shi a gida ba ta tafi barkan haihuwan kanwar hjy karima ita da hauwa da fa,iza sai Nabila ce kadai a part din don haka bayan ta bashi abincine ta kira mahaifiyar su a waya tana sheda masu zuwan yayan nasu.
Hjy tace ya jiramu gamu hanya tafe yanzun nan kafin su dawone Nabila ta tsegunta mashi duk abinda ya faru tsakanin iyayyen su da iyayyen matan nasa .
Amma kuma ta rokeshi kan kada ya nunawa mahaifiyar su cewa ta fada mai komai don zata yi mata fada saboda tace kada wanda ya fada mai wanan zancen idan ya dawo.
Ko lokacin daya fada cewa zai dawo ba abinda zai fitar da mommy din a wanan lokacin koda suka dawo din ma ta fara zargin Nabila din tana tambayan ta yace ban san ida ta shiga ba tunda ta ban abinci ta shiga ciki.
Zama tayi suka gaisa dashi da yan uwan shi kafin ta dauko mai zancen matar shi da cewa ka samu ganin ita Nazifa din kuwa.
Hannu ya cire a goshin shi daya dafe yana jin zuciyan shi na masa kuna a lokacin yace da mahaifiyar su din daga airport nan nanufo direct.
Basu san ka dawo ba ke nan yace yanzu ne fa saukana mommy ba sune a gabana ba dama a yanzu barsu can su zauba su huta nima a yanzu aiki yayi min yawa ai.
Horon ya isa haka duk da nasan sai kakai kanka garesu sun fada ma abinda sukaga dama yadda suke so don sin dauka da zafi.
Murmushi ya dan sake a fuskan shi ba tare da yayi mata magana ba ya mike yana fadin zan isa gida in watsa ruwa a jikina.
Yaushe zaka tafi ka dawo dasu yace sai naje gidan ya fita ta bishi da kallon tausayi don tasan donta yake daurewa komai da ake mashi din.
Haka ta zauna a wurin ta kasa komai don tunanen daya dameta kan auren dan nata daya dauko sabon sallo na son mulkan shi kota halin kaka shi kuma yaki yarda da hakan.
Ya isa gida wankan yayi kamar yadda ya fada ya fitone ya dauki wayan shi ya fara aiki a cikin sa yana neman wani labarin da yake so a cikine yaga taron manyan yan kasuwan da za ayi a garin kaduna din ranan Laraba mai zuwan nan.
Murmushi ya sake yasan zai samu dan haske ga abinda yake son samu da dadewa a wurin don haka ya hake wanan ranan yana murmushi.
Tun a daren ya bugawa duk wanda yake bukatan aikin nan dasu ya sanar dasu shirin shi da zai aiwatar a wurin.
Washegari shiru shiru mommy bata ji motsin shi ya shigo gidan ba har yamma ga wayoyin shi baya shiga a lokacin suna rufe.
Hankalin mommy ya daga take zaton ko yaje gidan yayan nata ne kamar yadda ta umurce shi wani abu ya faru dashi a can don tsoron ta Allah yanzy tsoronta yayan nata .
Tunda ya iya furta cewa a gaban ta yake fadin Aliyu kai ba komai bane kuma ba kowa ba kawar dakai da dan naka ba wani jan aiki bane a wurina.
Cikin karfin hali shima mijin nata ya mayar maida amsa yana fadin Nuhu kayi sherin ka ka barni don ta Allah ba taka ba duk kace zaka tabani ko ahalina wallahi karyan ka ya kare a garin nan ke nan.
Wanan hasumin mommy ta rike a zuciyar ta duk da manya sun shiga zancem sun sulhunta su an raba irin wanan fadan sunce sun bari.
Saidai sanin halin yayan nata da tayi yasa tasan zancen bai fita zuciyar yayan nata ba duk ya ce ya sake komai ya wuce tasan yana rike dasu rikicin duniya da mairai akeyin sa.
Ga dan uwan haihuwan shi Alh gyade ya nakasa yanzu baida wani moriya daga tsaye sai zaune bai iya komai anje asibiti da gurin yan tsubbo abu ya gagara tun lokacin har yanzu kuma ba a fasa ba don har kasan an bari dashi ba a dace ba.
Hankalin hjy bai kwanta ba sai lokacin da suka samu wayan shi ya shiga ya sheda masu cewa shi yana Abuja a lokacin.
Amma ka daina halin nan modibbo duk kabi ka dagawa mutane hankali har mahaifin ku na kira na sheda mashi bamu jika ba tun jiya.
Haba mommy sai kace karamin yaro tace umm, umm bari wanan lokacin da ba a dauki rayuwa a bakin koma ba ba yaro ba babba a wurin yaudara.
Yana dariya ya kashe wayan shi yana fadin a zuciyar shi ba inda zani mommy sai sun gane basu da wayau idan ma zai karbi yarsa ne ya karba wallahi.
Fita yayi zuwa wani unguwa a can samarin gidan su Nazifa suka ganshi har gaisawa sunyi dashi yayi masu alheri sukai godiya suna jin dadi.
Suka dawo gida suna murna suna da alherin da yayi masu din suna fada suna kari a cikin murna da farin ciki mamakine ya kamasu yan gidan abinka da gidan yawa take zancen yakai kunnen Nazifa.
Aiko har wajen Alh Nuhu yaji kamar ya hade ranshi a lokacin don takaici da bakin ciki yana fadin watau yaron nan ni zai nunawa shi dan iska yake ko ?
Shima kuma din yayi hakane don ya tura masu sako ta yayan shi su san su suka dauku Nazifan a bakin wata tsiya yayi alkawarin ba zai tafi ba sai ita data bar gidan don kanta ta gaji ta dawo.
Nikan zance shawaran umma yayi min rana sosai don naga fa,idan shawaran a yanzu tunda na fara aiki dasu wanan ne karo na biyu da zamu bar lagos zuwa wani gari na farko muje abuja dasu mun dawo a ranan.
Ga wanan katon


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login