Showing 174001 words to 177000 words out of 382072 words
mafalki da ita da wasu abu suna bina a baya zasu kamani kuma na fada maki tun kan muzo nan din.
Driver kan sai gudu yake shararawa da motan har muka kai gidan nasu a waje muka samesu da Felix da Jimoh zasu fita.
Fasa shiga motan yayi ya tsaya da mamakin ganin mu mun dawo lokaci yana kallon yaga hankalin su a tashe suna fitowa sai fada mahaifiyar su keyi abinda yasa ya fara takowa zuwa inda suke ke nan.
Baku sameta a gidan bane ya tambaya farko mun ko sameta saidai zance ya juyane kuma uwarta fada meya faru tace ka tambayi wanan yar ita ta gani koma meye tasa mu tasowa yanzu mu bar gidan idon shi ya lumshe yana fadin ya Allah.
Dama nasani nasani mama kada dai kice zan rabaki da kawarkine na yarinta don a tare na taso na ganku kike fada amma wanan matar yanzu ta canza saboda kudi.
Babu abinda zai faru dasu mugun abinta ya koma akanta ya bita ita da yaran ta yanzu kin riga da kunfi karfinta ko a duniya.
Duk suka tsaya suna kallona a inda nake tsaye kafin tayi karfin halin fadi No ki bari ke yarinyace baki san komai ba mun dade tare da ita mutane suna gada min wanan maganan gashi yau ya zama gaskiya .
Mommy idan baki yarda ba zata kawo kanta gidan nan a yau din nan ta roke gafara don tana can cikin wahala yanzu haka mun barta abinta ya koma a kanta.
Itace ta kiraki da safe kan kada ki wuce ba kizo gidanta ba kikai mata alkawarin zuwa din kafin kizo ta shirya abinda zatayi maki din taso amfani da jinin kune kawai ko naki kona yarki.
God forbid bad things Allah ba zai bata sa,a ba har abada cool down mommy zata zo yau din nan ta sameku ai na fada na juya zuwa wurin da abokan aikina suke na barsu a nan suna kara tataunawa akan zancen.
Karshe dai ogan mu bai fita zuwa inda zasu tafi ba din suka kwasa suka koma ciki don suna gardama cewa kodai firgitasu nayi kawai ba abinda na gani zan hadasu da mata yar tace ai a bari a gani tunda nace zata kawo kanta garesu ranan.
Duk muna falon gidan a zaune har su wanan lokacin hiran kasuwanci ake da mr Jimo muna sauraren su, muka jiyo hargowa a wajen gidan.
Felix ne ya mike yana fadin ihun meye haka yake ji a compound din gidan yana fita yake wanan maganan sai gashi baikai ga fita ba sun juyo da maigadi yana fadin.
Hjy na dat that ur friend come de shout ebi like say she don be mad today wooo .
U no here how she de shout ur name, saying dat make u na forgive am woo , d tin meke me surprisee amm woo, which one of my friend ta tambaya yace dat big Alaja who de always come dis house if u are around.
Tayi wani irin tabawa tana fadin shike nan batu ya zama gaskiya ke nan shi ya mike da sauri suka bi bayan shi zuwa waje a cikin mamaki.
Daga hjyn har diyanta duk sun firgice suke suna kallon kofa har yemisi dake wurin a tare damu don duk mazan sun fita a lokacin.
Sai gasu sun shigo falon tare da ita lokaci guda tana faman soshe soshe tazo gaban hjy takai gurfane tana fadin kimun rai ki raimakeni.
Nayi kuskure danayi kokarin taba ku nayi kuskure ba yau ba ina kai maki hari dake da yayan ki kuna kubuta daga track dina yau nayi niyar in gama daku gaba daya don haushin da nake ji naki na kin fini da komai diya ta nuna yaran kudi da gida da komai kin fini Fatma kin fini why zaki fini yanzu bayan nasan na fiki komai muna yan mata.
Hannu bibiyu hjy ta dora a kai tana fadin mabinu da harshen yarbanci tare da fadin na shiga uku dama haka kike mansura ban sani ba.
Ta kai ga cire dan kwali tana fadin ki min rai ki taimakeni nasan nayi ba daidai ba gareki don Allah ki yafe min ki yafe mun fatima tana hada hannayen ta wuri daya.
Hjy din da yar ta suna ja da baya ganin haka na dan tako zuwa inda ogan yake tsaye ina fadin yace ta tafi daga yau ta fita hanyar su ga baki daya.
Haka yayi sai tayi wani irin lankwasa can ta dago bata ko tsaya kallon su ba tafita daga gidan kamar mahaukaci duk wanda ke wajen lokacin jikin shi yayi sanyi sosai lokacin.
Mommy kan ta gaji da korafin nan nasu a yanzu don har tsoron ganin kiran wayan Nazifa take yi don tasan karane zasu kawo mata a lokacin.
Yauma din dai tana jin kiran ta saida gaban ta ya fadi tasan magana gudane dan kullun tana dauka ko sallama babu take fadin.
Nagane kece ke daurewa Abubakar yake min wullakanci idan bashi ba don me zaki dinga bashi abinci a gidan ki yaki cin girkin mu a nan.
Nazifa kinsan da wace kike magana kuwa nasani mana ba mommy bane ta fada a lalace tare da fadin kidai ja masa kunne kuma ki kiyayye mommy na fada maki don ni yake aure ba ke ba .
Tana fadin haka ta kashe wayan tabar mommy din tsaye da mamaki da al,ajabin yar nata kota manta da bayan uwar mijin ta take ita din kanwar mahaifinta ne ita.
A haka yar ta Nabila tazo ta sameta tsaye tana mamakin ta ganin mommy a haka take tambayan ta mommy meya faru halan dawa kike waya ?
Ta sake kallo yar nata da mamaki tana fadin barni Nabila yau kan naji abin mamaki a rayuwana duniyan nan waini Nazifa zata kira tana warning dina akan yayan ku.
Har da fadin wai idan ni yake aure sai naci gaba da bashi abinci gidan nan yanaci what mommy nazifa din ta fadi haka .
Yar abu kazan kazan nan wallahi bata kai yar iska ba tunda bata fadi a gaban yaya ba shigiya mai gadon iskanci kawai.
Ta shiga zage zage a dakin hjy din tace da ita tayi shiru kada wani yaji wanan cin mutuncin ko nabila din sai bayan ta fada mata taga yadda take fadan tayi da ta sanin fada mata ko meye.
Saiga hauwa ta shigo dakin ganin su hakan itama tambaya take wanaji kina zagine haka tun ina waje ?
Bar yar iskan nan Nazifa wai waya ta bugowa mommy na kai nabila kinga halin kike wallahi yanzu kun fara wanan zancen ke nan a gidan nan har hjy karima taji zancen nan.
Karshe ta kama yadawa a gari gari ya dauka kunsan halinta kuma sarai kan urin zancen nan.
Wai meta fadane haka hauwa ta kara tambaya tana kallon nabila tace wai cewa tayi fa idan mommy na auren yayan mune ta sani jimon yar iska wace bata samu tarbiya a gidan su ba kawai.
Kuma uban nan idan banje gidan nan na casa Nazifa shegiya nake don wallahi ban yarda da wanan cin fuskan haka na wullakanci.
Kada ki soma wallahi dama nayi take nema ita da iyayyen ta ba wani aiki bane yanzu mahaifinta yace zai sabauta rayuwan mutum kan an taba mashi ya kun sani.
Mommy sai a barta ta dinga yiwa mutane irin wanan iskancin nan tanaciwa mutane fuska ko yaushe .
Tsawa mommy din ta dakawa hauwa din ta hauta da fada sai hauwa din ta tashi ta fita daga dakin ta mayar da kallonta wurin Nabilan tana fadin kinsan hauwa fa tafiku zafi meyasa kika fada matane wai ?
Mommy zagin yayi muni dayawane wallahi amma barta idan ta kara wallahi bazamun kyaleta ba Allah ta mike ta fita hjy na nadaman fadawa yayan nata mata a lokacin.
Don tasan diya mace dajin zafi da kishin mahaifiya idan an taba maka uwa yadda kake ji a zuciyar ka.
Hauwa,u ko tana shiga dakin waya ta dako ta fara turawa Nazifa zagi ta uwa ta uba ta zage ta tas ta tura mata nabila na shigowa ta ganta da wayan take tambayan ta tace zagi na turawa yar banza taji inda dadi.
Idan anyi magana sai mommy tace wai a kyaleta don ubanta ubanta shi Allah ne da za a ji tsoron shi ?
Zaune take a cikin fushi da dan jin sanyin yadda tayiwa mommy din yau itama ko banza taji zafin da taji haka kawai zata batamasu shirun su bayan sun kashe kudi mai yawa su tafi a banza.
Hauwa aida kin barta sai mun hadu ba zamu hadu da itaba watarana sai mu nuna mata ai mun sani musan kai komai.
Wai anty tsoron ta akejine wai da zataci bulus ta zagi mommy a banza a kyaleta koshi yaya yaji bazai kyale wanan cin fuskan ba ai.
Ba fa zai kyale ba ni don mommy ne kada tace ta hanemu saida muka tayar da zancen kuma tunda bata son anty taji.
Taji mana ke barin fada maki nifa yanzu ban tsoron kowa wallahi duk wanda zaiji yaji ta zagi uwana na zagi uwarta da ubanta ba shike nan ba.
Waike har da ubanta kika zaga dama nabila ta tambaya tace me zan tsaya jira da yar banza cewa nayi ita tsafi uwar ta tsafi ubanta tsafi.
Kai hauwa baki da kyau wallahi kin mun daidai iyaka dai mommy tayi fushi shike nan ai.
Ranan kan sai waya na bugawa ummana kan cewa a gidan zan kwana har hjy ta karba ta roki umma din da kanta don yadda na nuna mata din na damu.
Don abinda ya faru ina fita tare da abokan aikina muga tafiyan hjy mansura sai hjy fatima din tace Sha,aban tell me inda ka samo yarinyar nan haka mai abin al,ajabi ?
A wurin aikin mu take hjy nan dai ya basu dan labarna daya sani da irin taimakon da nayi mai a rayuwa yake fadin she is tellent in dat way.
But a nan suna fadin wai jinnune a kanta eh sudin ne sune aike irin wanan aikin dama mostly ana samun su sosai acikin al,umma amma sai a mayar dasu abin wani tsoro ko mugaye kuma is natural habit din su suna gani sun sai mai zaifaru dakai.
Aisha ce take fadin amma dai a nan zata kwana tare damu yayana yace ina fa ita kuma gidan su fa idan ta kwana nan din.
Ai gaskiya Aisha ta fada gaskiya takwana damu a gidan nan yau don bazan iya kwana mu kadai a cikin gidan nan ba.
But mommy ba gamu ba a gidan ga Felix i beg idan ba zaka iya rokonta ba ni zan roka ya kara bata fuska shi ta yaya zaice ta kwana dasu bayan babu kwana acikin aikin su.
And beside mutanen nan suna da kokari sosai dashi kada fa hakan yazo ya jawo mata wani matsla ga yarinyan nan kan hakan.
Ita da kanta tasa Felix ya kirani take fada min bukatan su a take na bata raina Allah ya gani ba zan iya kwana ba tare dasu umma ba.
Sai naji tana fadin ummaki kike tsoro ko Sha,aban ya fada min komai ki kira mahaifiyar taki in fada mata da bakina please ki taimaka muna gobe da yamma zamu bar garin nan zuwa jos daga can zamu koma insha Allah.
Wayan na dauko na fara kiran layin umma din ta dauka tana fadin a sahiba na kira dazun baki dauki wayan ba.
Umma ina lafiya zaki dawone yanzu ta tambaya sai na mikawa hjy din waya don irin kallon da takeyi min lokacin har lokacin umma na min addu,a Allah ya dawo dani lafiya.
Tace hjy ba yarki bace nice mahaifiyar ogan su da mukazo addua don Allah ina son ki ara maki yarki na yau don gobe zamu koma ta kwana a wurin mu ta taimaka muna da shiri.
Kai kai hjy idan bake ba sam ba zan yarda da wanan ba yata marainiyace ban son wani abu yazo ya same ta a waje.
Insha Allah ba abinda zai sameki lafiya zata dawo gareki insha Allah ba komai don Allah a rike min ita amma ta fada tana kashe wayan.
Sai wayan shi yake dakila bai yarda ya dago kanshi ba kuma yana jin abinda duk akeyi a wayan.
Sai yamma muka fita tare dasu sayayya sukayi sosai har ni na samu shiga an samo min kaya kusan duk abinda Aisha ta dauka a wurin zatace nima indauka.
Muka dawo gidan bayan anyi sallah ne mukaci abinci dakin su muka kwana duka mu uku a tare ranan.
Washegari tun safe ake shiri karfe ukku suka dauki hanyar airport tare damu bamu dawo ba saida jirgin su ya daga muka dawo muna dawowa kayana a hade suke na shirya sai gida ban tsaya bako na minti biyu don dama na kagu in tafi gida.
Yana zaune sai kai yake kadawa daga zaunen yana kara nanata sakon Hauwa,u din a cikin wayan matar shi din dake tsaye a kanshi tana girgiza jiki don ranta ya gama baci sosai lokacin.
Meya kawo wanan zancen haka ya kara tambaya yana kallon ta tace na fada ma cewa ban sanni ba jin haka yasa ya mike da sauri ya tare da jawo rigan shi ya saka ya fita katfe takwasa na dare.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
5️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUQIT, , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
Ya is gidan suna zaune a falo suna kallo bai tsaya komai ba sai inda hauwa take zaune ya daga hannu yakai mata naushi ta gwauce bai sameta sosai ba ya kara kaiwa zai buga .
Da sauri Nabila tace a, a yaya ka tsaya mana kaji ba,asi zaka kama dukan ta haka bayan matar kace ta zagi mommy don me ba za a zageta ba itama ?
Da wani irin mamaki ya juyo yana kallon Nabila din tare da fadin ta zagi mommy fa kikace nabila tace kwarai yaya shine ita kuma hauwa ta tura mata da sakon zagi din.
What ita Nazifa din ta zagi umma how comes har ta iya zagin mommy akan me zata zagi mommy din ?
Kan abincin mana wai mommy idan ita ke auren ka taci da baka abinci idan basu saka kafan wando daya da ita ba.
Ita Nazifan ta fadi haka ya tambaya a cikin mamaki yana lallon kanwar tashi Nabila tace wallahi yaya itace ta kirata ta fadi hakan a gaban mu.
Yayi wani irin juyawa zai bar falo lokacin har mommy dake ciki cikin damuwa abinda surukar nata tayi mata yana cin zuciyarta tafito don jin hayaniyar su da tayi a falon.
Wai meke faruwa ta tambaya daga inda take tsaye tana fito zuwa falon hauwace ta turawa nazifa zagi shine yaya yaji yazo yanzu.
Na fada maku kada inji an tayar da wanan zancen ya fita baku jiba watau har saida kukayi yadda kuke so ko ?
Au da gaskiya ke na ma ta bugowaya din ya sake tambaya cikin mamaki nabila tace ta bugo mana kai baka yarda bane dama yaya.
Kai yasa zai fita daga falon mommy ta dakatar dashi da fadin kada kaje kace mata komai kyaleta iskancin kurciya ke cinta ai itama mace ce zata haifa.
Baice da ita komai ba yasa kai kawai ya fita daga gidan ranshi bace ya shiga motarshi ya tayar ya bar gidan.
A lokacin ne kuma hjy karima da suke jin hayaniya suka fito ta daiga fitan shi a cikin fushi amma bata samu jin kome ke faruwa ba a lokacin take tambaya meke faruwa ne wai ?
Nabila tace a, a hauwace yaya yakewa fada ba komai bane me hauwan tayi mai ta sake tambaya ba wanda ya bata amsa tace to kuma ku daina rashin ji mana kullun aitama fada baka barin abu hardai ta juya ta tafi ta koma part din ta.
Koda ya shigo ya samu har tayi barci irin matan nan ne dake barci suyi dadaya da cinyoyin su waje su sake tsirecin su don dadin barci.
Duka yakai mata a cinya yana sake tsuki gata yanzu tayi wani irin kiba don dadin data kara samu a yanzu din hankalinta kwace a gidan mijinta.
Ke tashi yace da ita a cikin takaici yana kura mata ido ta dan muskusa ta juya tana fadin