Showing 18001 words to 21000 words out of 382072 words

Chapter 7 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28421

mama cewa yayi in zo gida uwar tace ya dawo ne ko daga can ya bugo waya yana fadin haka.
Ya dawo umna don kawai bai sameni a gida ba naje aurin barka shine na dawo yace kada inyi girki inbar masa gidan sa.
Wanan ai daji wani sherine aka kulla a hakan amma haka kawai daga dawowan shi don bai sameki ba zaice wai kizo gida kuma fa mama cewa nayi gida nazo amma bai yarda ba ta kalli uwar.
Keko ya raina gidan namu mana ya manta a dai ya nemeki har ya aura kika hayayyafa dashi.
Kai kai tir da wanan halin mahaifin hjy karima dake fitowa daga bandaki yake fadan haka da buta a hannun shi yana kallon su.
Yanzu ke kande da zaki mata fada kan abinda ta aikata ba daidai bane tunda kin sani amma kike fadan wanan ga yarki da tayo ba daidai ba.
Shin kinsan girman zunubin da kika aikata ga hakan ko karima malamai da masana sunce da mijin mace yayi tafiya ya dawo gida bai samu matar shi a gida ba .
Gara ya samu gawan ta ace ta mutu da yasamu ta fita bada izinin shi ba ya fada yana binsu da kallo.
Ba komai ke damun ki ba karima sai shegantaka irin wanda kikaga uwarki tanayi a gidan nan ya kawo hakan.
Yanzu malam ni meye laifina a cikin zancen nan da zanka dauki laifin ka dora min nima ai idan nasan ita keda laifi nima ba zan kyaleta ba ai tunda mijin ta shine komai namu a yanzu.
Don haka ba zanso ta saba ba saidai a kan wanan dan zancen kawai zai turo muna ya gida da yamman nan.
Shine namijin kwarai malam ya fada yana kaiwa zaune bayab ya gama kallon iyalin nasa yaci gaba da fadin idan bai turota gida ba a yanzu ai ba zamun san abinda take aikatawa ba din.
Tabar gidan mijin ta bada izinin shi ba ta tafi wani wurin da ba wanda ya sani koke kin san inda ta tafi ?
Yarinya tayo laifi tazo gida ta kawo kara ba za a tsaya ayi bincke ba a bata laifin ta don gobe kada ta kara sai kawai a mara mata baya karshe auren ya mutu
Sai daga baya azo ana da an sani mafi yawan auren dake mutuwa a yanzu sakacin kune na iyaye daga dan magana kadan sai zancen saki ya biyo baya an bata goma daya bai gyaru ba irin wanan hasalan banzan da yanzu kikayi.
Yar kice mai laifin amma kina kokarin daukan laifin ki dora akan wani can da baiji ba gani ba har kina fadin wai ba banza bane wanan abin .
Idan ba banza bane shegan takane ko me yanzu yarinyar nan bata rasa ci ba bata rasa sha ba a gidan mijin ta amma don jin dadi har zata sa kafa ta fita bada izinin shi ba.
To ai malam ni ba nabi ta nata bane ganin zancen nayi dai ba wani zance bane wanan ya dago yana fadin agareki yake ba komai ba shi da yasan kansa ai kinga ya dauki matakin daya dace.
Nan dai yayi ta fada har akai kiran sallah ya fita ya barsu a wurin kamar jira asmau keyi ya fita sai ga sallamanta ta shigo gidan.
Da sallama sama sama tana fadin shi wanan tshon me yake nufi da zai turo ki gida a yanzu don kawai kin fita baya nan.
So yake ya mayar dake matar gida matar kulle irin kidahumar matar shi ko me da zaizo ya tayarwa mutane da hankali haka ne.
Nima shi nagani yar nan amma malam ya tatare don yana na miji dan uwanshi yace kada ai maganan wai karimar ce bata da gaskiya.
Humm baba baisan komai ba wallahi mama idan kinji tarihin uwar gidan nan nasa sai kin san karima bata gane ma koma a gidan nan.
A ko banji ba ai naga yadda take shimfida iko da idona don ko yayan data haifa iko take da abinta balle wani.
Indai zaku tashi tsaye idan kuna son zaman ta gidan nan wallahi ku tashi don in ba haka ba kuna kallo zata koma bora da karfi da yaji a gidan.
Aiko ba akai ga hakan ba don duk inda zan shiga in fita a gidan nan sai nayi don yata ta kafa nata gwaunatin a gidan.
Mama ni ba wanan ba kinga wanan dan nasu da suke ji dashi kamar kwai duk ilahirin zurian su yanzu kowa jinsa yake idan yana wuri ba a kallon kowa bayan shi.
Ba kinji ba mama dama irin matan nan ai ba kansu suke asircewa ba har da diyan da suka haifa sai sun nema masu farin jini.
Amma idan kaji Allah a bakin ta sai kace yar wani shehi ce ita wurin kawowa mutum Allah kusa.
Sallah da basuyi ba ke nan akan lokaci daga uwar harsu suna zaune suna kullin sheri a daidai wanan lokacin kuma hjy Addah tana can saman sallayanta ta mika bukatan ta a wurin Allah.
Har aka kira isha,i ta tashi ta mike ta gabatar ta dan dade a zaune tana addua kafin ta fito don shiryawa maigidan abincin dare akan lokaci tunda tasan baici kome mai nauyi ba tunda ya shigo gidan.
Saida ta gama shirya komai ta koma dakinta ta yi wanka ta tsula kwalliya kafin ta fito daga dakin.
Lagos Ajagule ruwa sahiba ta mika ma Amar dake kwace ya hade maganin data bashi kafin ta juyo kan mahaifiyar nasu da ledan maganin da ruwa tana kokarin barewa umma din nata.
Duk uwan na kallonta tana faman sake sake a zuciyar ta kafin Sahiban ta juya ta dauko ledan abincin da aka bata din ta fara budewa a gaban kanin ta data tayar dashi yasha magani ga abinci kuma duk da bata san wani kalan abinci bane a cikin ledan.
Tana budewa wani kamshi ne ya daki dakin sai da kowa ya kai idon shi kan miyan kafin itama ta dago kai ta kalli mahaifiyar su tana fadin.
Umma wanan abincin zaikai dubu biyar fa ko yafi haka ji irin girman naman dake cikin umma ta dago tana nunawa uwar miyan.
Kallon da mahaifiyar ke matane ya dakatar da ita daga maganan da takeyi din Sahiba uwar tace sai diyar tayi kasa da kanta cikin ladabi.
A tunanen ki idan naso mu rika cin wanan ko yanzu da banda lafiya na gaki ba nasan zaki iya kawo muna abinda yafi wanan din ma idan munso hakan.
Sahiba bata gane inda uwar ta dosa da zance ta ba sai da taji uwar mu matane kuma cikin bariki muke rayuwa muna da hanyar yin hakan ko karfina ya kare ga naki a yanzu.
Saidai ni ba abinda ya kawoni nan ke nan jin dadi na banzatar da rayuwaba da naku ba nazo nan ne nabaro yan uwa da kowa nawa don wani dalili mai karfi a garemu baki daya.
Saidai me idan kin fara ganin irin hakan dole ne duk ki yarda wanan tsarin namu na baya tunda naga kinga wanan kina farin ciki a yanzu.
A , da farko naso na hana ki cin wanan abincin amma daga baya da nayi tunane sai nagane gaskiya Allah ne ya tsaga hakan yau a garemu ya kawo muna wanan kyautar a matsayin abincin mu.
Amma said, sa hakan bai kwantar min da hankali ba don na kula a yan kwanakin nan abubuwa sun soma faruwa dake Sahiba.
Don tun ranan da kika zo min da kudin nan hankali ba a kwance yake ba yanzu dake don gaba daya na shiga rudani duk da ina da yakini kan irin tarbiyan dana taso dake a cikin shi sai dai dan adam ba ai masa sheda da sai ince ke din ba rokon shi kikayi ba don kinga halin da muke ciki.
Ki tsare kaki ki tsare mutuncin ki tsare marta ban gidan da nawa don Allah kin soma girma sahiba ki kula da rayuwan ki sosai fiye da yadda kike tsare a da can baya.
Jikinane yayi sanyi na kai kasa dabas na zauna ina sauraren umma din tana fadin garin nan duk yan kazo nazone a cikin sa kinga ba wani kwaba a nan .
Ni kaina maza sun sha kawo min hari Allah na kareni da yake sun iya dadin baki idan suna da bukan mace sai i lokaci guda duk zokimmm.m..m. n da nakeyi inci wanan ..... mmm. abincin ya kuma fice min a raina.
Sai da kyat na iya dan cakula muna ci umma na kara muna nasiha a bayanen akan zaman duniya a garin lagos din karshe na tsame hannuna a hankalin dan yanayin da nake jin kaina a lokacin.
Hannu na tsame na mike umma ta bini da kallo sai a lokacin na tuna da zancen kudin dana samo wurin tallan ruwa.
Tsorone ya kamani na yadda zan nuna mata wanan kudin dake hannu na a yanzu ba yadda na iya tunda ba yadda zanyi dasu na ciro kudin daga cikin aljihu tare da kiran sunan umma din sai kuma nayi shiru.
Kudin dake rike a hannuna ta kalla kafin ta mayar da wanda bakon fuskan gidan hayan mu ya bani suna aje saman tabarma a gefen ta.
Nan dai nayi mata bayanin komai akan kudin ta karba taba bina da kallo kamar na tuhuma hancin ta takai kudin kafin inga ta cire da sauri tana fadin.
Wanda ya baki wancan kudin ranan shine ya kara baki na yau din kuma don kamshin turare daya sukeyi da wancan din.
Cikin dan marairaice nace wallahi umma bashi bane asalima wanan din ba bahaushe bane kuma yana cikin mota mai kyau sukace na bayar da sadakan ruwan ga mai bukata .
Ya akayi idan bashi bane kudin suke kamshin turare daya da wancan din daya baki dole maishi bibiyan ki yakeyi ke nan sahiba.
Idan ko hakane ya zama dole mu bar wanan unguwan mu koma wani unguwa can mai nisa mu zauna ta yadda ba zai gane inda muke ba kuma.
Bakina yayiwa umma wani tambayan da banyi niyar mata shi ba a lokacin take yanayin umma din ya canza a lokaci guda har cikin ta yana dan shock don tambayan don cewa nayi.
Idan hakane umma ki kaimu Arewa gidan uban mu zaifi muna wanan yawon hayan muna zama da arna.
Sai kuma na koma dana sanin yi mata wanan tambayan don ni kaina abindake cin zuciyanane ya fito fili a lokacin.
Don legas din garin kazo nazone da ai daba haka ba da yanzu na fara shan gorin hakan a wurin mutane sunan babu abinda ya damesu da zancen wani ina ubanka can wa mutum.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA, , , , , ,

7️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,


BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IHHI, DINAS SIRATAL MUS,TAKKIN, , , , , , , ,


LITTAFIN KUDINE YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA, , , , ,


Kwana biyu kamar Amar yaji sauki sai gashi kuma mun wayi gari dashi ya kankame muna duk idanuwan shi baka ganin kome sai fari.
Ganin hakan yasa nasa ihu lokaci daya ina neman taimako ga mutanen gidan mu saidai abinka ga yare ba wanda ya leko waje don agaza muna a wanan halin.
Son kowa na gudun abinda zaiyi laifi ko ya jefa kanshi a cikin wahala a lokacin duk dai iya abinda suke gudu ke nan.
Ganin ba wanda ya leko waje don ya taimaka muna yasa na fita da sauri zuwa wajen gidan sai yan mutane tsiraru dake fito wa a gidajen dake gaban mu kawai nake gani.
Sai kuma motocin da na gani a kofan mu guda biyu ajiye da alaman dai bakine su don suna magana da wani dake tsaye daga waje yana duke a cikin motan.
Olon maja somebody help me please na kara yanka ihun ina dora hannu a saman kaina a cikin gigicewa don na bar umma rugume da Amar a dakin.
A hankali ya dago daga jikin motan a ciki irin shigan da yakeyi a kullun da ba a ganin fuskanshi gaba daya sai dai kasan fuskan shi kawai.
Ya sauke kallon shi a kaina na dan lokaci yana kallon yadda nake ina tsaye ina kururuwa ina ganin hakan na nufe shi da gudu na fadi kasa ina fadin please oga serve my broda from death.
A cikin wani murya na kasaita da nuna isa yace where is he now na nuna mashi da hannu yana ciki.
Da sauri naga ya juya zuwa cikin bai tsaya jira na ba nima na mike nabi bayan shi da sauri ina nuna mashi dakin mu bai tsaya jiran komai ba ya fada dakin da saurin shi.
Umma ya hango a zaune rugume da Amar dake cikin halin dana barshi har lokacin bai a cikin hayacin shi.
May we go hospital ya fada kawai ya sungumi Amar din umma ma ta mike tsaye tare muka fita motan nan da yake a wurin dana samesu ya nufa yana fadin open d door for me da sauri na cikin ya bude kofan motan.
Sai lokacin naga ashe mutum biyu ne a cikin motan zaune a lokacin yake magana dasu fada motan yayi rike da Amar din a hannun shi.
Ya umurci umma ta shiga nima na fada motan duk da bata daukan mu a cikon hausa umma tace Sahiba ki koma ki tsare muna daki kin san halin yan gidan nan namu ai.
Umma ba zan iya barin ku tafi ku kadai ba ban san halin da zaku kasance a ciki ba a can ?
Ki barta a tafi da ita idan hakan zai kwantar mata da hankali ya fada shima a cikin turanci ban tsaya mamakin yadda ya iya hausa ba har yaji abinda muke fada don hankalin mu dake tashe a lokacin.
Wani haddaden asibiti suka kai mu da sauri umma tace dasu we no get money to pay bill me we go d gonvement one .
Don't mind d money naw, we should pray for his health now god bless umma ta fada yace dont mind.
Su suka fita sukai dan cuku cuku har aka karbe mu a asibitin aka ba Amar gado ke nan an kwantar dashi haka ke nufi .
Daga yanayin fuskan umma zaka gane abu da yawa ya taru mata a lokacin sai dai kawai abarwa ciki sauran zance.
Gari na dan haskawa ya shigo dakin yana fadin mama we are going we pay for all his bill so don mind now nd collect din money, user, am for food nd trasport .
Ya dan tsaya ta window dakin ya kalli yaron da aka sakawa abubuwa a bakin shi idin shi suna rufe lub kamar bai a raye idan badon numfashin da yakeyi ba a lokacin.
Haka suka fita muka bisu da kallo kafin inji umma ta sauke ajiyan zuciya tana fadin kin koma neman taimakon su ne kuma sahiba.
Umma a waje na gansu lokacin da nake neman taimako kowa na gidan yaki fitowa ya taimaka muna a lokacin sai shine yazo har dakin ko magana bai mun ba.
Ki kiyayi wa yan nan ina fada maki don da ganin su akwai abinda suke shukawa wanda basu son mutane su gansu.
Ni kan shiru nayi na mayar da hankalina a wurin amar dake kwance tare da abin nufashi a jikin shi muryan umman ke fadin.
Akalla sun kashe muna kudin da zaikai daruruwa a take a wurin nan yanzu ba tare da sun damu da hakan ba.
Akan wani dalili har za suyi hakan a garemu alhalin ba yan uwansu muke ba sahiba dole sai idan suna da manufa akan mu ga nawa wautan nace nima ban sani ba Umma.
A gaskiya sahiba wayan nan mutane sun saka zuciya a zatgin hakan kwata kwata hankalina bai kwanta dasu ba ko kadan.
Don yadda suke facaka da kudi akwai alaman tambaya a garesu kuma suka zo a cikin wani yanayi dake nuna su din wasu marasa gaskiya ne.
Amma umma koma meye mu dai babu ruwan mu da su tunda sun taimake mu ai shike nan yanzu ba sai sun kara ganin mu ba kuma.
To Allah yasa sahiba ta fada tare da nisawa ta kalli kudin da ya bata musai abinci umma tana fadin wanan kudin duk abinci zamu saya dashi kamar ba jinya mukazo yi ba a nan.
Sai naga ta fara kirga kudin har ta kai karshe ta dago ta kalleni tana fadin kinga abin da nake fada ko dubu darine cif sahiba aikin me wa yan nan mutane sukeyi da har suka samu kudin nan a yanzu .
Watau idan uwa ta mayar da yarta kawar shawaranta zata zauna tayi hiran komai da ita koda shekarun fahintar yar bai kai ba akanzancen da sukeyi din daga dan hiran har yar zata fara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login