Showing 276001 words to 279000 words out of 382072 words

Chapter 93 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28349

muna kulawa sosai a zaman kotun.
A can kaduna kuma yau gidan nasa makil yake da yaran shi da wasu yan uwa da abokan arziki dake ganin kazafi akai masu don kawai a bata masu suna a gari.
Falon na cike da mata wata mai zakin murya a cikin matan dake falon take fadin kai wanan zamanin dame yayi kama haka ?
Wai ace yar dan uwanka daya mutu ya bari itace wai zatayi karan ka ta zauna kotu dakai tana sharia don lalacewan zumuncin zamani.
Yo keko dai akan kudi maye mutum ba zai iya yi a yanzu ba hjy hafsa wata karba daga gefen ta ni sai na dauka kamar hadin bakine don kawai anga suna samu bari a tsiyata mutum a huta a koma daidai.
Wanan yar ai ta bushe fitilan tako don ance ma ko shigarta kawai kagani kasan ta rika ta kuna bata taran kauri don idanuwan ta a bude suke.
To aini yadda naji ance tare da manyan kasa take kinga kuwa dole ta dauka zata iya can wata daga cikin yan uwa ta amsa su da fadin .
Ni har taysayi take ban bata san waye Alh bane ta kawo kanta Alh ai ba, ayi mashi wanan haukan yama kyaleta dai don tana yarinya ne karama kila ?
Nan dai suke ta shaci fadi dinsu har suka gaji sukai sallama suka tafi ba don sun gaji da gulma daga gefe wata yar gidan ta kalli nazifa tana fadin niko wanan shigan da za ayi har kotun zanje naga wanan yar iskan yarinyat dai a idona.
Baki nazifa ta tabe tana fadin kiga haushi dai kan din ance wallahi karamar yarinyace sa,an su manir kinga kuwa ai karamace sosai wuri ta samu kawai tana iya shegen ta kawai indai Abbane ai kar yake kallon ta.
Toshi mijin kiku fa da akace shi yazo da ita daga lagos din ya nuna mata gida fa tace wanan dan iskan ranan naji mahaifiyan shi na masa fada yace shi ina ruwan shi cikin wanan case din tunda bai shafeshi ba.
Ai baima zuwa kotun ina gani don ko wanan zaman ma yana Abuja aka zauna bai gari ai shiyasa na kyaleshi.
Da zai tafi na bugi cikin shi ina fadin gobene fa zaman su Abba kotu yace dani ina ruwan shi da zaman su shi wanan zancen ba nasa bane don haka zaije yayi mai fiddashine.
Shi zancen biyan wanan kudin company din yanzu ke gaban shi suga inda kudi zai fito a biya su kudin shine a gaban shi.
Kai gaskiya Abba yana da makiya wallahi ki duba fa Nazifa idan haka ba shiri bane ina Abba ya taba fadawa hannu irin wanan gashi lokaci daya .
Allah ya fisu ai kome kuwa zasuyi ba zasu taba cin nasara ga Abba ni shiyasa abin baya damunama sam wallahi don a shirme nake daukan zancen.
Wai ace anyi karan Abba haba kai jama,a da kuma laifin yin kissan dan uwansbi fa ?
Nifa har yanzu zuciyana ya kasa tsayi wuri daya wallahi tun maganan da mama tai muna ranan nake jin kamar wani abu zai farune dasu Abba din .
Don fa yarinyar nan ta shirya sosai wallahi ga ta ba tsoro ko shayin kowa haka zata tsaya tana fuskantar kowa a cikin kotun.
Ni yanzu so nake kawai naga an kare wanan sharian wallahi saina fadawa baffa hamza magana daga yau alakan namu ta jini ta bare ai yaga yadda nayi mashi dazun da muka hadu dashi wani kanin su ke wanam zancen a cikin takai .
Wai tace a bata dukiyan mahaifin nata kuma abi mata hakkin halaka mata uba dasu Abba sukayi idan ba tsoro ba uwar nata tazo ta tunkari su abba mana idan bataji tonon asiri ba a wajen su.
Saida suka kare barikancin su sanan yanzu suzowa mutane da wani zancen bamza cN



ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

8️⃣2️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AS SAMADU, , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋


Abubuwa sun rikice sun rabtabe a tsakanin dangin an kasu kashi uku kowa da bangaren da yake zargi wasu na ganin mune da laifin komi.
Wasu kumana ganin ai yadda mukayi din shine daidai don suma wanan sun san zaluncine ba dai yadda suka iyane kawai.
Yayin da wasu kuma suke ganin a,a laifin baffa hamzane tare da modibbo dasu baffah Abdullahi suke kulawa yan uwan su sheri.
Duk wanan ni bashine a gabana ba kawai ni burina naga mun samu freedom kamar kowa mu daina wanan boye boyen da muka taso a ciki umma na faman boyemu garesu .
Sun sa tabar yan uwanta da garin su duk saboda su komai namu ya fita daban da sauran yan uwa dake harkokin su a fili babu boyo a garesu.
Kome za ayi dai yanzu ni ba dukiyan dake hannun sune a gabana a dai gane gaskiya a inda take masu zargin umma suna dora mata laifi kan abinda basu sani ba su sani yanzu.
Don har yanzu ba ako soma shiga inda nake son akai ba din ummace ta turo kofan dakin nawa tana cewa dani na fito naci abinci don tun safe ban leko falon ba abinci yana ajiye.
Na amsa mata da zan dan watsa ruwa a jikina kafin in fito ta juya ta tafi bayan na fito wanka na zauna na shirya nafito abincin na nufa na bude har lokacin yana da zafin shi sosai da zan iya ci.
Zama nayi na dauki remote na kunna tv na fara cin abincin dana zuba din badon yunwa ko jin dadin bakina ba.
Wayana ne yai kara na dauka ina duban mai kirana a lokacin ya mustaphane dan gwaggo hari nabi wayan da kallon mamaki kafinnin kai hannu in dauki kiran.
Ina karawa a kunnena tare da sallama ya amsa da fadin hi baby ya kuke ya kuka isa gida dan jim nayi kafin in iya amsa mashi da fadin who is speaking ?
Dan murmushi naji ya sake kafin yace nufies dan gidan gwaggon hjy hari from kaduna i hope yanzu kin gane daidai ko ko a kara maki bayani yadda zaki ganeni.
Forget about that why are you calling me now ?
What a surprise question ne wanan bazan kira kanwata naji lafiyan ku ba sai ina da wani dalilin kiranki ko wani abu zan kira ?
To nakira kawai inji lafiyan kune a yanzu in fada maki kuma zan shigo kafin zaman ku na gaba da zakuyi don a kwai, , , ,
Bama bukatan hakan a yanzu ko menene Allah zai tsaya muna insha Allahu OK idan ke baki son jin me zai kawo ni umma tana so jin don zai karata a gaba.
Look mr don Allah ka tuna kaida kanka ka gargadeni da bani warning kada in nuna wani sananya a tsakanin wanan maganan ka tuna kaman a yanzu ka bani warning din a wurina.
Ok nagode naji ya fada a dan sanyayye cigaba da fadin sai dai ki sani wata rana keda kanki zaki janye wanan maganan a zuciyar ki.
Yana fadin hakan ya kashe wayan shi duban wayan nayi naja tsuki ina lumahe idanuwana a hankali don tunawa da wanan lokacin daya fada min hakan.
Yana ganin a yanzu zan jaye zancen a zuciyanane kome Allah ya gani shi din bai cancanci haka ba a wurin mu don ya taimakawa rayuwan mu alokacin da muke ciki bukatan taimako don haka bai dace da yadda nake mashi yanzu ba .
Saidai kuma yin hakan ya zama dolene don na fuskaci iyayyen su basu son diyan su jefa kansu a cikin wanan rikicin don gujewa fadawa halaka da tsoron abinda ka iyaje ya dawo nan gaba a garesu.
Wanan ne babban dalilin dayasa nake jan baya ga kowan su don ina ji masu tsoron da iyayyen su kejiye masu daga wani sheri saboda mu.
Saida darene muna zaune mun tare dasu umma da suka rufe shago don dare da yayi abinci mukaci bayan mun gama cin abinci ana dan taba hira a tsakanin mu.
Nake fadawa umma ya kira waya saidai umma ko kin kula cewa iyayyen nasu basu son mu,amulansu damu suna kokarin ko yaushe su yakinci diyan su akan kulamun da sukeyi.
Mommy tasha warning din haka a gaban ga ya Abubakar haka in zaki tuna itama gwaggo hari tayiwa danta wanan kashedin a kan mu ranan.
Haka na nufin dukkan uwayen biyu basu son wani abu yazo ya samu diyan su ke nan ta dalilin mu don hakane nake kokarin ganin na nusantasu da zuwa wirin mu ko shiga lamarin amma bayan wanan ai ba zan taba kin su ba don sun taimaka muna lokacin da muke bukatan taimako a garemu.
Shiru umma tayi kamar tana nazarin abinda na fada kafin ta nisa maidan bada sauti tana fadin nasan da hakan kwarai Sahiba nima nayi wanan tunanen a baya ai.
Amma kuma tunda su yaran basu nuna hakan ba a tsakanin mu dasu sai naga idan kina nuna masu haka zasuga kamar mu din masu butulci ne a garesu.
Nan dai muka dan taba hira a tsakanin mu kafin na mike na shige dakina zuciyana cike da tunanen irin maganganun da mukayi da umma kan hakan.
Wanan karon ma kamar wancan tafiyan mukayi shi da niyar kwana daya kawai zamu mu juyo idan an tashi daga kotun .
Mun shiga a kan lokaci ina sayene a cikin suit baki na mata wando da riga dinkin zamani sai takalma tom daya shiga da kayan.
Sosai shigan ya karbeni ya kara fito dani a yadda na koma yanzu wata classic sai dan jakar dake makale a kafadana karami.
Kotun kan ya cika makil da jama,a masu son jin wanan badakalar da ake gwabzawa a cikin ahalin namu na tonon asiri.
Dayawa nunani sukeyi a wurin har lokacin da aka bukaci da nataso mu gabata gaban mai sharia na mike na taso aka bini da kallo ke zakice diyar wani pastor ne ni in kin debe dan bakin half hijab dana dan saka daga samana ya rufe min kaina kawai.
Suma sukazo suka tsaya kamar yadda akeyi idan an shiga koto mai bayani ya fara karato dalilin zuwan mu da kuma inda aka tsaya ranan ga sharia.
Lauyan su ne aka fara ba dama ya mike tare da ban girma ga Alkali kafin ya fara fadin shi a matsayin shi name kare bangaren su..
Yau yana maganane da cewa yanzu dai a bisa bayanin baya da sheda na farko ya bayar sun gane cewa akwai hadin bakin wasu yan uwa a ciki da suka tunzura maganan.
Har suka turoni nazo nayi kara don kawai a tozarta su Alh din don haka zaiso yayi min wani dan tambaya.
Kotu tace an bashi dama ya juyo gareni yana murmushi ga mamakin shi nima murmushin yaga na mayar mshi a lokacin yace da kyau yarinya zaki gane kuren ki a zuciyarshi.
Sahiba ko ya tambaya nace that is my name yace good ko kina da shekara nawa mahaifin ki ya rasu ya fada yana wani kada kai nace dashi shekara biyar yace U see .
Kina da shekara biyar a lokacin ke yaya kikayi kika san da cewa hakan ya faru su Alh nuhu ne suka kashe mahaifin ki ?
Nan kotun ya dauki kus kus na jama,a shiko yana gefe ya zuba min ido na dan gyara tsayina kafin nace dashi kai tsaye.
Nace saboda ina da shedan hakan ga wace akayi abin a gaban idon ta , sai kuma sheda na biyu ina da littafin da mahaifina ya rubuta bayani shima a cikinsa a yanzu.
Yayi min wani irin kallo na gyada mashi kai zaiyi magana mai kare bangaren mu ya karba da fadin wanan ai ba hurumin ka bane kake kokarin shiga yanzu.
Alkali ya daga mai hannu ya mike ya karaso yana fadin kamar yadda kotu ta nemi da mu gabatar da shedu kan zargin mu a yau munzo da wace komai ya faru a gaban idon ta itace hjy maria matar shi marigayin uwa kuma gasu masu karan sai wanan lokacin sunan Amar ya fara shigowa a cikin sharian.
Kotu tabada daman fitowan umma din da sai a ranan mutane suka sheda fuskanta don basu ganin ta sai ni da Ammar ta shigo a inda take tsaye .
Kotun ya dauki surutu lokaci guda don ganin umma yadda ta sauya a yanzu ta murje tayi kyau sosai da ita.
Aka fara tambayanta sunan da matayinta ta fada Alh gyade sai gyara tsayuwa yakeyi nan aka fara mata tambaya tana bada amsa.
Abinda ya faru ranan ta fada tun kafin yaje ya gansu din ya fada mata da dawowan shi ya koma ba lafiya da wayan da sukayi da Alh nuhu.
Dakata hjy lauyan namu ya fada yace zan maki yar tambaya lokacin da hakan ke faruwa ke kina ina a lokacin ?
Tace duk muna tare rabuwana dashi shine dana kai yar mu daki wanan sahiba din na bata magani nima nasha wanda ya sayo min don ina da shigan karamin ciki dana dawo dashi lokacin ba kowane yasan dashi ba sai nida mijina din.
Na koma na kara samun shi cikin tashin hankalin dayafi wanda na barshi a cikin ina shiga yake ce min idan kuji ankasheni kada a zargi kowa yan uwan haihuwana ne su Nuhu suka kasheni.
Kai har takai da tabada labarin yadda kisan ya kasance da komai ya faru har fitowan su ai ga baki daya kotun ya dauki salati kowa na fadin albarkacin bakin shi.
Har saida alkali ya tsawata aka samu akai shiru taci gaba da fadi lokacin kuka ya rinjayi karfin ta lokacin da baffa buhari yake tambayan su sun samu ganin shi sunyi maganan dashi ?
Lauya ya tambayeta ke nan shi buhari baisan kasheshi akazo yiba kike nufi tace hakan nake tunane don daga inda nake labe a dakin maigadin ina jin yadda yake tsuki yana fadin wanan ai sai a zargi wani abu a garemu bayan sun fito yake tambayan su yaya ya yarda zai bayar ko nasan bai zaiyi gardama ba ai yadda kuke nufi.
Sukace ai zance ya kare tunda ya zama tarihi yanzu kuma komai ya dawo hannun mu ga baki daya da irin neman da sukai mata din a cikin gidan shi baffa buhari na fadin akan me zata gudu don ta ganku.
Har zuwa kashedin da Alh nuhu yai mata washe gari akan saura ita a gaban mutane yake fakan idon su ya nuna zai yankata itama haka ya sata dauki yarta ta gudu daga garin baki daya ke nan har taje can tayi renon cikin dake jikin ta tare da diyanta duk a can ta karashe a cikin kuka kotun ya dauki salati lokaci guda.
Haka masu raunin imani a kotun ma suma kukan suke taya umma na labarin data bayar din a lokacin mai taba zuciya
Ina gefe a zaune na hada kai da kujeran kotun dana zauna akai ina faman kuka sosai duk da kamshin da naji na turaren shi hakan baisa na dago kaina ba na daiji mutum ya zauna a kujeran kusa dani ya miko min handcarchef in share fuskana.
Bayan na gogene na dago da niyar inwa maishi godiya idona ya sauka ga ogan mu zaune a kusa dani daga bayan mu kuma sauran jama, an mune a zaune.
Dan zabura nayi dan mamakin ganin su a wanan lokacin yace be cool kada ki damu, damu a yanzu mu saurari mai wanan alkalin zai yake nan gaba.
Kai kawai na iya gyada mai a hankali naci gaba da goge hawayena dake zubo min muryan lauyane ya dawo damu kallon gaban kotun yana fadin.
Ya mai sharia wanan shine shedan mu ta biyu dake nuna su alhaji nuhu sune suka kashe dan uwan su saboda wani bukatan da sukaje wajen shi dashi a ranan.
Objection my lord wanan ai bai isa sheda ba don za a iya tsara mata fadin hakan tazo nan tana muna kukan karya don tana ganin ba zamu gane hakan ba.
Lauyan su ya fada namu zai tare alkali ya daga mashi hamnu ya koma ya zauna wanan ya tunkari umma.
Yace hjy mairo munji shirin da kika tsara muna a yanzu saidai abin mamaki ke a lokacin kina ina har haka ya faru baki sani ba .
Tace na fada ai jikin yarmu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login