Showing 186001 words to 189000 words out of 382072 words

Chapter 63 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28389

hannu su zo sukaki suka make a jikin mahaifin su daddy ya gama waya yake fadin ku ke nan baku san kowa bako ?
Zasu sani ai dole modibbo din ya fada yana dora karamar saman cinyar shi daddy din ya juyo yana fadin sai kaji ina zancen aure summaya ko ?
Wace summay ke nan kuma daddy ya tambaya yana kallon daddy din daddy yayi murmushi yana fadin har ka manta sunan baby Summaya ne kanwar ka na wurin karima dai.
Baby dai ta gidan nan daddy kake nufi yace ita fa uwart tace aure zatayiwa yarta ba zata tsaya yin karatu ba sun sama mata miji dan uwurin Alh gyade.
Wai Ma,aruf dai ko wa shi kuwa dai wai shine zanbin kanwar taka naso na hana uwar ta ta saka min tashin hankali ka barsu ayi tunda haka suka zaba da kansu ai.
Nadai fada masu duk abinda ya taso babu ruwana don kada su kuka dani tace ta amince da sauri modibbo yace amma daddy gaskiya kasan akwai matsala sosai yaron da ko karatun kirki bai tsaya yayi ba za a dauki ya a bashi do kawai yana wani guntun sana,an shi kuma yarinya karama kamar baby ?
Ai itama din bata yi ba kaga saisu karata can suji dashi tunda haka uwarta ke so don na nuna rashin yardana shekaran jiya nan taso rikita min gida da hauka.
Allah ya sauwaka ya fada yana mikewa tsaye daddy zan kai su wajen anty su gaisa ban shiga can din ba ya amsa da haka nada kyau kafin ka tafi zan fito waje in ganka.
Yayi ta sallama a falon hjy karima ba amsa ba ya juya zai tafine yaji muryan Fatima na amsa mashi daga ciki ya tsaya.
Tana bude labule ta ganshi tsaye tare da yaran shi take fadin lah yaya kune ashe ta juya tana fadawa uwar dake fitowa ga yayan mu yazo.
Ta wani tabe baki tare da fadin wani yayan ku kuma a lokacin ya shigo da sallama a bakin shi ta amsa mai tana fadin yaushe garin yace jina dawo anty.
Ya gaida ita cikin mutunci ta amsa mai kadaran kadaham sai fatimane tayi kokarin karban yar bataki ba taje wurin ta kuwa sun dai dan gaisa ya daga zai fita take fadin ka shiga wurin Alh ne ko yace eh daga can nake yanzu ai.
Yayi ma bayanin auren kanwarka daya taso ko yayi murmushi kafin yace ya fada min yanzun nan don nasamu yana waya akai yake min bayani.
Amma zancen karatu fa anty tace tayi a can ai munyi magana dashi kan hakan yace toh Allah ya sanya alheri yasa wurin zaman tane tace amin amin nagode don jin baiyi wani korafin kar ayi ba bayan haka.
Shima din yace hakane don yadda daddy ya fada mai sun kwasa da ita to tunda daddy ma bai iya da abinsa ba shi me zaice yanzu kuma banda fatan alheri.
Ya mike yana fadin ina ita baby din take tace tana ciki tana washe baki ya kamata in ganta kafun intafi inji ra,ayin ta anty kada a saya mata abinda ranta baya so.
Nan ma taji wani irin dadi sosai koba komai sa yaga a wurin shi dama dai rigimane bata shirya auren yar ba a lokacin zancen ya taso daga sama haka.
Baby ta kwalawa yar kira ta amsa daga ciki sai gata ta fito da dan wandon jeans da rigan bubu ja a jikin ta tana ganin shi ta washe baki yace see you .
Ta rakube tana dariya ya kara fadin amarya ke nan ashe zamu sha buki shine koki kirani ki sheda min ko ta dan boye fuskan ta ya miko mata hannu yana fadin zo mu saka labule kada anty ma tajimu dagani sai ke ta biyo shi suna rike da hannun juna suka fita daga dakin ganin haka sai kuma uwar ta dan tsargu da hakan tana gudun kada ya zugata
Suna fita cikin ikon Allah a daidai kofan su yaja ya tsaya yana fadin kin gane ko duk wani abinda kike so sai kimun list din shi kada kiji komai har in kina so ki rubuto min komai ba matsala insha Allah zan saya maki shi Allah ya baku zaman lafiya tace amin a kunyace.
Ya wuce yabarwa Fatima data dauki yaran ta shiga ciki dasu ya koma part din mahaifiyar su ya samu ta shiga dakin ya bita can suka zauna yana fadin ashe aure za aiwa baby ?
Mommy tayi wani ajiyan zuciya tana fadin ashe sun fada maka kai yanzu ba wanda ya fada min daga uwar har mahaifin ku.
Yin ma abin akeyi a boye kamar ba,ason naji ko idan naji bana bari ayi ko wani abu can dai indai wanan yaron ne ai gasu gashi ko.
Suma wa yan nan Allah ya zaba masu na alheri masu addini da sanin ya kamata, yace amin lokaci ne baiyi ba idan lokaci yayi suma ai yi zasuyi insha Allahu.
Hakane komai bai wuce lokacin sa ai saukin abindai ai sunyi karatu don haka naje na samu wai ashe Sahiba har ta hada digree dinta wanan shekaran harma tana aiki a wani company nan lagos din.
Ka san inda suke yanzu ke nan uwar ta tambayeshi yace na sani mana dama nasan gidan da suke ai bawai ban sani bane barina kasan nan daine .
Ita Sahiban har ta hada karatunta tana aiki ga wa yan nan zaune a gida aikin ya buwaya koda yake Alh ne dai bai yarda da wanda aka samu ba ai dama.
Bawai aikin bane mommy kinsan zan iya sama masu inda zasu jona su tsaya suyi karatun ne yadda ya dace amma sun tsaya wasa.
Ina yaran ta fada tana kawar da zancen kada yai nisa yake fadin suna gun su fatima na barsu suka zauna kuma ta kara tambaya ?
Yace sun yarda da ita nan dai sukai ta zancen kan abinda ya shafesu a karshe sai ga yaran an dawo mashi dasu ya daukesu basu jima ba yayi masu sallama suka tafi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

5️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL KARIM, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257


Nashigo gida na samu umma na shago don haka kai tsaye na nufi cikin gida na bude kai tsaye dakina na nufa kaya na fara cirewa ina wurgawa saman gado kafin na nufi bandaki.
Wanka na nufa na fito na saka daya daga cikin rigunan da nake zaman gida dashi ina fitowa kitchen na nufa na dora muna abincin na fara gyaran gida wanan duk aikinane kun sani bana yarda umma tayi don ba lafiya ya isheta ba saboda asman dake damunta.
Har na gama girkin nayi sallah kamar kullun sai lokacin na fara jin motson umma sun rufe shagon sun shigo cikin gida saboda dare yayi bata kaiwa dare a ka,idar zaman ta.
Nayi sallah isha,i na fito da wayana a hannu ina masu sannu da dawowa suma din gaisheni sukayi haka muka sabayiwa junan mu kullun.
Saida muka zauna cin abinci nan na fara labartawa umma zancen kiran wayan da Faiza tayi min ta kiraki fa yau kikace wallahi umma akwai wanda kika bawa layinane ?
Dan shiru tayi kafin tace dani kwarai kuwa don naba Abubakar ranan daya tambayeni da bakya nan.
Nace haba nikan nayi mamakin hakan wallahi don gaskiya bana bada layina haka barkatai saina yarda da mutum sosai.
Abubakar din baki yarda dashiba ke nan Sahiba shikuma macucin mune kome yake biyan mu dashi na girgiza kaina da sauri.
To shina gani don yaron nan yana da kirki da mutunci sosai ya nuna damuwa da kuma tausaya muna fiye da kowa da muka sani.
Shiru nayi ban bata amsa ba don bana son tana fadin haka dukda nasan gaskiya take fadi amma ni zancen sune gaba daya banson ji.
Ban kaiga karasa tunane ba wayana ta dauki ringing na dauka na duba lanban umma itace ko yanzu ta kirani dauka kila shine ya basu layin tunda yaran dama sun damu damu sosai ko zaman mu a can.
Dauka nayi tare da sallama muryan Faiza ne tana fadin haba Sahiba ko bakya son magana danine wai tun dazu ina ta kira yafi ashirin wayan ki yana kashe saboda ni kaka kashe wayan.
A harshen turanci nake bata hakkuri aina fada maki cewa aiki nakeyi dazun din sai yanzu na dawo gida yasu mommy dasu Anty Amarya ?
Anty Nabila da anty hauwa ya su Amira da fatima baby da kowa na gidan tace kowa na gida lafiya kalau suna jin ki ya umma ?
Gata ku gaisa na fada ina mikawa umma waya ta dauka itama da hausan ta daya fara rikedewa dana yare a yanzu .
Suka gaisa itama tana jero mata tambayan yan uwa da sauran tana fadin ga mommy naga umma ta kashe wayan a nan nagane itama akwai haushin su a zuciyar ta ashe.
Ga Mommy ita mommy bata sanda mu bane saida kika nemo yar uwarki zata wani karbi waya wanan zumincin zamani haka dame yayi kama ace yan mahaifi daya amma basu san zafin iyalin dan uwansu daya kwanta dama ba.
Wallahi irin wanan nakan tuna a rayuwa har wani lokacin in zauna inyi kuka ina meyasa gwaggo ta zaba min mahaufin ku a matsayin mijina.
Da wanine yau muna can cikin yan uwa a mutunce sun san darajan mu muma munsam nasu ana damawa damu amma wa yan nan kan abin duniya idon su da kunnuwan su ya rufe sun manta da cewa akwai ranan hisabi yana jiran kowa.
Duk da maganan umma din ya taba min zuciya sosai don ma kusan nafi umma din jin zafin amsam wayan da mommy din tayi niyar karba a wurin faiza din.
Sai gashi umma takai ga daukan mataki kafin nina dauka ban taba tunanen jin haka ba a bakin umma danaji din tana fada sai kima gata ta furta hakan yasa nasan ankai karshen umma ke nan.
Na bude baki ina fadin kiyi hakkuri umma saukin abindai akwai hissabi ga kowa idan suna ganin haka ba komai ko sunfi tsoron wani Allah da Allah din ai mutuwar data rabamu da mahaifin mu bata bar kowa ba.
Shiru falon yayi don tunanen da kowa keyi lokacin shigowan Amar daya sauka kasa bayan fitowana yasani dago kai ina kallon shi.
Leda ya shigo dashi gidan yana fadin saida kyar na wanan uwan kamshin da kuma maganan dayayine yasani dago kai na kalleshi da kyau har ya zauna yana aje kumshin a gaban umman mu.
Kallon ledan umma batayi ba don ranta da yake bace a lokacin ina ganin haka na bude baki da kyar ina fadin meye a cikin ledan Amar ?
Ya sunkuyo ya buda min ledan wani kamshin suya meat irin na hausawa din nan ne ya daki hancina ga naman an masa manyan yanka gashi yana maiko yana fitar da suraci acikin shi kuma na zafi.
Jeka kitchen ka dauko plate ka zuba a ciki umma dana san zaku saya ai tun dazun dana tsaya na sawo maku ai saidai nakan ji kunyar in tsaya a irin wuraren nan ne.
Amar ya fito da plate dauke a hannun shi yana wani rawan jiki nace kaikan kamar ba bafalatani ba kana rawan jiki akan nama haka Ammar ?
Abine yabawa umma dariya tace ashe kin kula dashi kema kamar nayi magana yadda naga yana wanan sabarin jikin haka kamar bayacin nama a kullun gidan nan.
Amar yafi ganewa magana da yarbanci don haka yake fadi da yarbanci aiba irin wanan bane muke ciko ?
Inda na kara godewa Allah ina jin fulanci saidai banyi don tun ina karama na bude baki dashine amma zuwan mu lagos din mu a sannu yarbaci da pidin ya shige bakin mu saidai umma bata yarda da hakan ba.
Tsoka biyu na iya ci a ciki koshi don ta sake jiki na kokarta naci na tsame hannuna na dan shiga tunane kafin nakai ga mikewa ina fadin zan tafi na kwanta kada in makara da safe.
Saida na lwanta din amma juyi da tsuki yafi yawa kafin barcin yayi gaba dani nine harda mafalkin su a ranan don kawai dan wayan da mukayi dasu din a ranan.
Washe gari kodana kunna wayana text massage na sama a cikin wayan mai tsawo nata banbi ta kansa ba a gurguje na shirya na fito na samu Amar ma ya fita ko zuwa school shi.
A gurje na fita gidan don ban son abinda zai ja min matsala a wurin aikina ko kadan don sun tsani wasa da aiki ina ganin yadda sukan sallami ma,aikatan su kan makara shiyasa nake kiyayye hakan a bamgarena.
Saidai kash duk saurina kuma na makara a yau don nayi saurin banza saboda ogan mu sha,aban daya zo ashe ba tare da sanin kowa ba ya zo tun safe ya kawo muna ziyara bazata don ko Felix ma kanshi baisan da zuwan shi ba asalima a club ya kwana don harshi na rigashi zuwa.
Allah yai min katari a daidai lokacin da ma,aikata ke halartan wajen da muke ganawa dashi na iso don haka nabi layi a tsarge duk da yana tsaye a cikin fararen kaya bai kallo wurin da nake ba amma kuma ai yaga shigowata ciki na nasa a raina.
A cikin takon shi irin na mazan da suka waye suka san kan duniya suka kuma zauna da kafan su ya iso har inda muke yana fuskantar mu bai aje idon shi kan mutum daya ba don sai bin kowa na wurin yake da kallo.
Kafin yayi gyaran murya wanda hakan ya kara karkato da hankalin kowa gareshi ya fara da sallama a cikon taushin murya irin nasa.
Ya fara fadin i am disappoint yau yadda na samu a wirin nan ada kune kusan wa yanda nake alfahari dasu gaba daya out of fiyty five ma aikar da nake dasu wurin tsare aikin su sai gashi yau idona ya gane min kun fara zama kamar kowa ku din ma.
Shiru wirin yayi kamar yadda shima yayi shiru yana dan bin kowa da ido kafin ya bode baki da kyar yana fadin why zaku zama haka har yakai na kasa alfahari daku kuma ?
Sorry sir aka fara fada maza da matan don ganin yadda ranshi ya baci yake nuna bacin ranshi kuma a garemu baki daya.
Jakkata dake rataye a kafadana na gyara kafin na mayar da hankalina inda shima yake kallo din Felix ne ke shigowa da ganin sa a rude yake ya karaso bai tsaya ba sai inda nake tsaye nima a tsarge.
Yayi fada sosai ranan duk muna tsaye muna sauraron shi kafin yayi sallama damu a cikin bacin rai ya juya ya bar wurin aiki babba na sauke ziciyana ina nasa hakan.
Ba tare dana tsaya kula Felix ba dake tambayana kasa kasa how come oga ya shigo kasan nan ba tare daya sani ba ya jefo min tambayan ko ke kinsan da zuwan shine ?
Wani kallo nayi mai ina fadi yaya zan sani shima da yake kusa dashi yace bai sani sai nice zan sani ta yaya kuwa ?
Har mun kusa kaiwa inda zamu hau masarrafin da zai kaimu sama naji ana fadin kubiyin nan guys oga yana son ganin ku yanzu.
Na kalli Felix a cikin zaro ido shima hakan ya kalloni kafin na juya na shiga masarrafin zuwa sama din inda office offices suke a can sama din.
A gidan su ya bar yaran don bai nufi gida ba daga nan ya wuce zuwa wani wuri yana a tsakiyan aikine saiga kiran Nazifa tana tambayan shi wai ina suke ne har warhaka ?
Ina wurin wani aiki ya bata amsa a takaice yaran fa ta tambaya da mamaki suna gida wurin mommy na barsu ka batsu can fa kace yace eh da matsalane barin su can din?
A,a saidai gaskiya kasan basu saba dasu ba ai kuma mimi nono take sha kasani eh na sani saidai ai akwai abincin ta idan tayi kuka yaran zasu bata.
Ji yayi ta kashe wayan sai yabi wayan da dan kallon mamaki kafin ya daga kafadan shi irin alaman ko a jikinshi din nan.
Tana kashe wayan na mahaifiyar ta takira bata sameta don haka ta kasa hakkuri don in akwai abinda taki jini a duniyan nan shine yaran ta su rabi kowa na gidan mahaifin su don wai basu son ta.
Daki ta mike ta shiga ta fitone sai ga kannen ta haka yasa taji dadi suta tura suje gidan su dauko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login