Showing 81001 words to 84000 words out of 382072 words
ya idar da sallah bai koma barci ba don mafalkin da yayi da su yaya Nuhu suna binshi zasu halakashi.
Jin haka a bakin shi yasa nabishi da kallon mamaki nakai zaune daga inda nake tsaye a cikin mamaki jin abinda ya fada min din.
Karfin hali da jarunta ya nuna min kamar zancen bai dameshi ba shi a zuciyar shi ganin da yayi kamar na damu yake fadin kada wanan ya dameki fa mairo wata kila sherin mafalkine hakan.
Ai ba yau ka fara fadin haka ba kuma abin ya tabbata suma sheri daga karshe abin ya zama gaskiya.
Kedai ki dauka a mafalkine wanan koda ma hakan zai faru yar nan nake ji da abindake cikin cikin ki a yanzu yadda zasu kasance a cikin makiyan su nan gaba.
Duk da nasan Allah ne gatan bawa kamar yadda ya rayani a cikin su nagirma na zama haka a yau duk da ba,a son inkai hakan din ba kuwa.
Idan har hakan ya kasance ki dauki yaran nan kiyi nisa dasu da gida inda ba a jin labarin ku ki renan min yarana a can yafi min komai kwanciyan hankali.
Hawaye umma tasake masu dumi tana sheshekan kuka a lokacin tace a karshe dai ya mayar da zancen kamar alamara a gabana ranan bai fita ba sai wajajen karfe hudu na yamma bayan sallah yace zai dan tafi unguwa.
Bayan fitan shima ban iya aikata komai ba don jikina da yayi sanyi da wanan zancen daya fada min game da yan uwan shi da suke binshi da sheri haka kamar ba jinin su ba shi.
Yarinyar dake gefena a kwance na dan kalla sai tausayin kanmu ya kamani har in abinda ya fadin ya kasance gaskiya yaya zanyi da yaran nan ke nan.
A take zuciyata tayi matukar yin rauni nakai hannu na shafo dan dake cikina wasu hawaye naji sun zobo min daga idona shar a dalilin tausayin kanmu danaji lokaci guda.
Lokaci mai tsawo na dauka ni kadai a dakin sai wanan yar dake barci a gefena ina kuka nayi nayi hawayen su tsaya min abin ya gagara hakan.
Sai gashi ya dawo gidan bai wani jima da fita ba na ganshi ya dawo rai bace ya shigo falon yana fadin wai ki duba wanan mafalkin da nayi da mutanen nan ashe zasu fito min da wani zancen banzane haka kuma.
Ja yayi ya tsaya yana kallona don yanayin da ya ganni a ciki na tashin hankali ya fara fadin me ya faru kuma wani yazo gidan nan a cikin sune yana tambaya tare da zuba min ido yana son jin amsa daga bakina a lokacin.
Nayi kwal kwal da ido na kasa magana takowa yayi inda nake yana fadin ke daina kukan nan ki fada min me sukai miki ne ?
Ganin yadda ya rude yasani fadin basu zo ba basu fada min komai ba maganan da mukayi da kaine ya tsaya min a raina nake tunane.
Ya dan kauda kai yana fadin Allah ya fisu don ba zasu taba shefe tarihina a bayan kasa ba kamar yadda suke son yi.
Yana fadin hakan ya tashi ya shiga daki ya barmu a falon saida ya dan dade a dakin kafin na sameshi a ciki zaune yayi tagumi yayi shiru yana tunane.
Ban iya masa magana ba har na aje mai flask na fita daga dakin zuwa dakina duk da ba raba daki mukeyi ba ranan a dakina na zauna kada na dameshidon naga yana cikin damuwa.
Wanan ne ranan da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwana ranan da kullun ina tunata a rayuwana kwakwalwata takan neme zaucewa .
Raina yakan sosu zuciyana takanyi baki kamannina ya kan sauya numfashina yakan dauke har wani lokaci nakan ji da rayuwata gwanma na mutu na huta idan badon yaran nan ba dake gabana.
Don na koma dakin ganin irin hadarin daya game gari a daren ranan yasa na koma dakin dubashi na samu ya idar da sallah magariba yana zaune yana addua.
Na dan tsaya ya idar yajuyo yana fadin meye laifina a cikin su mairo don Allah ya azurta ni fiye dasy suka dauko canfi suka dora min akaina.
Sunce ni din dan shege ne a cikin alhalin mu don kawai uwata ta sameni a bakwaini ni nasan ba da zina aka haifeni ba kuma sun koma sunce mahaifiyata itace mai kandun baka ta kwashe arzikin gidan su ta bawa danta.
Wanan mairo wani irin camfine da jahilci a kansu sun manta Allah ne mai bayarwa da hanawa idan yaso.
Kasa ci gaba da bayanin yayi ya dukar da kanshi kafin ya dago yana fadin bazasu barni ba subar diyana don wanan bakin akidar nasu na camfi da suka saka a zuciyarsu.
Sunce ni din da jinina idan muna cikin su ba zasu taba arziki ba a duniyan nan sai ya fashe da kuka zaune nakai ina bashi hakkuri akan zasu soshi zasu dawo suyi da sun sanin hakan da sukeyi a karshe.
Yace kaiya mairo baki san su bane su din fa jinin fulanine gaba da baya akwai riko da gaba garesu koda na shekara dubune kuwa.
Yar nan data tashi tana kuka yasa na barshi a dakin zuwa wajen ta dan rarashinta nakeyi har barci ya daukeni ban sani ba a wurin .
Can misalin karfe biyun dare a cikin barci naji wani kara kamar fashewan abu a gudan ashe karan bindigane nake jin .
Kafin na fara jin murya na tashi kasa kasa a gidan suna fadin ai mun fada ma ba zamu barka ba ka dauka wasa ne kome ?
Daukan yarinyar nayi na goya a bayana a cikin rawan jiki na fara sanda na fara fitowa daga dakina dake can dan gaba da nasa Allah ya taimakeni duk hankalinsu yana a kanshi lokacin gaba dayan su sun saka shi a tsakiyan su..
Naji muryan yaya Nuhu yana fadin ka fito muna da duk wasu takardun wanan filin dana bankin ka ga baki daya dana gida muddin kana son ka kara numfashi kaida iyalan ka.
In ko ba haka ba wanan na nufin ka dade da kama gida a kiyama kaida iyalan ka ko don kashe ku zamuyi mu kashe banza muga yadda kuma zakaci dukiyan da kake muna kuri dashi din a yanzu.
Gabana ya kara faduwa a hankali inajin hakan nayi kokari barin wurin Allah ya taimakeni na samu nafita daga falon ba wanda ya ganni a cikin su hudun da suke gaban shi.
Da wautana dakin maigadin mu na samu na shiga shima baya cikin dakin a lokacin sai bayan na shiga ne na boye ashe maigadin ne na tsalaka yana kwance a kasa cikin jinin dake malala daga jikin shi.
Goyon dake bayanane ta fara motsi na dan mike ina jijigata sai lokacin na kula da halin da tsohon dake gadin mu yake ciki na zubar jini daga jikin shi ashe shi suka fara kashewa da shigowan su gidan.
Innalillahi wa,inna alaihim raju, un suke fada dukka falon lokaci guda jikin su duk ya mutu ga sauraren labarin da umma ke basu har nima daga inda nake a labe ina iya jiwo abinda suke fadi sai hawaye ke zuba min don nagane kan labarin da umma take fada taci gaba da fadin.
Allah dai ya rufa min asiri yarinyar ta koma barci a lokacin ina wurin dana boye din a cikin tashin hankalin da bai musultuwa.
Ba komai ya hanani fitowa ba a lokacin don irin yadda nake ji a zuciyana sai zancen daya fada min da safiyan ranan akan yana rokona dana boye idan sunzo din ke nan yasan da zasu zo din ke nan dama har yake fadin hakan na tambayi kaina ?
Muryan yaya iliya naji yana fadin kun duba ko ina na gidan nan don nasan tana cikin gidan saboda bata je ko ina ba yau ai.
Naji wani murya da bansan ko na waye ba yana fadin bata fito ba muryan wani kato yace babu wanda ya fito a cikin gidan nan don ina tsaye wurin nan tun shigan ku ba wanda ya fito a cikin gidan nan sai gawan wanan tsohon dake kwance a nan.
Shima yaya Nuhun ya fito yana fada sosai dasu gaba daya yana fadin kada ku bata muna shiri mana wanan matar fa da yar ta dole ne suma su mutu kamar yadda shima ya mutu a yanzu.
Don gaba daya nake son a share min babin tarihin su don gaba wa yan nan tsinanun ba zan bar ko a duniyan ba cikin su don barin su wani barazanane a gare mu.
Don haka gara mu kashe su ga baki dayan su yadda ba wani wanda zai kawo muna cikas akan komai nan gaba.
Takon su naji suna ta bincikena a cikin gidan kafin wani ladani mai zakin murya ya fara kiran sallah sauran masalataiyan cikin gari suma suka dauka alaman asuba yayi a lokacin ke nan.
Na sake jin muryan yaya Nuhu yana fadin wanan yar takai shegiya yarinya irin kafiyan tsiyar dake ga uwarta ke nan take dashi.
Don ance kar kowa daga cikin dangi ya bashi yarsa amma uwarta ta dauketa don kwadayi ta aura mashi idan tana ganin ta tsirane ga hakan ba zan taba barin ta a rayeba cikin duniyan nan har shegiyar yar da suka fara haifa din nan kuwa ku dauke shi mu tafi don tsayuwan mu a nan zai iya kawo muna matsala idan mutane suka fara fitowa sallah yanzu.
Naji wani mai sanyin murya a cikin su yana fadin indan mun tafi dashi ina zamu kaishi yanzu a hakan ya Nuhu yace a hanzari rafi zamu jefa dan banza yaya Nuhu ya fada.
Rafi hjy Addah ta fada cikin sautin kuka tare da fadin ashe shiyasa aka kasa gane gawan shi ruwa suka jefa shi ke nan.
Sautin karan tashin motocin su na fara ji kafin can na fara jin muryoyin makwata mu da wasu mutane suna fadin sun tafi ai ga gawan maigadin sai alokacin na fito.
Daga inda nake boye da yata a bayana mutane suna ganina sukayo kaina da tambayan meke faruwa a cikin zaucewa da rudani nake fadin shike nan sun kashe shi.
Yan uwan shi sun kashe shi sun halaka min shi rayuwata ta mutu ke nan bani da sauran amfani a yanzu kuma .
Haka nayi ta maimaitawa har yan sanda suka iso wurin suna bincike akan abinda ya faru a gidan ba bakin da zan basu amsa a lokacin.
Wai kuma saiga yaya Nuhu na gani shine a gaba wurin bawa yan sanda labari saidai muna hada ido zai watsa min wani harara a fakaice wanda ni kadai nasan da yana min wanan kallon .
Gaba daya naji ban son ganin kowa nasa har ku din nan don har lokacin da ka iso yaya ban fadi komai ba ga kowa don na koma kamar kurma mai tabin hankali a lokacin.
Shine ana sallah magariba na sullace jiki na bar gidan da ba wanda ya ganni daga ni har yar tawa muka bar garin nan ke nan.
Sai umma din ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da sauri yaya Abubakar yace amma wanan mutumin anyi mara imani a duniya shine ya kakace komai da suka bari ayanzu.
Daddy lalai ya zama dole a tuhume shi kan wanan zancen zan tafi inyi aresting nasa kan tuhuman shi da kashe dan uwan shi tare da batar da gawan shi tunda ga shedu mun samu a yanzu.
Dakatar da Abubakar din mahaifiyar shi tayi tana fadin na fada maka ka fitar da bakin ka a cikin zancen nan don wanan zancen iyayyen ku ne ba naka ba.
Daddy ya katse ta da fadin Addah ba zaki godewa yaron nan ba bisa ga namijin kokari da yayi na dawo muna dasu gida yanzu ?
Ya dago kai yana kallon ta a cikin mamaki ta dukar da kai kasa tana fadin ba hakana bane yaya kasan fa halin wa yan nan mutane da sheri kai kanka kasan komai.
Idan na sani shine me yara sun dawo yanzu sai su basu hakkin mahaifin su da suka taushe ba shike nan ba kowa ya kama gaban shi.
Yara dai har uwar na fada maku a gidan nan zasu zauna don haka ko bayan raina ban yarda a kaisu wani gidan ba su zauna duk da nasan yin hakan zai kawo matsala a wurin, , , , ,
Dama ai tun jiya ina zargin hakan nasan yaran nan yayan kane da wanan matar da nake gani mahaifiyar yaran hjy karima ta fada daga kofa tana shigowa falon ranta a bace hankali a tashe.
Amma wallahi anji kunya girma kuma ya baci ka haifa a bariki an biyo ka dasu nan yanzu don ga asiri ya tono a yanzu.
Shine akazo nan a kulla yadda za ayi dasu ba tare da kowa ya sani ba to Allah yafi ku don naji komai a yajzu.
Har kana fadin wai a gidan nan zasu zauna don diyan kane su halal malal ba wanda ya isa ya hanasu zama a gidan nan kuma ko bayan ranka watau shi ya rike makasu amana ke nan ko.
To ai dadin abin basu dai da gadin ka tunda duniya basu sheda daurin auren ka da uwarsu ba ai kowa kuma a cikin dangi bai san dasu ba dama.
Murmushin manya daddy din yayi ya kalleta yana murmusawa yace kwarai kuwa yara yayana ne uwar kuma kanwata ce ita sai me kuma ?
Zaka dai fada tace tana huci tana kari don ranta ya ga ma baci da abinda zuciyar ta ya raya mata a lokacin game damu din.
Haba hjy karima ina kuma wanan zancen ya fito haka a bakin ki hjy Addah ta fada a cikin mamaki sai hjy kariman ta juyo a hasale tana fadin kaji munafukar mace a nan.
Idan ba yayan sa bane na waye har yake fadi yanzu a rika mashi su a cikin amana koda bayan ransa ne ?
Don kin mayar da kanki wata bagidajiya can har zaki yarda a yi wanan aika aukan dake ke gaki mai son miji kina son a kiraki da salihan mace ko mai rufawa miji asiri saboda son yabo da kikeyi a wurin shi.
Kaiya boyar Allah wanan mumunan zancen bai kamata kiyiwa bawan Allah nan shi ba don shi din yayanane na jini kamar yadda hjy take yar uwa a gareni itama.
Yaya kuma su ba shegu bane diyan dan uwansu ne da baya raye a yanzu don Allah ki fahinci abin da idon basira kafin ki furta kalamanki.
Abubakar daya gama cika a wurin ya mike yana fadin daddy sai kafito ni zan dan fita anjima zan dawo mu karasa zancen.
Daga haka yasa kai ya fice a dakin cikin takaici wai a gaban shi yau hjy karima ke dakawa uwarshi tsawa haka don rainin wayau.
Dama ba yau ba ya gama fahintar halinta matar yar bala,in rainin wayau ne sosai idan ta samu wuri haka kuma yaga karfin halin daddy da har tayi mai wanan mumunan shedan a yanzu bai dauki wani mataki a gareta ba.
Yau dashine gobe ba zata kara gigin raina mai wayau haka ba a gaban mutane ya kara jan tsuki yabawa motan shi wuta ya tafi.
Daga inda nake tsaye bayan labule na sulale a kasa ina hawaye tare da kare bakina da hannu kada suji sautin muryana a lokacin.
Can naji muryan daddy yana fadin modibbo kada kace zakayi wani yunkuri a yanzu kan wanan zancen ka bari sai mun zauna mun gama tataunawa sai mu san inda zamu bullo masu ga zancen.
Yace naji daddy ya figi mota zuwa gidan shi kai tsaye a falo ya kicibis dasu Nazifa a zaune da yan uwanta suna gaidashi da dawowa yayi kamar bai jisu ba ya shige dakin abinshi ya kyalesu yana maijin haushin mahaifin su duk ya shafesu a lokacin.
Sintiri ya fara yi a cikin dakin yana nazarin labarin da umma tabasu a yanzu a kan mu yaje ya dawo ya kasa zama a dakin karshe ya nisa yana fadin.
Wai imagin ace dan uwan haihuwan kane yai maka haka inaga wani sabba can bare na waje aida zai aikata wanda yafi haka ke nan gareshi duk saboda abin duniya sukaiwa dan uwan su haka.
Shine mommy ta san da hakan har ta yarda ta aura mashi jinin wanan mutum da yayan da zata haifa dashi suna iya kasheshi ke nan ashe ?
Hannun shi ya dunkule a wuri daya yana naushi kafin yace a fili na tsani wa yan nan mutane har cikin raina ga baki daya.
Wait yace da sauri ya daga kanshi yana fadin what harda su kawu iliya ke nan duk wanan arzikin dama ba nasu bane suke ci ke nan ashe hakkin wasune suka gina kansu dashi ashe.