Showing 258001 words to 261000 words out of 382072 words

Chapter 87 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28384

wai saida muka shirya mutumiyar ki ta bugo waya na sayo masu sarka.
Da hannu yayi signal sai ga yemisi ta biyo bayan mu da sauri a tare muka fita da ita zuwa inda motocin da zamu bar haraban suke.
Karshe ashe a can basuyi sallama da dadi dasu ba don yadda Alaja ta fara zage zage dole a bar wanan abinda yanzu yake ikirarin yasa aiki a gaba yana barnan kudin shi ga wasu.
Sai zancen ya koma tsakanin ta da yarta dan a gaban kowa ta fadawa uwar cewa abinda takeyi bai dace ba tayi fada sosai har ran uwar ya baci itama ta fara mayat da amsa a gareta.
Bamu dade a airport ba jirgin mu ya daga zuwa Nigeria kai tsaye har lokacin ina dai zaune ne banyi wa kowa magana ba saukan dare mukayi .
Don haka saida safe muka isa gidajen mu kamar yadda ya umurci akai kowa har kayan shi gidan shi idan mun sauka mun gama clearence din kayan mu.
Ni da Abdul ne zaune a baya sai Adanan a gaban motan tare da driver dake jan motan mu muna zaune a baya tunda naga na sauka kasa na lumshe idanuna a hankali don murna.
Ban kara jin dadin hakan ba saida muka tun karo unguwar mu na hango gidan mu wani dadi sosai ya kumeni lokaci guda.
Safiyane yara sun fita zuwa school sunyi resuming a wanan satin ya kasance unguwar ya kara yin shiru a lokacin kamar wani brack din sojoji.
Motan ya tsaya a kofan gidan nikan tunda muka sauka na sauke ajiyan zuciya da har yasa Adnan juyowa yana min sheri dayin hakan nan na barsu zuwa ciki sai ganina kwatsam umma tayi na shigo gidan.
Sun shiga muna da kaya cikin gidan har lokacin ina manne a jikin umma na ban iya yin komai ba sai da suka gama hawowa da kayan nayi godiya suka tafi.
Mikewa nayi na shiga dakina dana sama a gyare tsab kamar ina kasan dama don kullun sai an gyara min dakin an saka kamshi a cikin sa kamar ina nan.
Wanka na shiga na fito banko saka kaya a jikina ba na nemi wuri mm a kwanta sai wani irin barci mai nauyi koda umma ta lekoni ta samu nayi barci a lokacin.
Fita tayi zuwa gaida Abdul da dawowa suna dan hira har take fada mashi cewa ai nayi barci ko a lokacin yace Allah yasa koda zata tashi abubuwan nan sun fita kanta.
Nan dai yake ba umma labari sama sama sai kan umma din ya daure don ta kasa fahintar me ya kawo haka tsakanina da mahaifiyar ogan namu.
Barci nayi sosai a ranan don sai bayan la,asar na falka nayi alwala na dan saka riga a jikina zuwa falo.
Shidai a iyakan binciken shi ya kasa gano dalilin mahaifin su mm a boye wanan file di a lokacin yasa ya kara yarda dole akwai wata a kasa dai tsakanin daddy din da su yan uwan nasa.
A hankali ya jawo mota zuwa gida sai dai bai samu Nazifa a gida ba kuma bata fada mai cewa zata fita zuwa wani wuri ba da zai fita.
Har ya gama abinda yakeyi ya fito gidan bata dawowa ba restaurant ya nufa yaje yaci abinci inda sabo ya saba da hakan kamar wani gwauron da baida galihu.
Yasan dalilin yi mashi hakan don sun kwasa da safe da ita da yake tana son kudi a wurin yau sammako ta buga mai a daki ta sameshi yana shiri take fadin tazo ne taji guduwan mawan da zasu aikawa Abban ta dashi.
Do yan uwanta sun fara kawo mm nasu za a saka ido aga ita me zasu kawo a nasu bbangaren jin yayi shiru har ta kare zancen ta baiyi magana ba yasa ta kallo shi tana fadin kana ko jina.
Indai jine ina jin ki mana tunda ba kurma Allah yayini ba ke yanzu bakiji kunyar tunkarana da wanan zancen ba ?
Kallon shi tayi cikin mamaki tana fadin kunya a kan me don kawai ka taimakawa Abbana kome aida wanine a can gidan ku ko banyi magana ba zaka bayar.
Wanan kalamin nata yasa bai kara tanka mata ba sai yaga magana ma zai tsaya ta kara bata mashi raine a banza don haka yai shiru kawai ya kyaleta.
Karshema fita yayi daga gidan kai tsaye ya wuce headquater din su wurin aikin da yake son yi a cikin file din nan ranan haka kuma yasa ta fita zuwa gida don su tattauna da mahaifiyarsu.
Tako samu a jirace mahaifiyar take da ita nan ta fara mayar mata aikuwa bata kai karshe ba tayi cikin ta da sababi sosai ta zage ta tas tare da mata fadan fitar arziki.
Ta kuma umurce ta dace ta koma tayi mai magana a cikin lalashi da ban hankari don idan bai basu kudi mai tsoka suka ba Alh ba wallahi akwai matsala a surin su sosai.
Shine ta dawo bayan la,asar ta samu ya fita baya gida kuma taga alaman ya dawo gidan saidai bai dadeba ya fita kuma.
Zaman jiran shi ta zauna yi bai dawo ba sai gab da magariba ya shigo kai tsaye dakin shi ya nufa don yana son ya raba jikin shi da kayan daya saka lokaci.
Saidaya gama duk abinda zaiyi ya hau gado ya kwanta yana tunanen duniya don shi yasan idan ba gaskiyan zancen nan ya sani ba baida sauran shakat a zuciyan shi don alkawarin daya daukan wa kanshi kan haka sai ya gano gaskiyan maganan.
Duk da yana fargaban ace da hannun daddy su dumu dumu a cikin kisan baffan nasa da dawani ido zai kalli ahalin sa a matsayin dan wanda ya kashe masu uba.
Ido ya runtse a lokacin yana maijin zuciyar shi tana mashi zafi sosai mutumin da duk wanda zai fadi wani zance akanshi na alherine da yabo.
In ka debe wanan matsalan da yan uwa suka dora mai na cewa shi ya hanasu yin arziki saboda sun camfa mahaifiyar shi har shi din da wanan mumunan zaton nasu.
Shigowan Nazafi dakin ne ya katse mashi tunanen sa bita yayi da kallo har ta karaso tazo ta zauna a gefen gado yana yadda ta sameshi a rigingine bai motsa ba har lokacin.
Baban maryam na dawo ban hakkura ba ta fada a daidai lokacin da yaji wani irin zafi a zuciyar shi na yadda take kiran sunan maryam gatsau haka a gaban shi .
A cewan ta ta juye sunan mahaifiyar nasa zuwa na kanwarta da kakanta wai ai sunan sune ya saka bana mahaifiyatshi din ba.
Nan ma dai shiru yayi mata shi kadai ke jin yadda yake ji a zuciyar shi lokacin a kanta ta sake fadin bb maryam don Allah kayi hakkuri ka saurareni .
Kada kayi fushi don Allah dani kace ba zaka ban kudi ba in kaiwa Abba don wallahi duk yan uwana sun kawo masa nasu gudun mawar nice da hafsat muke rage bamu bayar ba a yanzu.
Nan kan ya dan muskuta yana fadin me kudin makiyi zai karashi dashi a yanzu tunda a matsayin makiyin shi nake nida kowa na gidan mu a zuciyan shi.
Shine kuma zan dauki kudina yau in bashi ai kema kin san ba zai karba tunda ni da diyana jinin makiyin shi muke.
Wanan zancen da kakewa Abba yanzu kan ko wanda bai hada komai dashi ba ya kawo mashi kudi ai karba zaiyi yadda yake neman kudin nan ido rufe.
A yadda naji har filincan nasa na hayin malali ya saka a kasuwa wai ba a taya filin da kudi me yawa ba yasa bai sake shi ba.
What ya fada da karfi yana dagowa daga kwancen da yake ya kara maimaita tambayan da badai filin nan daya fara gina company atamfa a cikin sa ba ?
Ta dauka ya damu da jin hakan ne sai tace a cikin marairaice wallahi kasan mutane da son banza suka dinga taya masa shi a wullakance shine ya fasa gashi ance lokacin da aka basu ya kusa cika dole yaje da wani abu mai dan tsoka da zai fara biya.
Umm,mm ya fada ya koma ya kwanta yana jin wani irin a zuciyar shi lale wanan mutumin da karfin hali yake sosai watau filin marayu din daya mallakawa kanshi da karfi da yaji shine zai saka kasuwa yanzu da yake ganin filin zai iya fita hannun shi duk da basu yarda da cewa iyalan mai filin suna raye ba .
Ba abinda ya kara daga masu hankali kamar jin wai harda da umma tazo masu wai dan dan uwan sune shima din wanan ya fi daga hankalin su sosai don a mota da zasu dawo daga karbo Alh Nuhun can abuja yake jin su baffa hamza na wanan firan.
Muryan Nazifa ne ya katse mai dogon tunanen da ya shiga din lokaci guda tana fadin kaji dalilin dayasa akai shawaran tara masa kudin a bashi.
Ok naji sai na duba ya iya fada don baison maganan ta kara masu nisa a tsakanin su yana son yin dogon nazari a lokacin.
Shine washe gari ya dauki waya ya kira umma yaji yaushe zamu dawo don asan abinda za ayi kafin Alh Nuhu yakai ga kadar da filin ya salwance a dauki mataki.
Bayan sun gaisa da umma ya tambayi lafiyan sune yake fadin ya labarin Sahiba umma yaushe zasu dawone daga tafiyan ?
Sai umma tace a cikin murmushi ai gata nan a gaba da safen nan suka dawo masha Allahu ya fada tare da fadin an dawo lafiya ko ya aiki kuma ?
Na amshi wayan ina fadin yaya mun sameku lafiya ya su mimi da maman su karo na farko tun farun matsala a tsakanin a baya .
Duk suna lafiya ya fada OK zan barki ki huta zan shigo zuwa jibi akwai maganan da nake son zamuyi daku na muhinmin idan nazo din.
Ok yaya na fada a lalace ina mikawa umma wayan dake hannu din ta karba ban san dogon bayanin da yake mata ba a lokacin na dai ga umma ta bata fuskan ta sosai lokaci guda.
Sai bayan sun gama wayan ne umma ta sauke ajiyan zuciya tana kallona take fadin wai filin mahaifin kune da Alh Nuhu ya mallaka har ya fara gina a cikin sa yasa a kasuwa zai saida ya biya basusukan da ake binshi yanzu.
Au filin yana nan ashe na fada cikin mamaki ina kallon umma tace haka dai yake fada min yanzu wanan akwaishi da karfin hali da iya cin amana.
Ya kai karshe don wanan ko ya sayar saiya dawo hannun mu na fada ina komawa kasan kafet na zauna tare da kallon ammar wanda nasan ni yake jira na bude kaya ni kuma naki bude mai.
Murmushi ya sauke a fuskan shi yana fadin anty please na nuna mai kayan da hannnu ya dauko muka fara budewa don ni kaina ban san meye a cikin sayayyan nasaba tunda bani na saya ba.
Allah da ikon shi kayan umma ne muka fara budewa kalla bakwai irin dunkunan Dubai din nan na manyan mata tun a jakkar na gane haka don an rubuta a harshen larabci da ~umma~ .
Nan muka duba mukaga komai na ciki harda wani handbag mekyau sosai na manyan mata na Ammar na jawo na duba suna na tura mashi gaban shi ya bude.
Komawa nayi na jingina kaina saman kujera tare da dan mayar da kan nawa baya ina lumshe idona ba komai nake tunane ba sai zance biyu na farko zancen sayar da filin Alh Nuhu sai kuma zancena da Alaja.
Ihun Ammar ne yasani dan dagowa ga yadda nake zaune ina kokarin ganin abinda yakewa ihun wasu suit ne size din shi masu kyau gaske irin da yaran su can ke sakawa ya dago yana fadin Antymi wanan rigan yai min kyau sosai wallahi ya fara min godiya.
Bani na sayama ba na fada kai tsaye don ban iya karya ba na kalli na umma da nawa nace ogan mune ya sayo wa yan nan duka a dubai.
Wani kallo umma ta jefo min mai alaman tambaya nayi saurin fadin wallahi umma ban san zai saya ba yanzu ma mamakin hakan nakeyi yadda ya iya zabe haka kamar an auna tsayin ku.
Wayana ne ya dauki kara na mika hannu saman kujeran na dauka ina dubawa don ba wanda ya kirani tun shigowana gida har washe garin nan.
Sabon layi na gani na kasan waje daga kasan Germany da mamaki a fuskana na dauki wayan ina daukan wayan a bangarena.
Irin sallaman dana tashi dashi a bakina na dabi,an yarbawa nayi a wayan muryan da aka amsa min sallaman ne a lokacin yasa gabana faduwa lokaci guda duk da na sheda muryan me kiran nawa a lokacin.
Kun isa gida lafiya ya kuka samesu duk ya fada a lokaci daya da kyar na samu cikin kyarman murya na hada dace masa Alhamdullahi.
Masha Allah ya fada sai kuma yai shiru kamar yadda nayi shiru a nawa bangaren bayan dan second na tsinkayi muryan shi yana fadin.
Ina Germany na samu contrac dasu zan shigo masu da wasu kaya daga Labeno sun yarda sun saka min hannu wanda hakan zai jawo min dagawa sosai da yardan Allah.
Masha Allah nafada tare da mashi fatan gamawa dasu lafiya na nuna murna a fili kwarai ya dan kara min bayanin yadda abun zai kasance mashi kafin ya dan sake yin shiru na wani lokaci yace.
Kiyi hakkuri da abinda mahaifiyarmu tai maku sahiba musanman ma ke kasancewa na bana wurin lokacin da hakan ya faru a tsakanin ku.
Murmushin dole nayi ina fadin haba dai wanan ba komai bane don muma ai tana a matsayin mahaifiyace a garemu na tsunci kaina da fadin hakan.
Nasan hakan Ganiyat da Jimoh sun fada min komai daya faru don haka kiyi hakkuri tunda mun san dalilin yin hakan a gareki.
Na fahinci yaji komai daya faru a dubai din nace kuskure fahinta ne aka samu duk wani mairai idan abu yazo masa a lokacin da bai zata ba zai iya aika kome yake gani a matsayin kariya a gareshi.
Nagode ya fada yana sauke ajiyan zuciya a hankali har ina iya jiyoshi ku zauna ku huta na mako daya kada ku fita gun aiki murmushine ya dan subce min nace.
Oga ai mun huta zaman yayi yawa hakana gara mu koma bakin aikin mu don nema ya kaimu wurin ka ba hutu ba don haka dole mu koma muci gaba da aiki hutun ya isa hakana.
Ke baki kama da wace zatai ta aiki ko wani lokaci ba hakana shigan ku office officialy ne yanzu sai idan bukatan hakan yataso a garemu.
Wani nauyi da kunya naji lokaci daya nace nagode yace kada ki damu nike da godiya a wirin ku ki mika min godiya ga mama ya kashe wayan.
Na dago muka hada ido da umma data tsura min idanu budan bakin umma tace min kiyi hankali da irin mutanen nan da suke yawan son diyan su maza .
Kallonta nayi cikin mamaki tace kwarai saboda data kula da cewa wani abinda batayi tsamani ba yana shirin faruwa a tsakanin ki da danta yasa ta fara bullo maki da haka.
Batayi karya ba don ko wani tsuntsu kukan gidan su yakeyi tana ganin ke bakiyi daraja da mutuncin da za a ce danta ya nemeki ba don kedin ba yar kowa bace take gani kuma ga wanan matsalan dake a kanki.
Sai lokacin nayi magana jin umma tayi shiru nace umma ki gafarceni ban taba saurayi ba a tarihin rayuwana.
Saidai a tunanen ita Alaja din tana ganin kamar muna soyayyane da dan nata wanda ba hakabane a wajen mu nasan dai ya bukaci in taimaka mashi in nuna kamar soyayyan mukeyi a gabanta.
Nan dai na labarta mata abinda ya faru a can kaf ban boye mata komai ba saida na gama take fadin wanan gangancin fa Sahiba ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA , , , , , , , ,

7️⃣7️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL QAYYUM , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Washegari tunda safe na fara shirin don samako nake sonyi zuwa inda na kwana ina kullawa a raina.
Koda na fito su umma basu tashi ba a lokacin ko Ammar dake fita school bai tashi ba na bar gidan Allah ya taimakeni na samu mai taxi irin masu sammakon nan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login