Showing 3001 words to 6000 words out of 382072 words
rayuwan su zai kasance a nan gaba dan sanin yadda suke fuskantar rayuwa a yanzu.
Ga tambayan fam a zuciyar su amma babu mai bata amsan hakan duk mutanen da tasan umnan su na zaman arziki dasu tun farko tabi ta tambaye su ko daga ina suke amsa dayane basu san garin su ba ko yan uwan su suma dai ganin su sukayi kwatsan a lagos.
Abinda suka sani shine daga dai arewa sukazo lagos din da goyon sahiba da cikin kanin ta kuma a jikin umma din amsan da take samu ke nan a gurin wasu da suka san su a baya.
A kullun ta shiga irin wanan tunanen ko wani matsin rayuwa irin kalaman umma gareta ke kara mata karfin gwiwa .
Har ta ji hankalinta ya kwanta da rayuwan su a nan din don ta fahinci inda umman nasu tabaro yan uwan su da mahaifanta yana da zafi da ciwo a garesu ke nan da zama can din.
Don haka takan kwanmacewa rayuwan su a nan lagos duk da irin gwagwalmayan tashin hankali da fitinan da suke gani yanzu a rayuwasu.
Indai hakan da umman nasu tayi na nisanta su da yan uwan su har take ganin shine mafita a garesu.
Idonta ta bude da suka ciko da hawaye ta nisa tana sharewa a hankali tare da tunanen yadda zata bada hinma ga rayuwan su dana mahaifiyarsu din duk da tasan abune mai kamar wuya a gareta a yadda suke nan.
Ganin ruwan saman ya tsaya cak ta mike daga inda suke zaune ta fara gyara dakin don su sami wurin kwana a ranan saboda haka suke a yan shekarun nan idan ana ruwan sama bata da huta a rayuwan ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI YAN UWA BARKAN MU DA JUMM,A
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SAHIBAT yarinya ce matashiya yar kimanin shekaru sha hudu a duniya sahibat doguwa ce kyakyawan gaske.
Tana da wani irin halitta na daban da ba a faye samun irin su ba da yawa a cikin mutane sune ake kira ace mutum kamar shi ya zauna ya tsara kanshi don kyau.
Haka launin fatan jikinta yana da haske da sheki ga jikinta a murje yana walkiya wanda hakan baiwane da kuma gado a bangaren mahaifin ta.
Ba zaka san baiwa bane hakan sai kaga irin wahalan data taso a cikin shi amma wahala da wanan rintsin bai hana fatan jikin ta sheki ba.
Duk da Sahiban ba fara bace irin sol din nan sai kuma dole a sakata a cikin farare ko a hakan sai dai kuma ko a hakan samun mai kyaun fata irin nata yana da wuya hakama mahaifiyar ta duk da wahalan da suke fuskanta na rayuwa.
Yadda Sahiba take da kyau a baiyane haka kuma take da kyau hali a boye don akwai kyakyawan zuciya da kyakyawan hali a tare da ita.
Haka idan maganan hakkurine idan anzo gun sahibata azon gidan hakkuri da juriya duk tsanani da wuyan al,amari bai wuce Sahiba ta kalleshi tayi mai murmushi ba.
Amma fa ba kowa yasan da hakan ba sai irin su iya Muluka da maman Bisi da suka kwashi shekaru a tare ne suka san wanan halin nata na boye.
Don idan ka ganta tayi shiga na bat da kama ga mazan zamani mayaudara a wurin neman abincin su ba zaka taba cewa ita keda wanan halin ba.
Amma idan mutum yana son ya gane waye sahiban na gaskiya to yazo gidan su a lokacin tana gida zai san da hakan dana fada a yanzu.
Kowa na yabon hali irin na Sahiba har kaga yarbawa nawa diyan su kwatance da ita da irin halinta na taimakawa uwarta da dan uwanta tun tana yar ficiciyar ta kuwa.
Tun tasowan Sahiba a duniya ta bude ido a cikin talauci da wahala da kunci irin rayuwa tun tana karama har dan tasowan ta din nan bata taba ganin wani abin jin dadi na zamani a tare dasu ba.
Daga fannin abinci sutura ko wani abin jin dadi komai zasuyi a rayuwan su sai da kyar da sudin goshi zasuyi shi tun dai a fannin abinci ba karamin wahala suke sha ba kafin su hada abinda zasu ciwa ransu gasu har su ukku kuwa.
Don hakane ma basu damu da wai wani dafa abinci ba donko ko sunce zasuyi din abinda zai dafa abincin a garesu shine aiki kuma.
Don hakane suka kwanmace a sayo garin kwaki da dan mangyada a yamutsa aci a tashi sai idan sun gaji da ci ko ranan data samo kudi da dan yawa wurin yin buga bugan ta zata dan sayo masu wake da bread da iya bisi ke dafawa a kofan gidan suci.
Kamar yadda Sahiba ta bude ido ta tsunci kanta a cikin kangin talaici da kakanikayin rayuwa.
Don haka ta bude ido data fara wayo taga mahaifiyarsu tana faman yawon bara dasu a cikin birnin iko din.
Har izuwa yanzu da ta karbi uwar nata ta dauke mata duk wanan wahalan don ciwo dake son ya nakasa masu mahaifiyar nasu a yanzu.
Don ga ciwo ga rashin gatan dake damun umma din yasa tun bata karasa kai hakan ba take iya kokarinta wurin fita ta nemo masu abinda zasu ci ga kanin ta karami ne sai kafa kafa sukeyi dashi don yanayin garin n a iko da ba kyau.
Tsakanin Sahiba da mahaifiyar su akwai shakuwa mai yawa don bata taba yin komai sai da yardan mahaifiyar nata takan fita yawon buga buga abinda zasuci din.
Sahiba ita ta saka kanta karatun boko na addinine ta dan samu a wurin mahaifiyar ta a gida don yanzu hakama har takai jss two a makaranta gwaunati na diyan tallakawa irin su dake can dan kasa da unguwar su kadan.
Da hakan ma yanzu ta saka kaninta Amar irin wanda take zuwa din duk a cikin dan abinda take samowa suke wanan hidiman a rayuwan su a wahalce.
Karan wayan ta dake ruri daga gefen tane ya ankarar da ita da sauri ta mika hannu ta dauki wayan tana fadin dan halas yanzu nake maganan shi a raina fa sai gashi ya kira.
Kallon ta yarta Nabila dake gefen ta tayi cikin ya motse fuska yar tace halan ya Abubakar ne ko tana danna daukan wayan take fadin shine dai.
Yar ta wani kara tabe fuska tana kawar da kanta gefe daya ta dauki wayan tana fadin ni har ka ban tsoro da banji kiran ka ba tun jiya nasan kuma ku ba kiran ku akeyi ba idan baku kuka kira ba.
Yace wallahi tun jiya kina raina aikine kawai da yai min yawa da gajiya kuma ya hana in kira ku jiyan.
Sai kuma ya juya yana gaida ita da kwana tare da tambayan ta mutanen gida tace duk suna lafiya sun raka hjy karima unguwa dagani sai Nabila ce a gidan yau.
Yace dama abinda suke so ke nan fita yawo aje unguwa basu da wani abin yi sai gulma a rayuwan su.
Kai Modibo har yaushe ka zauna kasan abinda yaran nan suke so yanzu kai da kullun kana faman yawon bin jirgi zuwa kasa kasa.
Dariya abin ya bawa Abubukar wanda mahaifiyar shi ke kira da Modibo don sunan kakanshi yaci ta wurin uba.
Ni fa yanzun ba abinda ke damuna kamar inga ka tsaya da gaskiya kan zamcen auren nan naka shine muradina a kullun.
Hajja Addah har nawa nake da kike min zancen aure a yanzu duka duka fa ban ko kai talatin ba balle in fara zancen aure.
Zancen banza ke nan me kake nema a duniyan nan da baka samu ba a yanzu kudi ilimi duk Allah ya baka fiye da yadda ake zato.
So kake duniya ta samu a baki dagani har mahaifinka da abokan shi kema tayin yayan su ka aura ?
Ganin ran mahaifiyar nasu kamar ya baci abinda yaki jini ya gani ko yaji ke nan yasa a cikin wasa yace yanzu ni hajja Addah ina nake da lokacin neman wata yarinya can sai ki nema min ai wace ta dace dani ko ?.
Cikin jin dadin zancem shi uwar ta sake murmushi ta yadda har yake jiyo ta a waya tana fadin to kokai fa modibo ka tsaya kana wahal da kanka dana mutane.
Aure fa shine cikar kamalan mutum yanzu kana aure darajan ka zai kara hauhawa ko ga mutane zasuyi ma kallon cikkaken mutum a idon su sabanin hakan da kake zaune kai kadai.
Dariya yayi kafin yace da ita wai daddyn mu ya dawo kuwa ko har yanzu yana can ?
Wanan zance kakeyi ai sai lokacin da muka ganshi yanzu kuma don dama ya fada muna wanan karon zai dan dauki lokaci a can idan ya tafi.
Allah ya dawo dashi lafiya ya fada tace amin kadai kula da kanka a cikin arna kun nan don Allah.
Insha Allahu hjy Addah babu abinda zasuyi dani sai Allah na zauna ma acikin wa yanda suka fisu zama arna Allah ya fito dani lafiya balle nan da suke da surkin musulmai a tare dasu ga hausawan mu ma ko ina a garin kamar kana arewa.
Allah ya tsare tayi mai kafin suyi sallama dashi tana jin tausayin dan nata da son shi yana karuwa mata a zuciya.
Idan bata manta ba haka mahaifin su ya tashi shima ya fara dan buga buga har yakai yanzu yana ketarawa waje ya saro kaya.
Shima a bangaren Abubakar din yana aje wayan nisawa yayi yana shafo kanshi zuwa fuska kafin ya furzo da iska mai zafi daga bakin shi.
Yana ci gaba da tunanen matsalan gidan su din da yayi yawa a yanzu koba a fada ba yasan iyayyen nasa mata suna hakkuri da halin mahaifin su a yanzu da can din ma da sam daddy din baida lokacin su sam sai idan yaso.
Sanye take a cikin kayan makarantar da suka amsheta masu ruwan blue colour buje da riga babu batun dan kwali ko hijjabi sai dan hular bareti da ke saman kanta wanda ta dunkule gashin kanta ta cusa a cikin hula yasa dole don yawan gashin hulan ya dan dago ta baya kamar tayi a cuci maza dashi.
Bujen ya tsaya mata iya gwiwanta sai takalman da data sawo masu ita da kaninta wurin yan gwajon su na lagos masu kama da kwabattan maza take jansu hakana don kwarin su.
Bata damu da kanta ba ta dauko kulanda take sayawa kanin ta abinci don tara kada yaga sauran yara naci ya saka kanshi a damuwa .
Yasa a kullun bata yarda kanin nata yaje ba wani abinci a tare dashi kallon mahaifiyar su dake zaune ta kura masu ido kan duk abinda sukeyi na shirin fita makarantar tayi tana fadin.
Umma mun shirya zamu tafi uwar ta dan nida tare da fadin to dahiba ubangiji Allah ya tsare mun ku Allah ya bada sa,an abinda akaje nema a rayuwa.
Suka amsa gaba dayan su da amin don inda sabo sun saba da hakan a kullun idan zasu fita daga gidan zuwa wani wuri.
Suka fito tana binsu da kallo tausayi ga yayan nata kafin ta mayar da idonta tana cigaba tunane rayuwan data baro a baya gida har ta saka yayan nata a ciki wanan halin kangin talauci a yanzu.
Eh dolene yasa hakan a garesu don ta tsaretar da rayuwan su ga baki daya da ake nema a halakasu kan abin duniya.
Hakan yasa tayi nisa da gida nisan da ba wanda ya zata ko ya tsamaci har zata kai wanan garin mai nisa haka da bata da kowa a cikin shi.
Hawayene suka zubu mata a fuska lokaci daya don wanan tunanen da tayi na dan lokaci daya tasa hannu a hankali ta share ta dauki abin karin da Sahiba ta sayo mata don ta karya dashi.
Bayan ta gama ta mike zuwa wajen gidan don tasha iska kamar yadda ta saba yi a akullun ta zauna tana kallon mutanen gidan suna gittaya tunda rashin lafiyan nan ya kamata.
Duk da tasan ta makara hakan bai hanata kai kaninta har makarantar su ba har bakin ajin su ta kaishi kafin ta juya da sauri ta nufi nata wurin karatun .
Tafe take tana sauri kada malamin lissafi ya shigo bata ajin don tasan yau dashi zasu fara darasi a jin nasu gashi kuma mugune don dole saboda halin shi ta koyi lissafi har ta iya yanzu.
Bata ankara ba taji an watso mata irin ruwan dake kwanci a gefen hanya da sauri ta daga kai ta kalli drivern motan dake tafiya a hankali kafin ta sake dago kai ta mayar ga tufafinta daya baci da ruwanba lokaci guda .
Rantane taji ya baci don ganin yadda kayan nata ya baci cikin lokaci guda haka bata san lokacin data bude baki tana fadi a cikin harshen yarbancin daya zauna mata a baki yanzu radau .
Tana fadi a hasale Abi wareni ?
Olesi omo buruku noses ta hada da turanci cikin daga murya da karfi ta yada har mai jan motan zai iya jin muryanta.
Gani mai motan yaja ya tsaya sai can ya bata daina zagin a cikin harshen yarbancin ba sai can taga ya fito daga motan ya tun karo yarinyar daya batawa jikin nata don bada hakkuri shi kanshi bai so hakan ya faru ba har a ranshi hakan ya faru bane wajen kaucewa hanyar da yaje yi ya watso mata ruwan a jikinta gaba daya ya baci .
Ganin haka yasa ya yanke shawara fitowa ya bata hakkuri don sanin zafin abinda ya aikata mata din a lokacin.
Saidai tun daya tunkaro ta din yana jin muryan ta cikon dan hasala ta sake fadin you, you no desi road, see d way you skarter my cloth ?
Mumu man wen no get sense ta fada da karfi tana juyawa ta fara tafiya ta bar wurin don ta makara sosai a lokacin.
Tsaye yayi ya kasa karasowa inda take tsaye din sai faman kakaban kayanta da takeyi rana ta a bace kafin ta ja tsuki da karfi kafin ta soma tafiya rai bace tana fada kamar sabuwar mahaukaciya da ita.
Yana tsaye har lokacin yana tunanen ina yasan fuskan yarinyar nan ne sai kuma ya tuna ina fa zai santa wanan yar kabilan yarobane fa shi kuma baida wani alaka dasu saina aiki.
Ganin ta wuce batama tsaya ba yasa shima ya juya ya shiga mota yana jan tsuki a fili ya ja motar shi ya bar wurin yana fada a cikin zuciyan shi ya koma motan ya shiga ya tayar ya bar wurin zuwa lokaci shima ranshi ya gama baci da abinda yar yarinyar karama tayi mai don rashin mutuncin da ake fada yan lagos basu dashi dama.
Yana fada a zuciyan shi tare da jan tsuki fili yana cewa wani irin garine wanan marasa mutunci da rashin sanin girman mutum.
Har yakai inda zai tafi ransh yana bace har lokacin yana fada a zuciyan shi kafin abokin aikin shi ya jashi da fira duk da ya fahinci ran shi a lokacin kamar ya baci sai bai kula da hakan ba gare shi sosai don ya dauka dare fuska na dayaga cikin dabi,un shi don ko yaushe shi fuskan shi a daure yake.
Haka yasa yaci gaba da masa bayani har ya manta da komai na bacin ran da yake ciki da farko sukaci gaba da tsara yadda zasuyi su cin ma abinda ya fito dasu a lokacin har zuwa yamma kafin su rabu ya koma masaukin shi.
Sai dai duk abin nan hankalin shi naga abinda ya faru dashi da safe don ranshi ya baci da zancen abin daya faru din dashi na yadda yarinyar ta zage shi tsab da safe.
Don haka ya zama mai dole a yanzu yayi taka tsantsan da kowa a garin saboda ya karanci halin sune rashin mutunci dai.
Sahiba kuma dai a nata bangaren ta kasa suke jiki a makaranta don haka tun shiganta ajin take zaune a cikin class sai faman cika take tana batsewa ga banza tana fada a zuciyanta ita kadai.
Har ta dawo gida tana zaune tana cire takalman dake kafatan da safa ta take labartawa mahaifiyar ta abinda ya faru da ita dasafe a hanyarta na zuwa makarantan ta
Nan uwar take mata fadan ta daina zagin mutane haka tayi mai uzuri wata kila shima basan rashi ai ya watsa mata ruwan kwata ba da gagan sai dai idan yanayin hanyar dake kwancin ruwane yasa har motar ya watsa mata ruwan bai sani ba.
Da yarbanci take fadin umma shi makahone da ba yaganin mutane a kasa suna tafiya, kawai dai wullakancin sune na masu kudi shiyasa yayi min haka .
Ai da naga ya fito a fusace na gudunayi ai