Showing 177001 words to 180000 words out of 382072 words
au ashe barci ya kwasheni ?
Yace ke me kika kira mommy kika fada mata dazun yana mai mata wani irin kallon tsana idanunshi a cikin bacin rai sosai yake kallonta din.
Kaje an fada ma munafunci da makirci da gulma a kaina yanzu kazo zaka tsureni ko ta fada tana kokarin komawa ta kwanta.
Ya wani irin fincikota daga filon data sa kanta dintace kada ka balla min habana don Allah a banza ta fada a fusace tana kokarin kwace jikinta daga rikon da yai mata din.
Nace me kika fada wa mommy a waya tace au an fada mane don kazo ka hauni da fada bayan zagin da kanwarka tayi min kuma ?
To ni zan iya dako wani munafuki wallahi tunda ba zaman lafiya ake so ganin munayi ba dama ai don haka anzugaka kazo kaci min mutunci don na fadawa mahaifiyarku gaskiya ko ?
Tass ya dauketa da wani irin wawan mari saida ta koma kwance yadda ya sameta ya nunata da yatsa yana fadin wallahi ahir din ki da uwata wallahi.
Duk iskancin da rashin mutuncinki da zakiyi ki tsaya a kaina nidake auren ki kada ki kuskura ki saka mahaifiyata a ciki don ban raina maki taki ba kema.
Kodon kinga ina kyaleku bana kula wallakancin da uncle yake jifanta dashi don kina mara hankali bari kema ki fara jifanta dashi ko ?
Mara hankali da tunane kawai ke idan kina da tunane kin taba ganin ina sa,insa da uncle ne duk abinda yake nuna min a fili.
Sai kece don kin raina min tawa uwar baki dauketa a matsayin da Allah ya bata ba a gareki na kanwar mahaifinki don baki da tarbiya zaki nunawa duniya kalan tarbiyan da aka baku na rashin girmama babba ?
Jin fadan da yake yine yasa yaran nasu falkawa a tsorace suna saka kukan firgita suna kokarin kankame jikin uwar nasu.
Nazifa dake dafe da kuncinta tace ni kamara Abubakar kan uwarka da yan uwan ka yace an mareki ke wacece zan gwada maka ko na isa wallahi don sai an rama min marin nan dakai min sai ka raina kanka.
Yace wallahi karya kike baki isa ba wallahi kuma banga wanda ya isa ba bayan Allah bata dadaraba ta kara fadin zaka gani wallahi kuwa.
Ya daka mata tsawa yace saina tattakaki yanzun nan wallahi mara mutunci ya juya yana jinta taci gaba da yimai suratai tana fadin zaka gani zaka san ka mareni.
Uwarta ta kira a cikin daren nan tana dauka ta fara fada mata abinda ya faru tun farko sai data gama fadi uwar tace rufamin baki sakarai kawai an fada maki duk son da yake maki sai ya bari ki zagi uwarshi ko yan shi a gaban shi ?
Allah ya aikeki ki fadawa Alh wanan zancen sai kin raina kanki a duniyan nan wallahi don dama neman hanyar da auren ki zai balle ake bida shiko Alh ba ruwan shi rabaku zaiyi kada ki koyi kisa da kisisina irin na kowa zauna kina masa gadara da isa a gida idan shi zai fitar dake ta kashe wayan tana jin haushin wauta irin na yarta.
Washe gari yana ganin kiran mommy yaki daukan wayan don yasan zancen ne zatayi masa shiko yanzu ko wanda yasan Nazifa baison jin sunan a gaban shi.
Shirin shi ya gama tsab ya dauko dan jakar shi da yake tafiya dashi ya fito a falo ya hangota zaune a saman kujera duk idon ta ya kumbura don kuka.
Ya iso inda take bata ko dago kai ta kalleshi ba ya dan tsaya tare da kiran sunan yarshi mai sunan mahaifiyarshi mairo .
Saidai ita Nazifan ta juye tace wai sunan kanwarta ce dake bimata mairo ya saka don haka take kiranta da mairo din ba sakayawa don shi.
Zanyi tafiya kinji saina dawo ya fadawa yarinyar tare da saka hannun shi cikin aljihun shi ya ciro kudi ya mika mata daga haka ya daga ya fita baiko jiyu inda suke ba yabar gidan ta bishi da kallo.
Tun dana dawo nake barci na kashe wayana don kada a sameni kiran ya tayar dani daga barcin gajiyan dana samu din.
Barci nayi sosai don ban falka ba sai yamma sosai gap da magariba na tashi gurguje ranan nayi sallolin dake kaina sai kuma yuwan da nake jin na fito umma basu ciki suna shago.
Kitchen din muna nufa don samun abinda zanci duk da yunwan da nake ji bai haba in gane cewa akwai sabon abu a cikin kitchen din ba da nabi da kallo ina mamaki akwai miya saidai ba a kaiga dafa abinci ba lokacin.
Saina yanke shawaran yi muna sakwara bayan na dafa indomie na aje na dora doyan dana fere na wankeshi na zuba a cikin tukunya.
Na fara cin indomie din sai naji baimun ba na aje fara aikin sakwaran da zan daka din miyan na saka bayan doya ya dahu nayi hadin miyan egushi.
Kafin a kira sallah na hada komai yadda nake son shi na gyara kitchen din naji ana kiran sallah magariba yayi har falo na gyaro na shige nayi wanka tare alwala .
Ban fito ba duk da kafin in idar din naji muryan umma sun shigo cikin gida ma,ana ta rufe shago sun shigo gida.
Saida nayi isha,i na fito ina gaida umma take fadin ashe na tashi har nayi girki tana fadin bari su shigo su girka abinci tunda ina barci.
Murmushi nayi na zauna ina gaida ita tare da tambayan ta kasuwa take fadin sai hamdala kasuwan ya dan tsaya saboda zuwan dama yanzu ba ciniki sosai.
Kasa na zauna na kalli Ammar dake ekujo anty mi na amsa mashi da yaya kake yace lafiya nace ga abincin ka nan na daka maka.
Da sauri ya dago yana dariya tare da fadin da gaske sakwara nayi yana kokarin bude kulan abincin yagani.
Sai ya kwashe da dariya ya nufi kitchen ya fito da plate biyu a hannun yazo ya zauna a gabana tare da jawo abincin ya bude yana kallona na dan kalloshi ina fadin ehhee mana ma,ana ya zuba muna muci.
Har umma shiya zuba mata ina nan zaune hankalina ya dauku a wayata ina karanta sokon da aka tura min.
Yace min bissillahi na dan motso muka fara cin abincin falin yayi shiru don yana cikin dabi,an mu hakan idan muna cin abincin.
Dazun yayan ku yazo gidan nan saidai bai shigo ba a shago ya samemu muka gaisa ya kawo muna kayan abinci nayi shiru ina ci gaba dacin abincina ban dago kaina ba.
Bakiji bane ta fada umma an fada mashi bamu da abincine daya kawo muna wani irin maganane wanan.
Shiru na sake yi banyi magana ba yaran nan sune ke kulamu a cikin duka yan uwan mu da muke dasu ina laifin su yanzu don yazo ya kawo muna abinci.
Sun san abaya mabukata muke ba zasuyi zaton a yanzu muna da dan dama ba duk da alama ma ya nuna a jikin mu cewa bamu tare da wahala.
Amma ko muna dashi ai ba a hana alheri sanan yaushe rabo dayazo gidan nan wurin mu tun lokacin da kikai mai wullakancin nan bai sake zuwa ba sai yau din nan yazo ya kuma zo muna da alherin sa.
Wani yayan namune ciki yazo umma ta kyaleni bata ban amsa ba sai Ammar ne yace mai bamu kudi din nan mana handsome din nan.
Dan gwagon ku hari umma ta fada a daidai lokacin da aka turo kofan falon namu bayan anyi knocking za a shigo.
Duk muka juya don ganin maishi yaya Abubakar ne ya shigo da sallaman shi falon muka karba mai ya shigo.
Mun gaisa dashi ya amsa tare da kallon mu ya samu wuri ya zauna umma tana tambayan shi mutanen gida .
Yace suna lafiya a ranan ma ai ya baro kaduna yazo lagos din aiki sai umma ke fadin intashi in kawo mai abinci da abinsha a dauko a shago.
Haka na mike zuwa dauko na dauki key din shagon don zuwa na dauko mai drinks din yana fadin a barshi umma tace haba kamar bako dai dakai modibbo.
Ko baka iya cin abincin mune kada a kawo maka da sauri yace No ba haka bane mama a koshe nake dama kafin nazo nan din.
Ni dai ban tsaya sauraren su ba na nufi hanyar sauka daga benen sai Ammar ya biyoni a baya muka fita tare dashi.
A can yake ba labarin zuwan mustapha da baiko tsaya don ya samu akwai custermers a wurin ta sunzo daukan kaya lokacin ya aje muna abinda yazo dashi ya wuce.
Koda muka fito ya tsaya ya rufe sai a lokacin na kula da motar da aka sake ajewa kofan gidan munga mota a kofan gidan bamu dauka gidan mu maishi yazo ba don akan aje motoci a haraban namu wani lokaci don muna da filin parking sosai a wurin..
Muka shigo saida naja na tsaya don ganin su, su biyun duka a lokacin daya gidan namu kamar sun hada bakin zuwa a lokacin.
Wani irin matsanancin faduwan gabace ya ziyarceni lokaci daya don ganin su a tare da nayi a falon namu suna gaisawa da umma.
Tunda yayi sallama ya shigo suka gaisa da junan su kowan su ya mayar da hankalin shi kan wayan shi yana dakila.
A sanyayye na bude baki ina gaidashi kafi yada kan shi ya amsa muna na aje drinks din a gaban ya Abubakar kafin shima na aje mai daya a gaban shi.
Na juya na shiga kitchen na dauko plate na zuba miya na kawowa kowan su plate din na aje gaban su.
Na juya na saka ledan sakwara bibiyu a cikin plate nakai gaban su na aje agaban kowan su sai shi mustapha din nema ya dago kai a hankali yake fadin thanks.
Na daga ba tare da yin magana ba ruwa na koma na dauko masu har na wanke hannu ina ajewa na nufi hanyar dakina naji muryan umma na fadin .
Ina zaki ga abincin kunaci da kanin ki zaki tafi kuma na juyo a hankali cikin harshen yarbancin ina fadin na koshi kuma bazan iya kara ci ba yanzu.
Yayyun na ki fa da sukazo zaki shiga ki barsu a zaune ta kara fada naji wani iri ina fadi a raina wayyyoni Allah na umma zata kwafsa min a nan kuma.
Da ace umma tasan yadda nakeji lokacin a raina da batayi min wanan maganan ba lokaci.
Yanzun dai komai ta famjama famjan inji yan iya magana bani da masaniya akan zuwan su a lokacin banda kuma dalilin shin .
Don haka zaman da banaso a wurin suna zaune ban kuma da dabaran da zanyi in shige ciki a yanzu don dole inbi umurnin umma din.
Haka yasa na dan dago kai na saci kallon inda suke naga mustapha shi dan duniyan har ya fara cin abincin dana aje masu din a gaban su yana ci a cikin sukuni da kwanciyan hankali ba wani damuwa a tare dashi lokacin.
Sabanin yaya Abubakar dako kallon abincin ma baiyi ba yana fama da wayan shi kodan yafi mustapha din zama bafulacen kidi ne oho.
Bani da zabi a lokacin illa kawai in dawo in zauna a tare dasu duk da yadda nake jin feeling some,how a gaban su din a yanzu.
Kodan saboda na girmane yanzu na fara sanin kaina ko kuma dai kawai don bana son wani halaka da yan zuri,ansu baki dayane a yanzu ban sani ba.
Yadda ya sake jikin shi yana ci abincin shi sosai hankali kwance suna dan hira da Ammar dake gefen shi zaune da gani kasan sun dan saba da yaron shima sosai.
Amma ya Abubakar uffan baice dasu ba yana ta faman dakilan wayan hannun shi kawai karshe ma wayan shi tayi ringing ya dauki kiran yana jin maishi.
Kai sai a ranan na kara sanin shi din miskiline na karshen karshe don ba zakace shi din ya taba sanin Almustapha din wani wuri ba ko suna da alaka ta jini da junan su bah.
Umma na a takure take zaune cikin su lokacin kawai dai ba yadda ta iyane ta zauna amma zuciyar cike yake fam da zargin su a lokacin.
Saida ya gama wayan shine yana sakawa a aljihu a daidai lokacin shi mustaha din ya mike yana cewa umma shi zai tafi jiya ya zo lagos shine yace bari yazo ya gaida mu.
Godiya sosai umma take mai tana saka mai albarka kan irin yadda suke kullamu suna zumuncin lekomu lokaci lokaci.
Duk abin nan da sukeyi ko ya dago kai yaiwa dan uwan nashi magana asalima ko sashen da yake ya Abubakar bai kalla ba lokacin, duk da yana jin shi yana sallaman da umma din ko dagowa baiyi ba har ya fita.
Nikan hakan sai ya ban mamaki sosai da tsaro tunda nasan yadda iyayyen su suke da zumuncin su ganin haka saina kara shan jini da zurian tasu ga baki daya.
Yana zaune a inda ya barshi sun fita da Amar sai ga Amar din ya dawo yana fadin ya wuce sister wai mu shirya gobe zai zo ya kaimu beach.
Umma ya akayi wanan ke zuwa maku gida haka har kuka yarda dashi baku san koshi waye bane halan har ku sake dashi haka ?
A, a modibbo baka gaje dan uwan naka bane halan don nima mamaki nakeyi tun shigowan shi yadda kuka nunawa junan ku baku san juna ba.
Saida ya dan murmusa ya dago kai yana fadin nasan shi mana mustapha dan gwaggo hari sister din daddy ko ?
Wanan ba mutumin arziki bane kada wata rana ya jefaku a fitina azo ana maku buncike a gida kan laifin da baku aikata ba.
Umma tayi wani iri da sauri ta kalli moddibo din a cikin mamaki tana fadin cikin sanyin murya
Shidin ai yana zuwa nan ne saboda alakan iyayyen ku modibbo duk da ba sanin dawwan mu gidan nan mukai mashi ba da farko .
Amma yanzu din da ya ganmu tare da mahaifinka zuwan mu kaduna shine karfin zuwan shi lokaci lokaci can ba a rasa ba yakan dan leko mu a gaisa.
Kada ku yarda dashi Umma don Almustapha ba mutumin kirki bane dan smogal din haramtattun kayan da gwaunati ta hana a shigo dasu cikin kasan nan ne.
Da sauri muka dago da wani irin kallon juna nan da umma lokaci guda yau ko ba komai munsan dalilin da yasa ake neman shi wanan can lokacin daya fake a gidan da muke haya.
Yanzun don mutum na smagal ya zama abin kyama ga kowa ke nan umma ta tambaya cikin mamaki tana kallon modibbo din dake bayani
Yace kwarai kuwa umma don yana cikin jerin mutanen da gwaunati ke hari sosai idan dubun shi ya cika zai rainawa kanshi ranan sosai saidai yana ganin shi mai wayau ne ba za a iya gane shi ba yake gani.
Don haka ku nisanci hurda dashi don ni sam ban yarda dashi ba ko kadan da zuwa nan din da yake maku don sam bansan yaddama ya gane wai kuna nan ba har ya biyoku ya fada yana min wani irin kallon tuhuma.
Banda alakan komai dashi banda na gaisu a tsakanin ga umma nan ka tambaye ta kaji asalima shida kanshi yayi warning din kan nuna na taba sanin shi a baya idan zaka tuna ranan dinner diyar gwaggo Asiya da mukaje tun wanan lokacin na rike wanan kalaman daya furta min gaisuwan ma sai da umma ta matsa min nake gaida shi idan mun hadu.
Yace kun gani ba idan ya yarda da kanshi ai ba ai ba zai fadi hakan ba gareki muna fukin kasa don suna yaudara saboda suyi kudi sufi kowa suke wanan harkan mai hatsari a garesu nina san mustapha don kusan tare muka taso a zurian mu dashi nasan halinsa sarai da kasada.
Ka yarda dashi don shi din ba wanda kuke zargi bane na tsunci kaina da fadi haka lokaci guda ina kallon yaya modibbo din da shima ni yake kallo da mamaki.
Yayi min wani irin kallo nace kwarai kuwa yaya babu ruwana dashi bayan gaisuwa tun baisan mu suwaye a gareshi ba kuma har yanzu din ma bai sani ba don nasan kan abinda yake zuwa gidan nan ke nan a yanzu ya binciko alakan mu da daddy ku kuma ko hakan bawai ya dameshi sai ya sani bane.
Yana dai zuwa nan ne kawai don nasu yazo daya da amar ya mustapha shi kanshi kuma ai baisan yaudaran shi sukeyi ba suna surka sana,arsu da miyagun abubuwa a cikin kayan su da sukai odan zasu shigo dashi kasan nan.
Don haka suke amfani dashi don ya iya harkan suka lababa shi