Showing 159001 words to 162000 words out of 382072 words

Chapter 54 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28351

nayi masa me mommy dako ya raina kanshi ranan wallahi yara kuma idan zasu rike sune su rike din nasan dai idan muna raye sai sun nemeni.
Shiru mommy tayi tana nazarin maganan su da fan nata shima dai hakan ne don mikewa yayi yana mata sallama ya fita ranshi a bace a nan waje ya samu sauran mutanen gidan a zaune inda ya barsu din Fa,iza tayi tagumi tana tunane.
Amirace tana ganin shi ta mike tsaye tana fadin kakaini wurun ta yaya sai yarinyar ta bashi tausayi ya dan kakaro murmushi yana fadin zan kaiki ai Amira yanzu akwai inda zani daga nan ne.
Sahiba din tana garin nan kenan yaya Fa,iza ta sake tambayan shi a karo na barkatai yaji tausayin yaran sosai saidai bai yarda ya nuna masu komai a fuskan shi ba sai murmush kawai da ya sake masu ya juya ya nufi motan shi ya shiga ya bar gidan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , , , , ,

4️⃣7️⃣ BY

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL GHAFUR, , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON GIRMAN ALLAH KI GUJI SHIGA HAKKON WANI KAN SON ZUCIYA KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA FITAR DA HAKKINA NA FADA MAKI, , , , , ,

Kwana biyu ina gida ina hutawa banje ko ina ba don dan wanan tafiyan da mukayi na kwana biyu bama gida kamar wace tayi wani tafiya mai nisa saboda rashin sabo da hakan.
Yau ma barcin Safe nakeyi nayi mafalki wai zan fita zuwa unguwa sai na fita wurin umma inda take a shagon ta zaine nasameta
Nayi sallama da umma a shagon ta na fito na nufi wurin motana ina kokarin bude motan na hango wata mota ta dumfaro gidan mu.
Sam ban damu da waye ba a motar har yakai na bude motan ina kokarin shiga naji an ambaci sunana daga bayana ana fadin Sahiba wai dama ke dai dince na gani a kaduna ?
Na juyo ina dago kai don ganin waye idanuwana suka sauka a kan yaya Abubakar dake tsaye yana kallona a cikin mamaki.
Saida na dan kadu lokacin kafin na jawo courage nasawa zuciyana lokaci guda ina dan sauke murmushin gefen fuska kafin nace dashi ina wuni yana amsawa na fada mota har na tayar yana tsaye yayi mutuwan kasko ga kallona na bar wurin duk yana tsaye ya zuba min ido ya karasa wurin umma din.
Wani iri nake ji ina jan motan wani tunane nayi na dauki waya da sauri na kira umma yare nayi mata ina fada mata cewa kada ta kuskura ta fadi wani abu game da rayuwan mu.
Daidai nan na falka daga barcin a hankali nakai ga bude idona ina bin dakin da kallo har nasan barci nakeyi nayi wanan mafalkin .
Zama nayi a bakin gado karshe don mafalkin ya tsaya min a raina tun falkawana daga barcin kafin in mike tsaye na fada ban daki na watsa ruwa na dan dade a ban dakin kafin in fito na shirya cikin wani dogon riga blue mai dan karamin hannu sai hula dana saka saman kaina don banda niyar fita a ranan duk da har yanzu bawai na daina zuwa shagon mu bane don ban bar wirin ba nakai matsayi mai girma a cikin shagon a yanzu.
Na samu umma na shirin fita wajen shagon ta don ina jin dadin yadda naga umma na son wanan sana,an nata sosai don yadda take kulawa dashi a kullun.
Kin tashi ke nan umma ta tambayeni nace eh tare da kara gaida ita ina zama nake fadin umma na fada maki cewa naga yaya Abubakar a kaduna.
Da sauri umma ta juyo tana kallona a cikin mamaki tare da fadin kin ganshi fa kikace na gyada mata kai a hankali kafin nakai hannu saman fuskana na shafo ina daga kafa na dora saman kujera ina fadin yanzun ma na gashi a cikin mafalkina nasan kuma zaizo gare mu bada dadewan nan ba.
Zaizo fa kikace dama baisan inda muke bane sai yanzu daya ganki a wirin taron ya tuno damu umma bana zaton hakan akwai dai abinda yafaru haka ya faru umma.
Don daga baya nayi tunanen sai na fahinci kamar shi kanshi an saka mai mantuwa a kan zancen mu kodai wani abu maka mancin hakan.
Umma ta dago kai ta kalleni don jin yadda na kirata din saida na dago kai sai nayi shiru kuma take tambaya mene ?
Nace barshi dai ba yanzu ba umma dama tambaya naso yi maki a kan daddy yanzu tambayan baida amfani don ba zaki fahuceni ba umma na fada.
Har lokacin umma kallona takeyi da mamaki saidai ganin banda niyar magana yasa taja tsuki tana fadin zaki fara kakaro shirmen ki ke nan kuma sahiba.
Umma dawa Abban mu ya fara shawaran filin shi da yayi sanadiyar barin shi duniya lokacin ?
Me kike tunane kike wanan tambayan kuma yanzu gaskiya nake hangowa dole da akwai hadin kai cikin abinda ya faru umma .
Bayan ansan da cewa su sukai kisan Abban mu kuma aka barsu suna harkokin su a cikin mutane a she ana haka a wanan kasan dama ?
Ke kada ki shiga aikin da banaki ba Sahiba har ki fara zargin wanda baida laifi a cikin zancen ni a yanzu nabarwa Allah sanin sa akan komai daya faru damu a rayuwa.
Umma ba zaki gane bane dama na fada maki tun farko ai bazaki fahinceni ba wani tsawa ta daga min har saidana dan kadu tana fadin kawai don kinyi mafalki da Abubakar sai kawai kiyi kokarin zargin wanda ya taimaki rayuwan mu a baya don nasan mahaifin shi kike kokarin jefawa zargi kuma yanzu.
Yi hakkuri umma ba zargin sa nakeyi ba kawai dai ina hasashen hakan ne garesu tunda zuciyana ya fara nasa zargin wani abu akan haka.
Ta dan tsura min ido na dan wani lokaci kafin naji ta mike ta fita daga falon zuwa kasa nasan shago zata bude a lokacin.
Ni kadai na wuni zaune a falon don suna kasa basu shigo ciki ba inda nake nima din dai tunane ya hanani fita inda suke.
Da yamma ma da suka shigo umma batayi wani sakewa dani ba a lokacin nasan duk zancen da mukayi da safe ne da ita yasa ta rashin sukuni.
Washegari na tashi da shirin zuwa shago don har yanzu ina lekawa don wanan tafiyan namune ban tafi ba kwana biyu.
Na fito a cikin shirina na dogon buje mai shara, shara green mai adon filawa fari sai farar riga mai dogon hannu da aninaiya har kasan shi dan half sunna hijab daga sama iya kafadana sai hular mata dana kafa irin na cow boy da ake yayinsa daga can saman kaina nafito.
Inda na samu umma a dakin ta nake fadin bayan na gaisheta umma zan tafi wurin aiki sai na dawo ke nan hope ba wani matsala na sake tambayanta ina kallon ta.
Ta dan dago tana min Allah tsare a dawo lafiya babu matsalan komai don sai yamma zamuyi abinci gashi har lokacin muna cin naman dana dawo daga jos dashi duk da mun dibama iyalin Abduhamid din.
Ina fitowa nan muka hade da matar Abdulhamid muniya muka gaisa take tambayana umma nace bata fito ba tukun zan tafi aiki na fada tayi min a dawo lafiya itama.
Gaskiya idan Allah ya tashi ikon shi ga bawan shi sai yabar yan Adam da mamaki don dai nikan naga amfanin adduan uwa da dogaro ga ubangiji a kaina a yanzu.
Don nida nake karamar ma,aikaciya yau gashi ubangiji yai min daukaka da shi kadai yasan sanadin hakan gareni ya daukakani ta inda ba,a taba zaton min ba a lokaci daya.
Sai gashi wai nice idan na shigo manyan mu nada a ma,aikatan yanzu suna kokarin gaidani a cikin girmamawa da kafa, kafa gareni don gujewa yin laifi saboda ina da matsayin da basu taba mafalkin kaiwa gareshi ba yarinya karama dani don yanzu ba inda nake aiki ba duk masana,antun Sha,aban dake kasan nan nasan abinda ke tafiya a cikin su a yanzu.
Duk da ba wani daukan kai nake dashi ba ko a baya yanzu ma hakan baisa ina masu daukan kaiba zan tsaya mu gaisa a cikin mutunci da mutu kafin na wuce.
Saidai har lokacin ban kai ga hada wani zumunci ba da kowa a wurin in ka debe Felix daba ma zama kasan yakeyi ba shi ya faye fita kasan waje lokaci lokaci sai Adnan da Abdulhamid da mukayi dan sabo dasu na zaman yau da kullun.
Iyakata in shigo mu gaisa dasu sama sama sai na wuce naje yin aikin daya kawoni wurin ban damu da kowa ba kamar yadda muka saba dai yi dasu a baya.
Kun san dan Adam da daukarwa kanshi zunubi kuma dole ne ai zargi ko tunanen hakan cewa wai kodai muna tare da Oga Sha,aban ne ?
Har yasa ya bani wanan girman haka a cikin lokaci guda don zargi kawai irin na dan Kansas da yake dorawa kanshi idan yaga wani ya samu cigaba dayafi nasa.
Duk da idan wasu sun kasa hakkuri sunje da tsegumin wurin manaja yakan fada masu gaskiya ba wani alaka a tsakanina dashi banda na aiki shima kanshi ya bincika hakan ya gane ba komai banda aiki dana sani kuma akeyi dani din shike nan.
Morning miss Sahiba aka fada nasan muryan waye don haka na juyo
ina amsa gaisuwan da fadin morning Adewale sai kuma na tsaya cak ina kallon wanda ke tsaye a bayan Adewale din cikin kaduwa da mamaki abinda yasa shi dan juyawa bayan shi shima yana kallon abinda nake mamaki din.
Mazane su uku a cikin kayan motsa jiki daga gani dai fitowan safe sukayi daga wurin motsa jiki suka nufo nan shago din.
Don ba kowa bane sai Ya Mustapha da muka dauki kusan shekara biyu da rabi bamu ganshi a idon mu ba don mun dauka ma gaba daya ya manta damune ashe wai baya kasan ne yayi tafiya a lokacin shima shine a gabana yanzu.
Ganin yadda yake kallona a cikin mamaki yasa na juya da sauri zan bar wurin muryan shi naji yana fadin dakata Sahiba na juyo ya fara takowa zuwa inda nake masu binshi a baya suna biye dashi lokacin mutum biyune a bayan shi.
Idan nace a zuciyana ina da abokin gaba gaskiya banda shi a raina hakama abokan aikina kuma saidai su a bangaren su na zama abin harin su a yanzu kuma don yan matan shagon yan kwalisa danazo na sama a wurin yanzu suke ganin nafisu ga komai sun dauki karar tsana da kyashi da hassada sun saka akaina har suna samin suna da yarinyar manya wai.
Don wai manyan nan duk nema na suke da harkan banza don sun ganni yarinyar mai kyau suke daukana a boye suna iskanci dani.
To ko a wanan lokacin ma dai Funke dasu Abeni na wajen suna gulma akan mustapha din da suka ganshi ya hadu sai gashi sunga ya tsayar dani ya nuna ya sanni dama a wani wuri sai kuma abin ya kara basu mamaki da haushi.
Ya tako yazo har gabana ya tsaya yana yimin kallon mamaki na nan dukar da kaina kasa kafin nace dashi ina kwana a cikin yaren hausa.
Ya amsa min tare da nunani yana fadin kece Sahiba ina mama da Ammar jin yadda yayi magana na amsa mashi da suna lafiya ya su gwaggo Hari da daddy ?
Lafiyan su kalau ya fada yana lumshe idanun shi kafin yace wai dama kece dai din na gani a kaduna tare da sha,aban muyideeen ?
Sam ban yarda ke din bace saidai mai kama dake a wurin don hakane ban yarda ke bace da zuciyana ke fada min ke din ce.
Excuse me na fada na fara tafiya na bar wurin yana tsaye ya bini da kallon mamaki kafin yace wa na tare dashi su tafi suka bar wajen .
Aiki na sama sosai don kwana biyun da nayi ban fito ba saidai haka nayi shi ina jin wani iri a raina ba dadi nasan haduwan mu da Al mustapha din ne ya jamin bacin rai din.
Don haka nake duk ranan dana hadu da wani daga cikin su zan yini ne raina na baci saboda mun tashi a rayuwan kadaici da badan Allah ya bamu uwa ta gariba Allah kadai yasan yadda rayuwan mu zai kasance a ciki.
Na taso daga a gajiye zuwa gida inda na dan tsaya lagos market nayi cefanen fresh vegetables da nama danya na koma gida dasu don zanyi girki dare ranan.
Tun dana doso naga mota a kofan gidan na dafe kaina don nasan mafalikina na jiya ke son zama gaskiya haka dai na daure na karasa na parker motan ina dauko kayan dana sayo ne suka fito daga cikin gidan.
Hankalina ya kwanta lokacin da naga Felix ya fito daga cikin gidan namu na dan sake murmushi yana fadin see you from where are you now ?
Na share ina fadin Amebo olofofo inda ka aikeni na fito na kara da fadin na dauka baka kasan nan ai har kun tafi ko ?
Yace ina oga na kasan nan ba zai koma ba sai munyi bukin zagayowan mutuwan mahaifin shi na shekara da yan dangin su suke yi a zuciyana nace wa iyazu billahi har dake kasan musulunci suna wanan dabi,an ashe ?
Yanzun ma naje can office din ku ban sameki ba shine nazo nan don na kira layin ki bai shiga sai lokacin ma na tuna da tun kashe wayan da nayi a daren jiya ban kunnata ba ashe.
Akan me kake nemana na tambaye shi yace aikine ya taso muna kan wanan shagalin da za ayi din don haka kinga muna da zama a gobe ke nan daku.
Fuskana bata kafin na wayence da fadin Allah ya kaimu goben na dan taka mai zuwa wurin motan shi ya tafi na juya na shiga cikin gidan namu.
Nazifa kan abubuwa nason su kwabe mata lokaci guda don in tabi ta mahaifin su shike nan ta rasa uban diyan ta tana ji tana gani don ya hana ta koma dakin ta.
Ga abinda kuma mijin nata ya fada cewa ai basuyi fada dashi ba balle ace sai yazo zata dawo asalima da zata zo din yai mata goma na arzki don kada su shigo su wahala a lokacin shi bai kasan tare dasu kuma.
Yanzu kuma abin ya koma mata ciki yadda mahaifin ta ya kafe kan wani dalili nasa da su suka kasa fahintar manufan shi akan haka.
Yau dai ta rufe ido ta samu mahaifiyar su da zancen komawa ta tace ita zata koma dakin tane tunda tasan halin Abubakar tunda ya fadi hakan bazai taba zuwa ba kome za,ayi ko bazai zo ba tunda ya fadi ta fadi hakan.
Kina ganin cewa komawan naki baizo ba shine mafita kinfa san halin mahaifin ku Nazifa haka zai iya jawo muna matsala dani dake a wurin shi.
Mama idan na zauna kuma shima matsalan aurena zai samu don haka gara ki bari in koma kawai tunda dama ra,ayinane nazo nan na zauna a gida bayan ya kara gyara min gida kafin inzo.
Yanzu ai kinga illan hakan don auren ki ya mutu ba komai bane ga Alh shi don bai daukeshi wani abin kunya ba haka.
Ta kasa ba mahaifiyarta amsa sai hawayen da take sakewa kawai a lokacin don yadda take jin kanta kiris ya rage takai ga aikata abinda take ganin zai dace da ita a lokacin.
Itama mahaifiyar nata a cikin wani hali take a lokacin don tasan mutuwan auren yar nata ba karamin hasara zai jawowa rayuwan au ba idan auren ta ya mutu a yanzu ta wanan dalilin.
Don duk ilahirin diyan gida dake aure babu wace tayi dacen gidan miji irin yar nata shi kanshi majaifin nasu yasan da hakan bakin haline kawai dai irin nasa ya taso.
Aikuwa da yamma mahaifiyar nata ta samu mijin nata a falon shi yana waya yana kumfan baki yana mazurai da idanu sai billahillazi bai isa ba shi waye har yaushe yazo kasuwa shi da zai kawo zancen sauke farashi.
Wuri ta samu ta zauna a gefen shi har ya gama wayan yana huci tayi shiru bata tanka mashi ha har lokacin daya kare hucin nasa tace dashi sai hakkuri mutane.
Yace aisun sanni sun san halina sun san kuma koni waye da abinda zan iya yiwa mutum idan yace zai ketare abindana sharadawa mutum.
Jikin tane yai sanyi don jin abinda ya fada a lokacin don ba zata iya fito da zancen daya kawota wurin shiba na yarsu a lokacin.
Jin tayi shiru yasa shi kallota yana fadin shi wanan karamin dan iskan baizo ba har yanzu ke nan ta gyara zama tana fadin wallahi baizo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login