Showing 333001 words to 336000 words out of 382072 words
yanzu saidai ganin shi da mutane sukayi yasa yan wa yanda muke hurda dasu suka san da zancen dawowan mu kasan.
Daga ciki ko har da abokan aikin mu na ma,aikatan mu dama wasu makwabtan gidan mu har suke muna sanu dazuwa a lokaci.
Tun bayan dawowan mu kasan wayana yana kashe ban kunna ba son banda aiki sai faman barcin gajiya da nakeyi lokacin.
Da farko na dauka ai wanan matsalan nawane dana dade banyi ba saida wata makwaciyar mu ta shigone take fadin ai haka akeyi don sai lokacim da mutum ya dawo gidane yake sauke gajiyan daya kwaso a can dama.
Ta wagan ma,aikatan mune sukazo don gaida mu da zuwa wanda a gaskiya badon ni suka zo ba sai don Abdul da yake ma,aikacin su a yanzu shi.
Amma saboda mutunci sai wasu suka zamo suka shigo namu part din daga ciki kuwa harda Adanan da Felix sune suka shigo part din mu don mu gaisa.
Umma ta shiga ta tayar dani jin sune yasa na fito daga dakin saye da wani fashion hijab dashi da babu dayane don kamar riga yake ya matseni ko ina amma a hakan wai mace ta rufe jikinta ke nan dashi a yadda sukayishi.
Tunda na fito Felix ya fara min ba,a da Amarya so na your eyes be dis ? See how you look fresh you, na de enjoy wooo ?
Daidai ina zama nake fadin who be amarya ? i beg de go joo, carry dis your amebo talk and go.
Gaskiya kin kara wani fresh dake fa wai da gaskiyane zancen auren ki gashi kin jefa min ogana cikin tashin hankalin tun da yaji cewa wai kinyi aure bai kara daga wayan kowan mu ba kuma a nan.
Na, so you hausa people de do your marrige no any cerlarbration or gathering ?
Why you too de talk about that da nayi aure zaka ganni gidan mu zaune a yanzu saboda wanan matsalan muharamin na kasan saudiyane fa na fada masu hakan don kawai ya bar zancen.
Ya dan bata rai tare da fadin haka mukaji ku musulmai kuna da ka,idoji masu yawa dama don a kawar da zancen nake tambayan su yaya office din su suke fadin office yana nan saidai yan canje canjen da aka samu a yanzu kawai.
Nan nakejin wai yanzu Adnan da Abdul din gidan mune a matsayin aikina su biyu saidai abubuwa da dan dama sun faru bayan barikink wurin felix ke fadi har oga saida ya shigo kan matsalan barin mu da kikayi haka kuma da yan matsalolin da aka samu.
Saidai yazo ya samu kunyi tafiya gaskiya baiji dadin hakan ba ashe ke matsala kuka samu da Alaja haka baki fada muna ba ?
Alaja mace ce mai yawan son kanta sama ga kowa ko mu hakkuri muke da al,amarin ta har muka kai wanan lokacin a tare dasu felix din ke fadin hakan.
Mikewa nayi zuwa daki ba tare dana bashi amsa ba na dauko masu tsaraban daya dace dasu irin na maza saidai da dan banbanci don na Adnan shida yake musulmi na dan banbanta masu.
Har kofa na rakosu sai wanan lokacin na fito daga gidan tun bayan dawowan mu daga kasan dana shiga gida.
Don hakan sai naji kawai gara na dan tsaya na sha iska a wajen kafin na juya zuwa ciki ban koma daki ba na tsaya na gyara gida don ganin yadda gidan ya dan hargitse min a idona.
Bayan na gamane na shiga wanka na fito ina shafa mai wayana dana kunna da safe yana caji a power van.
Na mika hannu na dauko wayan sai na samu miscall har hudu a wayan daga Faiza sai kuma shi mukhatar din da yai min kira uku ina falo banji ba yanzu kuma a kan meya kirani din na tambaya.
Faiza na fara kira don jin kiran da tayi min din dukda nasan dan sabon kwana biyun da mukayi ne a zaman mu kasan saudiya ya motso mata.
Aikuwa ina daukan wayan abinda nayi zato shidin ne haka kuma abinda nafi tsana shine ta fara fada min kalman amarya amarya!!!
Idona na dan runtse a hankali tare da fadin Abi waireni ? Ko kin haukacene wai ? Sai naji ta kwashe da dariya tana fadin keko boyar Allah kinbi waya haka kin kashe ko samun ki ba ayi ?
Ga maigidanki nason jin muryanki tare da sanin halinda jikin ki yake ciki ba a samun ki ba,a samun umma sai Abdul makwabcin ku shi kuma yace yazo garin su .
Eh ya dawo jiya tare da mahaifiyarshi da bata da lafiya ayyah Allah ya bata lafiya ta fada na amsa da amin kafin tace ke gulma kecina tun jiya fa.
Akan me fa na tambayeta saida taja kafin tace akan kishiyan ki fa Sahiba jiya sister ta kirani tana fada min cewa sunyi fitina sosai da mijin ki har yakaisu da batun saki saidai Allah ya gyara ba ai sakin ba .
Don hakane ita kuma tace tunda a kanki komai da bai taba faruwa haka ba tsakanin su ya faru yanzu sabodake ba zaki taba tarewa a gidan shi ba da sunan aure.
Faiza na katseta ina fadin ki daina irin wanan maganan ina ruwana da matalan shi da matarshi matsalan sune can tsakanin su bai shafeni ba.
Ya shafeki sahiba waiko kinsan me ake nufi da kishiya mu sanma ma irin taki din nan da ta tsare ciki ta tsare waje a gidan mijin ku yanzu.
Koma meye matsalan ta ni bai shafeni ba na bata amsa ta tareni da fadin keko ya shafa a yanzu sahiba don kece zaku zauna a karkashin innuwa daya da ita abinda bata taba zato ba a rayuwan ta .
Sam bai fada mata zancen auren shi dake ba sahiba idan ya fadi abune daba zai yuyu ba akace dole kuma tasa hakan don hjyshi ta hana ya fada ma kowa a lokacin tunda itama iskancin matar ya isheta zuwa yanzu.
Enough faiza enough please kin dameni da zancen wa yan nan mutanen kwata, kwata basu a raina balle zancen su ya dameni suje can suyi duk abinda zasuyi wanan ba matsalana bace hakan.
All what i know shine idan har ta shiga gonata sam ba zataji dadin hakan ba final amma ni zancen su a yanzu ba matsalan daya shafeni da hakan understand ?
Sahiba nasan da hakan amma kiyi tunane kema ki gane saboda wa take wanan haukan hakan a yanzu duk saboda kece fa ? don kawai kin auri mijinta,
Shi nake son ki gane don Allah ki sa umma ta nema maki tsari a jikin ki please kafin tarewan ki tunda babu isasshen lokaci a yanzu.
Katseta nayi da fadin Sahiba ni in nemi tsari bayan wanda Allah ya hore min a jikina ga kuma adduan dana sani a bakina ?
Idan wanan kike jima faiza kada kiji komai a zuciyan ki ni ina tare da tsarin ubangijina komai ba zata taba yiwa yar uwarki a duniyan nan ki sani.
Don zuwa yanzu na gama fahintar me faiza take ji ga hakan da taji a game dani gashi nikuma sam banji komai a zuciyata ba game da wanan labarin da take fada min din a cikin tashin hankali.
Don da gani yadda take maganan hankalinta a tashe yake sosai da abinda taji amma ni sai banji wani abin tashin hankali ba a lokacin.
Haka dai muka gama wayan da ita don sam bata fahinceni ba ita damuwanta shine muyi wani abu a cikin yarbawan mu da muke zaune dasu tunda ance suna da asiri muma kada wanan matar ta samu galaban illanta min rayuwana take nufi.
Har muka gama wayan da ita na kashe ina mamakin maganganun faiza din sai nasawa nake a raina watau yanzu dai a kasan hausa idan zakayi aure dakai da mahaifiyar ka ko yan uwa baku da shakat a zuciya saboda irin wanan dalilin musanman ma idan mai mata zaka aure sai irin zantukan nan ya biyo baya a karshe.
Ni yanzu ba shine damuwa na ba a yanzu abindake zuciyana yakuma tsaya min shine makomar mahaifiyata da inda zan bar dan uwana shine abin damuwa a gareni yanzu.
Don sam ba zan iya ketare kasa ba da sunan bin wani in bar mahaifiyata da bata cikin kosasshen lafiya hakama kanina Amar ince nabi wani namiji a yanzu.
Wanan dalili yana cikin abinda ya hanani kula wani namiji a bangarena bansan na boye ba don sam nikan bana kallon namiji da sunan aure a rayuwata.
Hakama yasa da oga sha,aban ya fito min da zancen naga ya zubemin a idona irin yadda na daukeshi kamar dan uwa a zuciyata.
Idan kana son mu zauna lafiya dakai kada ka gwada min wani tsagan soyayya a fili don yanzu ne zamu bata dakai.
Ban kaiga idda tunanena ba kiran mukhutar din ya shigo layina lokaci guda wayan ya dauki kara ina kallon wayan na kasa dauka don haushin da nake ji a raina.
Saida ya kusa tsunkewa na daga ina sallama naji wani irin ajiyan zuciyan daya sake yana fadin Alhamdullahi Sahiba i hope lafiya kuke haka da ba a daga wayan ki bayan sallama ya fadi hakan da yaji na amsa mai.
Lafiya muke bana kusa da wayane ina falo ina aiki nabar wayan a falo na basa amsa da hakan ya kara sauke dan guntun ajiyan zuciya kafin yace.
Aiki kuma ke da kanki da baki da lafiya a jikin ki aiki yanzu ba naki bane hutu ya kamata dake a yanzu kiyi barci ki huta gajiyan dawafi da zaman jirgi jinin jikinki ya dawo fresh a yanzu.
Idan na kwanta sai umma tayi aikin ke nan da kanta da sauri naji yace no no no ba haka nake nufi ba amaryata ai yanzu nafi son hutun mama sama da taki sosai.
Idan akwai abinda na tsana shine ya kira min kalman amaryata da yanzu yake yawan fada min daga bakin shi.
Amarya for where idan nayi aure a yanzu na dauka kaine mutum na fatko da zakai min fada don barin uwata da dan uwana da basu cikin koshin lafiya nace nabi wani da sunan aure.
Jin zancen yayi wani bambarakwai a kunnuwan shi kafin naji ya murmusa yana fadin a ina zaki bar mama din dama kina zaton zamu barsu a logos ne mu mutafi wani kasan daban ?
Idan nayi hakan naci amanan zaman amanan da nayi da ogana da ace tun lokacin mutuwan shi nasan abinda ke faruwa daku wallahi Allah da ba zaku taba zaman kuncin rayuwa ko kwatankwamcin wanan da kukayi ba a rayuwan ku.
Sahiba kin san zama na amana da mahaifin ki yayi dani a rayuwata kuwa banjin zan iya kara barin ku a wanan halin baku dawo kusa dani ba sai idan nayi hakan sanan hankalina zai dan fara kwanciya bisa ga irin abinda nake ji.
Na rike wa yanda basu san ya akayi na samu dukiyana ba har kowa nasu balle ku da kune silar komai nawa a yanzu.
Da ace kinsan yadda nakejin zafin Ali dcp a rayuwata da ko wanan zancen baki dauko ba a yanzu don komai daya faru daku shine silan hakan a gareku don shi ya boye min gaskiyan zancen ya rufeni.
Enough that Ali dcp da kake kira he is my reletive shine uba a gareni shine dan uwan da yai silan komai nasani amma wanan sharia ne tsakanin shi da wanda suka zalunta.
Bana son in rasa kowa a yanzu cikin su kamar yadda na rasa nawa mahaifin a baya shiyasa na roki Allah ya cire min duk wani zafi da takaicin su da nakeji na barsu da Allah zaifi.
Ba zanso suma iyalinsu suji irin zafin da mukeji ba a zukatan mu don Allah baiyi zukata iri daya ba idan mu mun iya daukan wanan halin wani ba zai iya ba shi a zuciyan shi.
Sai zumuncin yaci gaba da lalacewa har abada ba za a samu zaman lafiya a tsakanin mu dasu ba a rayuwa wanda ba zamuso mu zama silan hakan ba don bamu san me gobe zai haifa a garemu.
Don haka bari ga Allah shine mafita suje idan don dukiyane da komai mukan mun yafe masu mun barsu da Allah final.
Masha Allah ya ambata a cikin wani tsiga na ajiyan zuciya tare da fadin naji dadin jin wanan kalamin daga bakin ki a yanzu barin shine mafita .
Ba zaku karbi komai nasu ba ninan na isheku na mayar maku da duk abinda zasu ba ku a rana daya don haka kwarai maganan nan naki abin dubawane sosai Sahiba na fahinci me hakan ke nufi a cikin zancen ki yanzu.
Mun dauki lokaci kan dashi muna magana ta fahinta a wanan ranan kuma ya goya min baya ga hakan akan duk abinda na fada inda ya nuna min amincewan shi .
Da zaiyi magana a sassauta sharian don kawai diyan su da matan su amma kafin hakan zaije da kanshi ya zauna dasu su san cewa nice na yarda da hakan a garesu.
Don haka duk wanda keda wani abu a zuciyan shi a game damu ya fitar a zauna lafiya zaifi sauki ga mutum ba don tsoro kuma akai hakan ba.
Nagode idan kayi muna hakan ka gyara komai tabbas sahiba ke yar halak ce na yarda don zuciyan ki daya da mahaifin ki.
Da ace sun san da abinda yazo masu lokacin da suka kashe shi da basuyi hakan ba a lokacin don yazo masu da tarin alheri a rayuwa inda zai kafa kowan su ta yadda zurian su zata karfi a cikin duniya.
Saidai kadara ta riga fata kwana sun kare a lokacin sune sanadin barin shi duniya a lokacin babu wani mahalukin da ya isa hana kaddara a kan bawa .
Zan barki ki huta zan kara tunane mai zurfi akan komai na kuma gode da lokacin da kika bani a yau din nan har na kara fahintar yadda rayuwan ki yake a fili.
Sai yanzu zance ya taja jin sautin murmushina a fili tsakanina dashi don abinda ya fada din nace kada kace hakan a kaina yanzu don baka san wacece sahiba ta gaskiya idan an tabani na sani.
Shima din murmushi ya sauke tare da fadin hakane amma idan mun zauna a tare zan karasa sanin komai ina alfari da kasancewan ki daya daga cikin a halina koba komai nasan zan samawa gidana mace tagari wace tasan ya kamata ga kowa sai anjima ya kashe wayan kafin na furtawani kalman a garshi sai nabi wayan da kallo ina sauke ajiyan zuciya lokaci guda.
Muryan umma ce ke tambaya dawa nake waya tsawon hakane ta shigo tun dazun ta samu ina waya haka Abubakar ne ?
Bashi bane umma na bata amsa da mukhatar muke waya yanzu na fada mashi ya janye zancen kwace gidajensu da yai niyar yi kuma a bar wanan sharian a zauna lafiya.
Sai gani nayi umma ta zauna tana fadin kinyi daidai yar albarka kamar kinsan da wanan zancen nake kwana a zuciyana nake kuma tashi dashi.
Yadda su kudidi suka fada min halinda iyalansu suke ciki a yanzu don har yakai wanan yar da akai auren hadi da dan wurin gyade sun samu rabuwa a tsakanin su duk a kan wanan fitinan .
Wai baby kike nufi umma itafa bamu bari yan uwan nata sunji bane a can don kada su tayar da hankalinsu kan zancen
Shi kanshi Abubakar yanzu idan kin kula yana dari dari damu tun bayan da zancen mahaifin shi ya fito kowa yasan da hakan sam yanzu ya rage irin yadda yakeyi damu a da can.
Idona na lumshe don nina dade da sanin hakan kuma nasan abinda yakeyiwa ke nan ashe itama umma ta gano hakan da yakeyi din.
Ban tsaya mata dogon bayani ba don hakan kawai zamuyi mu zauna lafiya da yan uwan mahaifin mu har karshen rayuwan mu.
Karba ko daurewa jan wani sabon fitinane a tsakanin mu dasu tunda Allah ya hore muna abin da zamu tallafawa rayuwan mu a duniya don yanzu ko shagon da umma ke zama cikin sa kawai zai shemu muci musha har mu ba wani.
Kwana biyu tsakani na samu kira daga kaduna kan abinda ya faru inda yanzu aka gyara zancen kan cewa wai ai an gano gaskiya ba laifin su bane.
Amma kowa a cikin dangi yasani cewa su din daine sukayi kisan kuma suka wawashe mashi arzikin shi suka wofintar da iyalanshi da komai nasa daya bari.
A can wurin mukhatar kuma yana samun kalubali sosai gurin matarshi data kafe kan cewa ita sam bata yarda da wanan auren daya sakeyi ba a yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
1️⃣0️⃣2️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,