Showing 246001 words to 249000 words out of 382072 words

Chapter 83 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28442

min abinci din.
Na jaye ta shiga daga ciki ta ajemin nayi mata godiya ta fita abincin nabi da kallo abu daya ne daga cikin abincin ya dauki hankalina watau fruits salad din dake nade a cikin wani bowl mekyau dashi.
Fasa kwaciya nayi na zauna na bude na fara sha da bissimillah a bakina sosai naji dadin abin don yasha hadi na kayan lanbu sai lokaci nake karewa dakin kallo da ada ban damu da ko a ina nake ba.
Idona na lumshe ina mai hamdala ga ubangiji daya nufeni da ganin irin rayuwan da ko wace mahaluki ke fatan ganin kanshi a ciki.
Sosai na sake na kwashi harka a dakin don na manta rabona da tsayawa naci wani abu irin haka don na wancan kasan da muka baro tafarnuwa da wasu sanadaran girkin kasan ya hana in tsaya inci wani abin kirki.
Saida na dade zaune kafin i mike na nemi wuri na kwanta ina sake ajiyan zuciya wayana na lalubo ina duban sako kamar da wasa na kunna datana sai naga sakkon ni na shigo min a lokacin.
Mamakine ya kamani yasa na danna kiran layin umma da damuwa da rashinta a kusa dani ya addabi zuciyana a yan kwanan kin nan da mukayi ba tare dasu ba.
Saidai sam wayan nasu bai shigaba yasa na fara duban sakon nina saiga sakon ya Abubakar mm a gani a wayana yana fada min sunzo basu samemu a gida ba ya lissafo min sunayen wa yanda sukazo tare din nan lagos wurin mu.
Amsan dana bashi shine ayyah Allah sarki see u next shi kawai na rubuta mashi a lokacin karshema wayan na kashe na fada tunane.
Barcine ya daukeni a hakan yasa na manta da komai dake gabana don dama kuma barcin dai nake ji gaskiya don a takure nake sosai a lokacin.
Bude wayan yayi bayan ya kammala komai yana duba sakon nam shi dake shigo kamar a sama saiga amsan dana bayar ya baiyana mai ya soma karantawa.
Baiyi mamakin hakan ba don abinda yafi wanan ma din zan iya rubuta mai a lokaci idon shi ya mayar ya lumshe a hankali yana tunanen yadda abubuwa zasu kashe a karshe.
Naziface ta shigo dakin motsinta da taji yasa ya mayar da idanun nasa ya rufe a hankali yana ci gaba da nazarin abinda ke cikin zuciyar shi.
Saida ta zauna a gefen shi ta hau gado da kyau take fadin yanzu shike nan haka Abban mu zai zauna a tsare sai ranan da yar iskan yarinyar nan data tsaresu ta dawo daga balaguron ta ?
Wacece yar iskan ya juyo yana tambayanta a cikin mamaki tare da tsareta da idanun shi mai alaman mamakin abinda ta fada karara a lokacin.
Ehmana idan ba yar iska take ba gantalala har Abbane zata sa a kama don kawai su nuwa mutane su yan barikine basu san daraja da girman babba ba.
Shi kuma babban daya tabawa yara kayan sufa shi kuma meye ko wanda bai taba an kamashi duk idon shi na a kanta yana mata wani kallo na tsana.
Kafin ya kawar da kai yana fadin koda yake banga laifin ki ba don kin fadi haka yanzu don ke yarinyace baki san komai ba a zancen.
Wai shigar mata ke nan zakayi ko me ko dai ka shigan mata ai bata kaini a gurin ka ba kome ko Abba yayi ma da kake jin zafin shi yanzu.
Dama nasan ba wai ka damu da wanan abin bane tunda kowa yasan kaika nemisu ka kawo su garin nan har take ganin kamar ita din watace can.
Au ashe kin sani ai ban san abinda kuke fada ba ke nan nako godewa Allah da yasa nine silan dawowan su cikin yan uwan su a yanzu .
Ashe ku haka a wurin ku laifine ban sani ba to kije gun wanda ya fada maki nace ya dauki matakin hakan a kaina idan zai iya.
Tsuki taja tana juyawa baya taci gaba da fadin saukin abindai wallahi Abba yafi karfin hakan duk ko me zatayi ya riga da yasha gaban ta ko wallahi ai tazo zata hadu damu kowa na jiran isowan ta ai.
Za ko tazo din kuma zaku ganta sai muga wanda zai taba ta idan kun shirya mata don ma ki sani karewa a gidan ku zata zauna tunda nan ne tushen ta na asali.
Wanan kuma fadane kawai kayi a yanzu amma ko ubanta yayi kadan yace zai zauna muna gida balle ita don haka inma haka aka shirya gara tun wuri a bari tunda ba gidan ubanta bane.
Au ke na ubanki ne ya fada a hasale lokacin da baisan hakan zai fito daga bakin shi ba duk da hakan bai daina zancen ba yaci gaba da fadin ki koma ki tambaya wanan gidan na waye tun farko ?
Yana fadin hakan yaja tsuki ya juya baya tare da lumshe idanun shi kamar yadda ta sameahi dakin da farko shiru tayi na dan lokaci kafin ta mike fuu ta fice dakin tana fadin mutum kullun kazo mashi da zancen arziki sai ya nemi ya bata ma rai shi.
Washegari ya shirya bai tsaya karyawa ba don yasa tea sai bread zai samu kawai yasashi fita zuwa gidan daddy da safe don ya karya a can duk da yasan da wuya mommy ta bashi abincin don gudun zuciyar matar shi da takeyi.
Babu kowa a falon sai faiza dake karyawa a gurguje kada ta makara zuwa makaranta a lokacin.
Gaidashi ta fara yi a gurguje kafin tace mommy na ciki barin kira maka ita yace no barshi hada min abin breakfast in karya sauri nakeyi yanzu nima zan tafi abujane.
Da sauri ta juyo tana kallon shi Abuja yaya yace eh yi sauri ki ban ta nufi kitchen din part din su da sauri tana aje mai ita kan ta fita tana mashi Allah ya kiyayye hanya.
Saida ya kusa gama cin abincin mommy dake jin motsi a falon ta dauka faiza ce bata fita ba har lokacin ta fito.
Ja tayi wuri daya ta tsaya tana kallon dan nata da ya bata tausayi lokaci guda mutum magidanci ace bai samun kulawa yadda ya dace haka ga iyalin shi waima mai aikin meye ranan ta a gidan ne ita ?
Kai kuma ya haka ta fada a fili wai wama ya baka abuncine gidan nan yanzu kai tsaye yana daukan kofin ruwa yace faizace kuma ta fita.
Zaune ta karasa kaiwa tana fadin kai yaran nan basa ji saida fa na gargadesu da hakan su daina baka abinci bana son fitinan matarka wallahi don bata da kunya.
Mommy don Nazifa kikace su daina bani abinci ai kasan halinta dai wuri rashin kunya ta fada tare da daure fuska lokaci daya.
Ni zanje Abujane yanzu ya fada ko daddy ya tashi yanzu da wuya idan sun tashi tunda yara ba makaranta suke zuwa ba saidai ka duba in ya fito.
No indai ya tashi ki fada mai nazo bai tashi ba zance kan case din uncle Nuhu mu gani idan zasu ban belin shi.
Allah yasa su baka wanan abu dai baiyi dadi ba wallahi yanzu ita sahiban tasa dai aka rufeshi ke nan .
Mommy ko itace ai bata da yadda zatayi tunda baida niyar biyan su kudin da company ke bin shi kinga ai yanzu yasan da gaske sukeyi tunda shi komai yace aikin suhiri zaiwa mutum.
Sahiba ko ba ai mata wanan idan ya sani munyi magana da ita da safen nan tace ya fadi lokacin da zai bada kudin sai a bada belim shi shine zan tafi in ganshi yau din ko hankali zai kwanta.
Ni dai bana son kana saka kanka cikin wanan zancen gaskiya da zakaji ta tawa kabarsu can su karata a tsakanin su zaifi.
Bani kadai zan tafi ba tare dasu uncle hamza ne zamu tafi so ni zuwa kawai zanyi inga manya a can final.
Alh yasan da zuwan ku daddy bai sani ba ina ji amma ai yasan da zancen neman bellin don shima ya gwada ba a bashi ba.
Wayan shi ya dau kara ya dauka yana fadin gashi tafe yana tare da mommy ne daga haka ya kashe wayan yana mata sallama ya fita tana mashi addua.
A ranan kan basu dawo gida ba saida Alh nuhu din wanda ya fada sosai da dare suka shigo kaduna suka wuce dashi gidan shi kai tsaye nan iyali suka shiga murna kowa da abinda yake fada.
Bayan sun sauke shi gida ya nufa ya samu basuyi barci ba yaran ne da suka ganshi suka tare shi a cikin murna itako tana zaune a hakince tunda ta juyo ta kalle shi sau daya yana shigowa bata kara juyowa gareshi ba.
Dakin shi ya shiga ya watsa ruwa kafin ya fito yana tambayan abincin shi sai lokacin tayi magana tana fadin nasan ina kaje tunda safe ni banyi abincin dare ba yau naka na rana mukaci.
Kallonta yayi kafin ya juya ya koma zuwa dakin shi cikin takaici shirin kwanciya yayi kafin kira waya ya shigo mashi sun dade suna waya da wanda ya kirashi daga Abujan kafin suyi sallama yana kashe wayan a lokacin.
Iska ya furzo daga bakin shi tare da shafo kanshi yana gyara kwanciyar shi don abinda sukai magana a kai din yanzu.
Bai saba mata haka ba yanzu ma din daya share ta yana jin bai kyauta ba hakan yasa ya mike zuwa dakin da mahaifiyar nasa ta sauka.
Yako samu Alajan ta hau dashi iyakar hau don yana shiga tunda taga shine taci gaba da wayan ta da ya sama tanayi a lokacin.
Daga tsayen kaiwa yayi zaune saman gadon yana kishingidewa tare da zaro wayan shi daga aljihun shi yana latsawa.
Har ta gaji ta kashe wayan taci gaba da tsabgogin gabanta lokaci guda ya fara gaida ita bata juyo ba balle ta kalleshi.
Ummi wani abu ya farune ya tambaye ta a lokacin ta dago tana fadin sha,aban ban san me kake nufi dani ba a yanzu watau ban isa in ma magana ba kaji.
Magana ummi wace magana ke nan ya tambaya cikin mamaki kamar bai san abinda take nufi ba a lokacin.
Kada ka maidani mahaukaciya mana shaaban kana nufin gayatan yarinyar nan da iyayyen ta da nayi haka zasu zo ka nuna masu ban isa da kai ba ?
Har a gabana kake rike hannun yarinyar nan kana laluba wai ka nuna min ban isa da kai ba kome da har gaban kowa ka nuna min kai ga zabin ka.
Haba ummi kiyi min adalci wan can karon nayi maku biyayya ga abinda kuke so ya kamata wanan karin kuma ku bani dama nima in gwada sa,ata mana na fada maki bana son wanan hadin da kuke son yi yanzu .
Ya kamata this time ki bani chans nima in nemo abinda zuciyana ke so da sauri ta kallo shi tana fadin badai wanan zabin naka ba mara amfani a garemu .
Ko don jujun ta kake sonta ne sai ko kuwa don kyau da take dashi bayan nan fa ka fada man wani abu da yarinyar nan zata gwada wa wace na zabo ma yanzu.
Kai ya girgiza yana fadin ko daya ummi saboda halinta na gaskiya da sanin ya kamatane kawai nake son ta.
Gaskiyan ta na banza da wofi dama don ta kamaka haka yasa ta nuna maka ita mai gaskiyace ai .
Dama nasan abinda zai faru a karshe ke nan tai maka jujun da zaka mutu da sonta umiportant love zakayi don abinka take so ba kai ba.
Lalala haram Alaja ita ba yadda kike zato take ba asalima ni din ke son ta ba itace ke sona ba don haka ita na yanke a zuciyana zan aura final.
Yana fadin haka ya mike daga inda yake zaune ya gyara kayan shi da sukai dan squzing yana kokarin fita daga dakin ta kira sunan shi ya tsaya cak ba tare da juyowa ba.
Tace udan tace hakane zan nuna mata ita bata isa ba ko juju din gaba da gabanta wani jujun yafi karfin nata.


ZAINAB IDRIS MAKAWA




ANA DARA GA , , , , , , , ,

7️⃣3️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,ID, , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Wurin taron ya cika makil da yan kasan dama baki irin mu itako Aishat ganiya sai murna da farin ciki takeyi da zuwan yan uwa duk wanda ya taka a dalilin ta zata har kasa tasa gwiwa bibiyu tayima sanu da zywa irin na al,adan yarbawa don girmamawa.
Wanan abin da naganine yasani sake yan kwala watau dai gata wani abune nace a raina wata kila yanzu da ace mahaifin mu yana raye muma zamu iya samun wanan gatan da Ganiyat ta samu.
Ranan da na kare karatuna ko kaza bata biyoni ba balle dan mutum ni daya kwallin naje na dawo duk ko da nuna min kauna da wasu abokan karatuna keyi a lokacin gaskiya naga dabam a wurin saboda rashin kowa a tare dani.
Ganiyat zata iya girme min da shekara biyu ko ukku gaskiya amma shirun ta ita yai yawa sosai da kuma ba mutum girma.
Tunda muka gaisa da farko haba haba da ita mahaifiyar su da bakinta sukaja ta bata kara tako inda muke ba saidai tana daga muna hannu idan ta biyo ta wurun mu.
Yemisi da muke zaune a tare kusa da juna naji tayi tsuki tare da fadin Olon magge yasa na juyo ina kallon ta naji tace what a stupid tin be dat as dis gurl come here ke bakiga yadda ta mutatuntamu ba da farko amma ina kallo Alaja ta fada mata wani abu game damu nasan ko a kanki ne tayi magana.
Kaina kum na tambaya a cikin mamaki yes bake ke dating din danta ba dawa zatayi kuwa a daidai lokacin ya juyo yake fadin kinga waccan da suka shigo yanzu itace Alaja ke fada dake a kanta.
A hankali na dago kaina zuwa duban inda su Alaja suke zaune wata matashiya nagani a tsaye suna gaisawa dasu kallo daya nayi mata na kawar da kaina gefe daya.
Kamar sun san da hakan sai ga Aishat ganiyat, ta riko hannun ta a cikin murna zuwa inda muke zaune tana fadin brother meet mansurat .
Ya dan dago kamar da mamaki a fuskan shi ya furta who is she a take naga tsarguwan kalamin shi a fuskanta kafin ganiyat tashiga mashi dan bayani da cewa ai ita din diyar kawar ummice dake Manchester.
Oh sorry by the meet my Pierce Sahibat from Nigeria ya fada kai tsaye a wurin ba tare da jin komai ba ya dan gyaro wuyan rigan shi kafin ya daga hannu yana duban lokaci a agogon hannun nasa.
Dan dukowa yayi kamar yana min rada yake fadin ki mike tsab mu bar wurin nan yanzu yau din nan zamu wuce zuwa Dubai da dare.
Kaina gyada ina kakaro murmushin dole a fuska saidai daya san kiris nake a lokacin inyi cikin shi da masifa akan bata min suna da lokana danaga yana kokarin yi yanzu kaina don kawai wani plan nasa zaita nunani a matsayin piance din shi ceni.
Wanda ni kadai nasan wanan karyane shirine tsakanin nida shi kawai amma kuma shirin nason ya suce wuri a yanzu na fada don kula da yadda yake son batawa mahaifiyan shi rai a bainan jama, a.
Haka yasa na dan kallo Aishat Ganiya tare da bakuwan a cikin fara,a ina fadin kai sannu da zuwa fa kun biyo hanya mai nisa duk saboda Aishat Ganiya sannun ku da kokari Allah ya bar zumunci.
Sai lokacin na danga murmushi a fuskokin su naci gaba da fadin ga dan uwan naku nan ina mikewa zamu taka zuwa wancan wurin mu mike kafan mu na dago tare da hannun yemisi da yanzu don dole muke shirin dole da ita sama sama.
Wayan ta yai kara a daidai lokacin da take shirin tashi zuwa dakin ta har lokacin tana cike da mijin nata da jin haushin shi sosai kan zantukan daya fada mata daren jiya ta manta da cewa itace ta kawo mai zancen har ya bata amsan daya dace da abinda ta fada sai kuma ta dau zafi dashi.
Number mahaifiyar ta tagani take mamaki tana dauka take fadin lafiya mama babu ko sallama mahaifiyat nata tace mijin ki ya fada maki sun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login