Showing 345001 words to 348000 words out of 382072 words
Kada wanan yasa kuji komai a rayuwan ku kan zaman ta a tare damu ni dai bukatana a zauna lafiya su bawa mijin su kwanciyan hankali da natsuwa.
Don shi din dan ujulane da balaguro yau yana nan kafin gobe zakajishi a can haka sana,an shi ya kumsa hjyn ta fada.
Don haka Sahiba ban son naji komai ya fito na rashin hankali a wurin ki ki godewa Allah kin samu yabo sosai daga bangaren ki nima din shedane ga hakan.
Da sauri hjy halima ke kallon wadda aka kira da sunan data dade da sani tana kwankwanto a ranta kafin a natsu tace wai Sahiba dai dana sani a baya ko watace wanan din ?
Kaina dago a hankali ina kallon wace ke magana din nima din na shedata hjy Halimace dai dana sani a logos shekarun baya idan baki manta ba.
Matar da muka hadu asibiti da ita tana jinyar danta har tace muna ai dan nata ya rasu itace yanzu nagani a gabana dakin sarukata din tare dasu.
A zabure take fadin lalai kuwa Sahiba ina kuka shiga duk wanan dadewan haka ina mahaifiyar ki da kanin ki take tambayana a cikin mamaki tana min kallon bazata.
Nan ta shiga bada labarin haduwan mu da ita shekarun da suka wuce kowa saida ya tausaya muna nan suke fada muna cewa ai mijintane dan uwan mukhatar din ne.
Don da mahaifiyar mijinta da hjyn su mukhatar ya da kanwace suke nan aka shiga gabatar muna da yan uwan mahaufiyar nasa da suke zaune a falo din .
Mukaji kuma ashe su zamane yakai iyayyen su can suka zauna suka saje dasu an dai dan kara tataunawa kafin mu bar su zuwa wanan dakin muka barsu gwaggo tare dasu a part din.
Sai bayan dawowan sune suke fadin wai karfe hudu zasu kaini dakina sam ban taba zaton hakan zai sani fargaba ba sai wanan lokacin don wani iri naji a zuciyana tunda suka fadi hakan.
Suke fadin ance gidan a gyare yake basai munje munyi wani gyara ba a cikin sa komai an zuba kunga ko tunda har sun nuna kamar suma sun isa da itane ai sai suga kamar muna kwankwanto akai.
Nasiha sosai suke min tare da kara lurar dani a dakin da suke idan kinga yadda gwaggo Hari da yar uwanta gwaggo Asiya suka zake suna min fada zakice basu bane masu min bita da kuli a baya.
Yanzu sun nuna cewa ni din kan tasuce yar uwasuce ta jini dole yan uwan mahaifina suka dan rakube a gefe wanda saini din ke nuna sune nawa don komai zanyi ko nakeso su nake kira in tambayesu.
Nasan hakan yana dan taba zuciyar su saidai basu nuna min a fili ba amma suna kebewa suna gulma don anty Amarya ta rutsasu suna gulman a tsakanin su tazo tana fada min.
Kai mutanen halinsu saisu wallahi suwa ke nan na tambayeta wanda ba halina bane tsoma baki a maganan manya.
Su gwaggonin nan naku dai hjy hari man da tawagarta yanzun na samesu a can dakin suna gulma cewa Allah yasa dai ki iya zama yadda kika saba da harkan bariki.
Gadai gida kan kin samu amma bariki ba zai barki ki zauna a ciki ba dama watace a cikin diyansu ta samu wanan aida su tasu ta yanke ke nan.
Jimun fa mutanen nan wai har hari na fadi saboda idon ki daya bude da barki yasa ta shiga tsakanin ki da danta tunda wuri don ba zata yarda ki rabi danta ba.
Hakama modibbo shima ya nuna ra,ayinshi gareki amma sam ba zasu taba yarda da hakan ba a tsakanin ku don kin bude ido a bariki.
San nan kuma ai gashi ya tabbata kan camfin da akai maku tun kakannin duk inda kuka shiga sai kun dara kowa lokaci guda kema dake bariki za ace wai kece kika samu wanan daulan hakan amma nasu diyan suna zaune a gida.
Jimjn mutane da son kai haka don Allah ko me zakiyi da danta balle shi modibbo ma dayake da matarshi a gida harda yara.
Kawai dai son kaine irin nasu na banza da baida dalili su a ko ina saidai sufi mutum badai kafisu ba da zaran suga Allah ya doraka akan su shike nan a dauki karan tsana da sherin duniya a dora ma saboda hassada.
Lokacin nan shiyasa na rufe ido nayiwa baby aure saboda irin yadda suka fara nuna min waiga su Nabila gida amma zaice baby yake so shi.
Yanzu kuma da Allah yakawo rabuwa a tsakanin su ba abinda basu fada ko yanzu din nafi bukatan ganin ta koma dakin ta ta zauna don dai kawao badai aikin yine a yanzu din.
Don haka sahiba ki daure ki rugumi auren ki da hannu biyu kibi mijinki ku zauna lafiya daduk wanda ke kewaye dashi don Allah.
Nisawa nayi kadan ina fadin nagode anty insha Allahu zanyi yadda kikace din zan zauna lafiya da kowa insha Allah.
Kada kibi takan wanan uwargidan naki ki barta da halinta idan ba tashiga harkan ki intashiga kan ki nuna mata kema kin iya sai a zauna lafiya.
Yanzu bakiga gidan mu ya dan samu sauyi ba don yanzu na gama fahintarsu abudai ne idan yazo ya kama nabawa kowa hakkin shi na bayar idan mutum yabi shike nan.
Idan nace banji haushin zancen su gwaggo ba gareni karya nake fada maku don gaba daya nikan sun kara zubemin a idona.
Antyko taci gaba da fadin wai ga dukiya har dukiya amma bai samu mata ba sun san indai kece kwana biyu zaki fito ki koma barikin ki da kika iyane ai.
Jifa wai dan dan uwanka kake wa wanan fatan haka murmushin karfin hali nayi ina fadin ba komai tace don Allah sahiba ki daure ki zauna a dakin ki.
Kinga dai yadda Allah ya rufa maki asiri a cikin makiyan ku har gobe kune sama garesu ni yanzu na gama fahintar kowa wallahi.
Su mutanene masu dan banzan son kansu da mugun hassada a zukatansu basu son suga wani ya karu yafi ko yaushe su dai ace sune ke samu ko sune a gaban komai.
Wallahi kaf din su indai ba na bayan nan ba sune zance maki suna da dama a cikin su amma kusan manyan nan wallahi duk halin su dayane gaba dayan su saidai na wani yafi nawanine kawai a cikin su.
Wallahi shiyasa nake son modibbo Allah kinganshi sam bai kwaso wanan akidarba ko kadan yanzu ki duba duk da ake cewa komai ya wuce a zauna lafiya a tsakani.
Kinga dan gidan Alh nuhu a nan ko daya ko dan kidan Alh gyade bafa wanda yazo ko dayan su ai idan gaskiyane ko yadda kikai masu din nan zasuzo ko diyan su su turo amma mugun nufi ya hana .
To wallahi kaf dinsu kusan haka suke sai ka zauna dasu zaka san halinsu sosai shiyasa sam bamn dagawa Gwaggon ku kafa koshi Alh.
Nisawa nayi tare da fadin Allah ya shirya dama naga yadda take kallona idan mun hadu da ita tun a kaduna nayi mamakin ganin tazo har nan din duk da tasan kwana biyu za ayi kafin a koma.
Wanan ai sunyi ne da biyu wa yan nan da sai hannu mai mai suke bi idan baka dashi basuyi dakai .
Idan ko kafisu kaida su zaku koma kamar Annabi da kafirine a fili zasu nuna maka kiyayya ba gaira ba dalili don kawai hassada dasa abu arai irin nasu.
Anty amarya harta gama tafita ban samu abindana fada mata ko daya ba lokacin bayan nisawa da nakeyi ina tunanen zumuncin zamani yadda ya koma yanzu ga mutane.
A gaskiya bazan lamunci zancen wai ummana ta dawo cikin su kaduna ta zauna ba a yanzuma .
Don naji sun fara fadin wai ya kamata tunda nayi aure saita dawo gida itama su zauna a gaban yan uwa zaifi watau dai a can din sun dauke mu bariki muke shekawa kawai a zaman can din.
Haka har karfe hudu yayi kowa ya shiga shirin tafiya zuwa gidan da zan zauna din a cikin sa wanda ba kowa yasan da sanin cewa ashe ba gida daya zamu zauna da hjy falmata ba dama har danginshi basu sanda hakan ba sai lokacin da aka dauki hanya daban ba wanda suka sani ba zuwa wani sabon gida nashi dake gaban unguwar da mahaifiyarshi take kadan nan nawa gidan na Maiduguri.
Gidane na gani na fada wanda shine wanda ya gina a baya bayan nan don ba kowa yasanda cewa gidansa bane a garin .
Tsarinshi da komai ginan kasan wajene ba irin fasalin ginan mu bane na nan da aka saba gani ina jin gwaggo hari na fadin dankari saidai muce Allah yasa mu cika da imani kawai masu kudi na inda suke kasan nan ashe.
Aikuwa ciki taga mun shiga kai tsaye nan ta suma zaune tana raban idanu har motocin sukaja suka tsaya aka soma fita ga guda yana tashi a ko ina.
Bin gidan kowa keyi da kallo kafin wata mai zakin murya ta sake sake guda da habaici lokaci guda da sauri wanda ke tsaron gidan ya garzayo yana fadin sannun ku da zuwa.
Ikon Allah gwaggo ke fada tana fitowa yayin da suka zagayo a bangaren da nake zaune cikin motan gwaggo kudidi ta karaso ta bude bangaren da nake zaune naji gwaggo amina tace dakata da ita.
Wanan gidan fa kamar babu kowa a cikin sa kudidi sai nake ganin kamar ba nan bane ai kuwa nan daine gidan nata wata daga cikin yan uwanshi ta fada daga bayan su.
Inaga a nan zata zauna ita wancan dayan gidan kuma uwargida ke ciki tare da yan uwanta koni na dauka ai a gida daya zasu zauna tare sai naga an nufo nan yanzu.
Bin gidan sukayi da kallo kafin gwaggo Asiya tace dankari gwaggo haro tace bari kedai anty na aini nayi shiru ga baki daya wallahi.
Da sauri daya daga cikin yan rakiyan mu daga lagos ta iso dauke da buta a hannunta tare da sabon kafet din sallah magana tayiwa su gwaggp akan zanyi alwala nayi nafila kafin na shiga gidan ga yadda al,adansu yake.
Allah ya taimaka sai mere baki gwaggo sukayi don jikin su ya mutu a lokacin suka kauce na fito daga motar da taimakonta nan suka nuna min gefe na tsuguna na daura alwala kafin na gama sun shinfida carpet din na hau na tayar da sallah din raka biyu .
Kafin na daga hannayena biyu sama inayi suma sunayi da dan karfi duk wanda ke wajen yana amsawa da amin don sunsan addua sukeyi duk da hakan ya zama bakon lamari a wajen su kuma.
Kafin na shafa tare dasu sai lokacin wani kuka yazo min suka fara addua tare da rike min hannu kaina a kasa ina kuka wiwi zuwa cikin gidan da aka riga aka budeshi ko tun shigowan mu get din gidan.
Duk wani wanda ke wajen a lokacin na bashi tausayi dan yadda nake kuka wiwi zuwa cikin gidan a daidai shiga kofan suka tsayar dani .
Kafin su fara da hasbunallahu wani, imal wakil kamar a waka baka jin komai sai muryoyin su a haraban gidan lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
1️⃣0️⃣4️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, MUGHNI , , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋
Da haka sukaja hannuna zuwa cikin gidan wanda kamshi da sanyine suka bugi fuskokin mu lokaci guda su anty amarya sai masha Allah nake jin suna fada.
Ke kan sahiba kin gama da duniya saidai ki nemi lahiran ki kuma kai wanan daulan duniya haka kamar kana kasan masar azziki ya nuna kamshi wurin nan gaskiya.
Nasan da biyu take wanan maganan a lokacin sister ce ta iso da sauri tana waya tare da fadin ehh tagane take fadin ku shigo ga dakin amarya daga nan .
Subahanallah Walhamdullilah Allahu Akbar shine abinda yarbawan ke kira kamar da waka a bakin su wasu na amsa masu cikin yan uwana da nasa da sukai muna rakiya dayan kanwarshi duk tana vedioting komai da akeyi lokacin.
Nan dai suka kaini dakin daya bugawa soster waya cewa shine nawa dakin ya hadu komai na cikin gidan ga baki daya na wajene don haka tsayawa bayani bata lokacine gaskiya gida dai tubarkallah masha Allah.
Daga nan suka fara fita kallon yanayin gida sai aka barni da su faiza da saura a dakin sai lokacin na bude idona ina bin ko ina nagidan da kallo,.
Tirkashi yayi da uwargidana hjy Falmata ke can wancan gidan nasa suna ta buki da mutanen ta ana kisa yadda komai zai wakana idan mun iso .
Sai kuma labari yazo masu a nazata cewa ai amarya ta tare a ko da sauri hjy Falmata dake waya lakacin da yaranta tace mene kike fada ta tambayi wace kebada labarin tarewan a lokacin.
Tace ta tare a gidan ta mana tun karfe hudu da rabi suka kaita dakinta tana can gaba daya dakin yayi shiru na lokaci guda kowa da irin abinda yake tunane a zuciyar shi.
Mikewa tayi daga zaune sai wanan yatta din hafsat tace ina zaki koma ki zauna yanzu idon kowa yana kanki aga yaya zakiyi.
Zama tayi ba dan taso ba lokaci guda sukaci gaba da fadin shi kuma haka yaiwa mutane dama bai fadi inda amaryan nasa zata tare bane.
Kubar wanan zancen yar nasu ta kara fada don a bar maganan a bainan jamma,a saidai falmata din ta kasa controling din kanta a lokacin don jin zancen take kamar a mafalki.
A cikin hasala take tambaya wani gidan nasa ya kaita ke nan sai mai bada labarin take fadin naji ance kusa da gidan sarki nan dai unguwar nakune mana ba niss naji suna fada.
Katseta yarta da take biwa ga haihuwa tayi da fadin waike a ina kika samu wanan labarin ne ina nan daine yake nan kuma za a kawota wancan dayan part din ko ?
Ya canza shawarane dai wata daga cikin bakin kawayen ta ta fada ta bude baki da kyar tace ya canza ne kan don ko jiyan nan saida yan uwansa sukazo aka kara gyara part din ai.
Gyara ko na sosai don har mun leka ai komai a kwai ciki eh wanan makircin suka shirya yasa suka hana ta tare jiya din ai.
Wanan bashi zaisa na fasa komai a kanta ba tunda tayi gigin shiga harkan mijina zan nuna masu ni din nice don ba irin mu ake hawa a taka ba.
Falmata bakya ji a irin wanan lokacin kike wanan zancen haka haba dai ta fada a dan cikin daure fuska tana mai jin zafi da kuna a kasan zuciyarta na wanan sabon zancen da yazo mata.
Lamarin na mijinta a yanzu ya fara bata mamaki don yana abubuwa kamar ba mukhatar dinta data sani a baya ba.
Don a zamanta dashi sam baya boye mata duk wani lamari nasa koda kuwa yasan zata iya yin wani abinda ba daidai ba duk da tasan bawai ta kyaleshi hakana bane don ko yaushe cikin kara kammala abinta take don gudun irin haka.
Ba abinda ta tsana kamar kalman kishiya sam bata taba sarai cewa zai taba mata kishiya a rayuwan su ba duba ga yanzu yadda shekarun auren su yaja zuwa yanzu.
Amma sai gashi da rana tsaka yan uwa sun tasashi gaba a cewan ta har yakai ga sunyi galaba a kansu sunsashi ya kara mata wata a gida da sunan kishiya.
Ita tasan ba yinshi bane don yasha fada baida ra,ayin yin mata biyu a yanzu sam haka yasa ta kara sakankancewa da bai taba mata kishiya ke nan.
Ido ta runtse cikin takaici tare da fadin ina tausaya maki yar yarbawa ko yar filoce don zama gidan mukhatar saiya koma mata tankar zama cikin kabari.
Tasan irin taron data shiryawa zuwan amaryan wanda manyan malaman dake mata aiki suka tabbatar mata dashi kuma ta amince da aikin su dari bisa dari don sunsha mata ai kuma ta gani ta yaba da aikin nasu don hakanema akan wanan din bata da matsalan komai a yanzu don tasan karshen yarinyar waje road zata nufa .
Nan dai kowa ya shiga fadan abinda ke cikin zuciyar shi kamar yadda al,adan mata yake in iri haka ya faru suna goyon bayan bangaren da suke suna ganin ba ai masu daidai ba.