Showing 126001 words to 129000 words out of 382072 words

Chapter 43 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28435

koshi waye ba na dai ganshi da oga suna zagayawa haka yasa na fahinci yana da muhinmanci a wurin ogan namu.q
Har kusan lokacin tashi mun daga aikin suna tare da oga da sauran manyan shagon a lokacin ne na fito da abayana daga cikin jakkata na dora saman jan rigan dake da tabarin shagon da bakin bujen dake jikina.
Nayi rolling din kaina da gyalen kayan ina irin wanan shigarne don kare mutuncina don ban yarda in fita hakana idan zan koma gida saboda bata garin dake akwai a garin.
Duk dadewan shagon shine goma da rabi zuwa sha dayan dare mu mata goman ne namu sai dai wa yanda ke kusa da shago din ke zama har a rufe shagon su tafi.
Jakkana na dauka inda muke ajewa ina fadin good night oga da cewa manyan mu dake wurin suka amsa min da cewa night miss Sahiba na fito ina gyara dan kwalin abayan da yake dan sabulowa a jikin nawa.
Sai lokacin naga hadarin daya game gari yayi bakikirin yana shirin tasowa da iska ban damu da wa yanda ke haraban ba nake fadin ya subbahanallah Allah ka ceceni na samu abin hawa ya karasa dani gida kafin ruwan nan ya fado.
Na dan tsaya na minti biyu lokacin har an fara iska a garin kadan kadan yasa na fara dan takawa da kafa don kada ruwan ya tsayar dani a wurin.
Motocin dake fitowa nake dan waige kafin wata motar ubansu taja ta tsaya a gabana jan danjan bayanta yana dan haskawa kadan kadan har na tako ina kokarin wuce ta .
Glass din motan aka zuge lokaci guda naji wani murya na fadin can i help you don akwai hadari ruwa zai iya fadowa ko wani lokaci a yanzu.
Na duba da kyau na gane wanan guy din ne dana gani da shugaban shagon mu yake min magana no zan iya takawa ba nisa sosai na fada ina ci gaba da tafiya.
Kada kiji tsorona niba mugu bane ya fada a cikin hausan shi pure saidai hausan akwai dan bambamci dana yan kaduna dana kara gwanewa yanzu dashi.
Mamakine ya kamani jin hausa radau a bakin shi yasa naja na tsaya ina bashi hakkuri tare da fadin.
Ba haka nake nufi ba don kada in bata ma lokaci na fadi hakan banda nisa sosai da nan shiyasa nace hakan .
Kizo ki shiga na saukeki kada ruwa ya tsare mu banyi mussu ba ya bude gaban motan na shiga ya subbahanallah na fada a raina.
Kamshi da sanyi ne sukai min maraba a motan sai kuma karatun malamina dan india ne ko balarabe dake kira,a a cikin motan.
Saidana zauna nace nagode na gyara zama na takure a wuri daya kamar a tsorace idan ka ganni a lokacin don nasan ranan na shiga motan maya kan.
Bai juyo ko sau daya ya kalli inda nake zaune ba sai tukin shi yakeyi a hankali don ina shiga na fada mai layin da zan tafi yace nayi mai kwatance idan mukai wurin.
Layin nace ga wurin ko a nan ma ka saukeni ba nisa damu zan iya karasawa yace gidan nakune bakyason a gani nayi shiru har kofan gida ya saukeni ina faman yi mashi godiya yaja motarshi ba tare da amsa min ba ya tafi.
Umma suna waje suna hada kaya don sai na dawo nakan hada mu rufe shagon mu shiga gida zuwa sha daya don masu zuwa sayen kayan sanyi a lokacin.
Tun fitowa na daga motan umma ke bina da kallo har na karaso inda suke nagaidasu sukai min sannu da zuwa na karbi kayan dake hannun umma din don sun gama hada komai muka fara tafiya zamu shiga ciki.
Naji umma tace dani ina kika samu mai motar nan daya saukeki yanzu na juyo da sauri ina fadin wallahi umma ban san shi ba taimaka min yayi kada ruwan nan ya dukeni .
Sahiba kardai ince kin fara kula maza ne a rayuwan ki wani irin juyowa nayi na dakatar da tafiyan ina kallon umma din kafin incw maza kuma umma ?
Wallahi nafada maki nansan shiba ban kuma taba ganin sa ba sai yau din nan kuma banda gaisuwa da godiya ba abinda ya hadani dashi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

3️⃣8️⃣ BY, , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUDHELL, , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA DON ALLAH KAFIN KI KARANTA NA FADA NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANIN HAKAN, , , , , ,

Ni kaina yau dana tsaya a gaban mirrow nasan kayan dana saka sun karbeni sosai don yadda suka mayar dani wata preety girl kamar wata cerlebrity din lagos dani saidai inda na rago su na dora dan hijab dina da nake sakawa iya kafada na.
Turare idan an min biya shagon nan nake sayen oud a wajen don na koyo shafa turare zamana na kaduna idan ina kusa suka murza zasu miko min in shafa nima a lokacin.
Rigan bakace har kasa ta sauka min sai dairin mai fitar da sharp din nan ce ya fitar min da surana fili na ya mace sosai duk da ban damu da hakan ba tunda a ganina ai na suturta jikina ke nan ni ina shiga ta musulunci ke nan a can.
Jakkana na ratayo nazo nayiwa umma dake kokarin fita ta bude shago sallama ni kuma na leka dakin Amar na ce dashi mu tafi.
Tare dashi muke jerawa mu shiga mota ya sauka a hanya ni kuma na wuce zuwa nawa wurin mun sauke shi ya taka ya dauki hanya muka tafi ina bayan Nape kamar ance dani in dago kai mukai arba da dan gwaggo hari a inda go slow ya tsare mu .
Da sauri na kawar da kaina kamar ban ganshi ba lokacin, don wani irin faduwan da naji ga tsoro ya idda kamani sosai da ganin shi din danayi a wurin ina Allah Allah kada shima ya ganni .
Duk da nasan ganin shi alheri ne a garemu saidai yanzu da nasan ko shi waye bana son haduwan mu dashi a yanzu gaskiya.
Don haduwa zai iya saka ya tunawa mutanen kaduna damu har su dawo su nememu abinda kuma ban so ya faru a gare mu ke nan yanzu gaskiya.
Don nafi son sai na fahinci meye dalilin su na sharemu da kowan su yayi don daddy ma bai ko gari da muka bar kaduna din kuma bai nememu ba yanzun da ya dawo.
Allah ya taimake ni aka bayar da hannu motocin suka fara tafiya don barin wurin nace wa driver keken da nake yai sauri.
Na sauka ina mikawa mai keke kudi naji ance a bayana hello ban juya ba don ganin dawa meshi ke magana balle insan koda ni yake maganan.
Na juya zai wuce aka kara fadin hello miss jin hakan yasa na juyo don ganin mai maganan motar suce ta dazun da muka hadu a wurin yanzun ma a bayan mu ashe wani kallo kada ka raina ni nayiwa driver din .
My oga de talk to u, wanda ke wajen yace min wani kallo na watsa mai kafin in ce who be ur oga ?
Go tellam say , me i don't have business with him, nd i no be those gurl dey are chassing on d street sha .
Daga haka na juya na wuce ban yarda na daga kai ko ido na kalli inda shi yake zaune ba din kada yasani zuwan dole wurin.
Da dan sauri na bacewa ganin su na shege inda muke daukan lecture na nemi wuri na zauna abina ina dakon malami ya shigo.
Har malamin ya shigo ina zaune ina tunanen me yake nema a wurinane wai da yake bibiyata a yanzu don bai rasa sanin dililin da yasa aka jafar damu nan inda muke yanzu.
Ina murna na huta tunda nayi masu haka ashe ban huta dashi don kuwa ina sauka bus din school da nakan biyo mu sauka a jaction sai ga motar na sake gani kuma a wurin again.
Inda Allah ya taimakeni driver ne kawai shi kadai a motar ba maigidan nasa madam my oga send me to pick you, i dey follow you since u no see me.
Wani banza kallo na watsa mai ban tsaya bi ta kanshi ba na nufi wurin da yan nape ke tsayi suna shiga da mutane cikin unguwa direct nace ya wuce dani shagon da nake tsare kaya son kada inje gida ya bini har can.
Exacuse na basu na rashin sako uniform dina kuma suka daukan min hakan basu koreni ba a ranan nayu mamakin hakan don basu yarda a zo masu aiki hakn.
Na samu an kawo masu kaya shagon conteners suna ta sauke masu haja sai na dauka don shine suka barni na zauna haka ranan dai munsha aiki ga kyauta kuma da muka samu sai sha daya saura muka samu komawa gida da taimakon motan shagon daya kai kowan mu gida a lokacin.
Nayi duba a hanyar banga wanan mai bibiyana din ba waishi driver don haka na sake raina na isa gida lafiya da yar jakar dake dauke a hannu na na kayan da aka bamu a wurin.
Da shigana gida na samu umma a falo tana jiran dawowana hankali tashe nayi sallama ina cire takalmana tare da fadin umma na dawo sannu da gida umma.
Ina kika tsaya yau haka sahiba umma ta tambaya rai bace tana kallona a cikin daure fuskanta gareni dama nasan hakan zai faru nace wallahi umma daga can kada in makara shago na tafi don nasan idan na dawo gida zan iya makara kuma basa son ana makara haka su.
Amma ai ya kamata ki sanar dani kafin ki fita ba wai ki barmu haka hankali tashe ba tunda baki saba yin hakan ba.
A dan marairaice nace umma kiyi hakkuri don Allah ba zan sake ba insha Allahu tayi shiru tana kawar da kai gefe daya.
Anty ekabbo Amar ya fada na dan kalleshi nace dashi how are u Amar ya amsa da fine yana gyara kwanciya inda yake yana karatu ya zube littafi a gaban shi.
Ledan shango da na shigo dasu na zube a gaban umma kafin na mike zan shiga dakina in cire kayan jikina.
Muryan umma ke fadin yau yaron nan yazo gidan nan bakya nan da sauri na juyo ina fadin wani yaro ke nan umma ?
Dan wajen hjy harira kanwar daddy ku na kaduna kece kika nuna masa gidan nan har yazo ?
Umma wai ya mustapha kike nufin yazo gidan nan ko wa don dai ban taba nunawa kowa gidan nam ba wallahi ko abokan karatuna kuwa.
Shi din nake nufi mana diya nawa kega hjy harira din idan bashi kadai ba shi nake nufin yazo nan muke zaune dashi a falon nan ya dan jima nan kafin ya tafi.
Dawowa nayi na zauna nayi shiru ina dan tunane kafin can in dago kai ina fadin umma tun ranan da mukaje wurin wanan Alfa din idan kin tuna munga wani mota baka kusa da itaciyar dake wurin da mutane tsaye suna magana .
To sune muka gani a wirin kuma ranan ce na fara ganin shi tun dawowan mu garin nan a ranan na fara ganin shi sai kuma yau da hold up ya tareni hanya mm a gansu suka bini har school din mu ban kuma tsaya ba.
Don gaba daya bana son kowa daga wanan bangaren a yanzu gaskiya da kuma irin kashedin da yai min kada na kara nuna nasan shi a ko ina .
Shi din ya fadi hakan nace kwarai umma shiya fada min da bakin shi ranan da a kai bukin dinnan diyan gwaggo Asiya din nan .
Oh Allah kai kadai kasan dalilin halittomu a cikin wa yan nan mutanen da suke yan uwa a garemu kuma basu rike zumuncin nasu ba a kan mu.
Ban iya ba umma amsan komai ba illa dai nayi shiru ina nazari na dade zaune a wurin kafin in mike zuwa ciki na cire kayan jikina nayi wanka.
Ban fito ba saida nayi sallah na saka kayan barcina wando da riga sai bakin hula a kaina na cusa gashina aciki na dora zani a sama na fito kitchen na shiga na debo abinci na fito.
Cibi biyu nayi sai na kaaa cin abincin saboda tunanen daya dameni a lokacin muryan ummace ke fadin yace zai dawo weekend don haka zaku hadu dashi ke nan kuma ai
Saidai idan son samune umma mubar gidan nan kafin weekend din ko don ni yanzu tsoro mutanen nan suke ban baki dayan su .
Gara mu kara gaba can inda babu wanda ya san mu, mu zauna kuma zai fi muna don na fahinci gaba dayan su ba kaunan mu sukeyi ba.
Kallon da umma keyi mun saina dauka cewa shawarana ya karbu a zuciyarta na har zanci gaba da fadin kinga ai idan sun, , , , ,
Ashe har yanzu baki da wayau sahiba ban sani ba na dauki wayau na dora maki ashe ke har yanzu da sauran ki ban sani ba
To bari kiji sahiba daga wanan gidn babu inda zan kara tafiya kuma sai dai yanzu duk abinda zai faru damu ya faru.
Boyon ya isa hakana don na dauka yanzu lokaci ya kusa da zamu baiya a garesu su sanda sanin muna raye a duniya.
Bukata na kawai dama ki samu karatun da idon ki zai bude ko kiyi wayau da zaki iya tunkaran su su gane koke waye a cikin su.
Har idan ma basu nememu ba muda kan mu zamu nemesu nan gaba idan lokacin hakan yayi a garemu kedai kawai ki kara maida hankali kan karatun ki a yanzu kiyi hankalin da zaki iya tunkaran su akan hakkin ku.
Zaman mu a nan shine rufin asirin mu don yanzu idan kin kula bana cikin fargaba irin baya daku haka shi kanshi wanda ya kawo mu wanan wurin nasan yayi hakan ne a bisa wani shiri da yake muna nan gaba .
Bawai haka kawai ya kawomu nan ya zubemu ba dole da akwai shirin da yakeyi shima da zai samu mafita a cikin maganan nan.
Kuma ina sane daya dauke mune daga can ya gudo damu nan da yake ganin shine maboya a garemu don nan din kusan zagaye muke da gidajen security duk unguwan nan idan kin kula da hakan.
Dan nisawa nayi kafin na runtse idanuwana na dan lokaci Allah ya gani duk da tunanen umma na nufin haka ni dai sai hakan bai mun gaskiya.
Abincin na dan fara cakula da cibi ina laiwa bakina badon dadi ba ko dandanon shi sai dai kawai don in kawar da yunwar dake damuna a lokaci.
Banda aiki ranan Saturday amma hakan na kirkirowa kaina fita tun safe na shirya nacewa umma akwai screening da za ai muna a shagon da nake aiki .
Kallona umma tayi tana fadin wani screening zaki kuma yanzu keda kikace zaki bar shagon wahala yai maki yawa yanzu zaki daina aiki dasu.
Amma ai umma ban barsu ba tukun na kinga dole in je ayi min don sai karshen shekara nake son na aje dama lokacin sun bamu bonazan kaya yadda muma zamuci riban mu dasu.
Allah ya tsare umma tayi min na fita Allah ya gani banyi niyar zuwa shagon ba amma haka na daure na fita duk wanda ya ganni sai yayi mamakin ganina a lkacin haka na daure nayi signing na fara aiki kamar yadda muka saba dasu ban damu da kallon mamakin da sauran ke min ba don ba fuskan da wani zai iya tambaya don ko matan ma,aikatan daga gaisuwa ba abinda ke hadani dasu kuma.
Ni sam a rayuwana ban yarda da abokiya ba haka kuma bana sakin fuskan da zaka ga damana har ka samu shiga a wurina kowa ban yarda dashi ba haka Allah yayi min rayuwana ni.
Wasu mata da mijine hausawa ta shigan su na gane hakan don sunyi irin shiga na arewa har yayayen su biyu suka zo part din kayan kamshi dana gyaran jikin mata.
Matar ta daga wani set din man shafi take fadin su dauke shi mijin yace a cikin hausa nifa kin san bana son man da ke saka mutum haske ko ya canza mai kalan jikin shi.
Matar tace dashi amm kuma ai naga wanan din na larabawa ne nasan zaiyi kamshi bawau don fari na daukeshi ba mijin ya sake fadin ki dai duba wani zaifi.
Lah yayana daka barta ta dauka tunda tana so wanan baya saka haske sai dai ya gyara mata natural skin din ta zai kara kyau ne kawai nan babu kayan karin haske gasu can daga baya ku kun baro wurin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login