Showing 213001 words to 216000 words out of 382072 words

Chapter 72 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28396

wani abinda bansan na furtashi ba lokacin.
Na koma na kwanta abincin da banci ba ke nan kuma saida safe don kwanciya nayi dan wani irin barci daya ziryaci idona a lokacin mai nauyi.
Kamar a cikin mafalki take jin ihun yar ta dake dakin ta kwance kusa da ita zabura tayi don jin ihun yar natane dai ba wani a lokacin daga ita sai daura gaba a jikin ta tanufi dakin a gigice take lokacin.
Tura kofan tayi da karfi a daidai lokacin da sauran mutanen gidan suma suka fito don jin ihun daya karade gidan nasu a lokacin shima kanshi maigidan a rude daga shi sai dan short irin na maza katon cikin sa a waje ya karaso dakin a gigice .
Abinda kowa yagani nr yake sasu komawa baya da sauri suna salati ga makwabta a lokacin har sun fara fitowa don ba karamin ihu yarinyar takeyi ba yana bin dare.
Innalillahi Alh ya ambata tare da fadin Sanda kanka daya kuwa da hankalin ka kuwa kasan abinda kake kokarin aikawa ga kanawarka a yanzu.
Baya cikin hankalin shi don haka bai jin tsawan da mahaifin nasa da sauran yan uwanshi ke masa a lokacin.
Ganin zasu tsaya ya illanta mata yarta yasa uwar yin kundunbala ta fada ciki ta fincikoshi da karfi hakan yasa yaranta maza biyu suma suka taimaka mata wurin bambare shi sukaja yar uwansu tare da yaba mata zani da sauri a jikin ta.
Aiko binta yayi bayan mahaifiyar nata yana kokatin jawota ala dole sai yakai a jikinta kamar yadda aka umurce shi yaje yayi din.
Alh da baisan matakin dauka ba a lokacin nufar dan yayi ya kifa masa mari uku masu kyau rai bace ya fara magana yana fadin.
Don ubanka ka shiga hankalinka mana ko nan cikin gidana aka turaka kayi wanan aika aikan da zakazo kana neman hakewa yar uwanka haka ?
Jajjayen idanuwan shi da suka rine suka sauya halita don kana ganin shi kasan baya a hayacin shi gabaki daya yayi wani irin gumji ya juya yana kokarin cakumo yar dake makale a jikin uwarta yan uwanta sun masu kariya a lokacin.
Kai ranan nan dai ahalin gidan sunga tashin hankali don haka ya koma kamar mahaukaci saida aka ja yar a cikin dubara zuwa wani daki aka boye ta shi kuma maza sukai waje dashi don a samu natsa shi .
Alh ne yace a kawoshi falon shi kafin ya shiga wani daki ya debo wani abu da hayaki yana yayyafawa dan nasa dake rike ahannun mutane.
Haka gari ya waye kafin kace meye labarin hakan ya fara karade unguwa zuwa cikin gari har aka samu masu kari a zancen suka gyara labarin tare da kwaskwarima don zancen yayi dadin ji da bayarwa.
Irin barcin da nayi ranan bana kau sake bane don da kyar na iya tashi nayi sallah kuma na kwanta a wurin sai karfe daya saura na falka na shiga wanka tare da dauro alwala na fito.
Tsab na shirya na fito umma tayi mamakin hakan nace zan leka na dawo don ban san irin barcin da nayi ranan ba.
Na isa wurin aiki sai bina da kallon akayi niko ko in kula da irin kallon da suke min din kai tsaye na shige inda muke aikin mu.
Duk Sunyi mamakin ganina a lokacin niko ko in kula da hakan na zauna na bude laptop dina na fara aiki a cikin sa bayan gaisuwa ban kara magana da kowa ba a wurin sai kai da nake kadawa idan wani yayi min wani tambaya.
Aiki nayi sosai a ranan don har kusan biyar na yamma ina cikin ma,aikatan lafin na nade nu,uran na fito zuwa gida.
Ko a gidan ma bana magana Abdulhamid umma ta sama take fada mai halinda nake ciki shida matar shi suka biyo umma zuwa gidan.
Duk yadda sukaso nayi magana banda bakin hakan karshema na barsu a falon na shige ciki don kallo daya zakaimun kagane ba a cikin hayacina nake ba lokacin.
Hankali tashe aka kira Nazifa da sassafe ana sheda mata abinda ke faruwa a gidan kan yan uwanta.
Kukata saka a wajen hakan ya jawo hankalin mijin nata dake execise a lokacin ya fito yana tambayan ta abinda ya faru take wanan kukan haka.
Kasa fada mashi tayi don bata san me zata fada maiba a lokacin don maganan nada nauyin fada a bakin ta.
Daya matsa sai cewa tayi dashi gidan mune ba lafiya wai suna asibiti da safiya da ya umar cikin mamaki ya kara tambayanta da meya samesu haka lokaci guda tace saidai idan naje zanji.
Ga mamakinta sai taji yace da ita ki jirani muje tare mu gano su yanzu Allah dai yasa ba wani abu sukaci da yajawo masu kwanciya asibitin ba haka lokaci guda.
Ai kuwa dai taren sukaje suka samu yan gidan cirko cirko a haraban asibitin kowa ransa a bace ana ganin su hanlalin kowa ya koma garesu.
Bayan sun gaisa dasune yake tambayan su cikin son jin abinda ya samesu din sai kowa yayi shiru yana dukar da kanshi kasa lokaci guda.
Da yake yasan kanshi bai matsa masu ba ya wuce zuwa ciki ya kai tsaye don ya tambayi likita abinda ke samun su din ?
Saidai baikai ga shiga ba a bayan filawan dake wajen yaji muryan kawun nasa na waya yana fadin wallahi akwai matsala babba Alh ina fada maka.
Gaba daya hankalina a tashe yake don wanan abin ana ganin shi karamin magana yana son ya zamo muna babbba a garin nan.
Don gaba daya yarinyar nan tana son juya muna hankali tayi muna wasa da hankali wai yaron dana tura ya gama da ita jiya shine ya dawo ga kanwarsa haukace yana neman aika abinda na umurceshi dayaje yai mata a can.
Sahiba kawai ya anyana a zuciyar shi lokaci guda haka yasa ya juya bai shiga ba don ya gama jin komai a inda ya dace yaji gaskiyan maganan.
Sai waya ya bugawa matar cewa shi ya tafi idan ta gama ta dawo gida ya barta can ita da yaranta gidan ya dawo ya karya kafin ya fice a gidan zuwa gidan su.
A can ma labarin komai ya riski mommy ya samu tana waya don haka ya zauna kamar baisan akan me take wayan ba.
Saida ta gamane ta juyo tana fadin daga gida kake halan ta dan bata fuska kafin yace eh daga can nake.
Ka ji abinda ke faruwa ke nan ko yace namefa mommy tace zanceb gidan yaya Nuhu mana da basu gajiya da sake muna abin kunya a gida ko yaushe ?
Naji mommy don naje can din nida Nazifa saidai na fahinci reshene ya juye da mujiya ga zancen shine dalilin dawowana na barta can.
Me kake nufi da wanan zancen yace eh mommy don abindaka shuka shine zaka girba dan haka ANA DARA NE YA FARU DASU, , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

6️⃣3️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ASH SHAHEED, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Wasa wasa hakana kwashe har kwana hudu a zaune ba umm, ba umm,umm agida zaune saidai inta bin mutum da idanu saidai kallo daya zakai min ka fahinci ina cikin bakon yanayi.
Hankalin umma ya tashi sosai da hakan dole ta daga waya ta kira ya Abubakar tana sheda mai halin da nake ciki a yan kwanakin.
Yaji hankalin shi ya tashi don zaune suke falo lokacin shida Nazifa da yaran su saiga kiran umma ya shigo wayan shi ya dauka da sallama yana gaida umma din.
Abinda yasa Nazifa dan juyowa ke nan ta kalleshi don jin mama daya ambata bata gane ko wace mama bace alokacin suke waya da ita.
Yadda ya zabura yasata fadin lafiya wacece kuke wayan sai lokacin ya dan saita kanshi yana fadin gani zuwa mama yanzun nan insha Allah .
Ido Nazifa ta kura masa har lokacin daya kare wayan nasa idon ta na a kanshi don bata fahinci dawa yake wayan ba.
Mikewa yayi a daidai lokacin da yake kokarin saka talalman shi dake gefe yana daukan makulin motan shi daya aje saman table gaban shi don dama yana da niyar fita a lokacin.
Wacece ta jefo mai tambaya tana kallon shi a tsorace don sanin cewa yan gidan su na asibiti har lokacin don haka takai zuciyar ta can ko wani abune ya samu yanuwan nata .
Mamace ya fada kawai yana kokarin fita daga falon wace mama ke nan fa ta sake tambayan shi kai tsaye yace maman su yusuf da cewa Ammar kanina don yasan ba zata gane ba yana fadin haka ya fice daga gidan ya barta zaune tana maimaita sunan maman yusuf wace maman yusuf kuma ?
Sai kuma taja tsoki ai tunda ba yan gidan su bane shike nan ko wace mamace su karata can yanzu kila wani case din shinecan har ya dan ruta da hakan taci gaba da kallonta kamar ba kanwata ciki daya ke kwance asibiti ba a cikin tashin hankali.
Tuki yayi na tashi hankali yan mintuna kadan ya sadashi da gidan mu ya fito zuwa ciki misalin karfe biyar na yamma a lokacin.
Yana shiga falon dani yai arba a zaune na hakince irin zaman da manyan mutane keyi a da can baya na sarkuna kafafuwana biyu suna lamkwashe a tsakina duk da sama kujera nake zaune.
Ummace data fito kitchen rike da plate din dake shake da apple a cikon shi suka hade ta dan saki ajiyan zuciya tana fadin Abubakar har ka karaso ke nan ?
Yace eh mama fuskan shi a kaina yake gaisawa da ita kafin yakai zaune yana fuskantana umma ma zama tayi bayan ta aje plate din a gefena tana fadin gata nan wallahi yau kwana hudu ke nan na rasa meke damunta haka ?
A lokacin Abdul dayaga shigowan shi shima ya shigo don shi ya ba umma shawaran a fada mashi kada su barni a hakana don har yayi waya da oga Sha,aban yace su mayar dani lagos saidai ta yaya zasu daukeni a haka Abdul ya tambaye shi ?
Don hakane shi Abdul din yaga garafa su fadawa yan uwana tunda ina dasu a garin koda shawaran da zasu bayar a kan matsalan nawa don sun fahinci akwai sabon sauyi sosai a cikin lamarin.
Idon shi har lokacin yana a kaina koda yake amsa sallaman Abdul din ya shigo ya zauna shima idon shi dai har lokacin yana gareni.
Umma taci gaba da fadin mun rasa gane meke damun ta sai bakon yanayin da take muna komai a hakince ko a kwantace zatayi muna magana baki yaki budewa har yanzu.
Gaban shine ya fadi ras ras ya fara ambato innalillahi a fili tare da fadin dama nasan wanan aikin zai iya jawowa Sahiba matsala sosai don wallahi shu,uman mutane ne mutanen nan sam banu Allah ga al,amarin su ko kadan.
Su dai burin su shine suga sun gina kansu sun halaka mutum ko da gaskiyan shi don nayi bincike na gane wa yanda sukazo aiki a kansu a yanzu.
Abdul ne daba hausa yakeji sosai ba yake fadin yanzu meye abin yi ke nan yana tambayan su sai ya gyara zama yana fadin kuma gata da lafiyan ta balle muce aje asibiti ko ?
Abdul yace munce zamu tafi tayi muna kashe din hakan tun shekaran jiya ya kara zakudawa yana fadin innalillahi baya ko kitbta idon shi a kaina.
Yace gara kubar aikin nan nake gani don yana da hatsari sosai ga yinshi idan ta dan samu sauki sai a koma can lagos din zaifi.
Sai a lokacin Allah ya bude min baki a cikin wani irin muryan daba nawa ba kamar na maza na fara fadin a kansu zamu dakata ai basu ida ba basu isa suyi min komai ba don suna tare dani.
Shifa sarki ne gaba daya yake zaune haka a kaina sun taba ganin inda sarki yaja baya da yaki hutu kawai suke son nayi su tafi ba abinda zasu iya indai an yarda da Allah da kuma aljanni akwaishi to sune tare dani.
Kuka umma ta sake lokacu guda mai ban tausayi tana fadin shike nan yar nan abin nan ya tabbata gaskiya a kanki ina daukan hakan kamar dai baiwane ashe da abubuwa saman kan ki.
Baiwane mana shi shifa ba a kowani kazami yake saukaba sai a inda ya dace kuma ya kama yazo da kanshi ai da yaran shine saman kaina amma yaga ya dace shi yazo yanzu da kanshi.
Zakace wani babban sarkine a zaune yake magana da isa da izza kafin na juya na dauki apple din har cizawan irin na sarakuna nayi shi na aje a gefena.
Falon yayi shiru tsit kafin muryan Abubakar ya amayo yana fadin Abdul ya biyo shi akwai inda zasu tafi wanan ba abin su zura ido bane kawai sai lokacin da sukaga daman sake ni din.
Nan suka fita suka barni da umma zaune wacce ta kura min ido na lokaci guda tana mamakin budan bakina a yau din don ko ba komai zuwan Abubakar din ya taimaka mata ai tunda yazu tasan magana na yana nan bai dauke ba.
Gidan wani malami suka tafi can cikin kabala sai gasu tare dashi sunzo gidan da yar jakarshi bayan sun gaisa da ummane suka dan fita don yin sallah lokacin magariba ya kawo jiki.
Sun dawone lokacin duk munyi don ina sallah na daidai saidai murya a bayyane irin ta maza nakeyi a lokacin saida suka jira na idar malamin ke fadin da sauki lamarin don gashi har tana ibadan ta saidai inaganin kamar namijine a kanta yanzu idan kun lura da yanayin sallahta a yanzu.
Dama ya fada muna shi na mijine ai kuma sarki Abubakar ya fada don shi har lokacin mamaki yakeyi a zuciyar shi yadda yaji muryana ya canza a lokaci guda.
Jakkar dake gefen shi ya dauko ya ciro kur,anin shi tare da wani turare ya dan yayyayafa a gefen shi ya fara bissilah da sauri na daga hannu ina fadin ba sai kajaba malam.
Suratul sulaimana ko barin ja maka ya kalli littafin da nisan dake tsakanin mu ya girgiza kanshi kadan yana fadin kwarai.
Amma duk da haka barin dan ja kaji abinda Allah ya fada ya fara jawo ayah uku falon yayi shiru ana sauraren shi ya dago kallon shi nakeyi a natse .
Yace tunda kai musulmine muna son jin meya kawoka jikin boyar Allah nan kuke bata wahala haka yace wahala haram muke dai bata hutu a yanzu don ana son cuta matane.
Muyi hakane don masu son cutawan su dauka ko sunyi nasara a kantane malam yace na,am amma ai koda baku shiga jikinta ba zaku iya taimaka mata din.
Yace malam ba yau muke tare da ita ba tun ranan da aka haifeta muke tare da ita don haka idan zamu cuta matane da mun cuta mata tun lokacin.
Mahaifiyar ta bata da ganewa data gane tun a lokacin irin kukan da takeyi tana karama wanda hakan alamane wani abu zai faru dasu ai.
Ko ranan da aka kashe mahaifinta ya kasance watan azumine bamu aiwatar da komai a watan ibada saidai duk da hakan mun nuna mata alama saidai bata gane hakan ba.
Lokacin magariba a lokacin da ko wani mugu yake samun sa,anshi ke nan ya aiwatar da nufin shi a kan wani ko ya aika da sheri akn abin nufin shi.
Mun saka tayi ta kuka sosai har dare amma sam basu bar gidan basu kuma gane akwai kulli tafe a kansu ba sunyi nasaran hakane don irin sharadin bokan su ya basu a kan lalai su tun kareshi a wanan ranan .
Sauran basuje da niyar a kashe shi ba saidai a turasasashi a kan dukiyan daya tsone masu ido wanda suke ganin bashi ya dace ya mallaki wanan dukiyan ba a cikin su.
Malam yace umm,umm yana kada kai nan dai ya basu labarin komai tiryan tiryan sai lokacin da suka fara baiyana a kaina ya kare da fadin cewa yanzu duk wanda yace zai tunkareni a kwai aiki a gaban shi sosai.
Har yanzu da Nuhu ya turo danshi yazo ya illanta rayuwan Sahiba din da suka mayarda aniyar hakan a kanshi shine mafarin baiyanan su a yanzu don Nuhu shu,umine


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login