Showing 69001 words to 72000 words out of 382072 words

Chapter 24 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28329

kokadin shigowa dakin da nake din sukeyi..
Naji an turo kofan lokaci guda da yai daidai da shigowan wani dakin ke nan a lokacin nabi kofan da kallo tare da kallon wanda ya shigo dakin lokacin duk da duhun dakin nai bari inga fuskan maishi.
Why d u tie her like dis naji an fada oga u no how dis gurl be criminal stop calling her with that name aka fada a cikin tsawa naji wanda akewa fadan yace sorry oga.
Please don't cheat me sai kuma na shiga fadi da yarbanci suyi hakkuri ban masu komai ba idan ma nayi ban sani bane nayi na hada hannu a wuri daya ina basu hakkuri.
Fita naga mai fadan yayi sai dayan yabi shi a cikin daga murya nake fadin su barni inje gida kada mahaifiyata ta shiga wani hali.
Aka rufo kofan da karfi na sake fashewa da kuka mai karfi lokaci guda ina ihu duk hakan bai basu tausayi ba.
Sai can cikin dare aka kawo min abinci ban ko kalle shi ba bayan maishi ya banye min hannu yake fadin ga bandaki nan ina iya shiga nayi alwala ga kaya nan nayi sallah.
Yana fadin haka ya juya ya fita ya kulle kofan daga baya wasu hawaye masu dumi suka zobo min lokaci guda a wurin na samu na mike zaune da kyat duk jikina yayi min tsami sosai a lokacin.
Haka na samu na sauka daga gadon da kyat na shiga bandakin daya nuna min din wuri ne lafiyayye ko da ganin yadda ban dakin yake .
Bin ko ina nayi da kallo kafin na daure na dauro alwala na fito duk da naso nayi wanka amma tsoro ya hanani hakan don bansan a ida nake ba a lokaci.
Ledan dake saman gadon na bude a hankali kayane irin na hausawa sai hijab babba da nake ganin wasu matan hausa dashi a jiki a ciki.
Hijjab din kawai na dauka nasa nayi sallolin dake kaina don a gaskiya bana wasa da sallah a duk inda ya riskeni zan tsaya inyi shi don horuwa da hakan da umma tayi muna akan sallah.
Ina nan dai dakin a zaune dare yayi don alaman daya nuna hakan a nan kasa na kwanta inata faman sheshekan kuka har barci ya sace ni a hakan ban sani ba.
Sai gabanin asuba na falka naga alaman an shigo dakin lokacin ina barci don wani abincin da aka aje min gefe na duk banci ba.
Kiran sallah nadan fara jiyowa sama sama haka yasa na mike na shiga bandakin na watso ruwa a jikina a gurguje don nasan wanan lokacin wanda suka kawoni nan suna can suna barcin su a lokacin.
Hakan yasa na danyi amfani da wanan daman na watsa ruwa ko zan danji jikin nawa ya sake min a yadda nake jinshi lokacin.
Sallah nayi na idar nake ta faman tunanen yadda zanyi in kubutar da kaina har wani dabara ya fado min.
Plate din abincin nan na juye na rike a hannu na ban yarda nayi nisa dashi ba daidai kofan na tsaya lokacin da naji ana kokarin bude kofan.
Maishi yana sawo kai na daga plate na kai mai duka ya tare na samu hannun shi nayi kokarin gudu ta hanyar kusawa ta bayan shi har nakai wajen dakin na hango dogon korido ba kowa waje a lokacin.
Daga kafan da zanyi naji an jawoni an mayar a dakin da karfi ina jhu ina fadin help help somebody help me please.
Ba wanda ya leko har lokacin tsuki naji anja an fita tare da turo kofan na sake wani kuka mai cin rai.
Na dade a zaune ba wanda ya kara lekoni dakin idona nakai ga plate sin daya tarwatse a kasa da alaman na samu maishi sosai ga dukan dana kai mashi din.
Har zuwa karfe daya saura yan mintoci ba,a shigo dakin ba haka yasa na mike zuwa bandaki na dauro alwala gashi lokacin na fara jin yunwa a cikina.
Don rabona da abincin tun daren shekaran jiya da mukaci abinci da su umma kafin na kwanta koshi saida umma ta matsa min na daure naci don barcin da nake ji a lokacin.
Shine har wanan lokavin a cikina don abincin jiya da aka kawo min ya lalace ba zai ciwu ba saboda irin hadin da sukai mai.
Can naji anturo kofa an shigo su biyune wanan karon da yake akwai hasken rana a lokacin haka yasani gane fuskan maishi saida na mike ina fadin.
What have i done to you?
You kidnap me here god go punish u for dis sin u made na fada ina nuna shi da yatsan hannuna a cikin mamaki.
Common shutup ya fada a hasale yana fadin idan kina da sako gun mahaifiyar ki kiyi magana don yanzu zan tura a fada mata kina nan wurin mu, mun kama ki.
For what reason ta fada muna abinda muke son ji a wurin ta idan mun kamata an jima jin haka yasa na zube ina fadin No No mai mahaifiyana tayi maku zaku kamata.
Wayo kada ku kama min ummana bata da lafiya don Allah ku rikeni duk laifin da nayi ni nayi ba umma na ba na fada ina kuka.
Basu tsaya saurara min ba suka fice abinsu ina jin ana rufo kofan dakin da nake da makulli aka rufeni a cikin dakin.
Umma kan suna van sun shiga tashin hankali kamar zata haukace fun a daren da ban dawo gida ba lokavin dana saba dawowa.
Haka suka kwasa zuwa bus stop din unguwar inda muke shiga mota suna tambaya koda wanda ya gani a wurin tare da nuna masu photona .
Sai wani tsoho dan kamisho ne yace ya gane ni kuma yaga na shiga wata mota da ba bus ba da safe maishi yazo ya dade a gefen titi kafin can yazo nan inda suke a lokacin dana karaso wurin.
Ihu umma tasa lokaci daya tana fadin shike nan sun sace mata yarta yar aamana a nan dai umma tayi ta sake magana saida su ladi suka jata zuwa gida a cikin duhun dare.
Ranan kan, kan umma ladi ta kwana dole tana bata magana da ban baki haka suka kwana zaune hanlali tashe.
Washe gari tun safe sukai shiri suka bazama zuwa cikin gari har gidan hjy halima suka so zuwa sai basu gane gidan ba don rudewan da umma tayi sai bata gane gidan ba.
Haka suka juyo zuwa semi a nan kuma suka samu wani rabarin tashin hankali don ko gida ba, a bari sun shiga ba aka tare su da fadin wai yansanda sunzo neman umma din.
Yan sanda kuma Ladi ta tambaya sukace yansanda kuma ba masu saukin kaiba don har da sojoji suka zo da motocin su nan basu dade da wucewa ba duk sun shiga gidajen unguwan nan dazun.
Ai basu fargaba sai ganin umma ta tafi suuu kasa ta some sukayi nan kuma hankali ya kara tashi sosai.
Aka kwashi umma din zuwa cikin gida sai da kyat Allah ya farfado da ita duk hankalin ladi ya tashi ranan don ta shiga tashin hankali ba kadan ba.
Ranan dai a nan dakin mu Ladi ta kwana da umma sai sambatu take sakewa na fitan hankali a lokacin Ladi tana faman bata baki.
Jikin dai na umma yakiya shawara aka ba Ladi cewa takai umma asibiti dole haka suka shirya zuwa asibitin don a cikin sambatun umma tana fadin saida naja kunnen yarinyar nan.
Akan mutanen nan da take gani kamar son Allah da Annabi suke mata ni nasan da wata suna neman rayuwan tane kawai ga hakan.
Kinsan dan yau da rashin jin magana amma sai yar nan bata yarda da hakan ba take karbo abinda suke bata din.
Jin hakan ya karawa Ladi karfin gwiwan su tafi asibiti suga likita kada wani abu yazo ya samu umma din a yadda take kwance haka.
Sun fito yan gulman unguwa suka shiga fadin wai akan yarta budurwa take wanan haukan haka yanzu yarinyar nacan tana holewan ta ita tana nan tana hauka haka.
Yanzu ma wa zai tsaya wanan haukan kan yarinya ta bata idan ba gawan ta aka gani ba tana can wurin wani ya dauketa suna jin dasin su ko kuma ta hadu da yan Yahoo ta jona dasu a cikin gari.
Kowa dai da abinda yake fada akan wanan maganan a unguwar namu don halin da umma suke ciki na tashin hankali.
Ladi kan dole itace ta tsayawa umma din tunsa ba kowa ke garemu a unguwan ba daga Allah sai ita ladi din muka sani.
Suna adibitin kuma sai gasu sun sameta a can asibitin sun shiga sun fita sunga likitan da umma ke kwance asibitin nasa sun fada mashi dalilun zuwan nasu.
Sai gasu an kawo su har dakin da umma din take kwance suka duba jikin ta a haka kuma suke mata tambayoyi kan rayuwan ta take dan basu amsa sama sama.
Ganin ba zata basu hadin kaiba ne suka fito fili sukace da Umma din matukar tana son yarta ta dawo hannun ta sai ta fada masu duk wani abinda suke bukatan ji a wurin ta din.
Dole umma ta natsu jin hakan ta fara fada masu dan wani abu game da abinda suke tambayanta din da suke son sani.
Shi da kanshi ya nemi sauyin asibiti ga umma din ya sa aka kaita wani mai tsada wanda yafi wanan din da take kwance a lokacin.
Sai abin kuma yabawa umma mamaki a karshe don yadda ake kula da ita gashi ance sai idan ta kwantar da hankali za a kawo mata yarta.
Dole umma ta daure tana shan magani yadda ya kamata a lokacin don dai kawai na dawo gareta gashi har dan sanda aka aje a kofan dakin da take ciki kamar wata mai laifi babba can da aka tsare.
Ko wata matar babban dan sanda ko soja a cikin kasan nan don irin yadda ake nuna mata a lokacin.
Yayin da ni kuma na rame na koma kamar wata zarara a dakin da aka kullemi din duk da bamu da gata sai na Allah amma sai gashi Allah yasa mun samu kulla daga masu farautan mu din a yanzu da bamu san dalilim halan da ake muna ba.
Hankalin shi kwance kuma duk yasan abinda ke faruwa damu din daga umma dake asibiti a kwance har ni dake rufe a wani dakin cikin hotel din da ban sani ba.
Umma ta samu sallama don haka suka koma gidan Ladi inda muke da zama a cikin damuwa har lokacin zuciyar ta yake,
Hankalin shi kwamce ya gama duk wani shiri da zaiyi ban tsaya jiran wani zance ba sai zancen zuwa gidan da zaiyi gobe din.
Kuma da wanan yarinyar zai tafi aje a yita su kare a wuce wurin idan sunje zaiyi duk abinda ya kamata ace anyi akan zancen yaran nan a yanzu.
Ya fahinci cewa ita kanta umma akwai wani boyayyen sirin da take boyewa wanda bata son wani yasani a yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA, , , , , , , , ,

2️⃣1️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , ,

BISSOMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL AZIZ, , , , , , , , , , ,

PAID ONLINE NOVEL DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA YAR UWA KADA KI DAUKI HAKKIN KOWA A KANKI, , , ,

Umma kan abin duniya ya isheta yakai mata inda yakai don bata taba tsamanin za,a iya gano su din ba da sauri haka sai lokacin da yaranta suka isa idan girma ya kawo masu zata kwashesu su koma gida.
A cikin wanan jimamin na umma ne kuma washegarin dawowan su gida daga asibiti sai kuma ga mota da jiniya har kofan gidan.
Kai bayerabe bai iya samun abu ba a rayuwan shi don su basu raina abin gulma gashi kuma ko banza umma ta kasance ba yar kabilan su bace ita.
Din wurin namu Ajata sunfi yawa wa yanda akewa kirari da (eleyele) ma,ana farar tatabara da harshen su na yaroba ke nan.
Hakan yasa basu tsayawa umma din ba saidai su taru suna kallon abinda ke faruwa idan sun watse su samu abin gulma gun hausawa.
Yauma suna jin motan ta tsaya a kofan dan gidan namu na icen bamboo tree sukayo wurin caaa suna kallo.
Shugaban tawagan ya fito ya shiga wurin umma sun dan dade tare suna ganawa duk lokacin yan gulman na wurin tsaye sai kara yawa da sukeyi a wurin kowa da irin karyan da yakeyi a lokacin.
Acan cikin gidan kuma ummace da Ladi a dakin bayan sun gaisa yana bin ko ina na dakin namu da kallo a cikin tausayi da jimamen yanayin rayuwan da muke ciki a gidan yake fadin a ranshi koda ya kasance basu bane nake nema din.
Wa yan nan mutane abin tamakawane matukar ba harkan banza sukeyi a garin nan ba son yawancin hausawa abinda suke bata rayuwan su dashi ke nan idan sun bar gida.
Sai gashi kafin yai magana ya fara tsuntar wani abu ga bakin ladi dake ffadin mairo ki fada mai koda ya kasance bakr din duke nema ba.
Don ki ceto rayuwan yar ki daga ukuban nan da kuke ciki keda diyan don Allah ya gani yau kusan shekara goma sha da zuwan ku garin nan baki cikin kwanciyan hankali daga ke har yaran ki.
Don ma Allah yayiki natsatsa daga ke har yaran kin kama kanki da mutuncinki Allah kuma ya tsaya maku yana duban ku tunda baku raina mashi ga dan abin da kuke samu ga rayuwa ba.
Wahalan ya isa haka mairo Allah shike kashewa yana rayawa ba wani ba har idan Allah ya kadara rayuwan ki dana diyan ki a hannun yan uwan mahaifinsu yake ko nan ida kuke sai sun biyo ku sun kashe ku din.
Wanan kalamin yasa ya dago kai ya kalli Ladi din dake magana yaga tsohuwar yar barikice ita rikakka da ita don tsoro ya mutu a idon ta ko a yanzu.
Kai ya mayar wurin umma din dake duke ya dan saci kallon ta hjy maryam ya fada a zuciyar shi da sauri ya tunota ya gano ko wacece ita din a yanzu duk da wahala da girma yasa a yanzu kamanim ta yadan sauya sosai bisa ga yadda yasanta din.
Ga mamakin ta taji yace babba maryam wai dama kece din kuma kuna raye yan uwa suka shiga halin kuncin rashin ku a kusa daku , ?
Itama umma din kai ta dago tana kallon shi da alama har lokavin bata gane ko waye a gabanta ba har lokacin don koda ta barsu bawai ta wani sanshi bane sosai a lokacin.
Itama kai ta dago tana kallon shi don jin yakira sunan ta kamar yadda yawancin yan gidan suke kiranta da wanan sunan .
Duk da kasancewan ta karama sa,an yaran don da wa yandama suka haifeta a cikin su amma darajan kanin mahaifan su tace suke kiranta da wanan sunan a ko ina.
Bam, , shedakaba ta furta kafin tace dashi kuma dan wajen yaya DCP ko yace nice baabba.
Tace da kama nayi amfani na ganeka amma badon na sheda ka na gane ka ba ya dan murmusa ya gyara zaman shi tare da fadin.
Baabba me yasa kika guji gida kika dawo wanan wurin nisa da yan uwa kika zauna anan cikin kunci haka ga talauci da gatan ki baabba?
Har yau gidan ku na nan ba kowa a cikin sa kamar yadda kuka tafi kuka barshi ba wanda ya taba ko tsunke a gidan kullun ana duban zaku dawo ko wani lokaci.
Kaiya dawowan mu ai yana da wuya a wanan gidan sai dai wani ikon Allah dai kuma idan Allah ya nufi komawan mu gida ta fada a cikin hawayen daya gama wanke mata fuska ko a lokacin.
Wani irin ba dadi yaji har cikin ranshi don a matsayin shi na jami,in tsaro ga maganan umma din ya gane akwai wani abinda ta sani na boye da kowa bai gane dalilin gudun nata ba daga gida.
Umma din tace dashi ya wajen mahaifana ko sun saura a raye yanzu ko suna wani hali.
Kai ya dukar kasa don baisan amsan da zai bata ba a lokacin sai cewa da yayi duk kowa yana lafiya baabba.
Sai dau yau gaskiya ba zan kara barin ku kwana a cikin wurin nan ba zamu tafi daku can inda nake in yaso idan kun huta sai muyi magana don naga har yanzu akwai sauran damuwa a tare daku.
Amar dake gefen umma din a tsorace yace cikin yarbanci umma tsoron wanan nake ji sosai ya kallo yaron da yai magana yana fadin ya kake abokina yana mika masa hannu Amar din ya make yana labewa bayan umma din.
Ladi dai ido ta zuba masu cike


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login