Showing 252001 words to 255000 words out of 382072 words
yasan komai dake gudana ba shiya yai shiru yaki magana da kowa kan wanan zancen a yanzu.
Saidai ai sauki abin dai da hannun mutum.aka aiwatar da komai don haka ba wani hujja da mutum zai kawo a yanzu yace shi ya tsame kanshi yanzu.
Murmushin daddy yayi don jin wanan kalamin na Alh Bello babban aboki kuma aminin Alh nuhu tun na kurciya dashi kuma aka shirya komai a lokanlcin har zuwa yanzun da ake fadin wai sun dawo din.
Kwarai yasan da sanin hakan zai faru muddin suna raye suka baiyana sai dai tun a lokacin shi jami,ine dayasan kan aiki shi tun lokacin kuma ya shiryawa zuwan wanan ranan.
Kwana hudu a Dubai banga giccin Oga Sir Shaaban ga idona ba tun zuwan mu kasan saidai dadin kan muna samu shi har nake tunanen wai dagaske ko hutun da yace din mukazo yi ke nan ashe ?
Kai gaskiya idan kana dashi dai ka huta a rayuwan ka don bakajin kyashi ko zafin yiwa wani na kasa dakai idan Allah ya horema zuciyar alheri don irin wanan halin dace ne.
A rana ta biyar ne a garin don munsha hutu har mun fara jin zaman dakin ya fara isar mu don bama komai daga kallo sai charting ko karatu.
Sai hakan yai min dadi nikan don wanan wasan kwaikwayon da Oga keyi dani gun mahaifiyar su shi da nasan yana matukar biyayya gun mahaifiyar shi.
Don duk abinda zai mata wanda zai bata mata zuciya nasan baya so a dan zaman da nayi dasu a gidan su lokacin bukin tunawa da mutuwar mahaifin su.
Amma yanzu na rasa ko meye dalilin shi nayi mata hakan ga wanan hadin da Alaja din keson yi a tsakanin shi da yar aminiyar ta yanzu.
Yanzu kuma da Alaja bata tare damu bai kara nemana da nuna irin kulawan da yakan nuna min agabata din yanzu ko ina cikin dakin da aka sauke mu din ina tsabgan gabana.
A haka muka samu sako kan cewa mu shirya zamu shiga cikin gari muga yanayin gari da tsarin sa.
A zuciyana nace wani garin zan gani a yanzu makka kawai ya rage naje gani tunda naga england da ban taba zaton zuwan shi ba a wanan lokacin yanzu saurana makkan kuma.
Sai dai ina fatan umma ta fara zuwa kafin ni shine nake kokarin tara kudi a yanzu in kaita ga dan abinda muke samu daga aikina da kuma shagon mu insha Allahu shine burina kawai a yanzu gaskiya.
Don ni babu zancen soyayya ko wani mu,amula da wani da zai dauke min hankali balle ma ban taba bada fuskan da wani namiji zaizo ya nuna min soyayya ba sai wanan karon da muka nuna hakan da Ogana hakan kuma sai yake min bambarakwai don rashin sabo da hakan.
Haka muka shirya don fitan a daidai lokacin da suka aje muna time din fitan kafin lokacin kowan mu ya shirya don fitan da zamuyi din.
Sai a wanan lokacin ne kuma na sanya Oga a idanuna tun ranan da mukazo da ban kara ji ko ganin shi ba ko inji wani abu gareshi ba.
Yana tsaye a haraban wurin da wasu yan kabilan chana suna magana muka fito zuwa wurin motocin da zamuyi amfani dasu bisa jagorancin felix da ya fito damu zuwa wurin.
Gaidashi muka fara yi a cikin ladabi bayan ya iso inda muke ya fara umartan Felix da ya kula damu tare kuma yi muna bayanin cewa zamu dan shiga garin mu zaga muga gari muga yadda al,amura kasan ke tafiya a nan din.
Duk wanan bayanin da yakeyi kaina na kasa ina kallon wayana da nake charting da ya Abubakar a lokacin don haka ban yarda mun hada ido dashi ba.
Yayin da duk second shi sai ya dago ido ya kallo inda nake tsaye ina saurarenshi a lokacin da yake bayanin nasa har dai ya kaiga kiran sunana yana tambayan ina ko tare dasu ?
Sai lokacin na dan dago kai ina fadin yes Sir a gajarce har muka dauki hanya zuwa wuraren daya fada zamu kai ziyara din shi felix ya saba zuwa don kusan shida oga din akwai dan dangantaka saboda mahaifin felix din shine babban yaron mahaifin Ogan mu a lokacin da yake raye .
Yanzu ko mahaifin Felix din ya tsufa sosai shima ya koma kasan su na igbo a kauyen su da zama .
Wanan yasa yanzu shi kuma yajowo Felix din suna harkokin su a tare don yaci gaba da tallafawa rayuwan ahalin nasu Felix din.
Don haka kusan shi felix din yasan komai akan ogan namu saidai baya zama can Labeno a tare dasu yana zama a gida Nigeria ne sai in bukatan tafiya waje ya taso yaje.
Shine dalilin zaman Felix din na hannun daman shi sosai kamar yadda shima oga Jimoh suka hada halaka tun na kurciya idan sunzo Nigeria duk da Jimoh ya girmeshi amma suna tare koda yaushe dashi kasancewan su makwabtane a lokacin suna yara.
Shine abokin shi nakusa a nan Nigeria bai kuma manta dasu ba har wanan lokacin da suke komai a yanzu yana zaune tare dashi a karkashin shi.
Saida muka dawone daga fitan da mukayi nasan Alaja da Ganiyat sun iso Dubai din don ganin su tare da mukayi a haraban hotel din muka hade dasu sun fito shan iska.
Nan dai aka shiga gaisawa dasu ana masu bangajiyan taro da muka barsu sunayi a can tare da bakin ta data gayyato a bangaren ta.
Kamar yadda ta hade rai muna hada ido nima hakan na hade nawa a lokacin sai Ganiyat din ne ke fadin Oni wan kweb wa !
Tani ? yemisi ta fada tana kallon ta don son jin wanda yake magana dashi din a cikin mu don kanshi yana duke baka dauka ma yayi wani magana a lokacin.
Tace boda me wan kwebwa Sayiba na dago na dan saci satan kallon shi a inda yake tsaye a cikin fararen kaya irin na yan, kasan Pakistan
kayan su mashi matukar kyau sosai a jikin shi.
Yemisi ta dan zungureni tana fadin ke ake kira nace no ke dai amma ai yasan ba zanzo ba wanan wurin ga uwar Alaja a tsaye yadda ta saka min ido haka.
Ganin ko gezau banyi ba daga inda muke din yasa shi ya dan tako zuwa inda muke din tsaye zaikai tako biyu zuwa uku tsakanin mu dasu tun bayan gaisawan mu da Alajan .
Sai dai ina mamakin rashin ganin mutanen ta da sukazo mata ma,ana abokan tafiyan mu wata kila sun komane daga england su, sun juya zuwa Nigeria.
Kara gaida shi mukayi daya karaso wurin da muke din ya amsa a cikin sakin fuska yana fadin.
A kwai meeting da zamuyi a nan gobe karfe goma na safe ki tabbatar da kun shirya ke da Ad,nan da Jimoh nake bukatan muje tare don akwai abubuwa masu muhinmanci da zaku sani.
Allah ya kaimu goben lafiya na fada a cikin girmamawa daga hakan ya dan yi magana da yemisi kafin ya juya ya bar wurin.
Ajiyan zuciya na sauke tare da bin bayan shi da kallo na juyo ina kallon yemisi da niyar fadin mu shiga ciki sai na samu itama shi din take bi da kallo.
Tafiya na farayi ganin haka ta biyo bayana da sauri muka shige ciki a nan muka bar sauran suna magana da Alaja da su jimoh.
Kowa a falon yayi shiru yana sauraren abinda da daddy din ke fadi bayan ya gama sauraren shima inda ya soma da fadin yana kallon fuskunan su a daure yace.
Da ace kusan kowaye wanan yarinyar da kuke zancen ta haka a kanta da ko wanen ku a nan ya kama kanshi a yanzu ko kuma dai ya dawo mata da duk abinsu daya karba a baya.
Ko kuma mutum ya tozarta a idon jama,a kamar dai yadda ta soma maku a yanzu kan dukiyan wani hakan kuma zatayi a kan nata koma fiye da hakan.
Au kai zaga zugota ke nan tazo taci muna mutunci ashe idan ba haka ba har ina zata ji abinda ya faru a baya waye zai bata shedan wani abin da sai mu kadai muka san yadda ya faru ko kai daka shigo daga baya baka san yadda abubuwa suka kaaance ba a lokacin don gudun irin hakan muka rufe maka gaskiyan zancen.
Murmushi yayi wanan karon ya mike yana fadi ni zan barku saidai shawarana shine kowa ya hado masu dukiyan su baki alaikum mu basu.
Ba za a bayar ba Alh Nuhu ya fada a fusace yau kaci arzikin abu daya a wurin nan da ba haka ba da fita wurin nan gareka yau sai Allah .
Nasa zaka iya saidai ku sani mutum baya mutuwa idan kwanan shi bai kare ba koshi wanda muke zance akan iyalin shi yanzu kwanan sa ne suka kare a lokaci.
Don haka ni dai yau ashirye nake a duk lokacin da suka bukaci komai nasu in basu don dama ba karba nayi don naci ni kaina ba.
Ni na barku lafiya ya fada yana juyawa karya kake wallahi kayi kadan kace zaka juya muna baya a yanzu wanan ba mai yuyuwa bane a wurin ka yanzu don ya zama dole kamar yadda muka rufe komai a baya mukayi shi tare yanzun ma hakan zaka nuna baka san komai ba a wanan zancen.
Murmushi yayi ya gyada kai kafin ya juya yana tafiya tare da godewa Allah da yabi shawaran da zuciyar shi ta bashi kan yaje da security din shi.
Da Allah kadai yasan yadda zasu kwashe dashi a wurin nan tunda ba imanine dasu ba don su sam basu tunanen sun girma yanzu su koma ga Allah.
Ido ya lumshe yana tunanen wautan daya tanka a baya duk dama dai yasan yayi hakan ne da wani manufa wanda suma basu san da hakan ba.
Gidan sa ya nufa kai tsaye sai dai suna shiga get din gidan nasane ya hango hjy karima ta fito daga cikin gidan da sauri tana kokarin shiga motar ta sai gashi.
Kallon ta yakeyi a cikin mamaki inda zata fita haka hankali tashe bata fada mai ba itama din ganin shi ya dawo yasa ta dakata daga kokarin shiga motarta da takeyi.
Ta dagakata har motar nasa ya tsaya ta karaso wurin da yake fitowa daga cikin motan ta sameshi ya daure fuska lokaci guda tare da tambayan ta ina zaki haka yanzu kuma ?
Alh ba lafiya fa baby ce ta bugo min waya yanzu a cikin tashin hankali wai yaron nan yayi mata tsinanen duka ko tashi bata iyayi.
Kallon ta yayi cikin mamaki sai kuma ya fara takawa don ya bar wurin ja yayi ya tsaya yana kallonta yace sai ke kuma zaki tafi yin me gidan nasu yanzu ?
Ah zuwa zanyi muyita dashi wallahi tunda tace yanan gida yanzu zanje in sameshi in nuna mai karyan iskanci yakeyi shi.
Ki sameshi fa kikace ke da kanki karima keda kanki zaki fada gidan suruki haka idan kinje kice masa me to
?
Kallon mamaki itama tayiwa mijin nata tace in fada mai duk anin da yayi min dadi a cikin wani irin haushinta da takaici yace ke da dan karfi ta juyo yace koma gida.
Yanzun ne baida hankali ko mashayi ai kaqai ku koma ko kin manta da kikace kunyi bincike kun gano duk sheri akai mai kawai.
Kuyi gakkuri din Allah sai a hankali wallah
ANA DARA GA , , , , , , , ,
7️⃣5️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MU,MIT , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
A ranan nasan anci gaba sosai a hanyar kasuwanci son komai yanzu a zamanance akeyi shi kamar yadda muke dan kwatantawa dai a Nageria saidai gaskiya a can su kan aun muna fincin kau ma,ana an barmu a baya dai.
Mun fito dakin taron na karaw juna ilimi a cikin farin ciki da kwanciyan hankali sai faman binsu a baya nakeyi duk jikina ya mutu da abinda na gani .
Sai yaushe mu Nigeria zamuci gaba koda rabin haka abinda nayi ta tunane ke nan har muka fito gashi wurin dai matasa ne masu dan matsakaicin shekaru don tsofi daga ciki basu da yawa sosai.
Waya na hngoshi yanayi can dan nisa damu sosai kafin ya tako zuwa inda muke tsaye din suka fara magana da jimoh a cikin yarbancin da idan yanayi zakace wani yaren yakeyi ba yaroba ba.
Adanan ne yayi magana daga bayana yasa na juyo ona kallon shi yake fadin ya dai yan mata kingani tun a ciki nake ganin alaman hakan a tare dake.
No ba komai tunanen gida kawai nakeyi don ban taba tafiya ba irin haka ba tare da mahaifiyana ba.
Suma din basu taba zuwa wani wuri nisa dani ba sai wanan karon nan dai ya dan taba min hira har na sake muna wurin har suka kare tataunawan da sukeyi suka tako a tare inda muke tsaye nidashi.
Sun karaso boda jimo ke fadin yawa Adnan sai kazo mu tafi tare dakai ita Sahiba zata wuce tare da Oga daga nan zasu wuce wani waje suyi signing.
Sam ban kawo komai a raina ba tunda aiki muka fito a lokacin dukkan mu baya muka shiga don naso shiga gaba tare da driver da zai jamu ya dan daka min tsawa a cikin yarbanci da kada in bashi kunya mana wanan fa driver ne aikin sa yakeyi.
Dole na dawo baya tun zaman a motan ban dago kaina na kalli inda yake zaunw din ba shi ga kuma motan a hankali yake tafiya saman lafuyayyen titin dake shimfida a kasa ko ina na garin tsab yake sukan gaskiya sunci gaba ga komai na zamani sosai sun barmu a baya.
Eh mun je wani waje muyi signing ashe kayan da za,a shigo mai dasu wa yan nan company din da mukayi aikine a kaduna da kano zai kara farfado da wurin kuma sosai har yafi da can baya dayayi shi.
Daga nan zuwa karfe hudu da rabi muka bar wajen duk da agajeye muke hakan baisa mun nufi masauki ba don a kasalance naji yana fadawa driver inda zai kaimu kuma.
Kai Dubai kan taci gaba wani irin kantine na sayar da kaya tufafi da sauran abubuwa muka ziyarta tare dashi a zatona na dauka nan ma wani abin yazo yi sai da muka shigane na gane ba komai yazo yi ba a wurin don abinda naji yana fada da muka shiga ciki.
Zaki iya yin tsaraban komai da kike so a nan don ba lalai bane ki kara shigowa wanan wuri nasan ba zasu iya shigowa nan dake ba indan kun fito tare.
Na rasa me zan fada mai a lokacin don lissafi ya kwance min ba zan iya yin komai ba don kaina lokacin naji ya kara fadin har mama da brother din ki ki saya masu kayan wurin nan zaifi.
Tsaye nayi kawai ina kallon shi ban iya cewa dashi komai ba OK idan baki san me zaki dauka ba muje na tayaki kada mu bata lokaci don gobe nake son in bar kasan nan zuwa Cairo.
Lokacin ne na iya dago kai na kalleshi ido da ido ina mamakin jin abinda ya fada ke nan har mu zamu bar kasan ke nan yake nufi ko me oho ?
Kamar yasan me nake tunane naga ya fara tafiya yana fadin gobe zan koma Cairo zan barku a nan ku karasa hutun ku ranan tuesday zaku koma Nigeria.
A daidai lokacin da ya isa wurin kayan maza yake wanan maganan nan ya fara duba saidai hankalina baikai kan irin da naga yana zaba ba a wurin.
Yana jefawa cikin wani dan keken da muka sama a gefen wurin sai jidan kayan yakeyi kafin ya tura kekan zuwa wani bangare kuma da alama dai yasan kan shagon sosai nake gani.
Ina biye dashi a baya kamar zonbi da wata da muka sama wajen ma,aikaciyar wurin yake magana ta dan juyo ta kalle ni kafin ta fara zabo kaya tana jefawa a cikin basket din muna binta a baya can dai takai ga daga wani tana gwada tsayin shi a jikina saidai bana jin yaren da takeyine.
Wani irin mahaukacin sayayya yayi a wurin abin har ya ban tsoro amma kuma sai nasa a zuciyana cewa wanda zamu kara zubawa a shagon mune na lagos lokacin.
Don haka naye tsaye duk inda mukaje ina binshi a baya har muka kusan gamawa sai riga daya na iya zaba a wurin saboda tsadan kayan dana gani a