Showing 192001 words to 195000 words out of 382072 words
hudu plat dai irin na zaman family din nan ginan shi maikyau an saka gadaje da kayan kitchen a ko wani gidan bamu da matsalan komai da zaman nan.
Su Felix da jimo Adnan da Abdulhamid ne suka fara fita don ranan ni na tashi da ciwon kai ban fita ba ita kuma yemisi wai ta kwana gudawa.
Zuwan su tare da gabatar da kansu a sabbin ma,aikata ya dan kawo tsegumi a wurin sosai hakan ya kawo cecekuce wai ya kwaso yarbawa daga kudu yanzu su zasuyi aiki a wurin kuma.
A yadda suka dawo suna bamu labari komai na wurin ance ba tsaro mai karfi kamar yadda ya fada masu wurn ya samu matsala.
Kwana biyu suna fita ga rana na ukune na samu fita duk da naso makaran fita din haka na shirya na daure na fita a cikin motan da sai ranan na fara shigan shi tunda aka ajemin shi a kofan gidan.
Jikina yana saye da buje da rigan les pink maidan ado da blue din filawa sai gyalen dana saba saman kafada na da jakka shige da kayan.
Kayan sun kara fito min da kyauna a fili sosai tun shigowana nake bin ko ina da kallo a wirin a daidai inda naga motar Adnan na parker nawa motan na fito.
Na dan tsaya nayi nazarin wurin sosai sai hakan ya dawo da hankalin ma,aikatan dake waje a haraban wajen tafiya nakeyi a hankali ina waya da adnan dake min kwatancem wurin da zan samesu idan na shigo.
Duk wanda na wuce ina jin abinda suke fada game dani wanan itama din tare da sabbin oganin take kai wanan yarinyar karama haka ?
Kila dai ire iren yan matan su salman ne da suke daukowa aikun saba da ganin irin su a nan suna sintiri wani ke fadi.
Na wuce kamar banji su ba saidai maganan ya tsaya min a raina lalai dole mu saka ido ga irin wa yam nan da suke maganan su din.
Ina kaiwa tsakiyan wurin naja na tsaya wuri daya ina duban ta inda zaifito min sai gashi ya fito a sani dan karamin lungu yana min sannu da zuwa tare da nuna min hanya yana gaba ina binsa a baya na samesu a office din da suke ciki.
Har gida taje takaiwa yayan nata dogon list din da uwar nata ta zauna ta tsara matashi waiduk abubuwan da takw bukatane duk.
Duk daya gane sai ya karba yana fadin wai yan mata duk wanan ke kadai ke dashi da fatan dai kina iya amfani dasu bana son zancen daukan yar aiki ki zage kiyiwa mijin ki bauta ki samu ladan aure zaifi maki.
Ta dan yi murmushi na yarinta tana kawar da kanta gefe daya tana dan jin kunyan abinda ya fada mata din mika mata takardan yayi yana fadin ki rike wanan a wurin ki ki fadawa anty saina shigo mu zauna da ita.
Duk abinda suke fada Nazifa na jin su don tayu masu zaune a wurin taki dagawa tana son taji meya lawota wurin dan uwan nata.
Mata a kula a dan dagawa maigida kafa a duk lokacin da yake ganawa da yan uwanshi na jini ko aminan shi irin wanan zaman da kikeyi yana ja maki bakin jini a wurin al,umma haka kuma yana hana maigida yayi alheri wa masu bukata idan yana kallo idanun ki don wata kila kin rokeshi bai samu baki ba har wani ya kawo nasa bukatan a lokacin daya dace ya bayar.
Yar uwa kada ki zamo cilin silar hana alheri ki kasance mai karfafa kafan a yi zumunta don ki tashi da hasken hakan a goshin ki ranan gobe kiyama ubangiji Allah yasa mu dace amin.
Nazifa bata so hakan ba duk data dan dauki haske amma kuma rashin ganewa ya hanata fahintan komai a lokacin.
Itama hjy karima tana gida tana Allah Allah yar nata ta dawo taji yadda sukayi da yayan nata a lokacin.
Bayan baby Summay ta gama labarta wa uwar sai cewa hjy karima din tayi burgan banza dama ai nasan ba zai iya bamu abin kwarai ba don wanan munafukan uwar nasu bata bari yayi alheri ko kadan dama ta kara jan tsuki tana fadin aikin banza da wofi idan ma sirina suke son ji basu taba gane hakan wallahi.
Zato zunubi koda ya zama gaskiya da yamma sai gashi gidan direct part din ta ya nufa kuma Amira taga shigowan shi itake fadin ga yayan mu nan yazo.
Fatima na fadin tare da yaran sa ne yazo Amira tace ban tsaya ba ina shigowa na ganshi basu gama magana ba sai jin sallaman shi a kofan su sukaji.
Ya zauna an gaisa yake fadin anty baby ta sameni dazun a gida ta kawo min list din yanzu ga wanan sai ayi hakkuri dashi.
Nan hjy karima ta fara fadin kai modibbo wanan kanwar taka ta azama lalura haka har ka biye mata kai kuma.
Dan shafan fuskan shi yayi yana fadin hakan ai shine daidai anty ku godewa Allah daya nuna maku hakan kuna tare damu addu,an kune ke aiki a kanmu .
Wani iri taji tana kai idon ta kan takardan daya basu din saida ta dago kai da sauri tana fadin anya modibbo kudin nan basuyi yawa ba haka ya mike yana fadin bakomai anty kayan gado dai da sauran su nayi magana da Fatima ventures zasu shigo da kayan da komai na sakawa a daki a haka mata su sai a duba dakuna nawane a gidan yanzu don sun tambayeni hakan .
Shiru hjy karima tayi gaba daya jikinta ya gama mutuwa da bayanin ta sai ji tayi yana fadin na barku lafiya anty ya mike ya fita yana kadawa baby din data dago tana kallon shi hannu ya fice.
Yana fita yaran sukayo kan uwar suna fadin mama nawa yabadane mu gani summaya din ta fisge takardan a hannun ta.
Ihu ta sake tana fadin mama miliyon biyu fa ya bada tace bari kedai baby aini na kasa magana wallahi don na rasa mezan ce ga baban kunan muna kai ruwa rana dashi kan dan abinda na bukata.
Ashe yaron nan yana da kudi hakane Allah sarki mama har kina zagin sa dazin gashi ya baku abinda bakiyi tsamanin samun a wurin sa ba fatima ta fada daga gefen su inda take kwance saman kujera.
Harara uwar ta watsa mata tana fadin kaji yar baki na zageshi din duk cikin hakkin mune wanan din yaji dadin mahaifin ku cikin ku kamar shi ?
A wani matsayi kuke yanzu a nan din tambayan dana jefo masu ke nan bayan na zauna na dan bi office din da aka ajesu din da kallo.
Adnan ne ya dago kai yana fadin a cikin dariya ai shine muma har yau bamu gane ba madam don munyi tambaya bamu gane komai a nan din ba.
Ba gaskiya bane na fada ina mikewa a nuna min office din manage din yanzu na fada ina barin kujera.
Sahiba kibi wanan zancen a sannu don mutanen nan basu da kyau wallahi na fahinci hakan tun jiya da muka fara tambayan su Abdulhamid ya fada.
Ai ban tsaya sauraren shi ba nasa kai na fito daga office din ina bin rubutun office din da kallo.
Idona ya kai gana manager din ban tsaya jiran komai ba na nufi kofan zan shiga da sauri dan tsohon dake zaune a kofan ya taso yana fadin .
Hjy ina zaki ba a ban ikon barin kowa ya shiga a wanan lokacin ba don manya ke ciki suna meeting na dan kalloshi na sake mai murmushi komey ya gani oho naga ya jaye min da sauri na shiga ya biyoni a baya.
Jin an bude kofan an shigo yasa gaba dayan su su wurin goma suka juyo suna kallon wanda ya shigo office din.
Binsu nayi da kallo daya bayan daya har nakai kan manager din na tsaya a hankali na tako baka jin komai a lokacin sai karan takalmana dake fitar da sauti.
Good morning manager ya dan amsa min da sauri sauri files din dake gaban shi na kalla ina fadin zamu fara aiki akan wa yan nan now now.
Da niyar wullakanci ya dago ya fada min magana ko me ya gani kuma sai ya kasa baba kazo ka taimaka min mu kwasa zuwa office din da aka bamu muyi aiki a cikin sa.
Ina kallon tsohon nake magana shima dai ni yake kallo kamar kowa sai kuma na koma fadin zamuyi aikin da wasu daga cikin ku zasu taimaka muna .
Af kuyi hakkuri fa ban gabatar maku da kaina ba nazo na fara aiki kai tsaye kada ku damu don haka nake ni ban wasa kan abinda ya kawoni a wuri.
Kwana biyun nan ban fito ba saboda dan gajiya daya dameni sunana miss Sahiba daga lagos na fada tare da rokon su su yi hakkuri da shigowan da nayi masu kai tsaye.
Zamu iya daukan files din kun gama dasu na juya ina tambayan shi tare da kallon shi na tsure shi da ido OK zan baku minti talatin a kawo muna muna jira na juya na fara tafiya suka bini da kallo.
Har nakai kofa na juyo ina fadin saidai kada ka manta ka fito da wayan nan da kuka boye kai dashi na nuna mai dayan mutumin.
Daga haka nasa kai na fita shiru office din ya kara daukan kafin manaja ya cire hullar kanshi yana fifita dashi a kanshi da fuskan shi.
Yau naga shu,umar ya lalai mutanen nan basu zo muna da wasa ba a wurin nan saida suka shiryo muna amma barsu in sun san wata ai basu san wata ba.
Kafin su rike baki na turo kofan kai dakai dakai a tare zamuyi aikin daku sai ku samemu da files din muna jiran ku yanzu.
Wacece ita din wai wani dan kyamusasshe a cikin sune ya tambaya a cikin hausa azaton ba maijin ko zo in kashe ka acikin mu kaf, wa,iyazu billahi wanan mutumin ta nan ya biyo muna kuma yanzu ban taba kawo hakan ba wallahi ?
Suyi duk abinda zasuyi mana kudi daine sun shige bamu san inda suka shiga shike nan mana fakat .
Dayan su ya fada yana wani ware hannayen shi na dan sake murmushi daga inda nake tsaye din yaci gaba da fadin zai dauko muna kafirai suzo fitgita mu kome ?
Alhassan kabi maganan nan sannu don Allah kai ka cika danye kai kada abin nan ya dawo ya juye damu fa kana magana haka.
Ta kwabe din mana wake tsorin hakan yanzu duk iya binciken su dai ba zasu taba gano kudin nan ba tunda ba a hannun mutum daya suke ba yakarsa fadi a hasale na dan saci kallon shi da wutsiyat ido.
Kai manager din ya fada har lokacin yana fitara da hular kanshi yana fadin su Alh dai yanzu ai dole mu nemosu su sanda zancen nan gaskiya.
Office din na koma ban zauna ba sai bin ko ina na office din nayi da kallo suma abokan aikin nawa kallona sukeyi ba wanda yai min magana a cikin su.
Widow officen kawai nake kallon haraban wajen a tsaye kafin muji an turo kofan office din an shigo wa yan nan mutanen dana nuna ne su ukku dauke da takardun company a hannsu su.
Kallona abokan aikina suka fara yi kafin su shigo suna gaisawa dasu na nuna masu table din akan su zauna saidai kuma wurin ba zai ishe mu ba dole mu koma babban hall din taron cikin wurin da aikin mu na fada yes madam Adnan ya kara fada suma suka bini da kallon mamaki.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
5️⃣7️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUJIB, , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋
Sallama yayi ya shigo part din mommy ce ta amsa take fadin a, a ina kuma ka tsaya ai na dauka ka tafine don yaran sun fada min kazo tundazun na dauka Alh kazo gani bai nan ka tafi.
Ban tafi ba dama baby ce nazo gani ina part din anty ne tundazun din da sauri mommy tace me kuma ya kawoka wurin baby da uwarta ?
Yana kaiwa zaune saman kujera yake fadin akan sha,anin bukintane don dazun ta sameni gida nace tazo zanzo na ganta shine yanzu nazo.
Wani kallo uwar har yan uwanshi ke masa yace ba wani abu bane dai nine nace tayo min list don abinda take so shine ta kai min daga haka yaja bakin shi yai shiru bai kara magana ba kuma.
Idon ta kara zuba mai tana fadin ka fitar da kanka cikin zancem nan don koni uwarka ba,a saka a cikin shi ba banga dalilin da kai zaka wani zake ba haka ?
Ta manta cewa nima idan Allah ya kawo lokacin gani dasu har uku a gaba dama tayi hakanne don kawai ta kumsa min bakin ciki take tunane .
Ta nuna yaran nan basu da farin jini gashi har yarta ta isa aure ta samu manemi su suna zaune a gida shine kawai sai kuma dan kudin da yaron ke nuna masu yana dashi yanzu kuma.
Haba mommy ki daina damuwa da irim kananan maganganun nan don Allah suma din ai lokacine baiyi ba idan lokacin yayi yi zasuyi ai.
Yana fadin haka ya mike yana fadin zan koma mommy sai dai gobe in Allah ya kaimu don zan tafi abuja din a goben nan idan Allah ya yarda.
Ya kara mata sallama ya fita ba tare da ya fadi abinda yazoyi wirin su hjy katima dinba yana fita Nabila tace aiso nayi mommy ki tambaye shi muji ko wani abu ya basu ai.
Haba kema ai kin sani tunda kikaji ya fadi hakan aikin gama ya gama ko kwanan zakiga anfara sha,anin bukin nan gadangadan ke nan ashe hauwa ta fada daga inda take zaune.
Tsuki mommy tayi tare da fadin koma me zai basu indai wanan matarce ba zai taba haske ko ta wani so shiba indai itace.
Mommy shifa yaya ba don ta yayi ba ai kinji abinda ya fada baby din ce ta tafi wurin shi dazun ta ganshi yayine kawai don zumunci hauwa ta kara fada uwan taja wani irin tsuki tana jin wani iri a zuciyar ta.
Office din yai shiru dan dakikun mintina ba zamu zauna a yau ba don lokaci ya danja yanzu sai dai gobe idan Allah ya kaimu yanzu a samu wanda zai bude mana da addu,a bayan nan sai mu fita ga baki dayan mu zuwa cikin kafanin muga abinda mukazo zama a kanshi na fada.
Kallon kallo aka fara a tsakanin mu dasu jin abinda na fada wani daga cikinsu mai dan tsawon gemu ya fara da sallama.
Takardan dake hannuna nake karantawa har lokacin da suka shafa nima na shafa din na kallo inda felix yake nace yai muna addua ya dan kalleni ya fara.
Gaba daya muka mike muka fita wanan da yai muna addu,a shine ya jagorance mu yake nuna muna wuraren ai kafin kace me har an samu wanda yaje ya rsuguntawa manager ga abinda aka hangomu munayi a lokacin.
Don me ba zamu takawa yarinyar nan burki bane rankayadade haka kawai mu zauna karamar yarinya tazo tana kokarin juyamu muna zaune.
Nima abinda na gani ke nan ai gara mu nuna mata nan fa arewane ta shigo ba kasan su ba ita din me don Allah oga bala.
Kyautane zai rudemu ko shigarta na banza me akayi akayita ma da har take batun bude muna zani a kasuwa muna kallon ta in abin nan yayi nisa fa duk kan mu nan zai shafi kowan mune wallahi.
Shafa kai don duk masu laifi muke ai manager ya furzo iska waje daga cikin bakin shi yana fadin don me ba zamuyi wani dabara na sallon sayenta ba mu gwada mu gani idan hakan zai yuyu.
Da nawa kake ganin zamu saye ta a wuce wurin daga milliyon daya zuwa sama zamu fara kaftawa mu gani amma muddin muka bari wanan abin yai boosting wallahil azeem kowan mu nan sai ya raina kan shi cikin mu yanzu meye abin yi ke nan.
Abin yi na farko shine duk wani wanda ke da hannu a cikin harkan nan a sanar dashi ya kwana a cikin shirin kota kwana don fitana idan an san farkon shi ba a san karshen shi ba.
Tunda nake ban taba kawo sense