Showing 240001 words to 243000 words out of 382072 words

Chapter 81 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28370

a rayuwan ta wanda ba zan iya fadi ba a yanzu saidai idan kun ganta zaku gane hakan .
Kallon juna sukayi sunzo da niyar kwana garin saidai rashin samu yasa suka koma a ranan basu kwana ba a can gida kuma suke jin labarin cewa ai yarinyar da tayi karan Alh Nuhun an nemeta don ayi sulhu ba sai anje kotu ba wai tayi tafiya zuwa kasan waje bata kasan.
Baffa Abdullahine shi baffa hamza kallon juna sukayi tare da fadin kai anya ba yar nan tamu bane kuwa keda wanan aikin don yanzu haka bata kasan nan tayi tafiya itama zuwa America.
Sun tatauna sosai haka labarin ya fara tafiya ai ana ganin dai yarinya dayace tazo tana juya su Alh din haka har wanan zancen ya shiga kunnen su Nabila dake zaune falon lokacin da mommy take wayan.
America suka fada suna kallon juna ita da hauwa kafin suce wai Amerrica duk da ta samu aiki har wani girma da wani matsayine zaikaita wanan kasan.
Mutane akwai karawa zance gishiri wallahi yanzu an shiga fadin zantuka ke nan barkatai har sai ranan da gaskiya zatayi halin ta ai Nabila ta fada tana jan tsuki a fili.
Faiza dake zaune tana jin su haushi da mamakin su ya rufeta lokaci guda kasa masu magana tayi a lokacin sai mayar da hankalinta da tayi kan wayan ta sosai a lokacin.
Mun samu taro na musan man a wurin su duk da hotel ne aka sauke mu a lokacin Turkeya mun huta sosai don tunda na shiga na rama sallolin dake kaina a lokacin nabi lafiyan gadon dakin da aka saukeni a ciki.
Barci sosai nayi don har sunci abinci ogan mu ya shigo yagana dasu yayi masu bangajiya a lokacin sun gaisa dashi ya tafi.
Washe gari kuma ya dawo da rana don ba hotel daya muka sauka dashi ba shida mahaifiyar shi a wani shahararen hotel na kasan Turkish ya saukashi .
Zamu kwana biyu a garin don akwai abinda zaiyi a nan din kafin a kwasa zuwa wurin abinda ya kawomu na sister din nasa.
Karfe hudu da rabi zamu halarci wani wuri da zamu gana dashi da mahaifiyar shi lokacin zamuyi liyafa tare dasu muci dinner a tare a yadda aka tsara aka fada muna kuma .
Ba wani kwaliya nayiba na azo a ganiba, dogon rigace kawai kalan kakin soja a jikina gaban rigan yanada tsaga da filawowi zuwa gwiwan rigan sai igiyan daure shi dana daure tsakiyan kwankwasona sai dan kwalin shi a kaina saidai rigan gaskiya ba laifi don ta hadu wurin kyau dagani kasan na kashe naira a wurin sayen shi.
Muna cikin motan daya dauko mu zuwa masaukin su inda suke suna jiran mu ashe tsakanin mu da idan suka sauka din baida wani nisa sosai da inda muke.
Motar na tafiya a hankali saman titin ga ruwa daya kawata garin hakan nake bin garin da kallo ga gidajen wasu a tsakiyan ruwa da yayiwa garin kawanya ga gine gine iri iri sai inda kallon ka ya tsayama.
Hakan yasa na raina kyan lagos duk da a kullun garin lagos a cikin cigaba yake fiye da sauran biranen Nageria da muke dasu
Motan ya shiga wani kayattacen compound maikyau da ban sha,awa wanda kowan mu ya yaba da kyau wajen don wasu har magana sunyi.
Kusan saida kowa ya gama fitowa daga cikin motar na fito a karshe ina dan gyara rigan jikina cikin kamewa don yanayi zaka kalla kasan bawai tafiyan ina jin dadin shi bane duk daulan da muke gani a wanan tafiyan.
Wani mutum ne dake jiran mu a wajen wurin ya taremu yake muna sannu da zuwa shi yai muna jagora zuwa inda suke wurine mai kyau da aka kawata shi da sosai da kujeru na alfarma masu kyau da daukan hankali aga wani babban table din cin liyafa wurin ga manyan kayan cin abinci nan saman shi a jere.
Alaja kamar yadda naji yan lagos na kiranta dashi itace muka hango cikin shiga na alfarma zaune tare da danta a gefe saman wasu kujeru na alfarma a wurin.
Fuskanta ba yabo ba fallasa lokacin data hangomu kusan lokaci daya muka iso tare da wasu da nake zaton yan uwansune na jini kungiya biyu wasu daga arewa wasu uku kuma daga kudu suke.
Muka hade a tare dasu gaba dayan mu sun nuna farin ciki da ganin mu suke muna sannu da zuwa ba bata lokaci bayan gaisuwa aka nufi saman dinning table din don cin abincin.
Gaba daya a takure nake a wurin don nice karama cikin su gaba daya da muke zaunen addua akafara wanda shida kanshi ya jagoranci adduan .
Kafin abawa daya daga cikin kiristocin shima yayi addua a lokacin aka shafa jimoh ne ya fara magana yana fadin sunyi maraba da kowa daya samu halartan wanan tafiyan yadda kowa yazo lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya.
Sai abokan aikin mu ya nuno mu a inda muke zaune yana fadin wanan gaiyatan da biyu maigida ya shirya maku shi don kuzo nan ku huta na sati biyu saboda ci gaban da kuka samowa company a yanzu.
Nan dai aka dauki tafen jin dadi bandani da dan guntun murmushi na sake kawai iya fuska da baikai ciki ba a lokacin don jin har sati biyu zamu kwashe a wanan tafiyan da in mun dauko yarsu data gama karatu zamu wuce Dubai daga can muyi sati daya mu dawo gida Nigeria daga can.
Muryan Alaja ne ya dawo dani daga tunanen da nakeyi inda yemisi dake kusa dani zaune ta dan zungureni na dawo firgigit daga tunanen da nakeyi a lokacin.
Tana fadin yata ya kuma kamar bakya farin ciki da wanan albishir din da kukaji a yanzune na dauka kowan ku nan zaiyi farin ciki da wanan karamawan da dana yai maku a yanzu.
Don muma kun jawo muna cigaba sosai a cikin harkokin mu a wanan lokacin don gaba daya ma,aikatan da muke dasu sun mayar da himma wurin kawo muna dukiyan mu yadda ya kamata a yanzu.
Dan murmushi na kara sakewa ina fadi a cikin yarbancin da itama din tayi muna cewa nayi murna da jin hakan Allah ya kara rufa asiri aka amsa da amin lokaci guda.
Nan aka fara cin abinci ni dai na zubane amma sam banji dadin abincin ba sin haka cibi biyu kawai nayi na kurawa cup din dake gaba cike da ruwan lemo mm a ainihi idanu.
Daga inda yake zaune shima ido ya kura min babu ko kiftawa haka Alaja dake magana dashi ta dago tana kallon shi jin yayi shiru a lokacin ta kalli inda dan nata yake kallo din taga na kurawa cup idanu ina tunane.
Let me feed you by myself oyyah come close to me ta fada tana tayar da wace ke kusa da ita zaune a lokacin wace sai alokacin na shedata wanan kanwar natane dai da muke haduwa a sha,anin su.
Dan murmushi nayi na dauki cibin na dibi abinci da sauri don jin abinda Alaja ta fada a kaina don nuna damuwan ta kan rashin sake jikin da nakasa yi dasu.
Matsa min tayi akan na dawo kusa da ita din inda tasa wata tashi don dole na mike na dawo inda take na zauna.
Ana cin abincin ana hira da dariya ganin hankalin su ya dauku ana surutu yasa na mike daga wurin na nufi can inda muka samesu da farko na zauna ina bin wayana da baida amfani da kallo don katunan wayan mu basu da amfani a kasan yanzu.
Hankalina ya dauku ga wayan ban san zuwan felix inda nake ba sai muryan shi naji yana fadin meke damun kine haka yan mata ?
Kaina dago na dan kalleshi kafin in ce dashi nothing meka ganine kawai ina tunanen mahaifiyatace dana baro a gida.
Don ban taba tafiya haka mai nisa ba tare da ita ba asalima idan ba tafiyan da muka tabayi da oga ba yayi saurin fadin wanan da bom ya tashi ko kai gaskiya mutanen ku they are wicked.
Felix kazo kabi mutanen nan kayi muna odan abincin dare ya fada daidai lokacin da yake karasowa wurin namu.
Haka yasa muka dago kai da sauri muna kallon shi kafin ya karaso inda muke zaune ya zauna na yunkura zan mike ina fadin felix ya jirani zanga yadda wurin yake yace no in zauna magana zaiyi dani.
Felix din ya wuce inda ya aikeshi a lokacin ya kai zaune yana fuskantana kafin ya fara din miss Sahiba bansan irin godiyan da zan maki ba in nuna maki jindadina ga abin da kukai min.
Gaskiya na yaba nakuma gode sosai da wanan aikin da kuke gabatar min ko nawa zan baku sai dai kawai in baku badai kudin ladan aikin ba a gareni.
Aikine na kasada babba kukayi wanda ba kowa zai tsaya yai makashi ba don ni kaina da farko da Jimoh yace a baku aikin na tsorata matuka ina gudun wani abu mara kyau a sanadin aikina yazo ya sameku
Don na bincika naji labarin mutanen nan bashi da kyau sosai akan dukiya zasu iya salwantar da rayuwan mutum.
Kai na dago tare da murmushi ina kallon shi don jin abinda ya fada nace kome zasuyi nasan cewa Allah ba zai basu sa, a akan mu ba asalima ai sune suka taba abinka don haka kome zasuyi a kansu zai koma yanzu.
Gaskiyane sun kawo muna hari da dama dan zaman da mukayi dasu saidai Allah bai basu sa, a akan mu ba don muna tare da tsarin Allah hakane yace yana gyara zaman shi tare da fadin ina da labarin komai daya faru daku a can don nima nan ban zauna ba a kanku.
Daga ida suke zaune suna hango mu ta cikin glass din da yai muna katanga dasu saidai ba zasuji abinda muke fadi ba don dan nisan dake akwai a tsakanin mu.
Don haka sai suka dauki hakan da wani zance na daban mukeyi a lokacin kowa da abinda yake rayawa ga wanan zaman a zuciyar shi.
Sam ni ban dauki hakan da wani manufa ba tunda nasan akan abinda muke magana lokacin dashi.
Alajace da kanwarta tayi mata magana a rada ta mayar da idon ta a kanmu lokacin a cikin zargi zuwan felix wurun yana masa bayani ne yasa ta taso daga inda take zaune din zuwa wurun mu a lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA.


2ANA DARA GA , , , , , , , ,

7️⃣1️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUHSIH, , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

ALAJA macece tsayayya mai kiran karfi don garsakace yadda malam bahaushe ke fadin mace mai irin zatin ta zamu iyacewa kuma tsayin nata yayi mata kyau sosai gata farace ita jajir ga jiki daidai tsayinta sai abin ya hade ya bada ma,ana a gareta.
Ta karaso wurin tana fadin a a sha,aban wai kayi waya da Walida kaji ya jikin nata kuwa a yadda yake zaune ya mike kafafun shi saman dan stol dake gaban shi.
Takai zaune a kusa dashi jikin ta yana gugan nashi tana fadin ya kamata ace la kirata kaji yaya ta kara ji da jikin nata ai don kasan da tana nan a tare damu yanzu haka dukda mahaifiyarta tace zamu hadu dasu can england din.
A cikin harshen larabci yayi mata magana ba tare daya dago kai ga abinda yakeyi ba sai ita Alajan ta juyo tana dan murmushi take fadin.
Wai laifine ka kira matar da zaka aura kaji lafiyanta tunda da ita muka shirya wanan tafiyan rashin lafiya ya kamata .
Murmushi Allah ya ban ikon sakewa ina dan kallon shi jin an ambaci aure a gareshi nace sir gaskiya maama ta fada yana da kyau kakira kaji lafiyan ta.
Da mamaki ya dago yana kallona kafin yace I don't no who she is talking for kin dai san bansan wacece ba kuke zance a kanta ba na fada maku ba wanan zancen a zuciyana yanzu.
Don haka ummi ki bar zancen nan tun wuri ya karasa fada yana tanke fuskan shi a cikin harshen larabci da bama ji.
Dacewan hakan mama ta gani a gareka mune yanzu zamuyi hakan kai muna fada mutum musulmi bai cika cikkaken mutum a idon jama, a sai yana da iyali a gida.
Da kyau yata haka nake son ki da fadin gaskiya koda yaushe gara dai ku fada mai ta fada a cikin yanayin damuwa a fuskan ta lokaci guda.
Na rasa meye hakan yakeyi kai ba musulmi bane da baka yarda da kaddara Sha,aban nima ai mijina ya mutu danayi hakkuri ba gaku ina kalko ba to kai waye zaka kalla ya debema kewa a rayuwa kowa fa yana son barin baya a duniya ko banza zasu tuna dakai suyi ma addua.
Wana maganan da mahaifiyar shi keyi yasa jikin kowan mu yayi sanyi lokaci guda karshe sai mikewa yayi ya barmu mu uku zaune fita yayi zuwa wajen wurin yana shan iska rike da cup din lemu a hannun shi.
Felix har yanzu na kasa samun kan yaron nan na dauka zaiyi maraba da wanan dun da muka zabar mashi don yarinyar akwai kyau ga ilimi sanan gata yar manyan mutane a can Nageria din.
Nan Felix din yai magana yana fadun mommy kin fa san halin ogana kan wanan magana ko wancan ma kece kika matsa sosai akayi shi a lokacin.
Har kuma rasuwan ta bawai wani shiri bane sosai a tsakanin don kin san irin rayuwanta baiyi daidai da nasa ba kinfi kowa sanin haka.
Kai kabar wanan zancen don wacan ta riga data rasu ko yanzu wata nake son na nema mashi yana kuma bultse min akan zancen gashi na riga dana fadawa mahaifiyar yarinyar kuma sun yarda da hakan a yanzu.
Don haka kuyi min kokarin hakan gareshi ku biyun nan tana nuna mu da hannunta naga ke ya yarda dake sosai a rayuwan shi har wanan abin yana ban mamaki.
Yadda ya amince dake haka kina mace koda yake hakan ba abin mamaki bane ga wanda ya sanki kuma yasan kina tare da juju zaki iya juya kowa a yadda kike so.
Saidai ina ina rokon ki da kada ki shiga cikin rayuwan dana don Allah duk abinda zakuyi ya tsaya iya aikine kawai kamar yadda da farko shine ya hada ku ta kare tana hada hannayen ta a wuri daya alaman rokona.
Duk girma da nauyin Alaja da nakeji sai naji lokaci daya ta zube min idona ya rufe na kirata da sunan ta da Alaja me zancenki ke nufi a kaina yanzu ido babu nauyin ta ko tsoro a lokacin itama din kallon mamaki ta bini dashi a idonta.
Ni sahiba ba dan ki ba duk wani da namiji dake duniyan nan ban taba jin wani abu so ba ga kowa don ban taba soyayya da kowa ba a rayuwana balle na fara akan danki .
Na mike daga inda nake ina fadin idan ma har zuciyar ki ko wani ya fada maki haka yai maki karya don ni yanzu ba wanan bane a gabana ba.
Aikine da danki daga yau din nan na daina tunda har kike zargin wani abu ga hakan ba komai tsakanina da oga sai zalla biyayya da mutunci iri wanda shi ya nuna min hakan.
Kada kiyi zaton aiki da nakeyi a katshin danki zai baki daman hasko wani zaton dani koshi bamu tabayi a zukatan mu ba akwai dubun shi da suke jiran hakan ni ba matsalana bane a wurina aikine ya hadamu shi kuma nakeyi dashi ko yanzu din da kika ganmu a zaune.
Ina rike mutum ne yadda ya rikeni tun farko danki ya daukeni kamar yar uwanshi nima hakan yasa na daukeshi hakan kamar yadda shima ya daukeni din.
Don haka ki kwantar da hankalin ki kije kai tsaye ki nemawa danki yar shugaban kasan duniya wanan bai shafeni ba ni.
Kuma ki sani daga wanan ranan komai ya kare a tsakanin mu dashi na fada ina mikewa tsaye fuuu nabar wurin ina jin Felix na kiran sunana ban tsaya naji abinda yake son fada min ba lokacin.
Sai muryan ogan naji yan fadin meke faruwane felix mai kukai matane hakane wai ?
Sai kuma ya sake juyowa rai bace yana fuskantar su kafin kuma ya juyo da sauri yakai kallon shi inda nake ina kokarin fita daga inda muke tare dasu din wurin da suka gyace mu din .
Wani tsawa ya dakawa Felix a kan ya bini ya dakatar dani kada in bace a cikin garin mutane


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login