Showing 108001 words to 111000 words out of 382072 words
nufi kafin tace dashi lah yaya ai wanan bata jin hausa sai yarbanci da turanci kawai.
Allah ko haka ta fada maku cewa bata jin hausa amma ku da wani yare kuke mata magana ya tambaya a daidai lokacin da fa,iza ke kirana na tsaya tare da juyowa ina kallon su.
Ba tsoro ko dar dar haka na tsaya ina kare mai kallo a lokacin kafin ya dan yi wani iri yace anyway ku tafi ma ba matsala.
Mun juya ya ciro kudi yana fadin tazo ta karba tana washe baki you come here naja na tsaya kudi ne har lokacin a hannun shi ya miko min tare da fadin give dis to ur mother kamar kullun.
Saidana kalli kudin kamar ba zan amsa ba sai kuma na mika hannu na karba tare da dan rusunnawa alaman girmamawa a gareshi.
Allah ya taimaka fa,iza ta fara tafiya don murnan kudin nayi saurin tura kudin a cikin rigana na fito na samu harta sauka saman dan matakalan su ta fara tafiya.
Nacin mata da sauri take fadin may ya tambayeni nace sunana kawai tace idan yaso yana dan magana amma ba ruwan shi da kowa a cikin dangi.
Balle yaya Abubakar da basu shiri dashi ko kadan shine wai anty hauwa kuma take son shi a hakan.
Shi kadai gwggo hari ta haifa duk da ance itama ta haifa a bayan shi basu tsaya ba lokacin don ance kamar abinsu daya da mommy ne.
Ban bata amsa ba muka shiga mota driver ya jamu zuwa gida har muka iso tana ban labarin su har mahaifiyar shi din da mijin ta.
Ban yarda naje part din mommy ba kai tsaye saidana fara zuwa namu din na aje kudin na fito na sameta taba mommy sakon nace mata mun dawo tace ashe mun samu mijin ta a gida .
Ta miko min kudin da aka raba nace lah mommy dakin barshi ai a wurin ki tunda ba komai zanyi dasu ba.
Daga van fa,iza tace mommy anko fa zamu saya na fada maki mommy ta aika mata da dakuwa da hannu ta noke karshe cewa nayi abawa Fa,iza din ta saya muna anko din.
Ina fadin haka na fita anty Nabila tace ina sha,awan rayuwan yarinyar nan abin duniya sam bai dameta ba ita da watace ai bata tashi sai an raba an bata su.
Mommy da kanta yake duke tace ni har abin kamban mamaki rayuwan su kamar ba tashin bariki ba idan suna wani abu sun samu tarbiya sosai wallahi.
Ina komawa na zauna gefen umma tare da daga kujera na dauko kudin dana boye din nace yau ma yace a kawo maki su.
Kuma shi din dan cikin gwaggo hari ce ashe sai dai ban san dalilin shi na taimakon mu ba da yakeyi don yana kama da mugu sosai.
Anyanzu kan banda fargaba a gareshi don nasan koshi waye amma da farko nasha jinin jikina dashi sosai ganin irun alherin nan da yake muna haka.
Tunda nayi sallah na kwanta barci don haka da wuri na kwanta a ranan ashe wai anyi rikici da yaya Abubakar da matan shi da sukazo gidan da dare su jajantawa daddy zancen motan shi data kone.
Sai gashi an kira Nazifa din a gidan ana fada mata cewa mahaifin su ba lafiya tun jiya hannun shi ke masa ciwo suna asibiti dashi.
Bata jira cewan mijin taba ta mike da sauri tana fadin gata tafe yace idan ta tafi ta tsaya can shine rikici ya barke a tsakanin su a gaban iyayyen mijin ta kuma saida kyat suka samu suka shawo kanta ta yarda da safe kamar yadda yace yanzu dare yayi ta bari da safe su tafi.
Ban san anyi ba saida safe da Anty amarya ta shigo tana fadin zasu tafi asibiti su duba Alh Nuhu maifin matar modibbo ance haka kawai hannun sa ya kage ba a san meya sameshi ba.
Ashine aka kira matar jiya suna nan ake fada mata ankai mahaifin su asibiti ta tayar da fitina ga mijin wai sai ta tafi.
Kin san auren hadine mu iyakarmu kallo uwarshi ta sani cewa yaran basu samu tarbiya ba kuma mahaifin su da Alh nan kamar Annabi da kafiri suke ta yarda tayi wanan hadin a tsakanin don irin halin su dama ai duk haka suke nasa kawai ake gani shi daya tona zyciyar shi duniya tasan halin shi.
Umma cewa tayi jam abin baiyi kyau ba Allah ya sauka sai kun dawo ke nan insha Allah ba zasu fita ko ina ba suna nan balle sahiba tana nan itama tare dasu.
Ta fice ta barni da mamaki biyu a zuciyana na farko gulman mommy da yan gidan su da takeson yi a gaban umma don rashin sanin waye umma din ga mommy.
Sai na biyu shine ban san dalilin da yasa bata kaunan yayanta suna shiga cikin yayan dakin mommy ta kwamace su zauna a wurin mu duk da muna baki a cikin su din.
Mikewa nayi na dauko masu sauran sweet da biscuit daya rage na kawo masu suna ci saiga mommy ta shigo tana fadin zasu tafi asibiti da Alh su duba jikin yaya Nuhu haka kawai hannun sa ya rike bai iya motsasa.
Mukai mata a dawo lafiya ta fita umma ta kalleni cikin yarbanci take fadin anya mutumin nan ba wani sheri yajeyi ba ya koma masa kuwa ?
Shine mana naba umma amsa kai tsaye a cikin rashi damuwa duk lokacin da yace zai taba daddy ko wani nasa yanzu hakane zai faru dashi ai umma .
Sahiba a ina kike sanin wanan abubuwan naki nace nima ban sani ba umma ta wani irin kalloni kamar zatayi magana tayi shiru kuma.
Basu wani dade ba suka dawo din labarin baida daddy wai sun samu an dauko mai magani yazo ana masa magani.
Umma tace a asibitin ake maganin mommy tace shi ai kin san ya iya wanan abubuwan dasu ya yarda ko asubitin kila fin karfin shi akayi ko zafin ciwo yasa ya yarda yaje din.
Zaune yake yana breakfast amma hankalin shi bai kwanta ba yayi iya tunane ya kasa gane halakan wanan yarinyar da daddy da har suke zaune a gidan daddy din yanzu yarinyar daya sani da a logos suke ita da mahaifiyar ta da dan uwanta yanzu meye hadin su da daddy din.
Shigowan mahaifiyan shi falon ne yasa ya dago kanshi ya dan kalle ta itama din kallon dan nata tayi kafin ta kalli abincin da ta zuba mai bai taba ba.
Wai ya haka meke damun kane haka ka tasa abinci a gaba haka kana kallo ko wanan da aka dafa bai maka bane a dafama wani ?
No bana dai iya karyawa da wanan yayi min nauyi da yawa da safen nan haka sai dai tea zan sha dan anjima kadan.
Kujera taja ta zauna tare da jawo abincin zuwa gabanta tana fadin oya bude min baki wanan abincin ne zakacw yayima nauyi a ciki ban iya shiririta ba shiyasa kake rakewa haka yanzu ai.
Murmushi yayi ya dan dago yana kalon maman nasa yace kai haba mama yanzu fa na girma wani yazo ya samu kina bani abinci ga baki a samu abin fadi.
Haka yaran nan da suka shigo shekaran jiya suka fita suna gulmana basu san ina falo zaune ina waya ba.
Su Fa,iza da wanan bakuwar bayeran ban na gidan ko au bayerabace dama ashe haka nake zato don ance wai diyar abokin shine na can.
Ban san ko wani aboki nasa bane a can don ni ban yarda da wanan zancen ba don yarinyar sam batayi kama da yarbawa ba tafi kama da zuri,an gidan mu ma sosai don dai ita din farace sosai da tsayi kuma.
Dole dai suna da alaka mai karfi dashi tunda suke zaune agidan shi amma ai ya kamata ace kunsan ko iyalan waye su din ai.
Ban zauna bane ai ina son yin wanan zancen dashi koda yake ma ba abinda ya shafeni da zancen shiyasan inda ya samo su ai.
Don ance baison kowa yayi maganan su a gidan saidai kawai yana nuna suna da muhinmanci a gareshi sosai abindana sani ke nan.
Kawar da zancen tayi da fadin ance yaya Nuhu na asibiti a cikin wani hali tun jiya sai yau nake ji da mukai waya da mamanka Asiya.
Meke damun shi ya tambaya tace wai ance kamar jifan shi akayi don hannun likitoci sun duba sunce basuga wani matsala ba su.
Ina zasu gani mama tunda kila abinsa ne ya koma masa wai ki duba last da muka hadu yake fadin wai yaushe na fara wanan harkan business dina bai sani ba har na kai haka ?
A cikin wani irin zabura tace kada ya soma yin gangancin shiga harkana wallahi iskancin shi ya tsaya a wa yanda ya raina ya bar ganina mace don zan iyaja dashi don shima ya sani ni ban tsorin shi .
A,a mama kada wani abu ya hadaki dashi don ke mace ce ni ba abinda zai iya yi dani sai ta Allah kawai yana baraza nan shine ga masu tsoro ko kwadayin abin hannun shi.
Sun dan dauki lokaci suna magana kan Alh nuhu din wanan ya sa ya mike yana fadin ni zan fita mami wata kila in shiga kano zuwa anjima indai tafiyan ya yuyu garemu.
Yau din nan uwar ta tambaye shi tana kallon shi da mamaki yace mama kano nada nisane kuma da zan fita da anty Asiya don tace sai muje ganin yaya Nuhu din .
Amma yanzu barin bari ka tafi sai mu tafi zuwa gobe din in Allah ya kaimu a, a mama ku tafi kawai sai zuwa yamma fa nace zamuyi tafiyan tace to shike nan ai har maje mu dawo baku tafi ba tunda ba tsayawa zamuyi ba a can don ance ba a ma ganin shi don bokan shi ya hana wai a shiga a ganshi kaji wani shirme.
Mikewa yayi ya koma saman kujera ya kwanta ya mike tare da dora hannayen sa saman fuskan ya shiga tunane don a yanzu ba abinda yake tunawa sai hanyar da zaibi ya fitar da kanshi kan neman da jami,an tsaro suke mashi.
Duk da yasan hakan abune mai wuya a gareshi ya iya fitar da kanshi a cikin wa yan nan kurayen yan duniyan abokan sana,anshi marasa imani da tawakkali.
Don ba zai iya zama da wa yanda akan kudi zasu iya kashe rai don kawai bukatan su ya biya kudi ya shigo masu ta ko wani hanya.
Yanzu mutum kawai ka barahi inda ka ganshi kada ka tona cikin sa don ba zaka kara mai kallo biyu don abindake boye nasa Allah ya bamu cikawa da imani yasa mufi karfin zuciyar mu AminAmin.
A gidan daddy kuma yau dai da fitina aka tashi a gidan don fada ne tsakanin mommy da Anty tunda safe ya kaure inda anty ke fadan wai ana son a kashe ta aga bayan ta don haka aka bata abinda zai kashe ta.
Kai tun mommy tana hakkuri hardai takai ga ta tanka suka fara musayan harshe a tsakanin su abinda ya jawo duk wanda ke gidan ya fito a lokacin.
Kusan nice na fito a karshe na tsaya ina sauraren wanan zubar da kiman da suke yi a gaban yayan su suna kallo.
Anty sai kira take wai su mommy da diyanta basu kaunan ta gashi ana son a kashe ta har diyan ta daga ida nake tsaye nace haba anty whichi can of kind pf talk be dis?
No be belle sickness de worry u, which can of talk be dis, u cary belle for three months now, na him u go say mommy don send evils things for u ?
Wurin yayi tsit ana kallona son abinda na fada ido kakafe ban ko juya su nace is better to go and see d doctor first, before u talk dis mes.
Aikuwa tayo kaina da fada tana fadin ni har na isa in mata kazafin ciki ita bata da komai a jikinta saboda tasan cewa tayi planning don haka bata taba zaton ciki a jikinta ba a yanzu.
Don tana bin duk ka,ida daya dace kada tayi ciki a wanan lokacin sai gashi taji ina kira mata ciki haka yanzu.
Hannuna umma taja zuwa part din mu ta zaunar dani saman kujera ruwa ta debo min ta bani na girgiza mata kai alaman a,a nan na zauna ina ta faman hamma sai kafa da nake kadawa kamar wata basaraka.
Sai abin ya zama bokon lamari a wurin umma don haka ta fita ta kira mommy suka shigo dakin a tare.
Sai da kyat suka samu na kwanta ina dafe kaina a lokavin umma ta fara tuna abinda ladi da sauran mutane ke fada mata a lagos game dani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
3️⃣3️⃣ BY
ZAINAN IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAH RAHAMANIN RAHIM AL QABID, , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA KUDINE NA FADA NA FITAR DA HAKKIN RASHIN SANI, , , , ,
Gidanne ya koma shiru na dan lokaci kowa da abinda rayuwan shi ke raya masa kan abinda ya faru a lokacin .
Don mommy kan rayuwan ta ya gama baci da halin hjy karima wace bata yarda da Allah kan diyanta ko ita ba dan abu kadan zai faru yanzu Anty amarya zatace ai ai mata ne ture kishiya tayi mata don kawai taga bayan ta.
Yar uwa kokece a irin wanan rayuwan ki zauna ki binki imanun ki anya bakiyi zurfi ga shirka ga aikin sabawa Allah ba.
Tunda baki yarda da kaddara da duk ya sauka a kanki sai ki manta da cewa Allah mai yi a duk lokacin da yaso hakan a gareki
Ko ki koma kina dariya kan abinda ya samu wani na sheri karki manta wata rana kema yana tafe a kanki yar uwa don haka lamarin Allah yake .
Anty ko tana part din ta sai faman tunane da tsuki take ja tare da fadin jimin wanan yar iskar yar da zata lauyeni a gaban mutane tana fadin wai cikine dani har na wata uku har yaushe na gama wanka da zata kira min ciki a jikina yanzu.
Allah na tuba koda zanyi ciki ai ba yanzu ba dama kwadayin da namiji yasaka na haifo wa yan nan kai a kai don kawai ina zaton samun da namiji a lokacin.
Haka kawai zan zauna ina zuba yaya ga wanan tsohon karfina yazo ya kare na koma jagwal a cikin abokaina.
Tun tana yawan tunanen hakan har yakai ta daina zargin hakan ta gaji ta ba kanta shawara saidai washe gari saida takai kanta asibiti don bata yarda da awon da tayiwa kanta a gida ba.
Suka kara tabbatar mata da cewa su basuga komai ba a jikin ta daya danganci ciki ajikin ta don haka ta dawo gida da yamma sai gata dakin mu daidai mun dawo islamiyan yamma ke nan ina zaune.
Sallama tayi bata tsaya komai ba ta fara fadin wa umma nazo injawa yarki kunne a gidan nan kafin Alh ya dawo da ta shiga hankalin ta dani a gidan nan.
Idan ba rainin wayau ba ta yaya kamar Sahiba zata saka baki a cikin zancen mu har tana kira min wai ciki ne a jikina idan cikine ta fini sanin yadda ake daukan cikine ko kawai ta nunawa mutane ita yar zamani ne bata da kunya tasan komai.
Kamar ya tasan komai tace aiki tambayeta yadda har yakai tasan mace mai juna biyu da harta iya yanke min hukuncin ciki a jikina na dai fada maki ki mata kashedin hakan a kaina don bani da dadi idan na saka mutum a gaba tana fadin haka ta juya ta fita daga part din mu.
Umma ta jiyo ta kalleni tana fadin na fada maki ki kiyayi wanan matar Sahiba na dago ina fasin umma menayi mata ni da zata zo tana fadin wanan maganan haka a kaina sai umma tayi shiru.
Tun wanan lokacin sai naji kawai na tsani wanan matar na daina zuwa gaishe ta na daina kula diyan ta saidai hakan baisa yaran su rabu dani ba don dole na dan kama kula dasu saidai ba sosai ba.
A bangaren Alh Nuhu kuwa abin ya fara bashi mamaki yana tambayan kanshi har Alh Ali zai gagareni duk da nasan shima a tsaye yake kamar shi .
Don a zaton shi shima daddy irin abinda yakeyi daddy din keyi shima don ya kasa cin ma daddy din ya nakasa shi yadda ya saba nakasa duk wanda ya shiga mai hanci da kudundune.
A wanan halin kumane ya koma