Showing 339001 words to 342000 words out of 382072 words
cikin canza sauyi ake mai.
Don haka don Allah kada muce zamu wahal da kanmu wurin yin wani abu yanzu din haka kuma itama yarinyar da mahaifiyar ta na dan tuntubesu kan hakan uwar tace basu da damuwa a wanan don irin bukin suna lagos zasuyi kawai a can shike nan.
Lagos kuma ba a nan zasu kawota ba ke nan daddy ya tambaya sai baffah hamza din yace dashi kudidi ma tayi wanan maganan.
Shine mairon tace a dole gida ai za a kawota daga nan sai a wuce zuwa maiduguri din da ita bayan sun gama nasu abinda zasuyi ke nan acan .
Kai kowa ya gyada tare da gamsuwa da abinda baffah din ya fada yaci gaba da fadin yanzu kai modibbo mun kirakane muji mu a nan me yakamata muce munyi mata yanzu ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , ,
1️⃣0️⃣3️⃣BY, , , , , , , , , , , ,
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL, GHANAEI, , , , , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257
ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U 👋
Kamar yadda su baffah suka shirya duk da cewa ba zancen kashe kudi ko wani abu ga auren mu duk shi mukhatar din ya dauke nauyin hakan.
Saidai wanan shawaran bai sa sunyi sanyi a gwiwa ba don suma a nasu bangaren iyayyena sun tanadi irin abinda zasu kai koda shiba zaiyi amfani dashi ba yan uwansa su raba a tsakanin su.
Don hakane suka yanka kudi a tsakanin su aka hada har da shanu biyu a matsayin garan da za a kai sai buhuhunan abinci na hatsi da sauran abubuwan daya dace.
Sai kuma wani shanun da zasu yanka a nan don daddy sun tsayar da cewa a nan kaduna din za, a daukeni zuwa maiduguri don kowa yasan asalina hade da waliman da duk su suka shirya yin shi.
Lokacin da labarin wanan shirin ya fara zagaya danki wasu sunyi na,am da hakan da za aimun wasu kuma sin nuna hassada da bakin ciki a ciki kan cewa ai sunsan inda suke abinsu.
Nan lagos dai ba wasu kawayen kirki nake dasu ba sai su yemisi ne da saura abokan hurdana da sauran mutane aka danyi buki irin na al,adan yarbawa nan ma dai anci ansha daidai gwargwa don kima tare da raba abubuwa.
Kafin a dauka zuwa kadunan inda muka samu rakiyan abokan arziki na mutunci zuwa kaduna din a gidan daddy muka sauka inda a nan za ai duk wani abinda ya dace kagin ranan tafiyan.
Zuwa lokacin zuciyana ya gama dakewa sosai da komai na falwala Allah al,amarin ina bin kowa da kallo su faiza suke kai da komo sune yan buki.
Ida naji dadin abin shine duk manyan matan da sukayo min rakiya daga lagos wanda yawancin su ta dalilin Abdul muka sansu masu rikon addinine sosai basu wasa da ibada ga su kuma kamilai ba wani zancen watsewa a tare dasu kallo daya zakai masu kasan cewa su din hamshakai ne na fada.
Wanan yasa bakuna suka kara mutuwa a cikin dangin mu kuma sun nuna hali sosai yadda ya dace dama su suna girmama buki ko wani irine.
Munyi kwana biyu a kaduna ana bidia irin na hausawa ga kumshi na musanman da aka dauko maiyi tundaga maiduguri da gyara irin nasu hjyn su mukhatar ta turo ta nan.
Saboda ta samu labarin irin gyaran da uwargida keta faman yi a bakunan mutane wanda mu nan da mai kunshin ke muna hira na dauki hakan ga shirme a wurina.
Amma da dare yayi na kwanta ina nazarin zancen saina fahinci ashe abinda su muniyat da wata Aisha da muke shiri sosai tun dawowan mu unguwar mu ta lagos da muke zama sukewa ke nan har kasan ghana Aisha taje ta kwana biyu ta dawo min da wasu abubuwa saida kyat suka samu na danyi amfani dashi.
Hakama nan tun zuwan mu kullun safe da yamma sai mommy ko anty amarya sun tsureni nasha wasu abinda ban san kona maye ba saidai suna cewa na daure nasha abin amarene dai.
Kai duniya abin tsorone don a cikin yan uwa aka samu wanda ya tseguntawa wata dangin uwargida cewa tayi hankali dani don ni din rikakkan yar sikiroce ta kwarai.
Don sun kawo lefe na bazata da ba wanda ya taba tsanin itin sa don komai ya zama na kallo a ciki saboda an nuna bajinta da nuna halin akwaishi sosai inda zan tafi din.
Yan uwa sai sam barka da tubarakallah sukeyi wasu kuma fidin na bakin su sukeyi wai dama irin mu ai hakane muke samun maza mu cafke lokaci guda irin su Nabila and coo.
To a nan ne aka samu wata munafukan ta samu ta tsegunta masu wanan zance aiko kafin ace meye sun baza labarin cewa ai matar da ya auro din yar tsafice ita.
Har dai labari ya dawo kunnen yan uwar mukhatar din a yadda suka zauna suka tsara komai zakace aida gaskene labarin.
Haka dai suka dauki zancen wasu na fadin duk sherin kishine idan ma har manyace ita ai itace daidai da Falmatan tunda itama bin bokaye da malamai take sai su kara a tsakanin su yanzu.
Falmata ko haukan karya ta hauwa maigidan cewa wurin bakin jaraban shi gashi ya dauko masu wace zata kasheta ita da yaranta harshi din.
Dariya kawai yai mata don shi zuwa lokacin fitinan Falmatan ma ya isheshi a gidan don gudun hakan ne baiso tazo ba kuma gashi duk mutane basu yarda da zancen da suke yadawa din ba sai cewa ake zafin kishine kawai suke fadan hakan.
Suma din kwanan su daya a kaduna anyi dinner da aka shirya yi dasu washe gari kuma zamu kama hanya zuwa maiduguri saidai sauki abin jirgi zamu bi zuwa Maiduguri din.
Karfe tara muna gidan ya Abubakar da mukai mai diran bazata wanan umurnin ummace da tace dole akaini gidan shi shi matsayin jigona bayan iyayyen mu din.
Kowa yayi mamakin hakan don irin girman da mukeba shi yaya Abubakar din na musanman ne don a wurin yarbawa haka abin yake dama idan kaine babba.
Haka umma tabi wanan al,adan data koyo a can din sai suke ganin hakan a sabon lamarine a wurin su don ba kowa yasan ma,anan hakan ba lokacin.
Durkushe nake kasa a falon nasa inda gwaggo kudidi gwaggo Amina dasu anty Amarya da sukai min rakiya suna zaune saman kujerun falon gidan nasa .
Inda sai bin ko ina suke da kallo suna mede baki don yadda aka bar komai na gidan ba gyara ko kulawa wanda wanan aikin macen gidane gyaranshi .
Kota gyara ko tasa a gyara din amma ga komai dai an saka na alatun zamani a falon amma ba kula yadda ya dace duk kura ya rufeshi na hammatern da akeyi a lokacin.
Yana zaune suna gaisawa dasu gwaggo din sunawa juna yaya dawainiya da baki da sauran abubuwa kafin can ya juyo inda nake zaune ya dan kura min ido na dan lokaci.
Kaina yana kasa ni kadai nasan halin da nake ciki a lokacin ko macen da tayi auren soyayya ta kwatanta dani da akaiwa auren hadi na bazata kwatsam banda masaniya a wanan lokacin.
Muryanshi naji can cikin kunnena dawani irin kasalalen murya ya kira sunana da sahiba wanda hakan yasani runtse idanuwana a lokacin.
Ban iya amsa mashi ba amma haka yaci gaba da fadin yanzu zaki bar umma zaki barmu zaki shiga sabon rayuwa a cikin mutanen da baki taba sanin suba a rayuwan ki.
Wanan yasa ni sake wasu irin hawayr masu dumi a lokaci guda karo na farko tun bayan dakewa da bushewan zuciyana kan wanan zancen auren.
Ya kara fadin althoug sahiba a wanan fanin nasan baki da matsala saidai shi rayuwan aure wani rayuwane dake tafiya da ilimin zamani na lokacin da ake ciki a karnin da kai aure a lokacin.
Mace bata samun riban aure kin sani sai akwai fahinta a tsakanin ta da wanda zata zauna dasu musanman mijin data aure da yan uwan shi.
Daya daga cikin matan da mukazo daga lagos dasu da aka hadomu da ita cikin wanan tafiyan tace kwarai kuwa (Na true you talk )
Idoshi ya lumshe a hankali kafin yaci gaba da fadin kina da hakkuri da hangen nisa ga tausayi saidai duk wanan sai kin kara ga wanda kike dashi don shi zaman aure abune na daban ga masu yinshi.
Abinda mijin ki baya so kada kiyishi Sahiba wanda yake so ki kara sama da yadda kika iya nayi bincike mai zurfi mijin ki baya da matsala ko kadan a cikin tarihinshi.
Don haka ki kwantar da hankalinki ki natsu ki zama dasu na tsakani da Allah don ki samu riban auren ki ki zauna lafiya da kowa kiyi biyayya ga al,adun gidanshi matukar bai kaucewa addinin ki ba.
Zuwa yanzu kukana na kasa danneshi don sautin shi ya fito fili wanda shima yanayin muryan shi a yanzu din ya sauya ga yadda yake magana da farko a lokacin.
Kije ubangiji ya albarkaci rayuwan auren ki da komai naki ai ba rabuwa mukayi ba tunda zamu dinga waya dake lokaci lokaci.
A lokacin na kara karfin kukan nawa ina son in magana saidai ba zan iyaba a lokacin amma sai naji muryan shi yana fadin zamu baki Amirah ku tafi tare na dan lokaci kafin ki bar kasan nan.
Don ance zaki dan zauna da mahaifiyar shi kwana biyu kafin ki tafi muma kuma zamuzo insha Allah don muna son zamu dan zauna dasu a kanki insha Allahu.
Bayan hakan bai kara fadin komai ba naji yayi shiru da kyat gwaggo Amina dake kokatin dagoni daga zaunen da nake ta iya daga ni sai lokacin na bude dan guntun gyalen dana rufe fuskana kafi suyi aune na fada saman jikin ya Abubakar din daya riga ya mike shima a lokacin ina sake wani irin kuka mai ban tausayi.
Tare da fadin brother na fasa wanan aure bana so bana iya barin umma da dan uwana in tafi i don't want dis marrige at all.
Bayana naji yana dan bubugawa tare da fadin you most to marry Sahiba haka shine cikar imaninin ki a cikin al,umma aure dolene ga musulmi don sunace mai karfi garemu.
Ba abinda zai samu umma ko Ammar don suna tare damu nayi maki alkawarin kara saka ido ga duk wani lamari nasu daga yanzu.
Kai na girgiza ina sake fadin No i don't want zamana a gida yafi min wucewa na barsu idan na wuce wani wajen dawa za a barsu yanzu nice komai nasu a rayuwa Ammar ba lafiyane sosai dashi ba hakama umma din.
Saida kyar suka samu na yarda na barshi a lokacin muka fito tare dashi yana kara min nasiha jin su kawai nakeyi don takaicin daya rufe min zuciyana.
Nazifa dake tsaye bayan kujeran da yake zaune saida taga fitan mu daga falon nasu ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yar iska.
Ashe iskancin naki iya nan ya tsaya aje a iske kanuri can suci muna magininki da kyau ai zaki gane kuren ki yar iska kawai ance maki aure wasane dama.
Daga gidan ya Abubakar gidan tsofin nan biyu aka kaini dake zaman iyayyen su a yanzu kannen mahaifan ubanan mu ke nan daga nan muka dawo gidan daddy din .
Mun samu yan maidugurin sun iso wai yan daukan amarya bayan wa yanda suka kwana a nan mazansu da mata nagodewa Allah na kuma godewa yan uwa da suka taru suka fitar dani kunya suka nuna nidin yar dangice gaba da baya.
Don yan uwan umma ma da dangin mu na kauye ba,a barsu a baya ba duk sunzo daga kauye din don an aika masu suma kuma sunzo.
A yadda suka buga anko wai duk sabodani din ya kara sana fashe da kuka ga ko ina ya cika makil da dan mutum anci ansha sai sam barka ga kowa lokacin.
Yan kai amarya mutum ashiri aka bukata saura yan uwan ango ne da abokai wai ashe shima mukhatar din yana kaduna a ranan.
Jin cewa tafiyan na jirgine yasa su gwaggo hari da tawaganta dama wasu da ban zata ba duk suka shirya yimin rakiya don su karas da komai yadda suke jin labari.
Mommy ce akace su zauna su sallami baki a gida daga baya zasuzo tare da ummana da wasu sauran yan uwa ganin daki wanan alkawarine da akai masu.
Haka gwaggo Amina ta fito rike da hannuna zuwa falon daddy dake cike da yan uwa da abokan arziki kan inyi sallama dasu lokacin.
A tsakiyan falon aka zaunar dani bayan wasu daga cikin iyayyen mu mata sun rikoni zuwa falon nidai sai binsu nakeyi don ban taba sanin al,adan hausa fulani haka yake da akidu masu tarbiya ba idan bawa yabisu daki daki.
Daddy ne ya soma magana bayan budan taro da addua ya fara min nasiha saidai ince ya dora inda aka tsaya don nasiha kan nasha a wurin yan uwa dama.
Har yakai akaba baffah hamza dama shida wa yanda suke yan sa,oi kusan baffah hamza din shine ba karshe a lokacin.
To Sahiba Alhamdullahi mun godewa Allah daya bamu iko tare da lokacin sauke wanan nauyi da dan uwan mu yabar muna.
Alhamdullah don zan iya cewa kinyi dace da miji wanda yasan darajan ki tare da kimar ki kuma da tausayin ki a matsayin kina marainiya a yanzu.
Don Allah sahiba kije ki zauna tsakani da Allah a dakin mijinki kada ki yarda wani abin asha ya fito daga gareki ko wani hali da baida kyau damu bamu sanki dashi ba.
Kirike Allah da mairaicin ki Allah yai maki jagora da haske ga almarin ki ya baki zuria masu albarka yasa ku gama lafiya ki kara hakkuri shine maganata ta karshe dake.
Haka suka fito dani ga yan uwa nan kan sunzo bila,adadin gaskiya nidai kodan me sukazo naji dadin ganin hakan daga garesu.
Bayan mun shiga motoci airport aka nufa har yan rakiya sai a nan ne naji ana fadin aiga angon can ashe harshi sukazo suna gaisawa da mutanen mu.
Ba,a tsaya jiran komai ba aka fara kidaya masu zuwa dama sun fito da shirin su na tafiya har wa yanda ba,a kidaya zuwan dasu ba.
Nidai ina biye da gwaggo har zuwa cikin jirgin ba,a dade ba jirgin ya tashi wanan karon tare da anty Amarya hjy karima nake zaune.
Tun zaman take kara lurar dani abubuwa wanda hakan yakara sa kaina daukan hasken zaman kishintaka da mata keyi muna jin labari.
Yan uwane da abokan arziki sukazo taron mu zuwa gidan hjyn shi inda su gwaggo suka bukaci a kaini a cewan su sai na fara kwana wurin ta taimin masauki kafin zuwa gidan da zan zauna din a ciki.
Nan ma mutanene sosai muka sama anci ansha duk a gidan mahaifiyar nasa wanda ba haka ita uwargidan taso ba don hakan ya bata mata wani daga cikin tsarin ta da sukayi.
Don basu da kunya har gidan hjy sukazo wai don me za a ajeni gun hjy din ace sai gobe ko wani abu can su sam ba haka tsarin al,adansu yake ba.
Su gwaggo hari dasu Anty Amarya suka hayayakosu da fada suma kan cewa mu tamu al,adan fulanin mu haka muka gada sai amarya ta sauka wurin surukarta an bata girman ta kafin a kaita gidan mijinta inda zata zauna.
Kiri kiri suka nuna su basu yarda da hakan ba don sun shiryawa tarona gidan don me za a bata masu tsarinsu da sukayi yanzu zakace sune iyayyen miji a yadda suke kafa doka da fadi idan kana wurin a tare damu.
Nan su gwaggo hari suka nuna masu bafa su kadai suka iya iskanci ba suma da nasu a boye gwaggo harine ta fara fadin wai ku suwaye da zakuzo muna da wanan hayaniyan hakane ?
Munce ga yadda al,adan mu yake kunce sai mubar al,adanmu dole mubi yadda kuke so to mu ba hakan al,adan mu yake ba dole sai ta zauna a hannun uwar miji kafin ta shiga zuwa dakin ta itama ta saka mata albarka.
Ji mun mata da kafewan tsiya wata ta fada daga gefe to har in zaman lafiya kukeso a aiwatar dolene taje dakin ta a yau din nan kamar yadda kowa yasan anayi din, kuma wanan sallon uwargida kanta bata yarda dashi ba don ba haka aka san anayi ba ko ina.
Au uwargida ta aura ko mijin su da mahaifiyarsa sune muka sani a jigon aure babu abinda ya damemu da damuwar uwargidan a nan mu