Showing 66001 words to 69000 words out of 382072 words
Tace Surprise u small pikin u know all dis tins in ur life ? d u have d that my ogo no look anoda worman again after me.
Na shiga kiciniyar bude leda ina fadin if u use dis one e no go see any woman again i swear ina daga hannu.
Mukai ido biyu da chukuma dana fara zargi a yanzu don sau uku ke nan ina yawan ganin shi a inda nake yawon tallana.
Dan rudewa nayi na shiga yiwa matar bayani a gurguje ta karbi na haihuwa dana kama miji a cewan ta .
Ta miko min kudi mai yawa na karba ina godiya tare da fatan maganin ayi nasara abinda ake nema tana fadin Amen ta hanyar daga hannuwan ta.
Ina sauri nake tattara kayana in bar wurin naji muryan a baya na ana fadin i wan buy local medecine for my pikin.
Ba tare dana juyo ba nake fadin i no go sella,am for men ina sauri naga an tare min hanya bayan wanda ke bayana din.
Waitin u wan do for me now, comot for d road , or i will shout oley for u naw, na fada a dan hasale .
Katin shedan su ya ciro ya nuna min ban fahinci na meye ba sai kayan kakin dana gani na gane me hakan ke nufi.
Waitin i do for u, see me see wahala woo, me i no do antytin wain solder man wan cach me naw, .
Motan dake gefen shi ya nuna min da hannu na dan saci kallon bindingan dake gefen shi da ido ba musu na nufi wirin motan ina waige ko zan samu mai cetona.
Allah da ilon shi kuwa a take yan wurin suka taso suna fadin ogo waiti dis gurl do for u she no fait with any body here.
Why you go arest her naw, waitin she do for u ? suna kallona suke tambaya daga inda nake tsaye da naji sun fara magana naja na tsaya inacewa , me i no do anytin for dem broda.
I don't no dem, nd even who dey are ma self, still card din shi ya ciro ya nuna masu sai suka fara darewa daya bayan daya suna sulalewa daga wurin don ba mai son wahala ta ritsa dashi a cikin su.
Tare da buhuna suka turani motan suka bar wurin kamar walkiya har mukai nisan tafiya ban kula da wanda ke kusa dani ba a lokacin.
Duk ina sake sake a cikin zuciyana na yadda zan samu in kubuta a garesu shine kawai abinda nake yi lokacin.
Don nasan idan Umma na bata ganin ba ranan zasu shiga wani hali na tashin hankali su dauka an sace nine.
Duk a yanzun din ma ba zan iya cewa ga wa yanda suka dauke ni ba ma don ban san abinda nayi masu ba suka sakani motar su haka.
Saidai idona yana kyankyashe ko dar din hawaye ban sake ba sai bin titin nake da kallo naji an jefo min tambaya da what is your mother's name ?
Na dan juyo a dan firgice na kalli mai maganan saida na dan kadu da ganin shi lokaci guda haka a gabana .
Shiru nayi don ko bindiga suka saka min ba zance ga sunan umman mu ba a rayuwana saida na bayan yace min u no hear he de asking u.
Nace a cikin e,e niya i don't no her realy name we de call her with umma by name.
Dan shiru ya biyo kafin yace which tribe are you nace, my mama told us we are hausa fulani by tribe.
Okay yace ya dan gyara zaman shi kafin ya sake fadin, from which state nace she no tell me that i only know we come from north side dat what she told me.
Yace so ke baki san sunan gari ku bama a rayuwan ki yana gyada kai na dan bishi da harara muka shiga go slow daya fara marance.
Allah maijin kan bayin sa a haka yana min tambayoyin ina bashi amsa daidai gwargodon sanina wani yazo ya daki motan nasu sai wanda ke gefena ya fita fada da maishi.
Ban tsaya jiran wani abuba na balle motar nima na fita na yanka a guje sai gani na bullo wani unguwa da ma ban taba shigan shi ba.
Haka na tare me keke na hau zuwa wani titin ina zuwa na fada motar da zai kaini unguwar dake kusa da namu do ba,a samun mota daga nan .
Har lokacin gabana sai faduwa yakeyi Allah yasa kudina yana jikina can na barsu da buhun maganina na gudo har nakai gida ina tunanen hadina dasu da suke min wanan tambayoyin haka.
Sukuku na shiga gida har umma taso gane hakam nasan in na fada mata ba zan kara shiga gariba ke nan kuma ni ba zan iya zama a gida ba saboda sabo da fitan da nayi a rayuwana.
Don haka na shatata mata karya na samu na kwanta tare da karyan kaina ke min ciwo a ranan ina faman tunanen inda zan canza ba tare dana kara haduwa da wanan mugun mutum da a yanzu yake son shiga rayuwata ba.
Washe gari din na dai fitane ba zance ga inda zani ba kawai na sakai na bar gida na dade a bakin titi kafin na nufi surulere da niyan yin wani sana,a acan.
Ance ido wa ka raina don Alh Nuhu ga hjy Addah ya sauke haushin danta don ya taso Nazifa gaba da uwarta har gida suka samu hjy.
Sai abinda ya raga mata nacin mutunci hjy sai hakkuri da take bashi kawai a lokacin bayan haka bata iya furta komai ba.
Har yana ikirarin ta kira danta yazo ya sake mashi ya don ba gadin gida ya kawo ta nan tayi masu ba a cewan shi.
Hjy dai ta rasa na fada sai ayi hakkuri take fada jin abin yayi yawa yasa hjy karima fitowa daga part din ta kamar da gaske.
Tana dan basu hakkuri tare da fadin haka yake tun farko ya kamata, ace sun sanda hakan don haka aikin shi ya gada.
Nan dai ya kare masifan shi tare da jawa hjy kunne akan suyiwa dan su fada shifa bai daukan haka ga diyan shi ko kadan.
Tun fitan shi hjy ta zauna tayi shiru abin duniya ya isheta akan wanan aure da ba koyi wasu watanni da shiba an fara samun baraka haka a tsakanin iyayyen auren kan yaran nasu.
Abinda kowa ke gudu ke nan a yanzu yasa ba wanda ke sha,awan hada wani alaka dashi kan aure da diyan shi itama din dai kaddaran haka ya jata har ta furta a gaban yar uwanta cewa tana son zabawa dan mata .
Budan bakin ta sai cewa tayi da hjy me zai hana ki zaba mashi a cikin yaran yaya Nuhu gasu nan kyawawa dasu mazan yanzu ai irin su suke so .
Yan boka kuma ga wayewa wanan zancen ne yar uwan hjy din ta dauka kafin hjy takai ga yanke shawara takai gidan dan uwansu din.
Matar shi uwargidan shi naji hakan ta dauki zancen da zafi takai gaban mijin su tare da kara gyara zancen tayi mai kwaskwarima har Alh din yaji shima yana sha,awan wanan hadin a tsakanin yaron da dayan yarshi .
A take hjy ke fadin ai zasu fi dacewa da Nazifa nake gani don gashi dama shima din wayayye ne kuma dan gata kamarta.
Don shi kadai ne da namiji a wurin mahaifin su a yanzu sai nake ganin kamar hadin nasu zai dace gaskiya.
Shima Alh Nuhun a lokaci wani irin shu,umin murmushi ya sake don akwai abinda yake bukata a wurin wanan yaton nan gaba sai yake ganin ai wanan dama ne a gareshi ya samu.
Wanan ne dalilin hadin auren su daya taso haka kai tsaye kuma Alh Nuhun ya matse aka daura shi a kam lokaci.
Tun bayan daya gano cewa yaron yana son ya subuce masu a karshe yasa daurin auren cikin dan kankanin lokaci kuma akayi haka.
Yawan son diyan shi dayasa a zuciyar shi yasa yanzu da Nazifa ta kawo karan mijin nata ya rufe ido yayi masu cin mutunci ya tafi.
Tafiyan shi keda suya hjy Asiya ta shigo gidan a nan ta samu hjy a cikin tashin hankali da farko hjy ta boyewa kanwar mijin nasu amma saiga hjy karima ta fito itake labarta mata duk abinda ya faru da shigowan dan uwan nasu kan zancen diyan su din.
Budan bakin hjy Asiya sai cewa tayi ai dama yaya Nuhu mutumin banza ne baida tunane sam a rayuwan shi idan idon sa ya rufe yana iya yiwa mutum komai kan yayan sa.
Da alama kan yadda yazo gidan nan ido rufe shi da matar sa da yar tasu a gabanta ya fadawa maman Nabila komai da yake son fada.
Hjy dai tana jin su bata iya tankasu ba sai maganan banza suke fada game da dan uwan nata tana sauraren su kawai don tasan dama irin daman nan suke jira su fada mata cikin zuciyar su game da auren na Abubakar.
Don tana sane da son hadin yarta da hjy Asiya din ke so tun da dadewa kuma har ta gabatar da zancen gaban dan ta yaki yarda.
Wanan wace irin yarinyace haka kamar yar daba yarinya tana abu kamar wata mai tabin hankali ?
Anya ma kuwa wanan ba wahalan banza yakeyi ba akanta ita din kuwa yar uwasu ce kodai watace can na daban yake wahalal da kanshi akanta yanzu.
Zama ya gyara yana fadin to amma kuma ai kamarsu ya baci da yan gidan don ma har ita wanan din idan ga gata harta zarta yaran gidan yake gani wurin yin kama da iyayyen su.
Don da ganin ta kaga yar fulanin asali da ita saidai da ta bude baki tayi magana zakafi danganta ta yar wani kabila da ba hausawa ba.
Koma dai wacece ita ya sha alwashin cewa zai taimaka masu tasan ko ita wacece tunda ta shigo rayuwan shi a yanzu.
Haka kawai dan interview din da yayi mata da wanda ya hada tun farkon haduwan su sai ya gane yarinyar tana son tasan mahaifan ta da jaharta.
Kai mutanen mu na arewa akwai kaskantar da kansu a irin wanan wuraren da ba, a san daranjan su ba.
Ta yaya macen bahaushi zata zube yara kamar haka tana yawo a cikin gari wai tana tallan magani da sunan neman kudi.
Dan murmushi ya sake don tuno da kayanta data sake a cikin motar su ta gudu ta barshi garesu in ba shirme ba nawa zata samu ga wa yan nan kayan da ya gani a cikin jakarta.
Shawara da Nazari yaci gaba dayi shi kadai a dakin yaga dacewan bibiyan case din ya zauna mai a zuciyar shi yace koma meye tsakanin yau da gobene zai shawo kan matsalam su don zai binciko har uwan yarinyar nan yaji idan yaran ma suna da mahaifi.
Gaban shine ya fadi ya dauko waya ya fara neman layin chuku yake sanar mai cewa zuwa gobe yake son su kama yarinyar nan suzo da ita don akwai tambayan da yake son masu ita da mahaifiyar ta.
ALIYU MAKAMA THE BOY zaune yake a hadeden gidan shi dake Apapa Alabi street dake tall get .
Yana zaune kasa don nan yake zaton zaiji dadin zama a wanan yanayin daya daure mai kai a yau don yau dai taron nasu ba,a watse shi da dadi ba.
Don shawara yasha bambam a tsakanin da abokan kasuwancin nasu dake da shawara daban daban kan yadda suke son su canza arkalar su a yanzu.
Shikan gaskiya a wanan katon yasan zasu raba hannun riga dasu don baida ra,ayin shiga wanan harkallan tasu tun farko.
Don bai fara wani kasuwanci ba irin na mahaifin shi saida ya dan koyi wasu abu daga halaiyar mahaifin nasa na gaskiya.
Shi tun farko dama bai yarda da wa yan nan kurayen kudin da yake tare dasu ba kuma bai taba zaton suna wanan haramtacen sana,an haka a cikin tafiyan su.
Hannu ya mika ya dauki cup din dake gaban shi cike da lemo tattaciya ya dan kurba ya mayar ya aje a inda ya dauka.
Don yadda yake jin kanshi a yau sai yaji kamar ya kurba ruwan guba ne a cikin sa lokacin don bacin rai.
Taya yayyafi zai masa haka ya boye mai abinda ya saka a cikin kayan shi har yayi kasadan fitar mai dashi tun daga turai har nan kasan ba tare daya san hakan ba sai yanzu da yaron shi ya tsegunta masa hakan da sukai mai.
Akarshe dai yasha alwashin zai masu yankan baya ta yadda zai iya fitar da kansa daga zargin da aka fara jefan shi dashi zai nuna masu shi din jan koma ne idan su kifaye ne masu kwakwalwa daskare.
Da wanan tunanen ya mike tsaye daga inda yake zaune din zuwa dakin kwanan shi don yau baijin fita ko ina don yadda yake jin kansa din.
Haba dole ashe yan sanda su nemesa haka ruwa a jallo don wanan abin yace a fili rai a bace dan guntun murmushi ya sake don shawaran da zuciyar shi ta zauna a kai lokacn.
A haka barci ya dauke shi mai nauyi har da mafalkin sun hade da yan sanda ana gumu dashi kan wanan case din daya zauna mai a rai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , , , , , ,
2️⃣0️⃣
BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUHAY,MIN, , , , , , , ,
PAID ONLINE NOVEL DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA KADA KI DAUKARWA KANKI NAUYIN WANI KI KWASHI ZUNUBI, , , ,
Yau kan da farin ciki na tashi duk da ina jin abinda yanzu ya zame min jiki ko yaushe har zan iya cewa na yau din yafi na kullun .
Sai dai hakan bai dameni ba a yanzu don kamar ya zamo min jiki a yanzu din
Nayi sallama da umma kamar yadda na saba a kullun idan zan bar gida na kama hanya zuwa neman sa, a a gari tare da tunanen ina zan dosa a ranan.
Tsayuwana na gyara daga inda nake tsaye ina tunanen inda zan dosa naji murya a gabana a na fadin ekeja.
Ban tsaya tunane ba ko la,akarin motan na going ya tsaya na shiga daga ni sai driver a lokacin daga shigana sanyi da kamshi ya daki hancina ban kara sanin inda nake ba sai dai na bude ido na ganin a cikin wani saki mai kyau dashi ga sanyin AC ga kamshi na tashi a dakin duk da dakin na da duhu a lokacin .
Sai dai duhun bai hanani gane hakan ba abinda mutum bai saba dashi ba dole inga bambamcin ga hakan.
Kokarin yunkurawa nayi don in tashi naji ban iya koda motsawa a lokacin innalillahi na fara fadi ina hawaye tare da tunanen shike nan na fada hannun yan mafiya ke nan a yau abinda kullun umma ke min addu,a kanshi ke nan yau na fada tarkon su ke nan Allah ka fitar dani hannun wa yan nan azzaluman lafiya.
Ya Allah kada ka basu ikon cutar dani koda dingon kwayar zarah duk a cikin raina nake wanan adduan ni kadai a dakin kwace an dare min hannaye da kafa.
Duk wani kokarin da zan iya don in kwance kaina saga daurin da sukai min nakasa yi gashi dakin shiru baka jin motsin kowa a cikin sa lokacin.
Don zan iya cewa nikadai ne a wanan gidan ko daki zon rashin jin motsin komai da banyi tun lokacin dana falka din daga barcin dole dana tafi.
Hawaye ya fara zubo min lokaci daya ba abinda nake tunane sai mahaifiyana da dan uwana irin halin da zasu kasance na rashi a yanzu.
Kai hardai na gaji na daina kukan na koma ihu duk da banyi zaton akwai wani a wanan gidan da nake ba a lokacin ina nemam ceto da fadin.
Somebody help me, help please, help help sai kuma na fashe da kuka mai tsuma zuciya lokaci guda.
Nayi ihun na nemi taimako ba wanda ya lekoni dakin nagaji nabarwa Allah ikon sa na shiga yin addu,a ido rufe .
Gaskiya tashin hankali baida dadi a rayuwa don nayi tunane kala kala lokaci guda har na rasa na kamawa a cikin tunanen nawa da nakeyi.
A haka har dare ya riskene a wurin kwance a daure a cikin yanayin gala baita da tausayi ga duk wanda ya ganni a lokacin.
Duk da ban san lokaci ba a yadda nake a dakin tun safe har wanan lokacin da nake tsamanin dare yayi a lokacin.
Naji ana kokarin bude kofan tare da jin muryoyin maza a kokafan da alama