Showing 309001 words to 312000 words out of 382072 words

Chapter 104 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28358

Alaja ke son ta nuna min ina bin danta da mugun nufi saboda wani manufan da nake dashi kanshi na daban .
Dole haka zan daure in saba duk da nasan nayi rashi sosai a yanzu din amma haka zan daure in bar aiki karkashin danta ga baki daya don taron mutuncina kawai.
Ba,afi minti ashirin da fitan su ba gidan mu saiga kiran oga Shaa,aban ya shigo wayana har ta katse ban daga kiran nasa ba.
Bayan wani lokaci kuma ya sake kirana din wanan karon kan na daga mun gaisa sama sama yake fadin yanzu jimoh ke fada mai wani magana akan me zan aje aikina haka kawai.



ANA DARA GA , , , , , , , ,

9️⃣3️⃣BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL MUTA, ALI , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Dan shiru nayi kafin na bashi amsa nace is my wish na bar aiki daku a yanzu haka zaifi kwanciyan wasu na kusa dakai dake ganin ba aiki bane ya hadamu dakai a yanzu.
What a noses talk kike min haka akwai wani wanda ya ban shawara na daukeki aiki lokacin dana daukeki da har zaki aje aikin ki don jin dadin maishi ?
Hakan yafi min sauki na riga dana aje aiki dakuko ba zan kara shiga ma,aikatan ka da sunan aiki ba kuma hakan shine kwanciyan hankalina nima a yanzu.
Saidai na gode da duk irin taimakon da kayi min a baya Allah ya hada fuskokin mu da alheri amin na kashe wayan .
Duban wayan yayi yana mikewa tsaye don jin dadin tunanen da nazarin dalilin wanan maganan daya zo mashi a bazata.
Dole akwai wani abu a cikin magana na don nace nayi hakan ne don farin cikin wasu na tare dashi .
Toh waye har zan iya sadaukar da nawa farin cikin haka saboda maishi tunda yasan banda wani aiki bayan wanan da nakeyi a karskashin shi din yanzu.
Idan hakane ya zama dole ya kara bincike tsatsaura yaji a inane wanan matsalan da nakeyiwa barazana haka ya fito ?
Sam baiyi tunanen ya fara binciken Alaja dake kusa dashi kan haka don yasan banda wani matsala dasu da zaikai har ta kirani irin haka muyi magana da ita din.
Saidai hankalin shi ya tafine kodai akwai wani abu dake faruwa a cikin company daya hadani da wani dake kusa dashi har ya jawo haka ?
Jimoh din ya kara kira bayan sun gaisa yace ina son ka bincika min abinda ke faruwa koyi fada da wanine a cikin ma,aikatan mu ya jawo hakan.
Gaskiya banyi tsamanin hakan ba ga mis sahiba don ko kawa ko wani aboki bata dashi asalima kaika sani idan ta shigo aiki bata tsayawa kula kowa saidai ta wuce zuwa aikinta.
Yanzu taki fadama matsalan da aka samu ke nan ko me don nima nayi da ita ta fada min meke faruwa taki fadin komai sai cewa da tayi tadai dakatar da aiki damune don kanta.
Nisawa yayi a hankali kafin yace ni ta fada min ta dakatane don farin cikin wasu na tare dani kaga kenan akwai matsala ke nan a cikin maganan.
Lalai kan dole akwai abinda ya faru wanda bata son ta fadi dalilin yanzu saidai gaskiya barin ta tafi ba alheri bane a wajen mu don samun mai aiki tukuru kamar sahiba yanzu sai an tona gaskiya.
Abindake damuna yanzu ke nan akan wanan maganan don dole mugano inda matsalan yake a gyara haka kawai ba zata yanke wanan shawaran kai tsaye ba.
Haka suka aje maganan suka kashe wayan kowan su yana cikin damuwa lokacin shikan Jimoh bincike ya fara yi sosai ko mun samu matsala da wani a ma,aikatan saidai bai gano komai ba.
Dole a karshe ya nemi Abdul akan ya taimaka masu ya zauna dani asan abinda ya faru har nake ikirarin barin aikina dasu.
Daukan wayan yayi lokaci guda don yasan tun bayan aikin daya bashi yauce rana na farko daya kirashi a waya haka gaisawa sukayi mai kiran na bashi girma suka gaisa kafin ya fara fadin.
Yallabai yau kusan sati ke nan yarinyar nan bata fita zuwa wurin aikin taba kuma lafiyan ta kalau don ina ganin tana fita zuwa cikin gari yin tsabgogin gaban ta ta dawo gida saidai sau biyu ke nan naga ta fita .
Amma takan dan leko mahaifiyarta a shagon su na kofan gidan ta dan zauna lokaci lokaci saidai abinda na kula kuma su ma,aikatan aikin nasu manyan ma,akatan sunzo gidan kusab sau biyu ke nan.
A yadda na samu labarin cewa wai ta aje aikintane don karankanta kawai don hakane ma,aikatan ke binta ta dawo.
Guntun murmushi ya sake har wanda suke wayan yana jinshi kafin yace good dama irin daman da nake jira ke nan a samu daga wurin ta zan kiraka idan na kare shirin da nakeyi nan gaba kadan.
Sukai sallama a gurguje yace zakaji sako daga gareni ka kara saka ido ga komai nasu dake gudana kamar yadda ka dauki alkawarin yi da farko yace insha Allahu yallabai za ayi yadda kace.
Bayan sun gama wayan dashi kasa ci gaba da aikin da yakeyi a gaban shi yayi ido ya lumshe a hankali yana tuno suran daya ganta ciki a ranan.
Ta ina zai fara ya tambayin kashi yana mai bude idanuwan shi lokaci guda ya sauke a saman laptop din shi dake bude a gaban shi.
Aiki zan jawota tayi ya ba kanshi amsa da sauri yace Nop ba zancen aiki a tsakanin mu sam dolene in fito fili in nuna masu kudirina a kansu yanzun kan.
Kaima kasan da wuya su iya tattarowa su dawo gareka kai tsaye haka yadda kake nufi dole sai ka juye zancen a cikin siyasa wanan lokacin.
Don yarinyar tana da balain wayaun tsiya irin na matan zamani idanuwan ta da gani a bude suke ba irun su bane akewa farat daya a kamasu ba.
Yaya zaiyi ke nan hakan yasa ya dan kishingida ya tokare haban shi da hannun shi daya dake rike da biron da yake rubutu dashi yana dan juya kanshi saman kujeran.
Kafin can ya sake wani malalacin murmushi a fuskanshi lokaci guda yana aje biron wanan karon hannayen shi ya hada wuri biyu ya tokare haban nasa yanaci gaba da tunane.
Wayan shi ya danna yana gyara tsayuwan bluetooth din shi a kunnen shi ya soma magana cikin bada umurni ya fadi abinda yake son fada a daidai lokacin da matarshi hamida ta shigo office din nasa na gida da yake zaune.
Har ta karaso wurinshi yana zaune yadda yake saidai zaka dauka ita din yake kallo a lokacin sai lokacin da tazo ta zauna a hannun kujeran ta dan shafo jikin shi ya dan sauke siririn ajiyan zuciya yana dago kai gareta.
Ya na ganka kamar kana cikin damuwa dan murmushi ya kara sakewa kafin ya shafo fuskanshi da tafin hannun shi yana fadin.
Ba damuwa bane hakan nasarane nasarane akan rayuwan mu ga baki daya na hango na gane yanzu lokaci yayi da gurina dana maigidana zai fara cika.
Tsaman ta cire hannun ta saman suman kanshi da take dan yamutsawa tun zamanta gefen shi tana mikewa tsaye tare da dab takawa daga inda yake zaune din takai wurin window ta tsaya tana kallon haraban wajen.
Allah ya gani a rayuwanta taki jinin yai maganan wanan ubangidan nasa dashi da mahaifiyar su duk magana suce da badon ubangidansa marigayi ba da yanzu suna cikin wahala tsunbul ko.
Yaushe Allah zai hadashi da iyalinshi ya rama masu Alherin shi gareshi Allah ya gani a wurinta wani tunawa da ubangidanshi ko wani zancen tausayi yanzu duk bai taso ba a gareshi.
Su iyalinshi ya kamata ya duba ya ginasu kamar wasu yayan lu,u,lu,u ta zama abin kwantace a duniya ita da yaranta biyu da Allah ya basu.
Saidai kassh koyi da wanan mugun ubangidan nashi da bata sani ba da yace yanayi a yanzu shine mafi girman abinda keci mata rai a rayuwa.
Duk da yana sake mata hannu yana kuma kyautata ma yan uwanta duk wani bukata nata ya tsare saidai ita kan ba hakan takeson shi dashi ba.
Taso ace ta sameshi a hannu tana juyashi yadda takeso sai abinda tace dashi zaiyi a rayuwa ko kuma ta hanashi ya hannu.
Duk da hakan ma ba laifi tasan tayi dace tabada tazara ga sa,oin tashin su ana kuma kwatance da ita a cikin matan da suka isa suka kai a yanzu din.
Dan tunane tayi da sauri ta washe don tunawa da tayi idan ta nuna hakan a fili akan wanan zasu iya samun matsala dashi don ta taba gwadawa bata sha da dadi ba.
Hamida ta kasance irin matan nan ne da basu son mazansu suna alheri don a cewanta yawan alherin shi kamar ita da diyantane yakewa illa da hasaran dukiyan su don shi bai iya alheri kadan ba.
Wanan yasa sam bata son kowa ya mameshi shima din zuwa yanzu ya gama fahintan waye ita don haka bai zama dole tasan komai nasaba a yanzu.
Shida ita aurene kamar na gida duk da ba wani zumunci bane a tsakanin iyaka dai alkawarine tun na kurciyana da akan fara soyayya iyayyen su mata kuma kawayene shine ya kara kulla alakasu har ya kaisu ga aure duk a lokacin mutane na fadin tama girmeshi amma shi yasan bata girmeshi iyaka dai yan sa,a guda suke da shekara ma ya darata da aji.
Koshi don ita an mayar da ita bayane a lokacin yasa ya fita da ajin haka kuma bayan bin wan mahaifin shi da yayi zuwa waje da sunan za a sama mashi gurbin karatu a can inda suken.
Saidai suna zuwa labari ya canza inda yazama yaron gida shine aike da duk wani sauran aiyuka nagida a lokacin cikin haka babban dan wan baban shi da yake hannun shi ya kwashe wa mahaifin nasa wasu makudan kudi a karshe aka laka mai duk da iyayyen nasa sun san bashi ya dauka ba dansu na cikin sune ya hada gagarumin party da turawa da kudin .
Bayan sun rufe ido sun mashi bugun tsiya tare da kora gashi baisan kowa ba a kasan passport dinshi kuma yana hannun su sun rike wanan duk muguntan matar wan baban nasa ne wace take yar uwa a gun mahaifiyarshi a gida .
Amma take nuna mashi tsana da tsangwama kasancewan shi a cikin yayanta da sam.bata son hakan ya kasance dashi tunda saida ta hana mahaifiyar shi auren dan uwan mijinta taki yarda a lokacin.
Ya Abubakar ne zaune a kasa gefen kafan mahaifin nasa da suke ganawa na siri dagashi sai dan nasa a lokacin don maganan da dan yazo dashi tanada muhinmanci sosai a rayuwan su.
Ba wani magana bane illa gaba da gaba da Abubakar din yayi da mahaifin kan lalai ya fada mai gaskiyan maganan dake tsakanin shi da dan uwanshi marigayi da tuhuma yai yawa akan mahaifin shi din.
Don wanan dan takifin mutumin mukhatar din da gaske yakeyi a kansu kan duk abindaya sani sai an tsaya a kotu sun fada.
Daddy idan baka fada muna a yanzu mun san komai ba zaiyi wahala mu iya kwatoka a hannun wanan mutumin a yanzu don yana da burin kargameka a gidan maza.
Nasan yana da gurin yin hakan don da gaske yazi lauyoyi a can sun fada muna duk wani tuhuma da ake muna wanda mamu nan mun manta da anyi hakan .
Daddy ya gyara zama yana fadin watau mudibbo na dade da sanin wanan lokacin yana tafe son zuciyana yana bani cewa da akwai wani wanda yasan komai na Sambo bayan ni.
Don hakane na zauna na tsara komai amma kuma kasan dukiya da shiga rai da ace nayi dubara lokacin da kakawo min iyalin sambo da farko na mika masu dukiyan su a hannun su da duk haka bai taso a yanzu ba.
Hakane daddy modibbo din ya fada tare da fadin ko zan iya ganin takardan a yanzu inda ka rubuta komai din don asan inda za a fito masu.
Dan shiru daddy yayi kafin yace da dan nasa inaga basai an duba wani takarda ba nima a yanzu nafi bukatan na dakawa mutanen kayan su a hannun su ko hankalina zai kwanta ga komai.
Daddy idan kayi hakan yayi kyau sosai ga al,amarin amma kuma anya duniya zata yarda da mika masu komai haka tsakanin ka dasu kuwa ?
Bandamu da zancen mutane akaina ba yanzu abinda nayi niyar aikatawa shi zan aikata akaina dasu final.
Kai ya gyada cikin gamsuwa da abinda mahaifin nasa ya fada lafin yaje bakin shi yayi shiru lokaci guda yana nazari kalaman mahaifin nasa.
Kafin ya daga kanshi dake duke yana fadin daddy zan koma Allah yasa mu dace mahaifin nasa ya busar da iska yana fadin amin zan kokarta naga hakan ya faru.
Part din mahaifiyar shi ya nuna bayan sun gaisa da kanin shi da a yanzu sauyin rayuwa ya samesu na dan aikin da suka samu suna biyawa kansu wasu bukatu nasu da ba sai sun roka ba an ja masu rai a yanzu.
Hankalin shi ya mayar gun mahaifiyar shi ya kara gaida ita a natse kafin ta jefo mashi tambaya kaje kakai masu abincin kamar yadda mukayi dakai zaka kai ?
Na dai tura ankai masu don ni banje da kaina ba kamar yadda mukayi mommy don ko naje gidan da kaina ba lalai bane in samu shiga ciki mu gana dasu.
Kana ganin hakan yayi maka ke nan kowa ya ganka yasan abinda ya kawo ka ai donme zaka damu sa zancen wasu can a kan ka ?
Shiru yayi babu amsa a lokacin don yasan ba zai iya shiga gidan ba a yanzu gaskiya saboda gidan babbam gidane mai tarin mutane da yawa a cikinsa.
Don haka ba zai shiga ya dinga faman gaisawa da tarin matan da zai sama a tsakar gidan ba gungu gungu ya dinga gaidasu.
Hauwa ce ta taimaka mashi ta jefo mai tambaya akan aikin ta ya tsaya bata amsa har hankalin mahafiyar nasu ya dauke ta shiga daki ya samu ya sulale daga gidan ya nufi nasa gidan kai tsaye.
Zaune muke da umma da muniya har matan kanin mijinta da suke zaune dasu a yanzu a wajen gidan mu muna hira mukaga dawowan mijita daga wurin aiki.
Itace ta tashi ta nufi wurin shi sai gasu sun samemu a tare dashi zuwa inda muke ya gaida umma dagida dake mai sannu da zuwa.
Sun dan taba hira kafin ya juyo kaina yana fadin eh sahiba na your eyes be dis i no see u all dis days.
Na dan sake murmushi ina gyara zama tare da fadin i dey wooo bani dai son fitowa wajene koda yaushe na bashi amsa a takaice kafin na dukar da kaina ga wayana lokacin.
Zanso ganin ki anjima idan na dawo daga magariba ya fada sai lokacin na kara dagowa ina fadin OK.
Basu dade da shiga part din su ba namike na shige namu part din yan aikace aikacen gida nayi a lokacin na dora muna girkin abinda zamuci.
Nagama tsab dama ga al,adan bayerabe kafin ya dora girki ya tanadi duk wani abinda yake bukata ga abinda za a girka din muma zama a cikin su haka muka sabadayi.
Shiyasa da mun dora girki yan lokaci kadan sai kaga an gama shi a cikin lokaci haka kuma abincin dai bawai wani dahuwa ake bari yayi sosai ba don haka suke girkin su dama.
Bayan isha,i saigashi yayi sallama falon ya shigo suna gaisawa da umma na fito muka gaisa yake cewa dani dama ba wani abu bane don Allah tambaya yake son yai min.
Zagayowa nayi na samu kujara na zauna ina fuskantar shi yace ya dauka a matsayin da muke yanzu dashi mun zama yan uwa mu dashi.
Saidai ashe abin ba haka yake ba mu a wurin mu don inda na daukeshi kamar yaddashi ya daukemu ba zan aje aikina ba tare dana fada masa dalilina ba nayim hakan.
No kada ka damu da wanan ni a wurina wanan ba wani abu bane da zan dinga bin mutane ina fada masu dalilina shiyasa ban fadawa kowa cewa ga dalilina ba ai.
Amma ai ko bamu fada ba ansan mun daukeka a matsayin dan uwa yanzu don mun wuce makwabtaka damu dakai.
Wanan amsan da kika ban yanzu Sahiba bashi zai sa na gamsu ba har sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login