Showing 183001 words to 186000 words out of 382072 words

Chapter 62 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28393

ko aminiya ba sai zuwan mu kaduna shakuwa na da Faizan daddy yasa nasan muhimancin mu,amula da sa,an ka.
Abubuwa da dama nakan so in damu wata muyi shawara saidai wacece zan sama tunda ban shaku da kowa ba a rayuwana dan dama wani lokaci mukan zauna idan weekend ne ban fita ba tare da muniya matar Abdulhamid muyi hira .
Saidai tsiyan abin ban yarda hiran yai tsawo don rashin sabo da mutane da bamuyi ba sai tsakanin mu kawai muke mu,amula mu kadai duk wanan kuma yana cikin tarbiyan da muka samune a wurin umman mu don kokarin nisanta mu da mutane da tayi.
Ranan da ya Abubakar yazo umma ta sheda mashi na tafi wurin aiki yake tambayan aikin me nakeyine ta fada mai a wani company nake aiki kuma a na samu sosai ga aikin .
Don yanzu dana kare karatuna akwai samu sosai a wurin Alhamdullahi gaskiya mama dama Sahiba tayi karatune ya tambaya a cikin mamaki.
Ikon Allah umma ta fada ta mike ta shiga daki ta dauko mashi takardun karatuna ta bashi ya duba ya dade yana nanata karantasu.
Ya dago kai yana fadin ikon Allah dama ashe ta tsaya har tayi karatu haka toshi yana ina har haka ya faru wai ?
Gaskiya dolene yaran nan su ja baya da kowa a yanzu duba ga yadda aka watsar dasu haka a cikin duniya bayan kuma asan suna raye a doron duniyan kowa ya fita batun su har daddy din.
Wai dai zancen Nazira ko yana da kamshin gaskiyane daddy na da hannu cikin wanan kisan da akayi yasa baya son a tayar da zancen yake ta fadin lokacin tayar da zance baiyi ba.
Wani lokaci yake jira ayi wanan case din sai lokacin da wani daga ciki ya mutu ko sai lokacin da ba musu case din za ayishi.
Ya gama tunanen shi ya dago kai yana cewa umma kai gaskiya mama wanan abin alfaharine ga kowan mu wallahi saidai bai kamata ace ta tsaya aiki a company ba don basu da tabbas ga hakan.
A, a a kada kace hakan don wanan aikin mu mun samu rufin asiri sosai a cikin sa ta yadda ba zamu raina hakan ba a garemu.
Na sani mama amma ina nufin tunda tana da takardu haka masu kyau me zai hana a sama mata aiki a karkashin gwaunati tayi zai fi wanan din da takeyi yanzu idan an samu.
Koda kuma za,a samu din ya kasance dai a arewa za a samo mata don yanzu in son samune nafi son ku koma gida kusa da yan uwa ku zauna.
Take annurin fuskan umma ya canza lokaci guda take fadin a, a ka barmu nan inda muke don zaman mu nan yafi min kwanciyar hankali da komawa can inda fitina da tsegumi zai hanamu zaman lafiya.
Sai dai idan har kun yarda mu dinga kai ziyara muna ganin wanan baida matsala amma a yanzu hankalin mu ya fi kwanci da zaman mu a nan.
Shiru yayi yana dan tunane kafin yace mama masan abinda kike tunane don matsalan ku dasu uncle nuhu ne hakan kuma a sannu an kusa kaiwa karshen zancen insha Allahu.
Don ina bincike yanzu sosai akan matsalan ba tare da sanin kowa ba don bana son kowa yasan da ina wanan binciken gaba daya har daddy ban yarda da su san da zancen ba don na kula indan na yunkura kamar ana tosheni ga hakan.
Idan har haka zai ja matsala a rayuwan ka modibbo gara a rufe wanan zancen mu hadu a lahira dasu Allah yai muna hissabi a gaban shi umma ta fada da sauri ta kara da fadin.
A yanzu bamu da abinda zamuce sai godiya ga Allah da kuma gareku kai da dan wurin hjy harin nan dake zuwa wani lokaci haka kuma inda sahiba ke aiki a yanzu gaskiya banda abinda zan fada sai hamdallah.
Jin an ambaci sunan mustapha ya bata fuska don baison jin hakan ba sam bai dau son mu,amulan mu da wanan guy din yasa yace na dai fada maku kuyi hankali dashi mustapha din.
Ya kwana biyu ma baizo nan ba ai tun lokacin da yazo kan matsalan maganan da kai masa mutanen kan Sahiba suka taka tafada mai abubuwa da dama a game dashi tun ranan ban sake ganin shiba gidan nan.
How comes mama har kuka yarda yasan da wanan matsalan nata har yaji komai a bakin ta ya fada a dan tsorace cikin mamaki yana buga hannun kujeran da yake zaune a kai.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


ANA DARA GA , , , , , , , ,

5️⃣4️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL JALIL , , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

Duk yadda yaso yaja ra,ayin umma ta yarda da shawaran daya zo mata dashi umma taki yarda da hakan karshe sai cewa yayi idan na dawo tayi shawara dani taji.
Don shi dai yana son komawan mu gida kaduna sai asai muna gida can mu zauna yafi zaman mu nan da muke mu kadai.
Kallon umma nayi bayan ta gama fada min ina fadin umma me haka ke nufi dayazo dashi ko yana ganin nan din zama mukeyi cikin rashin kamun kai ne ?
Ko kuma gidan sa daya saya muna yake son mu bashi idan ba haka ba muna zaune kalau zai fito muna da wanan maganan yanzu.
Ina ganin dai wani abu yake hange ga hakan har yakawo wanan maganan don nima dai nayi tunanem dalilin shi na fadan haka ?
Babu ida zamu saidai din in yakama watarana mukai masu ziyara a can amma yanzu gaskiya umma zancen su kaf ya fita a raina tunda sun nuna duk suna kyaman mu.
Munjima muna zance da umma kafin kowan mu ya kama gaban shi don dare yayi a lokacin haka na kwanta da jin zafin maganan a raina sai fadi nake ina ruwan shi da aikina kuma idan ba hassada ba ko kyashin hakan.
Naga dai hakan ai abin farin cikin ne ga duk wani mai kaunata da ci gaba in koma arewa in zauna yadda saura suke zaune ko me ?
Tun safe aiki nake yi tukuru don haka ban diba wayana ba sai lokacin da nafito zuwa sallah azahar muna gaisawa da wasu daga cikin ma,aikatan mu lokacin na nufi inda muke sallah na gama daga inda nake zaune ne na jawo jakkata don gyara fuskana.
Lokacin ne idona ya sauka a wayata na dauko don in kira umma inji lafiyan su don haka dabi,atace duk inda nake a daidai wanan lokacin zan kisu inji lafiyan su.
Miscall din da nagani ne a wayan da bakuwar nomber ya ban mamaki sosai don nasan ban ba wani layin wayana da banda sunan shi ba.
Umma na fara kira kafin na kira mai layin wayan dana sama an kirani dashi ringing uku aka daga nace sallamu alaikum who is on d line please ?
Sahiba aka fada a cikin wayan nace yes its me Sahiba who is speak na tambaya a gagauce don jin muryan mace da dan hayaniya a wurin maimakon inji anyi magana sai ji nayi ance .
Wayyo Allah na kuzo wallahi ga Sahiba ta dauki wayan jin hakan yasa naji gabana ya wani mugun faduwa sosai na kara fadin who is on the line please karo na barkatai.
Sahiba Fa,iza ce daga kaduna take magana Fa,iza na kara maimaita sunan a cikin mamaki ina fadin who is Faiza is wrong number you dial bye.
Da sauri tace your sister from kaduna so kon manta dani ke nan sahiba long time ?
Wait Faiza where do you get my number first ?
Bata bani amsa ba sai ihun da takeyi tana kiran sunayen yan uwa suzo ga sahiba yau a waya .
A take naji wani iri a zuciyana duk yadda naso in kashe wayan da farko duk da nagane mai magana a lokacin amma sai naso in share su kamar yadda suma suka sharemu tsawon shekaru basu nememu ba shine yau zasu kirani.
Sai naji kuma tana fadin kai itace kuwa wanan kamar ba muryanta bafa wallahi amma kuma daidai nasa number da yaya ya bani din ke Sahiba nice faizan mommy ina umma da Amar jin haka yasa.
Na sake dan murmushi nayi karfin halin fadin it, is you Faiza long time ya kuke nan ta amsa da lafiya ina umma nace tana gida ina wurin aiki yanzu
Ya kuke ya mutanen gida a cikon hausa da yanzu ya kara barkacewa don sai a gida gaban bako mukan juye harshe a cikin hausa don haka dole hausana ya fita daban a yanzu.
W Faiza ce a ina kika samu layina na tambaya a cikin mamaki ina kallon kasan wajen da nake zaune ina saka safa a kafa don ranan kowa shigan suit yayi a ma,aikatan namu.
Don haka nima shi din ke jikina da dogon bujena wanda ya banbanta da dinkin sauran don su dan karamine iya cinyar su suke sakawa nawa ko har kasa yake kai min ina dan banbanta kaina dasu.
Hankalina ne yadawo lokaci guda don ganin yadda hankalin mutane ya dawo kaina don ganin yadda nake waya a cikin fara,a ina nuna jin dadin haka.
Da sauri nake fadin i will call you back letter na kashe wayan ga baki daya don nasan zata dameni da kira idan wayan yana kunne yasa na kashe gaba daya.
Saidai ina aiki ina kallon wayan zakace fa,iza dince a gabana lokacin Allah Allah nakeyi a tashi inje gida in ba umma labari.
Tunda ya tun karo kaduna yaji kamar zuciyar shi ba zata daukeshi ba lokacin do bayan zafin da yake ji na ki yarda da zancen da yazo ma umma dashi ta nuna rashin amincewan ta ga hakan.
Sai kuma na samun Nazifa da hitinan ta da zaizo ya sama a gida don yasan ba zasu kwashe dadi da ita don ba irin matar da miji zaizo ya samu yaji dadi a wurinta bane.
Saidai a rabu da tashin hankali da fitina wanda duk itace kuma mai jawo hakan ya faru a tsakanin su yana kokarin yaga sun dan samu fahinta kodan mahaifiyar shi.
Amma kuma ya lura hakan ba mai faruwa bane don yarinyar ta dauki girman kai da raini ta dora a zuciyar ta sam bata zo da zaman lafiya a gidan shi ba.
Itace fada da yan uwanshi nuna kyama ga kowa nasa uwa uba ga rainin ta yanzu har ya kawo ga mahaifiyar shi don tana doluwa.
Mace mai son mijinta ta hanyar uwan miji take fara neman zuciyar mijin ta da sauran yan uwan shi koda kuwa yana nuna cewa shi bai damu da yan uwan nasa ba a fili dole in an taba su yaji kishin hakan.
Don haka ki zamo mai nunawa dangin miji kamar kece yar uwansu bashi ba a gaban su kada ki yarda ki dinga fada da dangin mijin ki haka na kawo ki fita ran mijin shi kansa watarana.
Ko ya kasance ranan da aka kara maki kishiya duk sai su watse su koma gun sabuwar suna yayin ta dole kina kallo hatshi mijin gaba daya sai a sayesu.
Amma Nazifa gaba daya bata tunanen hakan din batama taba wani tunanen ko zai iya karin aure ga mijin nata ba don tana ganin ita ta gama dashi ga wautan irin nata.
Tsoki yaja lokaci guda yana gyara zaman shi don yasan takaici zaije gidan kawai ya sama a lokacin zama ya gyara daga inda yake zaune a bayan motan ana jansa yana mai lumshe idanun shi a hankali don yadda yake jin kansa.
Bayan sun isa gidan ya sallami drivern shi bai shigo ciki ba sai daya dan zaga ko ina na gidan nasa don dai kawai ya rage tention din da yake ji a zuciyar shi..
Kafin ya samu ya dan saita kanshi zuwa ciki bai sameta a falo ba lokacin hakan ya bashi daman wucewa dakin shi ya kimtsa har ya dan kwanta don ya huta ba tare daya sanar da ita zuwan shi ba.
Saida tayi batcin ta ta tashi koshi yaran tane suka tayar da ita daga barcin don hayaniyar da sukeyi sun gaji da kumshewa a cikin dakin su ga ba wanda yashigo gidan kusan kwana nawa ba wani daya leko su sukade a gida sai uwarsu suke rayuwa.
Don ko makwabta bata taba shiga gidan su da sunan ziyara ba don gani take ita tafi karfin bin makwanci ai.
Watace mama Abdul ta danso shige mata karshe dole ta jaye don ba fuskan hakan zata zo tayi ta sallama har ta gani dole ta juya ta koma ko idan ma ta amsa ta fito zata tambaye ta da lafiya ?
Bata da laifi wurin yin hakan don a gidan su bata saba ganin hakan ba saboda har makwabtan su suna tsoron mahaifin ta kowa ya kiyayyi kanshi dasu su kadai ke rayuwan su da iyalinsu.
Yayi juyi yagaji yayi tsoki karona barkatai a saman gadon kafin yaji turowan kofan ta shigo koshi saida ta jima zaune falon kafin ta kula da sautin karatun da yasa a dakin nasa dake dan fitowa zuwa falon.
Shine ta tashi a cikin mamaki ta nufi dakin tana mamaki a fili har ta karasa ta hangoshi a kwance yaba kofan shigowa baya.
Baban mimi yaushe ka dawo ta fada tana karasowa cikin dakin tare da mamaki karara a fuskanta lokacin.
Saida ta fada kusan sau biyu gana uku ya juyo yana amsa mata a dakile don baisan da wace zata tare shi ba ga yadda suka rabu dashi da zai tafi.
Na dawo ya bata amsa tun dazun nakai kusan awa biyu ai da shigowa ya fada har lokacin duk yana kwance bai mike ba kafin tayi wani magana yar babba ta shigo tabar karamar a falo zaune hakan yasa tayi mai sannu a tsatsaye ta juya ta fita.
Ya jawo yar a jikin shi suna gaisawa can sai gata ta goyo yar da ruwa a gora gami da cup ta kawo mai saidai bai taba zaton hakan daga gareta ba gaskiya.
Mikewa yayi zaune a karba baya ta tsiyaya mai a cup yakai baki yana fadin bissimillahi a fili ta yadda duk wanda ke kusa dasu zai iya jin hakan.
Yako sha sosai don a gaban shi ta murda gora ya gani sabon budewa ne yasa yasha daba haka ba zaice ai yasha ruwa a jirgi kafin su zo.
Zaune takai a gefen shi tana fadin shine koka sanar damu zuwan ka gashi ban dora girki ba a gidan don yau mai aiki ta fita unguwa ta fada dama matar zata zo tayi masu abinda zatayi zuwa karfe daya sai ta wuce don bata yarda wai ta zauna ba.
Baida damuwa amma me kika bawa yaran nan sukaci tace aiba abincin sukeci ba cornflakes ne zan hada masu idan sun bukata.
Fuska ya kawar don baida abin fada a nan tunda yasan koya fada din ba gyarawa zatayi ba take fadin kona shiga na girka yanzu ne yace barshi kawai ban tare da yunwa yanzu ya fada yana mika hannu ya karbi yar dake bayanta goye yana dan mata wasa.
Daga inda take tsaye tana kallon su gwanin ban sha,awa bata san lokacin data lumshe idanun ta ba a hankali don sai yau data natsu ta samu kulawan shi take ganin ba macen data fita jin dadin miji ashe duniyan nan.
Shiko dan duniyan duk da sun ya kasance da mace dake damun shi bai yarda ya nuna mata damuwan haka a bangaren shi ba ya daiyi kokarin sassauta natsuwan shi da kuma maida hankali wurin nuna kauna ga yaran shi har yaga iya gudunta.
Kai ya dago ya kalleta itama dai din kallon su takeyi saita bashi tausayi a yadda tayi din hannu ya mika mata yana fadin zauna mana kin tsaya kina kallon mu kuma.
Dole in kalleku kun maidani ta ware kana zance kaida diyan ka kawai kun barni to ayi hakkuri ya fada sai ta kai zaune.
Bai samu leka gidan su ba sai washe gari da yamma ya kwashi yaran shi bayan ya zauna ya shiryasu da kanshi don ita madam din sai aukin barci da takeyi wai duk ta gaji shine ya shiryasu da kanshi zuwa gidan su su gaida iyayyan shi.
Tunda yai sallama mommy ta ganshi tare da yara wani irin dadine ya kamata lokaci guda saidai tana mika hannu yaran sukaki zuwa wurin ta hakama kannen shi.
A nan ya samu labarin mahaifin shima yana gari sai bai dade part din mommy ba ya je tare da yaran su gaisa da daddy din.
Sun sameshi yana waya ya mika


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login