Showing 129001 words to 132000 words out of 382072 words
wacan yarinyar.
Bayani nake masu amma su sun tsaya suna kare min kallo a cikin mamaki har na kare masu bayani suna tsaye sororo suna kare min kallo.
Ikon Allah matar ta fada tana murmushi yanzu ke din nan ashe kin iya hausa a bakin ki haka radau kamar jakar kano.
Amma dai ke haihuwan arewace ko nace ni bafulatanan jalingo ce saidai a kaduna aka haifeni na kuma tashi a lagos kamar yadda kike gani na yanzu.
Ta dan sake dan murmushi har hakoran makkan ta na gold suka dan bayana fili tana fadin aiko ga kama nan mun gani a zahiri da fulani.
Amma ke bakuwace a shagon nan mijin ya fada daga bayan ta yana rike da hannun yaran su , nace a,a na dan dade a nan kuwa.
Saidai da yamma nake aiki dasu na tashi da dare don ina zuwa makaranta da rana mijin ya dan taka ya barmu a wurin tana dan dariya kamar taga wata yar uwanta na gida.
Mu muna nan Apapa ne zaune kusa da Olamide eyes center sai na danyi murmushi don Olamide yana bayan mu kadan nace kinga kuwa muma a ta gaban shi muke zaune ai.
Zuwan wasu custemers yasa na barta na dan tafi wurin su ina masu bayani baisa matar nan ta barni ba sai ta tsaya tana jiran in gama dasu.
Ban gama da wuri ba har mijin ya kirata suka nufi wani wurin na fita zancen su nikan na kama aukin gabana na saka ido ga kaya tare da jagoran masu zuwa sayan kaya kamar yadda akeyi.
Na dauka sun tafi sai gasu sun dawo inda nake matar ke fadin kinga yar uwa har zamu tafi ban san sunan ki ba nace mu dawo don Allah na tambaye ki.
Sunana Sahiba amma Fatima nake da Sahiba din ake kirana har a gida gaskiya kina da suna mai kyau shigowan wani ya dauke ma mijin ta hankali har ya barmu mukai musayan lamba da ita da kwatancen gidajen mu sai gasu sun tako zuwa inda muke daga bayan mu ana fadin.
Kai madam yau kece da kanki kika shigo shagon mu ta waiga tana dan murmushi tare da fadin wallahi oga Sha,aban .
Nice fa yau a shagon naku mai a lbarka nace bari dai yau na biyo shi nazo naga shagon naku don oga saidai yazo shi yana ban labarin girman shagon nan
Good day sir na fada daga bayan matan inda nake tsaye na juya ban jira amsan shi ba nasa kai na bar wurin ga baki daya.
Wani irin faduwan gaba nake ji wanan ne karo na biyu da muke haduwa dashi a shagon sai kuma ranan nasan ainihin masu wanan katon shagon haka.
Zasu tafi wanan matar ta kara magana akaina don naga duk sun juyo gaba dayan su lokaci guda sai kuma sukaci gaba da magana don ina dan nisa dasu banji me suke fada ba a lokacin.
Da hannu ta kirani nazo da sauri wanan karon don ganin su tare da wanda nake zaton a yanzu sune masu shagon nan da muke aiki a cikin sa shine kuma wanda ya kaini gida ranan idan baki manta ba don yanzu ankai wata shidda sai ranan kuma na sake ganin shi na kuma shedashi.
Take care of her ya fada lokacin da suka dan fara tafiya da mijin matar sai matar tace dashi wanan ma ai kusan ta fika iya hausa zance.
Yayi murmushi sukaci gaba da tafiya da gani suna wani magana ne mai muhinmanci a lokacin don yadda naga suna zancen daga nisa.
Kin gashi can shike da wanan shagon a waje yake zama don rayuwan shi gaba daya a can yayi shi .
Yadda ma,aruf ke fada min sunyi karatu tare dashi aminin shine sosai suna karatu saidai kasancewan shi dan masu hali suna gama karatu ya fara harkan business shi kuma ya fara aikin gwaunati a nan kasan.
Shidin dan wani shararen dan kasuwa ne dan arewa saidai mahaifiyar shi ta kasance yar garin nan ne ita don haka yake ruwa biyu shi.
Yana zama a kasashen labawa ne shi can yake harkokin rayuwan shi sai dai a yanzu naji Ma,aruf na fadin yana son ya dawo nan gida Nageria da zamane.
Wanda nasan mawuyacin abune ya iya hakan Allah sarki azuciyana kuma nace wai fadi ba,a tambayeki ba ke nan mata da bakin zuba haka sai kace wata aku.
Ni a tsarina ban son yawan surutu gaskiya haka Allah yayi min rayuwa na hannuna naji ta rike tana fadin zo mu zaga ki tayani zaben kaya dama ya hanani zabe shi kuma ba mace ba yar uwana.
Ina mamakin wasu abin komai tsadan su zanga ta dauki biyu har dai takai mun gama a daidai lokacin da suma suka dan fito mijin na fadin idan ta gama ta sameshi waje.
Sai bayan anyi komai an saka kayan a cikin leda ne kawai naga ta miko min dayan ledan tana fadin wanan nakine kanwata don yau kin debe min kewa sosai wallahi.
Ga abokan aikina sai bina da kallin mamaki sukeyi har dai lokacin da suka tafi na dawo cikin shagon naci gaba da harkokina ban dawo gida ba sai dare lokacin dana saba tasowa daga wurin aikin na shigo gida.
Umma har sun kwashe sun shiga ciki nayi mamakin hakan sai kuma nayi tunanen saboda sanyin da akayi ranan ne yasa ta kwashe da wuri haka zuwa ciki.
Da kayana niki niki da matar nan ta saya min na shiga gida da sallamana umma na zaune a falo da gani hankalin ta a tashe yake.
Ledan dake hannu na tabi da kallon har na aje ina fadin umma sannu da gida na juya wurin Amar ina fadin kai how far ya kake ?
Ke gidan ubanwa kika shiga haka umma ta fada a cikin wani murya da ban san tana dashi ba nima dan tsorata nayi ina fadin umma na fada maki shago zan tafi ai dazun da safe.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA, , , , , , , ,
3️⃣9️⃣ BY, , , , , , , , , , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AS SAMI,E
ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KAFIN KI KARANTA DON ALLAH KADA KI SHIGA HAKKIN WANI CIKIN RASHIN SANI, , , , , , , ,
Sahiba yaushe kika fara karya hakane har yaushe kika zama haka ban sani ba kin maishe ni karamar yarinya ko me a yanzu sahiba ?
Innalillahi na ambata a fili tare da kallon umma ina nuna kaina da hannu kafin na fara kada kai a hankali ina fadin.
Wa iyazu billah umma kada ki soma don Allah kada ki fara zargina da irin hakan har idan zan iya aikata wani abin assha a duniyan nan dana fara aikatawa tun zamanin da nake yawon talla.
Amma umma sai gashi yau ke da bakin ki kike kokorin furta abinda ban taba tunanen yinsa ba a rayuwana ba ko wani ya fadi hakan a gabakin umma ke mai iya shedatace ga hakan duk da ina yarki kuwa.
Amma ba komai umma Allah ne shedana tun safe ina shago don neman kudin da za a ba Amar ranan monday don sunce shine dateline din da suka diba a kai kudin school fees din yasa nayi double din aikina a yau da gobe insha Allah.
Amma umma don Allah kiyi hakkuri haka ba zai sake faruwa insha Allah sai na zube kasa alaman bata hakkuri hawaye na zubo min a idona.
Ki shiga umma ta fadi na mike gwiwa ba lakka na nufi hanyar dakina wanka nayi ban fito ba duk ko da uban yuwa da nake ji a lokacin .
Tunda na watsa ruwa ina wanka ina kuka na fito nayi sallah shafa,i da wutir nabi gado hakana na kwanta ban fito ba ranan a dakina na kwana banje na lakewa umma ba yadda na saba.
Itace ma data jini shiru ta leko dakin ta samu na kwanta duk da lokacin banyi barci ba sai na lafe kamar ina barci zuciyata tana cunkushe da bacin rai .
Ba fushi nake da umma ba sai abinda take zargina dashine yake damuna don ni a ganina ban taba tsayawa har wani namiji ya bude bakin shi ya furta min kalman so ba balle har in yarda in bishi yawon banza yadda take zargin na fara a yanzu.
Wani tunane nayi dayasa na dan mike zaune kafin in koma na kwanta don bayanin a yanzu baida rana a gareni wurin umma din tunda har ra riga da ta saka zargina a ranta.
Ba komai na tuna ba sai ledan kayan da matar nan mai suna zakiya ta saya min a shagon mu wanda na shigo dasu niki niki don umma bata saba ganin na dawo haka da kaya a hannuna ba gashi kuma na dade yau a wajen dole nasan damuwa ne har ya sakata fara zargina din a lokacin da ganin wanan kayan kuma dana shigo dasu din a lokacin.
Da yake barci barowon gaskene duk halin da kake ciki sai yasan dabaran daya sace ka kona yan mintuna ne ko awani shine kadai yaceni a ranan don irin yadda zuciyana take ciki a wanan ranan.
Washegari lahadi nayi sallah na idar na fara gyara dakina na fito na shiga kitchen don na dora ruwan zafi saman gas.
Ja nayi na tsaya ina bin ko ina da kallo don na fahinci akwai sauyi a cikin kitchen din namu a lokacin na kara bude dan store din dake manne da kitchen din buhuhunan shikafane har biya gasu tumatur da jarkan mai biyu dana manya sai wasu irin doya manya manya a wurin da dankalin irish azube kasa.
Mamakine ya kamani na ganin hakan saina fara tunanen ko ya Abubakar ne ya dawo garemu kuma yanzun.
A hankali na rufo store din kafin na fito na fara gyara gida har lokacin dana gama banji motsin umma ba sai dai dakinta yana bude na juya na shiga dakin da sallama.
Umma na zaune tana jan tasbaha a hannun ta na tsuguna yadda muke gaida ita na gaida ita da kwana kai ta gyada na mike na dan gyaro dakin na koma kitchen ban daki wani lokaci ba na hada muna abincin na gyara kitchen din na fito.
Dakina na koma nayi wanka na fito na shirya cikin wani dogon rigan nealon idan na sakasu haka na nufin a gida zan zauna ke nan ranan bazan fita ba.
Na koma gado na kwanta sai ga Amar yayi sallama a dakin don shima yanzu a dakin shi ya koma kwana don dan girman daya kara yi yanzu.
Da littafi a hannuna na mike saman gado ina karatu ya shigo na dan dago kai ina kallon shi kafin in dan sake murmushi gefen fuskana a lokacin.
Fadawa yayi saman gadon dakin yana fadin anty na naga tun jiya kina fushi da maganan da umma tayi itama umma din bayan tayi kuma daga baya naga ta damu da hakan sosai kuma.
Bana fushi da umma kokai Amar ina dai damuwa ne da yanzu umma ta fara zargin zan iya aikata wani abu mara kyau a rayuwana bayan nasan koni wacece a cikin dangi mu.
Idan ban yi abinda zai daga martaban mahaifin mu ba ba zanyi wanda zai sa ayi tir damu ba a rayuwan yan uwan mu .
Fatana da butina Amar shine kullun inga na tsaya karatun mu yaci gaba inda zamu iya tallafawa kanmu basai wani daga dangi ya kara taimakon mu ba kuma mun koma abin tausayi.
A yanzu na daina ganin laifjn kowa da nake gani a baya don yin hakan a garemu ya kara koyar damu abubuwa masu muhinmanci a rayuwan mu yanzu.
Ya Abubakar yayi muna komai shima kuma yayi hakan ne don ya tsira da rayuwan shi dana iyayyen har da yan uwan shi bai fada muna bane amma yanzu na gano manufan shi nayin haka garemu.
Kin daina ganin laifin shi ke nan a yanzu yaron ya tambayeni nace kwarai kuwa Amar don hakan yasa na kara gane ko mu din su waye a yanzu a cikin su don zama a cikin su zai iya sa mu shagala mu manta da komu suwaye amma kada ka damu lokaci na zuwa da komai zai zama tarihi a garemu da yardan ubangji.
Jiya wanan dayan mutumin yazo gidan nan bai sakeki ba kuma duk dana gane wa yake nufi amma bai hana nani tambayan shi ba ko waye yazo din.
Mai bamu kyautan kudin da babu mai bamu irin shi din nan jiyama ya baku kyautan ke nan na tambaye shi.
A, a bai bamu kudi ba sai dai ai kinga kitchen din mu cike da kayan abinci ko to shine yasaya yazo muna dashi .
Shiru nayi ina tunanen shi kuma dame yazo muna yake kokarin shiga cikin rayuwan mu a yanzu kuma haka don dole sai akwai wani bukata da zai sa ya shigo rayuwan mu din.
Don yanzu nasa mutane basu shiga rayuwan mutum duk halin kuncin da yake ciki sai da wani dalili nasu na daban can.
To yanzu shi din dame yazo muna ko shima din yana da wani falili nasa na daban ne da yake son aiwatarwa a kammu kuma na tabayi kaina ko kuma shidin ma maganan mahaifimu ya shafesu ne suma yake son yin amfani da dama hakan wurin jawo mu jikin shi yanzu.
Amma naga sun dan dade da umma suna magana da ban san abinda suka fada ba Amar ya fada daga gefena shiya dawo dani daga zurfin tunanen dana shiga lokacin.
Maganan su ce ta manya na fada don na kawar da zancen ya kara fadin monday din zan shiga school din ke nan ya tambaya yana kallon fuskana lokacin don son jin amsan da zan bashi.
Zaka shiga insha Allah zanje na biya ma kudin da komai yadda ya dace in Allah ya yarda ranan monday din kamar yadda nake so Amar bana son karatun ka ya samu targada ko kadan.
Da ace yauma na fita zuwa aikine da zan hada kudin gaba daya don in sun ban wanda nayi da rana tare dasu a hannu sai na hada dana jiya da dan kudin dake hannu zasu kai a biya ma sin amma yanzu zan kai masu abinda ya samu ko zasu yarda ka zauna dasu.
Yay ba zaki fita ba ke nan ya tambayeni nace umma bata so don haka ba zan fita ba kayi hakkuri Allah zai kawo muna mafita da yardan Allah.
Mikewa yayi ya fita ba tare da yayi min magana ba na bishi da kallo ina mamakin hakan har ya karasa fita na juya na mayar da idona kan takardan dake hannu na lokacin.
Ba a wani dauki lokaci mai tsawo ba sai gasu tare da umma sunyi sallama a dakin na amsa umma ta samu wuri a gefe ta zauna tare da kiran sunana na dago da sauri ina kallonta.
Itama kallona tayi ido cikin ido sai na dukar da nawa idon kasa da sauri kafin inji tace Sahiba duk da kinman bayani na gamsu da hakan kin kuma saura da zancen ne a zuciyar ki har yanzu don Amar ya sameni wai kince yau ba zaki fita ba zuwa shagon yau ?
Dan murmushi na sake nace umma ba hakana bane naga kamar ranki baison hakan ne gara na bar fitan kawai a nemi wani hanya mai sauki da za a biya kudin gobe in Allah ya kaimu.
Ke nan ke ba za,a lurar dake hanya ba ke nan don Allah umma kiyi hakkuri tunda har kokai magana hankalin kime bai kwanta umma kuma na fahinci me kike nufi da hakan.
Bana zargin ki ga aikata wani abin daya danganci maza Sahiba saidai ina tsoron dadewan ki a waje ga abinda hakan zai iya jawo maki a rayuwa.
Nagode umma na fada tace amma yanzu kona fita na makara zasu iya cewa ban fito da wuri ba tamike tare da fadin shike nan tunda haka kikace ta fita Amar ya bita da ido kamar zaiyi kuka.
Kafin ya juyo kallon shi a gareni fuska ba annuri a cikon sa sam ina ganin haka naji ba dadi a raina na mike ina fadin kaga barin fita in gwada ko zasu barni in shiga nayi na yau din ba shike nan ba na mike ina sauka saman gadon.
Ban dauki lokaci ba wurin shirin na fito har daki na samu umma a zaune tayi shiru na shiga ina fadin zan gwada fita umma ko zan samu su barni in shiga.
Rana ya danyi don haka ban samu mota daga cikin unguwa ba sai nayi shawaran takawa da kafa nabi hanya jiki ba kwari don nasan zuwan banza kawai zanyi.
Wata Jeep ce fara lafiyayya mai kyau ta wuce ni a hanya duk da basarwa irin nawa saida na yaba da kyau motar na dan bita da kallon basarwa .
A kofan shagon na samu motan tsaye da