Showing 99001 words to 102000 words out of 382072 words
gidan mu bamu jin ko zo in kasheki idan an fada balle shi amar da har yanzu bako yake a gidan ga kowa.
Sai dana hada komai cikin dauriya na na dan rage yawan gas din na fito don tunda daddy ya dawo wanan can karon akai rikicin girki kowa ya dauki girkin shi a gidan shi da yaran shi .
Don anty ce ta tayarda fitinan don me za a bamu girkin mu daban a gidan su kuma a hade masu suci na yawa a gidan da yaran su.
Allah ya kawo saukin kai daddy din yace ai sai kowa din ya dauki nasa ba komai bane idan sunga hakan yafi garesu dama shi don yaran sa su hada kansu yace hakan .
Kuma abinci da suke gani bashi ke saya muna ba modibbone yace a bar masa wanan nauyin don yana kwadayin ladan da zai samu ga ciyar da marayu ya dauki hakan.
Daga wanan ranan aka kaiwa kowa kayan girkinshi a part din shi har muka samu arzikin saka muna freeze a dakin mu muma da aka sawo wa kowa don aje abin amfani karya baci.
Na fito ban ko kalli inda suke ba son suna yan dararakun su a lokacin nasa kai na fice a part din cikin kunan rai.
Ina shiga wurin mu na zauna na fara cire safan kafana na nufi cikin dakin kai tsaye wanka na fada yi saida na fito ne nake ba umma labari abinda ya faru .
Murmushi umna din tayi tana fadin wanan haka hakin matan mu yake ga kishi su a zaton su kada daddy ku ya dawo ya aure ki.
Idan ma harta dauka haka din ne daga baya zatayi kunyar hakan don zata gane shidin ubane na kwarai a gareki kudin ba kalan dangi bane gunsa yadda suka dauka din.
Fatima ce tayi sallama ta shigo dauke da abincin da suka dafa tana fadin ga abunci inji mami nakawo maki ina fadi da sauri koma dashi ga wanda umma ta girka nan banci ba ma .
Zoki aje umma ta fadawa yarinyar ta aje abincin a gaban umma ko kallon abincin banyi ba karshe ma tashi nayi na koma daki na kwanta.
Barci nayi sosai ban tashi ba sai karfe biyu saura na tashi don Allah koda na fito har lokacin kwanon abincin yana nan dakin mu ba alaman an tabashi.
Fita nayi zuwa part din mommy nan samesu ga turamen zani masu yawa a gefen ta a zube bai shafeni ban kuma tsaya kallo ba nake gaida mami kafin in wuce zuwa dakin kwanan su don nasan mutumiyana fa,iza tana can dakin tunda ban ganta a falon cikin su ba.
Tana zaune tana waya na shigo ta kalleni da murmushi taci gaba da waya har ta gama ina dan duke ina karanta wani takardan da nagani.
Tace ina jiran ki tun dazun kinga kaya a falon mu anko ne aka kawo muna na yar kanwar daddy da zata aure.
Ke ai kin santa wace sukazo ranan har take fadin ki bata kanki kuyi musaya da ita nace na gane ta.
Itace zatayi aure kin san yayan modibbo taso kamar ta mutu amma yanzu zata auri wani dan uwan baban sune a jos shine .
Jos na tambaya tace min eh ko kin san jos din ne ta tambayeni tana kallo na nace ban san ko ina a arewa, ba banda wanan garin.
Zaki sani har idan mun dace za a tafi damu ai zakiga gari na danyi dariya ina fadin wa zai tafi dani bansan kowa ba ?
Tace aukin san mu ko kuma tare damu zaki tafi don su anty Nabilace manyan kawayen bukin kinga kuwa ai damu za ayi komai taso muje falon mu duba ankon.
Ta daga na bita a baya muka zauna ni dai ina a takure ta jefo min zanin daya a jikina tana fadin wanan nakine.
Na nuna kaina da mamaki ina dagowa nace ni tace eh zaki koyi daura a tamfa ko, kome kuke kiran shi a can nace ankara.
Tace akwai wasu da za,a kawo muna wani irn dinki zakiyi da naki duk a cikin turanci buga buga muke maganan mu din dasu.
Kafin nayi magana mommy tace a cikin hausa ina tasan inda ake dinki ko tasan inda za a dinka din balle takai ayi mata ku kai mata ayi mata.
Nabila ta dago tana fadin ni kin san aiba irin dinkin su zanyi ba don haka karma a dora min wanan nauyi ban iyawa .
Tellana zamu kaiwa yayi muna dinki ta fa,iza ta bada sai hauwa tace dama kun fi kusa da ita sai kukai ai maku tare din.
Mommy tace na rabaki da wanan halin Nabila yarinyar nan idan bata biku ba wata sani a garin nan yanzu zaki wani fara fadin maganan banza a kanta tun yanzu.
Shiru sukayi ga baki dayan su a falon har mommy din ta kare ni ke tambaya me ake dinkawa ga ango zanine ko buje ko dogon riga ?
Wanda ranki ya zaba idan muje gun maidinkin zai baki hotone ki zabi wanda yai maki kyau sai a dinka maki nace buje nake so ba zani ba ko dogon riga.
Mun dan dade muna hira a dakin dasu har zuwa yamma na koma part din mu ina bawa umma labarin zance zanin da yadda akayi.
Washe gari ko sai ga Fa,iza har dakin mu tace in shirya zamu kai dinkin ankon namu saida ta jira na shirya duk da ni ba wani kwaliya nakeyi ba mun fito ne sai muka hadu da ya Abubakar zai shigo gidan mukayi mashi sannu da zuwa.
Ya amsa yake tambayan mu inda zamu tafi Fa,iza ta fada mai yace kada mu dade mu daina fita wuri mai nisa haka.
Bada motan gida muka fita ba taxi muka shiga zuwa wurin akwai mutane a shagon dinki tayiwa tellan bayani ya kawo min photuna na zaba sai suka saka min dariya wai ai din kin iyamurai ne wanan dana zaba nace shi din dai nake so ni akai jinga ya fadi kudin shi.
Mun dawo gida take basu labarin irin dinkin dana zaba sukai ta min dariya wai ni zan dawo ince ban shi wata rana aka shigowa masu da nama kallon naman nayi sai gabana ya fadi.
Da sauri na fita zuwa part din mu har na zauna zuciyana yana tashi hankalina kuma bai kwanta ba da ganin wanan naman .
Hardai hakan ya jawo min yin amai bayan na fitone na kasa daurewa na fadawa umma abunda nake ji game da naman .
Sai hankalin umma bai kwanta ba da zancen dole ta kira mommy ta fada mata abinda ke faruwa game da naman da nagani a part din ta dazun .
Sun ki ci zuwa safe naman yayi wani irin baki ba dadin ganin hakan ya kara tsora mommy hae umma ga lamarina ga buki kan sun fara a gidan sosai kullun cikin fita auke yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ANA DARA GA , , , , , , , , ,
3️⃣0️⃣ BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , ,
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL RAZZAQ, , , , , , , ,
ONLINE PAID NOVEL DON ALLAH NA KUDINE KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA DAUKAN NAUYI BA A KANKI YAR UWA, , , , ,
Wasa wasa buki ya fara kan kama zakace ko a gidan daddy ake bukin duk wanda yazo ba zaice yaga umman mu ba a taron nan saidai nikan dani ciki tsunbul ake komai ko banzo ba fa,iza saita kirani a lokacin.
Anko har kala biyar akai muna ko wani da sunan shi inda Allah ya kara rufa min asiri akwai baki da suka zo masu daga illorin da ibadan kawayen gwaggo Asiya da diyan su.
Duk da manyane sun girme ko anty Nabila balleni karaman su sai ya kasance sunji dadin hakan a tare damu duk inda na shiga zasu nemoni su fada min abinda suke so.
Sai itama gwaggo din hakan yai mata dadi don na zama kamar ta gida a cikin su yanzu din tunda ba sanin matsayina sukayi a garesu ba.
A gaskiya naga mutane masu son junan su da kaunan zumunci a wanan bangaren nasu daddy don har daddy din da kansa saida ya shiryawa amarya dakin guda nasa na kansa hakama gwaggo Hari itama tayi nata bajintan sosai a matsayinta na kanwar mahaifiya kuma mai buki.
Duka gidajen nasu ga baki daya ya kicime da baki yan buki don haka ko ina ba masaka tsunke a gidan lokacin haka yasa tausayin umman mu da azzalumi Nuhu yasamu zama a cikin hijabi don tsoron sherin sa da halinsa sai naji tsanan wanan mutumin a lokacin ya kara shiga na sosai wallahi.
Tundai da Fa,iza ta nuna min iyalinshi a wurin kamu take fadin ga iyalin gidan matan yaya modibbo can sune iyayyen matansa da yayan su.
Na kalli wurin sai wani hura hanci da jiji da kai da sukeyi suko mutane yan uwa sai wani basu girma akeyi a wurin ana fadin wai buki yayi buki tunda har yan gidan Namadi sun halarci wanan bukin haka kwansu da kwarkwata.
Wasu dake kusa damu suke fada daya tace don sun san su din masu bukin masu hali ne kamar su da ai basu zo ba yo gwaggo Hari ai itama tana nuna masu itace ki duba shigan ta ki gani wane nasu Allah dai ya cece ta kada kuma a sakata a baki don kinsan su basu son suga kafisu fitowa a wuri yanzu suna nakasa mutum ya koma baya .
Keko dai kinsan fa sune kusan abokan karawan su a cikin family din nan anty hauwa ce ta kwala min kira daga wurin da yan gidan suke zaune nazo.
Tunda na tunkari wurin suka zubo min idanuwan su banjin zan iya gaida kowan su don haka ina zuwa nake fadin gani tace jeki ki kawowa su mommy wasu kujera guda biyu.
Nace me i don no, where to find chair now, people are sitdown on it, who igo weak here ?
Ina fadin haka na bar wurin don idanun da suka zobo min din suna magana a kaina don naji daya ta fara fadin wai wanan yar ce dama ba bahausa bace gata da ka ganta zakace yar filoce ita.
Waima me sukeyi a gidan har wanan lokacin basu koma bane daya ta fada sai lokacin dana juya zan wucene na farga da matar ya Abubakar a wurin na sakai na koma inda na fito.
Duk da bukin ya kawatar dani saidai hakan bai hana zuciyana jin bakin cikin dake damuna ba na duba duk taron nan amma ummana na gida a kumshe ta dalilin su.
Taro yai taro don bansan kowa ba ga iya yi dana koya a geto kuma tun ina karamana na bude idona a geto ne yasa suka ban raba kayan buki don su yan gida kada suyi laifi a wurin su.
Aiko ido rufe tunda ba sanin su nayi ba nake ba kowa daya daya ko kin dawo kina min guntun turacin ki bazan kara maki ba.
Har kowa ya samu da hannu wata yar gidan ta kirani kamar in shareta sai naje take fadin i beg give three servoner for our moms na dan kara kallonta kafin in tura hannu cikin buhun na ciro jakkuna guda ukun daidai na mika mata da sauri tana magana na bar wurin.
Idan ka jawo rigana ta baya zan sa gwiwan hannu in buge inci gaba da tafiya bana waigen bayana balle inga waye ke jana yar Geto ke nan sai ido.
Anty amaryan daddy ta yafotoni da hannu nazo wurin take fadin in ba bakinta da yan uwanta baida yawa na mika masu buhun duka na koma wurin motan da muke dauko kayan a nan na samu gwaggo hari tsaye.
Tana ganina tace dani ance ba a bani sai kinzo ki ban na mutane na gasu can dan murmushi nayi karo na farko a warin gabanta ne yayi mugun faduwa saida ta kadu ita kadai tasan abunda idon ta ya hasko min a kaina lokacin.
A sanyaye nace gwaggo how many a cikin murmushin da har lokacin kesa gabata faduwa tace give me firty, na bata ashirin ina dariyan daya daga mata hankali don su suka san mahaifina da tashin shi sosai don a dakin su ya tashi in kin tuna da labarin mu.
Tun wanan lokacin take bin na da ido da kallon tsoro a zuciyanta tabbas yayan su ya boye masu wani siri duk yadda akayi ba zata taba manta dan uwa kuma abokin shawara a gareta ba sambo.
Kai yar sambo fa da matarshi sunyi tambaya fun ana cewa suna raye har aka koma cewa indan sunje gun malamai duhu ake gani ba a ganin ma,ana ke nan mun mutu saida kama kawai don haka taba zuciyan ta salama a kan abinda ya fara raya mata din.
A can gidan ta muka nufa bayan an tashi a taron kowa yana mayar da fadi ina zaune nayi shiru don hankalina ya koma akan umma lokacin.
Muryan gwaggone dake fitowa tana fadin yau kun bamu wahala kun dauki rabon abu kuba wanan bobanyan da bata san nagida balle na waje.
Da sauri na dago kai don wanan hausan yaimin tsaurin fahinta take fadin ai kunyi daidai don da an wawashe shi duka lokaci guda amma yanzu kunga kowa ya samu ai .
Wallahi gwaggo idan ba haka mukayi ba ba zamu iya da mutanen mu ba amma kinga ta raba an zauna lafiya har yan gidan kawu Nuhu daya daya ta mika masu shine suke fada wai ba,a karamasu ba a wurin.
Kyale yan sallo da jin kai ai na hangosu suna min wani kallo na fita batun su wa zasu dinga hankadawa su a dole ga matan mai kudi dole a bisu da ace ma mutum baisan asalin kudin nasa bane zasuyiwa mutane iskanci.
Wani irun kallo nayi mata kafin nayi kasa da kaina lokaci guda ina duban wayan Fa,iza dake hannuna lokacin don ni banda waya ba a sai min ba.
Wayan gwaggo ne yayi kara lokacin ta dauka tana waya sai na bita da kallo don matar nada sha,awa gashi tasan kanta sosai irin wayayun matan kaduna din nan ne da suka san duniya ta waye har ta gaji gidan ta tsab dashi babune kawai babu a gidan don tsaruwan shi.
Da murna ta juya tana fadin ashe kace yau ina da bako ke nan barin fadawa driver yaje dauko ka kome na wayan yace naji tace kwarai kuwa abokin kane dole kazo bukin shi saika iso din banda dare kasani.
Gwaggo halan ya Mustaphane zai shigo hauwa ta tambaya tace shine dan ka,ida aikinji yace kada azo taron shi sai na ganshi dai kin san sune angon ne ai.
Sune fa ya modibbo ma daya koma shekaran jiya na ji matar shi na fadin yau ko gobe zai dawo dazun .
Mikewa nayi tsam dayan yan ibadan din bakin nan tace dani enbalalo nace i wan go see my mother nasan yanzu tana can ta damu da rashin dawowana gida.
Na kalli inda fa,iza take ina fadin tashi muje gida tace min da wani mota mujira anty Nabila ta kaimu ai yanzu zamu wuce.
I go track na fada tare da daukan jakkana na fita banyi sallama da kowa ba a get na hadu da motoci suna shigowa gidan sun wuce niko na fita na fara tafiya don nasan wani hanya kawai zan dauke ya kaini unguwar mu don na gane hanyar.
Na shigo gida a gajiye kamar walkiya don saurin da nakeyi suma suka shigo suna tambaya ko na dawo mommy yayi min fada sosai da na biyo kasa ban jira yan uwa ba.
A part din mu na shiga na samu umma zaune tana lazumi ga tv an kunna yana aiki gaida ita nayi ta amsa da kai na shige daki na kwabe kayan da suka dameni a jiki don ban saba saka atamfa ba a jikina haka.
Duk dasun bani kaya amma nafi son saka yar katin dogon riga ko yaushe ko wanduna nafi jin dadin su a jikina idan suna saka din.
Wanka nayi nayi sallah ban fito fallon ba na kwanta tunanene barkatai na dinga yi har barci ya daukeni a hakan sai safe harda makara don umma na tayar dani ina kin tashi don gajiya.
Sai bayan na hada muna abin karyawane daga baya aka aiko muna da abinci part din mommy da aka kawo muna an dafa don bakin da suka kwana gidan.
Haka dai nake jin kaina ba dadi a ranan don bakin rai dana wayi gari dashi haka kawai na dunga jin raina yana baci ga komai dan haka ban fita ba ranan saida yamma koshi Fa,iza ce ta matsa min na fito mu tafi wurin event din da za a