Showing 48001 words to 51000 words out of 382072 words

Chapter 17 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28347

kuma katako da katako aka hada aka mayar dashi daki mai kyau a ciki.
A haka muke zaune cikin sa saidai mu namu ya nuna tsohon yine don ya dade ya soma dan fadawa amma bai lalace ba.
Nikan muna shiga wuri na samu na kwanta don wani iri nake jin jikina ba karfi yayin da umma tana aje gyalen ta ta dauki buta ta nufi ban daki a lokacin.
Har ta idar da sallah ban ko iya motsawa ba a lokacin ina kwance inda nake kuma ba barci nake yi ba sai can na iya mikewa naje nayi alwala na dawo.
Ina sallah Ladi ta shigo tana muna sannu da zuwa da alama daga unguwa take a lokacin don shigan danaga tayi ya nuna hakan.
Bayan sun gaisa tayi min ya jikin an samu ganin likitan tace mun ganshi yace makariya ne ke damun ta ya bata magani har ni ya duba yace mu koma karshen wata dai akan nawa jikin a kara awo.
To Allah ya sauwaka ladi ta fada har ta juya take fadin wai gajiyane hakan yasaki laushi naga yanayin ki ya dan canza kuma ?
Ke dai uwar dakina bari kawai abine da daure kai wallahi wai neman mu akazo yi a wanan can gidan da muka taso.
Ke ki bari don Allah Ladi ta fada tana dawowa cikin dakin namu umma tace bari ke dai yadda jaga iya Bisi na rawan jiki da ganin nasan akwai wata a kasa.
Don har cewa tayi wai meshi babban mutum ne yace kuma shine mahaifin yaran nan shiyasa data tambayeni inda muke Allah ya rufa min asiri ban fada mata gaskiyan inda muke yanzu ba da zama.
Na dago daga inda nake kwance dunkule tun bayan idar da sallah na na dan kalli umma din don jin abinda ta fada.
Ladi tace anya ba wani ne ke bibiyan rayuwan ku ba dama, umma tace nima abinda ya daure min kai ke nan yanzu.
In har hakane kuwa ya zama dole un bar kasan nan mu kara gaba wajajen shagamu ko zuwa kamaro ko ghana mu samu wuri a can mu zauna.
Umma na fada cikin mamaki don ban san lokacin dana saka baki a zancen su ba akan mahaifin mu yazo neman mu zamu kara gaba ko me ?
Ni gaskiya na gaji hakana umma na gaji inma kashe mu zaiyi ya kashe mu matukar dai zanga mahaifina a duniyan nan.
Ke ar ke me kika sani Ladi ta fada a hasale an fada maki neman arziki suke maku a yanzu dole neman rayuwan ku suke maku su halaka ku ai.
Halakawa kuma da mukai masi me zasu halaka mu kuma ni dai koma meye su halaka mu din ma mu huta zaifi.
Duka umma tayi niyar kaimun daga inda nake kwance Ladi ta tare tana fadin kada kiga laifinta yarinyace ita bata san komai ba don haka kyale ta ai jiki magayi.
Har suka karaci fadan su suka kare ladi tabar dakin ban kara dago kaina na kalli inda suke ba nan ta bar umma da tunanen a zuciyar ta nawaye mai neman ta kuma ita da diyan ta.
Shin wa yanda ta bari arewa ne suka biyo ta ko kuma nan ne kuma ta samu wasu masu bibiyan lamarin su kuma ?
Ya isa kaduna a cikin tashin hankali misalin magariba don haka kai tsaye dakin shi ya nufa ya bude ya shiga.
Wanka yayi ya dauro alwala ya fito zuwa masalaci a nan ya hadu da mahaifin shi suka gaisa yasan yazo garin suka shiga sallah a tare.
Sai bayan isha,i suka shigo gidan tare lokacin ne kuma kowa yasan da zuwan shi garin ranan suka shiga taron shi a cikin murna banda hjy karima da gaisuwan kazo lafiya kawai ya hadasu ta wuce.
Abinci aka gabatar masu ya dace da hjy mahaifiyar sune da girki tayi masa irin abuncin da yake so tuwon alkama da miyan danyan kubewa da kassan rago yaji daddawa da kayan yaji ya sake don anaci a cikin taro yaci sosai.
Hjy Addah kallo daya tayi wa dan nata tausayin shi ya sauka mata sosai a cikin zuciya don yanayin sa kawai da ta kalla tasan yana cikin damuwa.
Har suka bar wurin tana satan kallon yadda dan nata ke ciki hakan sai ya saukar mata da damu kan abinda ke damun shi din balle zuwan da sadiqa tayi gidan da sunan wai tazo ta gaidasu kuma su santa a gidan ya kara saka hankalin hjy tashi.
Iyayyen su na barin wurin Nabila da gulma yace ta matso kusa da yayan nata tana fadin ai yaya baka zo tun jiya bane da yau kasha kallon mamaki a gidan nan sosai.
Dame ya faru ya tambaya cikin son ya san ko meye saidai har lokacin idon shi na awayan shi yana karanta sakon da aka turo mai wanda ya dauke mashi hankali.
Wai ashe wanan Samiran zaka aura yar gidan kawu Nuhu din nan yau ai tazo gidan nan gaida su daddy, wai amma dai tasha mai gaskiya a jikin ta kamar a gidan su aka bude kamfanin bleching fa.
Au baki sani ba a gidan nasu kamfanin yake ko bata kawo maki tsaraban irin sa bane da tazo ?
Ta saki yar dariya tana fadin kai yaya bafa kushe mata nake yi a hakan ba daga fadin gaskiya naga ka hasala dani mana yanzu ?
Daga fadin gaskiya Allah bana son na ana shafa wanan mai din ne yace ai amsa na baki zaki tambayeni nasan ko wacece kike zance akanta asalima yanzu naji zancen a bakin ki ai.
Tana dariya ta sake fadin kai kaji yaya abin ya koma yar boyone yanzu kuma ai zamu ganta har mu gaji sai dai gaskiya akwai aiki kan gare ta yadda nasan halinka da tsanani din nan.
Dama ai nasani mai shegen zuban nan sai ta tare ka da zancen nan tunjiya take mita a kai hjy ta fada daga bayan su tana karasowa a inda suka barsu zaune har lokacin.
Kai ya dago a lokacin yana duban hjy din har ta karaso inda suke zaune ta zauna Nabila tace Allah mommy abin ne ya ban mamaki sosai yadda tazo muna da fitsara a gida bako kunya wai ita tazo nuna kanta gareku.
Sai akace kuma ki fada mai hakan ko don shegen surutu irin naki hjy ta fada tana hararan yar nata tayi dariya tana mikewa tare sa fadin mommy abinda nagani fa na fada .
Kallo Abubakar hjy tayi tana fadin malam ka koshine ko s zubama ferfesu ka kara dashi dan murmushi ya kakaro a fuskan shi tare da fadin .
Mommy ins zankai abincin nan danaci yanzu haka ma yana damuna don shine yasa na kasa tashi a nan tun dazun.
Wani abinci kaci bayan wanan dan cakulan da kukayi daga kai har Alh bakuci komai ba ta fada tana kallon shi dole in dan zauna ya fada min kafin naje na kwanta ai .
Sai da safe mayi zancen da wanan fadi ba a tambayeka din data fara ma don yarinyar dazun an turo ta gidan nan da safe ta gaiyar damu.
Suhaila tace mommy ki bar cewa ta gaida ku tazo dai tayi maku fitsara a gidan nan dai ita da yan uwanta.
Kai kukan yaran nan akwai iya sa ido da shishigi da gulman tsiya ina ga sai dai na maku tsiya akan zancen nan.
Mommy ai abinda suka ganine suka fada da bata zo tayi ba ai hakan ba zai damesu ba son basu saba ganin irin fitsaran su ba a gaban manya.
Wallahi yaya zama fa tayi sosai suna hira da daddy da mommy a falon nan har tana tambaya wai yaushe zaka zo .
Murmushi yayi na mugunta tare da fadin oh ni take son gani ma ke nan ya fada yana girgiza kai da sauri hjy tace kaga kada ka biyewa yaran nan kaje ka aikata abinda bashi.
Mu zumunci muke son gyara mu hada a tsakanin don zumunta yayi karfi ba abinda zai sake wargaza kanun ba a hakan ta fada cikin dan bacin rai.
Mikewa yayi yana dan buga cikin shi alaman ya koshi da yawa don ya kawar da zancen don ganin ran mahaifiyar nasu ya fara baci da zancen.
Har ya shiga dakin sai mamaki da al,ajabin abinda sisters din shi ke fada mai yakeyi saidai abinda ya kula hjy tana son zancen ko don abinda ta fada a gaban shi yanzu a falonsu.
Da wanan tunanen barci ya dauke shi sai washe garine days zo gaida daddy ya fito mashi da zancen dif ya dauke kamar ruwa yaci shi a lokacin.
Don irin albarkan da daddy din ya dinga saka mai kan amincewa da zabin da mahaifiyar shi tayi mai kuma yabi irin al,adansu na iyayye da kakani da aka shimfidasu akanshi duk zurian su kuma suke bin hakan har yanzu .
Saidai duk bayanin da mahaufin ke masa hankalin shi baya jikin sai lokavin da daddy ke fasin mun yanke shawara karshen wanan watan da zamu shiga za,ai komai har daura aure tunda duka bangarorin bamu da wani shirin daya saura akan hakan matace kawai dama kake jira ka tare a gidan ka ita kuma iyayyen sunce a shirye suke ko wani lokaci dama.
Kaga shike ka zama cikakken mutum a yanzu don duk wanda yakai ga aje iyali girma ya haushi ke nan a rayuwa zakaga ko mutane suna mutuntaka fiye da lokacin da baka da aure.
Don haka kafin ka koma inda ka fito sai kaje kaga yarinyar da idon kaga irin zaben da mahaifiyar ka tayi ma don suma suna son gani jiya har nan gidan take tazo gaida mu ita yarinyar da yan uwanta nima kuma bazan so har ka koma waje a yanzu ba tare da aure akanka ba kuma.
Ya dago idanun shi da suka canza launi yana fadin zan shiga kafin na tadi daddy insha Allahu ya fada a gajarce.
A gundure da jin zancen mahaifinasa ya samu ya mike tsaye yana fadin zaije ya karya don tashin ke nan daga barci yazo nan gaidashi.
Bin bayan dan nasa yayi da kallo don ya fahinci akwai damuwa a tare da Abubakar din dole akwai wani abinda ke damun dan nasa.
Ya dade a dakin hjy yana nuna mata rashin son wanan hadin da suke son mashi amma ta nuna mashi ai bakin alkalami ya bushe a yanzu don ba zai hadata fada da yan uwan shi .
Mikewa yayi yafice daga dakin kai tsaye motan shi ya shiga ba tare da yasan inda zai nufa a lokacin.
Daga wanan fitan sai mota aka dawo dashi gida shi ya wuce hakan ya kara sa daddy zargin akwai wani abu ke nan da dan nasa ke nufi.
Wai sabo turken wawa nikan ai ban saba zama wuri daya ba gashi ina ganin dan abinda ke garemu umma ke zara munaci muna sha a cikin sa wanda nasan zara bai barin dami.
Sai faman shawaran mafita nakeyi a raina na kasa cin ma mafitan abinda zamuyi don wanan ungywar kan kamar garine komai kake idon wasu ba akan ka tundai ace neman na kanka yanzune sun gama dakai kamar yadda naji ladi tana fadi da bakin ta.
Hakan yasa gaba daya garun ma nikan ya fice min a raina ga baki daya yanzu zama dai nake a cikin sa ga ba karatu garemu dagani har kanina muna neman kwashe wata uku zaune a gida muna zaman banza.
Duk da karatu ni ba damuwa na bane illa neman abinda zamu rufawa kanmu a garin shine kullun tunane.
Zaki ce fa ko ni din wata babbace mai shekaru a yadda nake wanan bakan wahalan sha hudun dai nake ina harin sha biyar ga shekaru a lokacin .
Hakanan kuma nake buga buga a cikin wahala don umman mu bata da lafiya da za tayi wanan wahalan a yanzu.
Safiyane na gama muna abin karyawa na kaiwa umma na aje ba wani abu bane taliyane dai muka dan sulala da safen don ciki ya dauki nauyi ba komai a cikin sa sai manja da dan attah dana jajaga na dafa sai kamahin attah ke tashi a ciki kawai ba wani nama ko kifin ice fish da yai banza a can.
Na dafa ya fita raina sai dan cakula nake ina kaiwa baki suko sai kwasan abin su sukeyi hankali kwance suna ci.
Saida na daidaici umma ta kusan gama ci nace umma dama ina son muyi magana zaman nan ya isheni haka kudin mu ya kusa karewa a yanzu gashi bamu komai da kudi zai shigo muna a yanzu.
Cire hannu umma tayi cikin abincin tana kallona tare da sauraren abinda nake fadi din sai da nakai karshe tace akwai Allah sahiba shi zai duba muna Insha Allahu.
Nasan kina kokari sahiba baki gajiya da kula damu ga komai nima kuma ina wanan tunanen da kikeyi a yanzu.
Sai dai na barwa Allah zabi akan hakan yanzu ke wani shawara kike ganin zamu bi don dai gaskiya ban yarda da sana,a acikin semi ba kuma.
Zan dinga shiga cikin iko ina neman abinda zamu ci nayi maki alkawari duk inda na taka zan tsare mutuncina kamar yadda kike min addua a kullun.
Sam ba zan yarda da wanan ba ki shiga cikin iko ke kadai ki yawats iko ba karamin gari bane sanan kiji ance akwai masu neman a can cikin iko din wanda bamu san suwaye ba kuma akan me suke neman mu din.
Nasan ds haka umma kuma ba zan taba yarda in koma ajagule ba zan canza unguwane wanan karon .
A lokacin naga umma tayi dan ajiyan zuciya tana fadin yanzu na danji sanyi zan iya yarda da hakan.
Ta ina zaki fara da garin nace zan koma ikoyi na duba ko zan samu abinyi a can din daga gobe zan fara shiga insha Allah zan shiga da dubu biyar na duba nagani ko zan samu abin juyawa a wanan side din.
Nayi murna jin umma bata hanani wanan shawaran dana kawo mata ba sai albarkan data saka min a karshe wanda naji dadin hakan har kasan zuciyata.
Washe gari tun safe na fara shirin shiga gari in zaga inga abinda zan kama a cikin garin.
Nayiwa umma sallama na dauki hanyar sai ikoyi kamar yadda nayi alkawarin anan zan fara gwadawa.
Tafiya nake ina bin layi layi a cikin kasuwan ina kallon ko ina tare da nazari har naje na tsaya gaban wani shago sayar da kayan miya ciki na shiga na samu mai shagon akan ya ban sari.
Ya gaya min dokokin sari a wurin nace na yarda ina dauka na nufi cikin unguwar gadan gadan na fara ihun buy fresh vegetables fresh tomotors .
Sai gashi Allah yaban sa,a lokacin dama mutumin yaban in dawo dashi bai ko yi ba na sayar da wanda na dauka duka har ana nema.
Ban koma ta kanshi ba na dauki pure water na zagaya inda motoci suke cinkoso sai gashi na sayar kwara biyu suka rage min na zauna a wani innuwa nasha daya na wanke kafa da hannaye da dayan na koma kasuwan nayiwa su umma sayayyan da zankai masu gida nakuma yiwa mai shagon dana dauki kayan miya don ba karamin riba na samu ta hanyan daukan kayan da nayi ba a wurin shi.
Don jin dadi har diban min yayi nakai gida nayi godiya na wuce zuwa semi boda shidda na isa gida a cikin farin cikina su umma suka tareni suna tambayana ya kasuwa ina washe baki nake fada masu irin sa,an dana samu a ranan.
Na fitar da abinda nasayo daki na shiga na sako dan guntun wandon da nakan saka idan zanyu aiki na dauko doyan dana sayo muna na zauna na fara ferewa kafin na tashi na hada suta ranan dai munyi girki da kanmu munci abinda bamu faye yi ba sai lokaci lokaci.
Na kwaso na kawo daki kamshin ice fish yana tashi da danyen Attarudu irin dai miyan yarbawa din nan dan shi na iya shi kuma muka saba dashi.
Haka nake fita a kullun kuma ina samo sa,an da umma ke kira min idan zan fita zuwa wurin sana,a na din.
Sana,a sun kai kala goma da nakayi hakan zan wuni a wahalace wurin neman kudi inayi ina share zufa dake tarso min idan na dawo kuma nayi girki muci .
Wani lokaci zan samu Amar ya danyi min jajage don yanzu bamu rasa kayan miya a dakin mu don haka yakan diba ya dan gyara min ya kuma hura wuta ya rage min aiki ke nan kafin in dawo din.
Ga zancen makaranta dake raina ko wani lokaci nakanyi wanan tunanen koda ni banje ba Amar shi ya samu ya tafi ni din a yanzu ba dole bane karatun a gareni
Bukin ya taso gadan gadan kamar yadda daddy ya fada don tako wani bangare sai faman shiri sukeyi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login