Showing 102001 words to 105000 words out of 382072 words
yi a ranan yasa na daure muka fita.
Saidai muna kawowa wajen gidan daddy din matasa ne a wuri sun kai su biyar ga daddy a tsakiyan su muka fito da sauran yan matan da sukazo ta hanyar su Nabila da hauwa.
Ya Abubakar da fuskan shi ke fuskantar cikin gidan ya dan tsura muna ido har muka fito aka fara gaida su na kawo wurin ina gaida da daddy jin yadda na amsa yasa wanda yaba kofan baya ya dan juyo don ganin me maganan.
Saida na kadu sosai don ganin wanan fuskan da ba zan taba mantawa ba komai dadewa a idona don ranan nayi mai kallon tsab a asibitin duk da kusan shekara biyu ke nan yanzu da watani da faruwan haka .
Shima dai din yaso kaduwa saidai a can kasan zuciyar shi saboda iya duniya da yayi wajen mu,amula da mutane ya nuna bai taba ganin fuskan ba ko sanina.
Duk abinda ke faruwa ba wanda ya nuna yasan da haka a wurin in ka debe mutum biyu da suka gwane da aikin su na jami,an tsaro a lokacin.
Yadda ya nuna min din yasa na gane ko bai ganeni ba ko kuma kuma wani abu dai amma yana da wuya yace bai shedani ba a yanzu gaskiya.
Da sauri na bar wirin gabana yana faduwa don nayi bala,in kaduwa da ganin dan hayan gidan hanyan mu daya zauna na yan kwanaki a ikko s gidan daya damu yanzu a gaban daddy din.
Muka bar wurin sai gasu kuma har yaya Abubakar din sunzo wurin event din matar shi sai wani jiji dashi matar shikeyi a wurin har akayi taron aka watse haka kawai na tsunci kaina da boyewa ina Allah Allah in dawo gida in fadawa umma gamon da nayi a ranan.
Daga can nisa kadan damu suke zaune don a cakude ake a wurin maza da mata ana ciye ciye saman table din kowa da irin zancen da sukeyi a wurin su.
Ya hango ni zaune na rungume hannayena saman kirjina kamar ina tunane kafin in juya ina magana da Fa,iza dake gefena.
Har lokacin mamaki da tamtama yakeyi na ganina kuma a gidan su tare da yan uwan shi na kusa kuma alama ya nuna cewa sun saba dani a gidan.
To udan nice yaya akayi nazo gidan su ga guma mun saje da yan uwan su mata don zubin mu daya dasu wurin kama saidai ni ina da haske da tsayi fiye dasu.
Kai anya ba kama bane yake gani a hakan to ga wanan din ma da turanci ai yaji uncle yayi mata magana a yanzu a fili ya furta how comes haka ya faru ya dan kira yaron shi yana masa rada ya duba ya ganni a zaune yadda nake ina faman tunanen da nakeyi a lokacin.
Duk da taron yayi kyau amarya da angon ta sun sha kyau sunji kayan alfarma a jikin su kowa ya yaba da hakan sai fadi ake an nuna hali a wurin sha,anin bukin gaskiya ba bangaren amarya ba bana angon ba kowa ba a barshi a baya ba .
Amma ni duk wanan bai burgeni ba kwatsam naji wai ana kiran sahiban lagos da mansurat ibadan, da idayat da kubura illorin su fito su nuna farin cikin su a wajen nan MC yana ta faman nanata hakan .
Atake ya furta impossible a fili how comes wanan yarinyar tazo nan kuma ?
Kidan yarbawane ya fara tashi a wajen a daidai lokacin da nake fadin emmi ina karkada hanayena sai Nabila ta taso a fusace ta rada min idan ni yar gida banyi ba ai sauran ba zasu yi har bukin ya kawatu.
Tana wucewa na fara takowa daga inda nake lokacin da kowa ya baza ido yaga su waye ake kira a filin yan kudu da suka.
Nasan yadda rawan su yake tafiya da kidan don haka nake bin wakan ina juyawa a hankali suma sauran ukun suka fito da irin rawan dukan muna da ankon a jikin mu da suke kira da dinkin kabilu na zaba akai min sai gashi, duk dinkin dana sa sai ya zarta na sauran manyan yan matan masu ji da kai a wurin taron sai bina suke da kallo yadda dinkin ya dane jikina.
Holl din ya dauki ihu don rawan da mukeyi din fuskana a daure nake rawa, dama rawa kan ai ya kare a wurin yarbawa don haka mukayi yadda suke rawa suna dukawa har kasa .
Nan aka shiga muna mannin kudi daga abokan ango yan uwa da abokan arziki wasu suka fito suka tayamu rawan har da iyayyen su kubura din suna manni suna rawa don su a ganin su an karrama masu yaran sune a wurin.
Kidan ya kare muka fito mc nayi muna godiya na nufi wurin da nabar su fa,iza a zaune na same su na zauna suka shiga min dariya wai ashe na iya rawa haka shine basu sani ba .
Na danyi murmushi da shine halina sai dimple dina ya dan lutsa ina dariya dago kan da zanyi sai a table din su yaya Abubakar da yake min wani kallo mai kama da harara nayi saurin kawar da kaina gefen da suke din .
Sai idona kuma ya sauka kan wanan bakon da ban san matsayin shi ba a gun su daddy tunda tare na gansu.
Ni da kaina na tsawala da zama a wajen taron, na mike tsaye kamar zan tafi wani wuri na faki idon mutane na nufi kofan fita daga hall din taron ko zan samu idon sani ya kaini gida duk da dare ne a lokaci don indan ta nice zan iya bin duhun dare in kai kaina gida a wanan lokacin ba don fadan mommy da zatayi min ba.
Don Allah kadai yasan iya inda na taka da kafa a cikin garin lagos kan talla dan neman abinda zamuci wa cikin mu nida dan uwana da mahaifiyamu.
Zama nayi saman wani dankalin dake kofan shiga wurin taron ina bin mutanen dake shige da fice a wurin ko zanga idon sani da zai kaini gida .
Duk da naji mutum ya zauna a kusa dani hakan baisa na dago kaina ba tunda nasan wurin taro ne muke dole akwai mutane da yawa a wurin dake cikin irin yanayina.
Saida muka kwashi kamar second goma a hakan naji ance dani how comes you come to kaduna ?
Na dago kaina da sauri na dan kalli gefena koda wani maishi ke magana banga kowa da yake magana dashi ba dama kuma ba sake murya yake kamar sauran mutane bashi.
Nan ma din kanshi a duke yake kafin ya dago ya kalleni ido da ido gabana ya fadi rass tabas shi din daine a zaune a kusa da inda nake zaune daga gefena na kara juyawa naga wa yan nan yaran nasa dana san shi dasu a baya dan nisa dashi kadan suna tsaye kamar suna gadin shi.
Bakiji tambayan da nayi maki bane ya fada a tsawace na dan kadu da tsawan da yayi min din sai na mike tsaye yace don't try that, or my guys take u out, of dis place now.
Tsoro ya kara kamani don nasan zasu iya min abinda ya fada din saidai a irin karfin halina ban nuna hakan ba a fili nace dashi shabi u no me before ?
Sai ranan nasan shi mutum ne don karfin halina daya bashi dariya a lokacin yasa shi dan murmushi mai sauti har ina jin sa mikewa yayi kafin yace.
Well if u continue to pretend like u don no me before is good for u, and if you tell any body in this town about me.
That i am d guy living in ur compound for some days, i will cut that ur yeye tongue, ya watso min wani kallo ya fara tafiya sauran suka bi bayan shi da sauri kamar walkiya suka shige motar su na bisu da kallo.
Sahiba what are u doing outside muryan yaya Abubakar ne a bayana ya fadi hakan a cikin tsawa na juyo da sauri cikin dan kaduwa don na firgita tunda a tsorace nake lokacin.
Duban hanyar da suka bi nayi kafin na kara juyowa gareshi ina fadi a cikin i,iniya da cewa i just come out to have some fresh air.
If u are tiered, call some one to take u home, why are you staying here u alone ?
Sai kuma naga ya fara dan dube dube kamar yana neman wani ashe tare da matarshi suke tafe ta tsaya magana da wasu yan uwan su a baya sai gata tana fadin honey na barka kana jiran, , , ,
Sai ta kasa karasa abinda zata fada din don maganan ya makale mata a daidai lokacin da ta gani tsaye dashi muna magana .
Idan gida zaki sai mu sauke ki don gida zamu koma yanzu ya fada da sauri nace zan tafi nabi bayan su ina baya zaune shida ita suna gaba.
Ya ciro waya a cikin aljihun shi yana neman layi kafin ya gyara zaman ear pods din shi yana fadin hello Nabila idan zaku gida kada ku nemi sahiba gata nan a tare damu zamu koma gida.
Sai lokacin na gyara zama da dan kyau ya kashe wayan ya kada gaban motan yana fadin kada suje suna neman ki idan angama event din basu ganki ba hankalin su ya tashi.
Dan tsuki Nazifa tayi tana kawar da kai gefe ya kallota ta sai ta dan wayance da fadawa saman kafadan shi tana fadin wallahi duk na gaji yace idan mun isa sai ki kwanta mana.
Bai kaimu gida direct ba saida ya tsaya a wani wajen ya shiga ya barmu a motan waya Nazifa ta fara yi aka dauka take fadin mufa mun tafi gida meshi ta tambaya tace wallahi mun tafi me zamu tsaya jira mukan da auren mu bamu gama amarcin mu ba.
Tace Allah gamu wata yar iskan kalan dagi nasu nason ai ta kwabsa muna wallahi sai nayi maganin yar iskan yarinyar nan idan bata fita min a ido ba kan mijina.
Wallahi fa itace ta sake fada ko meshi ta tambaya a ina suka hadu dani take fadin ba yar bariki bane ki duba fa yar nan dufa bata fi sakina ba a shekaru har ta iya son maza haka.
Bari zan kiraki idan mun isa ta fada da ta hangoshi daidai zai karaso inda ya aje motar shi din, damu a cikin ta muna jiran shi.
Ledoji ne guda biyu ya shigo dashi motan yana zama ya juyo ya miko min guda a baya inda nake zaune take dis ya fada ita kuma ya mika mata daya.
Naji tace dashi ka aje nan mana ya dan kalleta kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru baice komai ba ya tayar da motan muka tafi.
Har suka kawoni kofan gidan daddy ba wanda yayi min magana a cikin su na sauka da ledana a hannu ina masu godiya na shige cikin gida.
Da sauri na nufi part din in fadawa umma abinda nagani yau a garin wanda nake cikin mamakin hakan da zullumi.
Muryoyi nake ji a part din mu a ciki harda na umma a cikin muryan don haka na shigo falon da mamaki ina sallama aka amsa min sallaman.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Too., ANA DARA GA, , , , , , ,
3️⃣1️⃣ BY
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA FATTAHU, , , , , , ,
ONLINA PAID NOVEL YAR UWA KIJI TSORON ALLAH A DUK LOKACIN DA AKA AMBACI HAKAN A GAREKI KI TUNA DA AKWAI GOBE .
Har wani riba zaki samu a wurin abinda akace ba a yafe a kansa ba ki nace sai kin karantashi kamar wani zancen daya yafi karuwa akan addini iyakafa rayuwan zaman duniya ce labari.
Allah yasa mufi karfin zuciyar mu mu gujewa duk abinda zai kaimu ga halaka Allahuma amin.
Ba kowa banw a dakin Asabe ce mai aiki ta kawo wa umma hira sai fatima da bata da lafiya aka barta a gida wurin umma tana kwance tana barci a dakin namu.
Gaidasu nayi na aje ledan da na shigo dashi na nufi hanyar bed room din mu kai tsaye ina jin Asabe na fadin an tashi ke nan tunda ga yar nan ta dawo.
Ban tsaya sauraren ta ba na shige ciki kayan jikina na cire na daura zani kana na shiga bandaki na watsa ruwa don nayi sallahna a can.
Fitowa nayi na samu Asabe ta fita ta koma part din da take sai fatima dake barci tana jin muryana kuma ta mike ta taso zuwa inda nake zaune tana kwanciya saman jikina.
Hannuna nakai na dan shafa wuyan ta har lokacin da sauran zafi a jikin ta na tambaye ta ko taci abinci ta girgiza min kai alaman bataci ba.
Na zauna a kasa na bude ledan nace ta taso taci takai idon ta a ledan sai ta dan bata fuska dana matsa sai ta sauko na fara bata drink din milk sai gashi tasha sosai umma dai tana zaune tana kallon mu na bude kajin da kamshin shi ya hade dakin yasha kayan hadi irin na sayarwan su.
Yakai kamar sau uku data karba saiga uwar ta shigo ta dawo don yar data bari a gida mukai mata sannu da zuwa take fadin ashe sauki ya samu .
Yanzu jin dawowan yarta ta tashi dazun ai har ta bamu tsoro don amai tayi sosai ga jikin nata yayi zafi sosai kuma .
Nayi mamaki jin Anty na godiya kan abinda akaiwa yarta matar da take dagawa kowa kai a gidan tana nuna ita tafi kowa da komai kan yarta sai gashi tana muna godiya goran milk din gaba daya da naman na raba biyu na mikawa fatima din suka tafi .
Mikewa nayi na rufo kofan dakin na dawo na mikawa umma kayan na zauna a gefen ta da alaman magana a bakina lokacin.
Meya faru umma ta tambayeni tana kallona na nisa ina fadin umma na sake ganin shi a garin nan fa yau a gidan nan da zamu fita tare dasu daddy sai kuma a wurin wanan wasan da mukaje yanzu.
Wa kika gani umma ta tambaya nace wanda ya kai Amar asibiti da soja sukazo nema a gidan mu rana wanda yake ban kudi idan mun gashi.
Gidan nan fa umma ta tambaya nace wallahi umma kuma yau ma yace kada na kuskura na nuna nasan shi a baya idan nayi haka na kyautawa kaina.
Innalillahi umma ta ambata kafin tace Sahiba ina tsoron lamarin ki wallahi tun ranan da za, a kashe mahaifin ku irin kukan fitinan da kikayi sai yanzu nake gane hakan nada dalili ashe.
Yanzu abinda nake so dake kada ki kuskura ki nunawa kowa cewa kin sanshi kamar yadda ya fada koma me hakan ke nufi ubangiji Allah ya mayar muna dashi alheri.
Amin na fada a sanyayye kafin in koma tunane take tambayana wanan fa tana nuna min ledan dana aje da kayan sanyi, nan na fada mata komai daya faru har wayan da naji Nazifa tanayi a motan game dani.
Haukan kishi ne wanan shi din ai yasan abinda yakeyi duk da sheri gadon shi tayi abin a jinin su yake masu dama.
Washe gari ma hakan na tashi babu walwala duk tunane ya dameni a lokacin bayan sallah asuba na koma na kwanta lokacin na farka da sauri don mumunan mafalkin da nayi na tashi a cikin damuwa.
Daddy nayi mafalki dashi mota tanata turnbuling dashi saman hanya ga shi yana neman taimako a cikin motan ba wanda ya kawo mai dauki a wanan lokacin ne na falka nayi wani irin zufa sharkaf na mike zaune.
Ina bin falon mu da na kwanta bayan sallah asuba na dawo nan na kwanta a nan na yi wanan mafalkin da daddy din da nayi ya kuma tsorotani.
Mikewa nayi da sauri na nufi wajen gidan babu kowa a wurin sai yan aikin gidan dake aiyukan su a lokacin.
Na dan bi ko ina da kallo idonane ya sauka kan mai,aiki dake faman wanke motan da nayi mafalki da daddy a cikin sa ya samu wanan hatsarin.
Juyawa nayi na koma cikin gida har lokacin gida na tsit kamar babu kowa a cikin sa don kowa na daki yana barcin safe a lokacin.
Part din mu dake can kuryan gidan na nufa na tura kofa na shiga sai naga umma a tsaye tana mamakin ina naje a lokacin don bana fita a irin wanan lokacin.
Tambayana tayi a cikin harshen yarbanci da ina na fito nace na fita waje ne ina zama ta bini da idanu kawai.
Bamuyi wani girkin abinci ba tunda aka fara sha,anin bukin