Showing 24001 words to 27000 words out of 382072 words

Chapter 9 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28418

Dont mind tace tana tafiya sai dan kayan matar ya tashi barewa tace subbahanallahi ina can ina mamaki har zan fadi.
Jin hakan yasa Sahiban dan tsayawa a cikin mamaki tana fadin hjy dama kema hausace a cikin hausan da baka saba yi kullun ba dole harshe ya juya saboda rashin sabo dayi din.
Au shike nan ashe kina jin hausa ta fada cikin mamaki tana kallon yarinyar dan murmushi sahiba tayi tana fadin me na hausa sai dai ba sosai ba irin naku amma ina ji deye deye.
Ke kice kina jin hausa kawai wallahi ni na zata kema irin suce ai danaji kun juya harshe a cikin su kunayi.
Ta sake danyin murmushi da har kumatun ta suka lutsa lokaci guda yan hakoranta masu kyau da basu samun gyaran daya kamata suka dan baiyana a lokacin.
Kuna jinyan wanine kuma a nan ta tambayi sahiban tace eh kanina ne baida lafiya shine muka kawoshi tare da umman mu tana ciki.
Allah sarki nima kinga danane baida lafiya shine muke nan ta fada a daidai lokacin da suka shiga ta cikin dan dogon dakin dake dauke da dakunan kwana na majinyata.
Daki dayane a tsakanin su dana su sahiban don haka sukai sallama kowa ya shiga dakin sa da yake.
Umma na samu zaune bakin gado tana magana da Amar daya farka ina shigowa yaron ya bini da idanu na aje kayan ina fadin .
Amar ka falka ya jikin naka na nufo wurin gadon ina dan duba jikin yaron muryan ummane naji tana fadin anya sahiba abinda mutumin nan ke muna baiyi yawa ba kuwa.
Da sauri na kallo umma ina fadin umma anyi wani abune kuma yanzu da hannu ta nuna min baske din abincin dake gefen mu aje.
Na juya da mamaki ina kallon wurin naji taci gaba da fadin yanzu likita ya fita dakin nan shi da nurse wai zasu dubani yadda ya dace an biya suyi min haka din.
An biya umma na fada a cikin mamaki kafin in dora da fadin towa ya biya din bai fada maki wanda ya biya din ba umma ?
Kai ta fara girgizawa kafin tace nima nayi wanan tambayan ai yace ai tare ya ganmu da maishi wanda ya kawo mune ya biya kudin.
Umma karde zancen ki ya zama gaskiya akwai abinda yake son yi damu yake muna hakan don ni nafi tsoron sherin ojuju da komai a lokacin.
Tace ban tsamanin hakan don likitan ya fada min wai yace mu din ai yan uwan shi ne musulmai .
To kinga kenan shi musulmi ne koda yake musuluncin mutanen kasan nan baikai ciki ba ai koma meye Allah ba zai bashi ikon da zai cutar damu ba insha Allah.
Dauki abincin kici kada haka ya zama barnan dukiya don mu da zuciya daya muka dauki ko waye a yanzu.
Na nufi wurin abincin na fara budewa egede kwamo da dan kalin turawa sai kwai soyayye sune cike a cikin takewa din sai abin sha kuma a cikin kwalayen su.
Har na mika hannu zan dauka mukaji sallaman wanan matar bahausan a kofan dakin mu tana fadin nace bari nazo na duba yaron nan a cikin hausa.
Mikewa nayi ina wasan baki kamar naga ta gida a lokacin sallamanta umma ta karba suka fara gaisawa tana tambayan jikin Amar umma tace da sauki.
Take fadi kamar yadda ta fada min da farko dantane baida lafiya suke jiyan shi a nan itama don yau kwanasu biyu kenan cikin asibitin .
Umma tai mata ya maijikin ta amsa da sauki saidai yanayi na skilar sai a hankali don lafiya muka haifishi sai daga baya da yaki lafiya muka gane laluran dake damun shi.
Oh subbanallah ubangiji Allah ya yaye masa ya bashi lafiya idan da rabo wata rana sai ya mike kamar bashi ba.
Tace to Allah yasa umma tana kallona a fakaice don tana mamakin ko wacece don matar ta cika mata ido sosai da gani dai ita din watace ko matar wani.
Kamar ta gane mai umma din ke kiystawa a zuciyar ta tace yar nan taki tana da mutunci sosai wallahi ta sanadin kirkin ta na gane kudin hausawa ne yan uwan mu ai.
Nan taba umma labarin dan haduwan mu ina jin lokacin da umma ke ajiyan zuciya da jin hakan barin kawo maku abincin yanzu aka shigo muna dashi yayi muna yawa.
Ai da ki barshi don ga wani nan wani bawan Allah da yake taimakon mu shine ma ya kawo mu asibitin nan yake daukan dawainiyar mu da komai namu a yanzu.
Allah sarki dama haka duniya ya gada duk inda kake baka rasa na Allah ai nima ba gashi mutumiyar ta hadamu a yanzu ba umma tayi murmushi.
Tace bari a kawo ko kadan ne kila shi mara lafiyan zai danci don abincin marasa lafiyane ga baki daya don mahaifiyar maigidana ne a tare damu itama dai sai a hankali.
Kin san halin tsofin nan da jiki taki ta zauna gida saboda shakuwan da sukayi da dan nawa sosai
Fita tayi tana dan dariya bayan ta fadi hakan na dukar da kaina kasa muryan umma naji tana fadin .
Sahiba idan banyi hankali ba zaki dauko min magana a garin nan muna zaune cikin rufin asirin Allah.
Umma taimakon ta nayi kawai don naga bata iyawa shine na taimaketa na fada a sanyaye kaina a duke.
Taimako ke kadaine kika san hanyar taimako nace umma hausace fa ita din shine yasa na taimaketa.
An fada maki duka hausawa ne yan uwan juna sahiba wani bai san garin wani ba wani bai taba jin yaren wani ba ko a cikin hausan.
Ba zan kara ba umma na fada zaki kara don taimako a jininki yake sahiba ba zaki san lokacin da kikai hakan ba.
Kawai abin da nake so dake shine ki san wa yanda a yanzu kike dauko muna kiyi hankali dasu sahiba ki kula da kanki da mutuncin ki a duk inda kika samu kanki.
Nagode umma na fada sai ga nurse ta shigo dakin da file din umma tace ta taso su tafi da ita likita zai fara ranan.
Umma ta dan kalkeni tana fadin ki kula ki zauna min dashi kada ki yarda kije ko ina sai na dawo don nasan halin ki da rigiman tsiya ki fita azo a sace min yarona.
Na dago da sauri na kalleta kafin in mayar da kaina kasa suka fita umma na fita saiga matar hausa din nan ta shigo da katon kulan abinci da plate na tashi da sauri na karbe ta.
Ina maman taki ta tafi tambayeni ni nace ta tafi ganin likita au itama ba lafiyane ko kan matsalan dan uwan kine ?
Itace ba lafiyan za a dubata na fada na koma na zauna ta dan kali Amar tana fadin zakaci abinci ko ya kura mata ido saida nayi mai yarbanci ya dan kada kai kadan alaman eh.
Hakan yasa ta kalleni tana fadin ki zuba mai kadan ya danci na mike don bin umurnin ta ina bude warmer din wani irin kamshi ya bugine dafa dukan anta ne don shi yafi yawa a cikin abincin sosai.
Na dan debo na kawowa yaron a irin hikimar su na uwaye ta bashi yana karba a hankali har yaci sosai.
Ta dan jima a wurin mu zaune tare damu tace sunyi barci kada ta tashe su ni kuma ban yarda na gusa a dakin mu ba don tsoron da umma ta bani da zata fita.
Na kasa na tsare tare da zubawa wanan hjy idon da zaman datayi a dakin mu din kafin inji ta jefo min tambayan dayasa na dago da sauri.
Cewa tayi dani meye sunan ki ne yata na dago ina fasin Sahiba ta kara maimaita sunan Sahiba kafin tace ok.
Ku mutanen wani garine wai don yanzu hausan ku ya juye ya hade da harshen kasan nan kamar ku din ba hausawa bane don kun saje dasu tsab a yanzu.
Sai dai kamanin ki dake nuna zubin fulani ko shine kawai za a yarda ku din hausawane da kuma mahaifiyar ku da nagani a yanzu ya kara yardan min da hakan.
Kin san su fulani zubin su na daban ne tundai fulanin shiyan sokoto adamawa da da bauchi ta kalleni.
Wallahi mama ban san mu ko daga ina muke ba umma dai tace a arewa muke mukazo nan tun ina karama kafin a haifi amar.
Cikin mamaki tace kina nufin mamanku bata fada maki daga inda kuke ba har wanan lokacin da kika fara girma ?
Kai na gyada a cikin dan damuwa nace ba a fada muna ba kuma ina son in sani amma umma tace sanin baida amfani a wurin mu a yanzu.
Don me zata fada maku haka idan ma wani abune ya faru a can ta bargida ta dawo nan ya kamata ace ta fada maku.

Moddibo halin matar nan yana damuna a yanzu ina gudun kada hakan ya saka min hawan jini.
Ya dago kai da sauri yana fadin hjy na fada maki ki daina damuwa da zancen matar nan kada ta jefa muna ke a cikin wani hali.
Zanwa daddy magana yayi maku iyaka da ita tun kan wani abu yazo ya sameki nan gaba kuma
Da sauri ta juyo tana fadin karka soma tsoma bakin ka a cikin harkan mu na fada ma wanan bai shafeka .
Ka barmu muyi ta abin mu a tsakanin mu saukina shi Alh yana da kula don bai yarda ya bata power da take son samu ba.
Ranshi ya gama baci dan haka bai saurari sauran bayanin da uwar ke masa ba don a lokacin ya fara tunane kala kala.
Don da yayi aure zai iya daukan mahaifiyar shi har yan uwan shi su zauna tare duk da yasan abune mai wuya mahaifin nasu ya yarda da hakan.
Sai dai zai gwada hakan don ya samawa mahaifiyar shi sauki ga hakan don shi gaskiya sam hankalin shi bai kwanta da hakan ba a yanzu idan akwai abinda yafiso shine mahaifiyar su.
Bayan ya fita daga dakin ta kai tsaye gun daddy su ya nufa ya gaidashi da kwana suka hade a kofa da hjy karima a tsatsaye ya gaida ita ba yadda ya saba yi ba dama bai faye damuwa da lamarin ta ba shi.
Sai cewa tayi Alh bai tashi ba yana kwance har yanzu jin muryan da Alh yayine yake fadi daga ciki ba moddibo bane ki barshi ya shigo mana tunda idona biyu.
Ta matsa Abubukar din ya shiga bayan yayi mata wani irin kallo na ke waye abin kulanan shine mata masu shiga gidaje sy iske maigida da manyan diya suce sai sun dauki power gida da karfi da yaji su kula .
Shi girma yau idan akace wanan ce uwargida idan kin gane ki bita da hikima ba a cikin tashin hankali ba yadda wasu keyi.
Don irin haka na kawo maki matsala ga yaran matar nan ta yadda baki taba daraja a idon su wani lokaci har abin ya shafi diyanki da suke kanana a cikin su.
Ya kutsa kai ya shiga dakin mahaifin nasu a daidai lokacin daya mike zaune daga kwancen da yake yana gyara jalabiyan dake jikin shi.
Har kasa yakai ya gaidashi kafin ya dago yana gyara zaman shi a kasa saman carpet mahaifin yace ga kujera zaka zauna kasa yace ban yayi min dadi.
Mahaifin yace naji ance wani aiki kazo yi a iko ya dago kai don har lokacin yana jin haushin hjy karima a cikin ranshi yace.
Eh daddy saidai har yanzu muna kan binciken wanda nazo nema din don shi din yahoo ne na kwarai babba ne a cikin su sosai.
Modibbo kana ganin zaka iya kasan fa yadda lagos yake da girma da kuma wanan matsalan ya dan dago kai sai alokacin ya samu yin guntun murmushi yana fadin insha Allahu daddy.
Addu,an ku nake bukata a yanzu fiye da komai insha Allahu zan iya indai har shi din mai laifine kuwa ina bin abubuwan a hankaline har na gane.
To Allah ya kyauta Alh ya fada yace amin daddy ya jikin naka yanzu kuma dan murmushin manya yayi kafin yace jiki da sauki yanzu saidai abinda ba a rasa ba kwai tunda girma ya kama yanzu kuma.
Hakane daddy kuma sai dai a rage yawan tunane din nan don koshi yana kawo ciwo sosai ya dan kalli mahaifin nasa.
Kai yaro dai ho ai tunane ya zama dole a yanzu don kaga rashin sanin inda mutanen nan su, , , ,
Shigowan hjy karima yasa daddy din yin shiru ya fasa fadin abinda zai fadawa dan nasa ta aje kayan break din data shigo mashi dashi tana fadin yanzu zakai wankane a hada ruwa ?
Kina iya ki hada muna magana ne da tsohon gida ya bata amsa da bataji dadin hakan ba don taso ta nuna mashi shi din ba kowa bane gun ubansa sai kuma Alh ya bayar da ita.
Ta dan tsaya jim kafin ta juya ta fita daga dakin tana jin zafi a zuciyar ta wani zance kuma Alh ya dauko suka fita zancen da suka soma din.
Ya dan jima a aurin mahaifin nasa suna hira kafin ya mike ya bar dakin yayun da hjy karima nacan cikin damuwa a lokacin.
Har aka kira matar umma bata dawo ba sai bayan tsawon wani lokaci ta dawo dauke da ledan magungunan ta da aka bata masu tsada don abinda ke damun ta din.
A lokacin har na fara barci don zaman kadaici ni kadai don Amar ya koma barci shi tun bayan cin abincin shi.
Jin motsin umma din yasa na falka ina fadin umma kin dawo ashe tace wallahi da yunwa don na wahala.
A zuba maki abincine kici don yanzu dankalin yayi sanyi nake gani ikon Allah shi mai nema ina ruwan shi da wani sanyi ganin dai abincin yasa kika fadi hakan.
Mikewa nayi na dauko kulan abincin matar hausa din nan iina fadin ci wanan umma da gani zaiyi dadi.
Ina kum kika samu wanan abincin nace matar hausa din nan ce ta kawo muna ban ci ba fa umma na fada ita daice ta bawa Amar yaci.
Yaci na bata amsa takai zaune tana kallon yaron na bude abincin ta gani tace ki zuba min sai ki zubawa kanki .
Wanan matar bata kara leko mu ba har yamma ni kuma ina fama da tunanen zacen da mukayi da wanan matar akan ya kamata ai mu san garin mu yanzu.
Duk da nasan hakan zai iya kawo muna matsala da umma don ba son zancen nan takeyi ba tuna hakan yasa naja bakina na kyale ta.
Da yamma sai gata dakin tare da tsohuwan data kira da uwar mijin ta sun shigo duba amardin da jiki sun dan jima kafin su fita su koma dakin su.
A cikin dare har mun kwanta aga buga kofan a zaton mu ko likitane sai dai muna bude kofan tunanen mu ya canza don ganin wasu mutane da suka shigo muna dakin.


ZAINAB IDRIS MAKAW


.ANA DARA GA, , , , , , , , , , ,

9️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM GAIRUL MAGDUBI ALAIHIM, , , , , , , , ,


YAR UWA PAID NOVEL NE DON ALLAH KI BIYA KISHA KARATUN DUNIYA A ZAUNA LAFIYA, , , , ,

Dagani har umma a lokaci daya muka mike zaune don firgita saboda yadda aka bugo kofan dakin da karfi aka shigo.
Su ukune ko wanin su yana saye da bakaken kaya sai bin mu sukeyi da kallo kamar yadda muma muke binsu da kallon saidai bamu ganin fuskokin su a baiyane.
A cikin karfin hali umma tace masu una de look for somebody here ba magana ko daya a cikin su illar takawan da na tsakiyan yayi zuwa bakin gadon da Amar yake kwance da karin ruwa ya tsaya yana kallon yaron kafin ya kai hannun shi saman ledan ruwan ya dan duba.
Duban yan uwan yayi kafin su tako zuwa gadon su dan dubashi suyi wani magana duk muna binsu da kallo da mamakin hakan a cikin zuciyar mu.
Can dayan ya dago yana fadin mama ur son will be fine very soon my oga say he go live d town today.
May u colect dis money manage am with ur pikins take care of dem yana mikowa mama kudi a cikin wani bakin leda.
Umma ta kalli hannun shi da kudin kafin ta dago tace dashi tellam say me no want his money naw.
D tin wen he do for us is ok for us now, make he cary his money go, Allah will reward


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login