Showing 111001 words to 114000 words out of 382072 words

Chapter 38 - ANA DARA COMPLT BY MAKAWA

MAKAWA   

29 Jun 2024

28326

gwadawa ta wani hanya da yake ganin itace mafita na karshe da zai iya gwadawa a kan daddy din.
Yaron shi aminin shi kuma yardaden shi ya kira ya sameshi a gidan hutun shi a nan suka kulla abinda suke shitin aiwatarwa akan daddy din ya ciro kudi masu yawa ya bayar wanda abubuwan zasu kankama a gareshi yadda yake so da sauri.
Ranan ko iyalin shi sun san yana cikin farin ciki don yadda yake masu idan yana cikin nishadi haka ya kasance dasu a gidan.
Yau a falon da anty ta hanasu zama a baya a gidan, muke zaune tana dakin ta bata san da muna falin zaune ba har yakai anty hauwa ta kunna muna kallo sai hankalin mu ya dauke ga hakan.
Fa,izace ta dauko zaren kitso na kama mata kai don haka muka fara duk da ni hankalina ba a kan kallon yake ba na mayar da hankali ga kitson da mukeyi din sai jin muryan Anty mukayi a daidai lokacin da fa,iza ke fadin kan ya fara mata ciwo na dan sasauta mata kitson nake fadin hakana iya nima.
Ai yau kuma kun dawo da iskancin zaman naku nan falon ke nan ba na kashe wanan zaman naku a nan ba dama ta fada tana wani zare idanu a garesu.
Ban kula da ita ba a irin sai dariyan da nakewa fa,iza a lokacin ta juyo gareni tana fadin ga yar iska ina magana kina dariya kin daukeni mutumiyar banza ke nan.
Ni nice yar iskan na fada a cikin hausan da ba daidai ba nace look woo don abuse me with dat name again wooo.
Da mamaki anty ta bude ido tana kallona kafin tace ke bude idon ki ki dubeni banyi kama da wanda zaki raina ba a nan .
Duk barikin ki keda uwarki kar nake kallon ku gidan nan don ba zan dauki iskacin yancin arziki ba yan gida basu raina ni ba .
A wurin ki ne nake yarcin arziki amma wurin daddy da mommy ni ba yarcin arziki bane don diya nake a garesu kamar kowa.
Idan kika bincika har nafi diyan ki power a gidan nan don su din ba a san ya aka samesu ba ma a gidan nan .
Muko da kike kira da yan bariki da asalin mu da kuma nasaban mu don nasan munfi wata yar a cikin gidan nan.
Fa,iza zata tashi nace ina zaki bana zuwa ko ina a nan zan zauna tunda ba gidan uban wani naje ba a gidan uban mu muke zaune kuma daddy bai hanamu zama a nan din ba shida keda gidan sa.
Na fada ina murguda baki son na fahinci matar kanta kawai ta sani sai diyan ta bayan shi kowa ba mai mutunci bane a idonta gidan yasa na rufe ido nayi mata hakan nidana saba fada da su iya bisi ko iya wale balle anty da albarkacin daddy ta samu a wurina dama .
Sallaman gwaggo hari ne tare da danta suka shigo tun kan ta karasa shigowa gidan take fadin wai hayaniyan me nake ji haka yana tashi tun muna waje ?
Gara da Allah ya kawo ki wanan tsuntattan mage din nan daba wanda yasan asalin su tazo ta samu wuri tana son fin yan gida iya shege.
Kai hjy karima me ya hadaki da wanan kuma kike irin wanan maganan haka gaskiya haka bai dace ba don Allah ai wanan kamar yar mijinki take a wurin ki.
Yau mutanen nan suke zaune tare daku a gidan nanb ai inda sabo an saba a yanzu kun zama daya dasu haka gaskiya bai kamata ba.
Shiru falon yayi kafin gwaggo hari ta juyo kaina tana min fada nayi shiru a daidai lokacin ya shigo gidan aka shiga yi mashi sannu ana gaida shi.
Yau kam shigar kayan hausawa yayi duk da rigan irin dinkin zamanin nan ne mai tsayawa maza iya cinya din nan yayi matukar kyau dashi.
Don kwarjin shi ya fito fili ga wanan shiga da yayi don shigar ta karbe shi matuka.
Gashi da ganin shi kasan naira tayi aikinta wurin don ko shigar gwaggo hari itama abin kallo ne a lokacin.
Nan falon suka zauna daga shi har mahaifiyar shi mommy dake daki tana jin abinda ke faruwa a falon ta fito tana masu sannu da zuwa tare da gaisawa.
Wayan shine yayi kara ya dauka yana fadin ya akayi arrow duk akai shiru ana sauren shi shima din dai shirun yayi yana sauraren abinda jibrin arrow din ke fada mai take yanayin shi ya dan sauya.
Yace Okey kana jina kada kowa yayi yunkurin yin komai gani nan zuwa kana jina zan biyo jirgi yanzu inzo lagos din in sameku.
Na fadama kada kuyi komai sai idan nazo din don dama nasan da hakan zai faru ai don haka ku jirani inzo.
Yana fadin hakan ya kashe wayan shi yana dago kanshi ranshi a bace sai mahaifiyar shi tace dashi meya faru ne kuma, ?
Yayi saurin dawowa daidai yana fadin wai kayan mu aka kama shine suke son su tayar masu da rikici nace su bari inzo dai.
Gara daisu bari kazo don jami,an tsaron nan wani lokaci ba tausayi ke garesu ba anjima zan je inji meke faruwa ya fada kafin ya mayar da hankalin shi wurin mommy yana fadin.
Mommy nacewa mama ta kawoni wanan karon ina jin nauyin korafin da kike min na rashin zumunci idan mun hadu .
Mommy tayi murmushi tana fadin ka kyauta wallahi baba ko kaifa ace mutum ko yaushe kamar injin ku bakwa samun lokacin hutune a rayuwan ku wai kaida dan uwan ka kullun a zurce kuke kan aiki.
Mommy kuyi hakkuri wallahi yanayin ne na yanzu ya koma hakan ya fada yana dan sune kan shi kasa saboda nauyi ya kasa ci gaba da magana.
Amar ne dake fitowa daga part din mu ummace ta toro shi ya kirani idon the boy ne ya sauka a kan yaron haka ya kara tabbatar mai da ba karya nidin daice ya gani a kaduna.
Tunda ga kanina ya gani a gaban shi yanzu da yarbanci yaron ke fada min na mike a lokacin ne kuma Amar shima ya juya zai koma part din mu.
Alokacin na Ya mustapha din yace dashi ya abokina zo mana haka baisa ya tsaya din ba nace a harshen yaruba bakajin ana magana sai yaton yaje wutin shi inda yake zaune ga kamshin turaren shi har ya fara hawa min kai a lokacin.
Ya rike shi yana mai dan magana kus, kus wanda ba lalai bane wani yaji me yake fada mai a lokacin ga falon yayi shiru kafin ya kai hannun shi daya cikin aljihu yana ciro kudi masu yawa ya mikawa Amar din.
Mukan gaskiya munci gajiyan wa yan nan mutanen don ba zamuce mun shiga duniya mun dawo hannu sake ba ko yanzu aka bukaci wani abu a wurin mu za a samu sosai kuwa duk da ba kidayawa nakeyi abinda muke samu din ba.
Kowa falon ya fiddo da ido yana mamakin wanan kyautan daya bawa yaron daga gani daya da yayi mashi a yanzu zai bashi wanan kudin haka.
Muryan gwaggo hari ce ke fadin kai har yanzun dai kana nan da son yaran ka ashe saidai maza sune abokan shi ai mommy ta fada suka dan kwashe da dariya a iya nan na bar wurin banji sauran maganan su ba kuma na dai fito na samu sun tafi ya bada alheri mai yawa yace a raba.
Har ni an cirewa nace lah dakun barshi ai tunda amba Amir mun gode na fada a karshe naji Nabila na fadin shi ya mustapha har yanzu ba zancen aure gareshi ga yan uwan shi duk sunyi aure a dangi.
Idan lokaci yayi shima ai yi zaiyi ko ita uwar nasa data damu da hakan da farko ai yanzu naji ta sake sai a lokacin Anty Amarya ta fito kallon kowa batayi ba a falon haka tasa kai tafice daga gidan.
Falon yayi shiru bayan fitar ta Allah da ikon shi ba wanda yai maganan ta a falon har ta gaji da tsayuwa tana saurare ko zataji anyi maganan ta sai taji shiru sai hiran hausana dana fara koyo sukeyi ana kwasan dariya.

Su ukune a zaune a falon duk biyun sunyi shiru suna sauraren shi yana fada masu abinda yake shirin aiwatarwa ga dan uwan nasu.
Karamin nasu ne ya fara magana a cikin su yana fadin kai haba yaya abinda mijin ta yayi muna ba matarshi ko danshi yayi ma haka ba .
Kuma karka manta da matarshi ai yar uwan mu ne ta jini don uba daya ba wasa ba duk daba cikin mu daya dasu ba amma kuma ai uban mu guda kuma tana girmama mu tankar ciki daya muka fito da ita .
Kai dakata Dule nifa ban dauki duk wani dan uwa a matsayin dan uwa ba a yanzu duk wanda yayi kokarin ketara layina saina saba mashi ko waye shi din kuwa.
Amma dai yaya kasan in har kai haka har iyalinka ka saba masu don har da yarka zata cutu ga wanan shirin naka.
Kai Dule dayan da baiyi magana ba ya fada ka bari tunda ya shigo hancin yaya ayi maganin sa su wullakanta a idon yan uwa su gane su ba komai bane a yanzu.
Wanda ake kira da Dulen yace amma dai ni naga a duba tunda ba wani abu bane mai girma ya hada ku dasu karku manta akwai yarmu yanzu a cikin zurian su fa dole komai mu dinga duba a yanzu yaya .
Shiru yayan nasu yayi baiti magana ba hakan na nuna cewa ran yayan nasu a bace yake sosai a lokacin kan maganan sai dai kuma yana nazari akai.
Gyaran murya Alh Gyade, yayi kafin ya fara fadin kai Dule na fahinci kamar kana tsoron Alh Ali a yanzu don kana ganin kamar shidin wani ne to sai mun nuna maishi ba kowa bane a garin nan.
To Allah ya kyauta ya fada yana mikewa tare da fadin ni dai shawarana shine ayi diba akai fadan zumunci ba karewa yakeyi ba idan yazo hakkuri akeyi a kai kada a maimaita abunda mukaiwa Sambo a baya yaso zama muna matsala.
Sun san halin sa idan har ya fadi abu to gaskiyan zuciyar shine ya fada don haka yana nufin bada shiba cikin wanan shirin ke nan duk da sun san ba zai fada ba kuma.
Yana fita sukaci gaba da zancen tare da dan uwan nasa guda yayin da yaton shi ya kawo mai labarin dawowan daddy a ranan.
Sunji dadin hakan har suna kyalkyalawa tare da fadin dan iska yau zaka san ba a ja damu a cikin lamari har kana nunawa yaya yatsa waishi yaya kai waye da zaka ce fadan ka yafina Allah mu zai gwadawa Allah a baki.
Ya gama hiran shi ya mike yana fadin shi zai koma sai dai udan sunyi waya ke nan duk yadda abin ya kaya zasuyi magana .
Alh Nuhu yace ko sai mun hadu wurin makoki ba a gidan Dn filo suka sa dariyan keta kamar ba wada kani ba a lokacin.
Tun zuwan gwago hari da danta gidan suke ta faman hiran su har na gaji dajin hakan kuma na tabbatar da son shi sukeyi su gaba dayan su.
Daga Anty hauwa har Anty Nabilan don zancen su ke nan hiran shi da zuzutashi shida yayan su hakan ne ma ya dan rage min zargin su da nakeyi jin har yayan su suna zuzutashi sai na dauki hakan dai wani nau,in wayewa ne kawai irin nasu.
Muna zaune Nazifa matar ya Abubakar ta shigo gidan kwatsam muka ganta kamar an jefo ta suke gaisawa da ita na dan dago nace da ita sannu kawai na kawar da kaina ta shige wuein mommy bayan ta tambaya tana ciki suka amsa mata.
Sun dan dade a dakin tare da mommy sai gata ta fito ranta a bace suna mata sallama bata ko samu amsa mata ba duk suka bita da kallo.
Yar matsala aure ba a ko haihu ba amma kullun a cikin matsala ake Nabila ta fada sai hauwa tace ta samu wurin yin hakan ne.
Ni da nice mommy wallahi va zaki ta kawo min sukan dana ba ina kyaleki hakan sai ga mommy din ta fito daga dakinta tace .
Au ta tafine ni wanan yar naga ranan da zata san aure takeyi a yanzu sai abinda aka tsara mata ba wai wanda take so ba ita.
Wai yanzu tazone a nema mata yar aiki don yace shi bai yarda da yan aiki ba shi kuma inba tsiyarshi ba ta yaya zata zauna wanan katon gidan babu maitaimako kuma wai yace tafaye kazanta kinsan sanshi da shegen akidan tsiya.
Ita kuma yanzu tazo tun bai yarda din ba da shegen sallonta wai in tabbatar yar talakawace lis wace kuma bata da kwadayi da saka ido za a samo mata.
Wanan yar rainin wayau ce wallahi wai me Nazifa ta dauki kantane yanzu tunda tayi auren nan ta dauki girman kai ta sakawa kanta Allah.
Yanzu mommy samo mata din zakiyi fa,iza ta tambaye ta mommy din tayi mata wani irin kalllo ba tare da yin magana ba ta shige dakin ta.
Nikan na mayar da hankalina gun karatu na son cin jerabawan da zamu fara karshen sati don daddy yai min alkawarin kyau idan jerabawan nawa yayi kyawo.
Haka yasa na dadage na mayar da hankalina kan abinda aka koya min din don daddy ya tsamini yai min register a wani makarantar wanda ba namu ba.
Bakin sune ya kama Nazifa don yaya kan yace bai yarda ba yaki amincewa sam da wanan zancen.
Alh Nuhu dake zaune yana zaman jiran jin labari mara dadi daga bakin yaron shi amin shi wayan shine dake gefen shi yai kara.
Cikin rawan jiki ya dauki wayan yana fadin Gyade ya akayine ai har yanzu banji komai ba jiran su kira nakeyi.
Malam mun kira mu fadama cewa mai wanan wayan yana hannun nu yayi hatsari dazun nan a nan hanyar by pass.
Innalillahi ya fara maimaitawa zaiyi tambaya yaji an kashe wayan dabas yayi wani irin zufa ya fara keto mashi dole ya cire hulla yana dan fifita kan shi .


ZAINAB IDRIS MAKAWA



ANA DARA GA , , , , , , , ,

3️⃣4️⃣ BY

ZAINAB IDRSI MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL BASIT, , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA DON ALLAH KI BIYA KAFIN KI KARANTA NA KUDINE ALLAH BADA IKON BIYA, , , ,

Daddy ya iso muna murna da dawowan shi lafiya sai layi mukeyi muna zuwa masa sannu da zuwa yana zaune da alaman agajiye yake a lokacin yake hakan kuma yake amsa muna.
Mommy da Anty suna zaune daga gefen shi tare da yaran anty din dukkan su a cikin kulawa sai hakan ya ban mamaki.
Ban taba jin kewan namu mahaifin ba sosai sai a wanan ranan yadda naga daddy din zaune tare da iyalin shi a falon shi sai tausayin mu dana umman ya kamani lokaci guda.
Juyawa nayi zuwa part din mu na samu umma zaune tana shafa magani a kafanta dakan dan mata ciwo take tambayana ya dawo lafiya nace lafiya kalau umma na shige ta bini da kallo.
Can ta fara jin kukana sama sama har yakai ta mike ta leko kuryan dakin da nake nayi rub da ciki ina barza kuka .
A hankali umma ta tako zuwa inda nake ta kai zaune tare da tambayana tana kai hannu saman kadana tace ke lafiya kike wanan kukan ?
Ban iya magana ba naji ta kara matsowa gareni tana fadin ba zaki fada mkn meke damun ki ba ko anyi wani abune kuma na gurgiza kai.
Sai dai ba magana don yadda nake jin zuciyana tana min kuna a lokacin na rashin mahaifin mu a tare damu don ban taba sanin dadin mahaifi ba sai yanzu da nake zaune a gidan daddy din.
A wana lokacin nasan muhinmanci uba a tare da iyalin shi wanda mu muka rasa wanan gatan tun muna kanana bamu san dadin mahaifi a tare damu ba.
Mikewa naji umma tayi ta fita daga falon can sai gata dauke da goran ruwa da cup a hannun ta tana fadin ki karbi ruwa kisha komai ke damun ki Allah ya yaye maki shi kiyi bissimillah kisha ruwan ta fada tana tsiyayawa a cup din.
Dole na karba na dan kurba kadan nasha na mika mata cup din har lokacin tana tsaye a kaina ta kasheni da idanun ta alaman tambaya.
A dan maraice nace umma ba komai bane fa na koma na kwanta a yadda nake da farko din naji tace Allah ya kyauta ta fita.
Ban kara fitowa ba kuma bata kara lekoni ba sai wajajen la,asar na fito umma na zaune a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login